Showing 18001 words to 21000 words out of 30696 words
Chapter 7 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf
kwashi gaisuwa ga Baddadul-ulƙas.
Daga bisani ya ɗago da kan ya dubi waɗansu dakaru yayi musu inkiya da sannu,
Take zaratan dakarun su hamsin suka shiga wangane kofar birnin,
Sannu a hankali sai kofar ta buɗe aka kunna kai izuwa ciki, ana shiga nan fa kowa yakara cika
da mamaki, yakama kalle kalle,
Bakomai ne ya bawa Kowa mamaki ba sai bisa ganin yadda birnin madinatul-shaja'a yakasance
kasaitacce tamkar aljannar duniya,
Gine - ginen birni anyi su bisa tsari mai kayatarwa, gwanin ban sha.awa kowace unguwa kalar
tsarin ta daban iri ɗaya sai !
Ko ina a tsaftace yake a birnin babu wajen da ake zuba shara ko kazanta,
Hatta manyan sarakuna dake cikin tawagar wato sarki uslaim,shazwan, sarauniya Nuwairat da
Abidatul-auliya sai da suka re na kan su,
Domin sun tabbatar da cewa gaba da gaban ta aljani ya taka wuta.
A dai dai lokacin ne aka hango tawagar wani mutum ma'abocin sarauta ya durfafo inda ake
tsaye,
Tun da ga nesa mutumin ya ƙura wa Hibairu SARKIN SADAUKAI idanu ko ƙiftawa baya yi,
Lokacin da ya karaso sai tari sarki Baddadul-ulƙas suka rungume juna daga bisani mutum ya
janye jikin shi daga na sarki Baddadul-ulƙas suka fuskanci juna
Cikin kakkausar murya mutumin yace "Lale marhaban da zuwan sarkin sarakuna, baban
attajirai da matsafa,
Sarki Baddadul-ulƙas ya dube sa yace"yakai Abu - Ɗariƙ ina Fatan
A tanadar mana dukkanin abinda muke da buƙata da ya danganci masauki,
Abin kalaci har izuwa lokacin da za'a kammala gasar jarumataka,
Koda jin wannan tambaya sai Abu-Ɗariƙ yayi gyaran murya yace"An tanadar komai ya shugaba
na yadda ka bukata,
Sai dai a wannan karon tsarin gudanarwar gasar ya canza,
Ina da a wannan karon dole ne dukkan wanda zai shiga kallon gasar ya bayar da bayanan sa,
Sannan ya shugaba nayi mamakin yadda kake tafe da wannan tawagar haka,
Koda jin wannan batu sai Baddadul-ulƙas ya bushe da yar karamar dariya yace
"Wannan ai ba abin damuwa ba ne ya Abu-Ɗariƙ
Game da tambayarka akan tawagar da nake tafe da ni wannan bayani mai girma,
Nasan dai abinda kake muradi shine kana so kasan wane ne GOGA SHA FAMA da nake tafe
dashi ko,
Ya Abu-Ɗariƙ kayi sani cewa haƙiƙa a wannan karon nazo da jarumin da babu kamar sa a
duniya a halin yanzu
Ba wani bane jarumi na ba face HIBAIRU SARKIN SADAUKAI na duniya,
Ɗa ga Barde Shabbaru tsowon GOGA SHA FAMA na shekaru ashirin da suka gabata,
Koda jin wannan batu sai Abu-Ɗariƙ ya sake ƙura wa Hibairu idanu,
A wannan karon sai yaji kirjin da ya buga da karfi tsoro ya kama shi,
Don haka sai ya kawar da duban sa daga hubairu izuwa ga Baddadul-ulƙas cikin ladabi yace
dashi
"Haƙiƙa kyan ɗa ya gaji Uban sa ya shugabana kayi sani cewa tun sa'adda da na hango nake
yiwa wannan baƙon jarumi kallon sani,
Nasan cewa Barde Shabbaru bashi da aure ballantana nace ɗan sa ne na cikin sa domin
tsananin kamannin su ya ɓaci tamkar an tsaga ƙara,
Amma ya shugaba na dama Shabbaru ya na da ɗa ne a boye ban sani ba?.
Koda jin wannan tambaya sai Baddadul-ulƙas ya yayi murmushin mugunta yace "Mu ƙara sa
izuwa masauki za ki dukkan yadda al'ummarin yaksance,
Abu-Ɗariƙ ya risina yace an gama ya shugaba na yana Gama faɗin hakan sai sarki
Baddadul-ulƙas ya koma izuwa cikin keken dokin sa ya hakimce,
Abu-Ɗariƙ ya shige gaba take aka sakarwa dawakai linzmai aka cigaba da tafiya.
Nan fa jama'a suka dinga bin tawagar sarki Baddadul-ulƙas da kallo cike da matukar mamaki da
al'ajabi,
Abu na farko da ya basu mamakin shine yadda tawagar Baddadul-ulƙas takasance mai
tsananin yawa, da ta haɗar da aljanu da miyagun dabbobin daji,
Abu na biyu da ya fi basu mamakin yadda suka ga fuskokin baƙin sarakuna waɗanda ba'a taɓa
ganin fusakun su a halartar gasar ba,
Haka dai tsoho Abu-Ɗariƙ ya cigaba da jagorantar tawagar sarki Baddadul-ulƙas suka wanzu
suna masu ratsa unguwanni gami da saƙo da lungu na birnin,
Tafiyar daƙiƙa saba'in a kayi aka iso wata ƙasaitacciyar unguwa,
Unguwar an jima ta manyan gine gine benaye Masu tsawon ainun,
Idan mutum ya ɗaga kansa sama sai yaga cewa tamkar benayen sun shige cikin gajimare
saboda Tsawon su,
Hatta kayan ƙawa da zanen tambarin gidaddajin irin ɗaya ne sak gwanin ban sha'awa,
Duk inda Mutum ya kalla dakaru ne shirye shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar
kwarjini daban daban ɗauke da miyagun makamai suna ta kai komo domin tabbatar da tsaro,
A ta dai wannan unguwa ana kiran ta da suna
Manazil-tijjar
Bisa wani katafaren gida aka ɗauke su sarki Baddadul-ulƙa,
Tun kafin su karaso waɗansu samudawan dakaru suka wangame musu kofar birnin ana zuwa
aka kunna kai izuwa ciki,
Duk inda Baddadul-ulƙas ya gifta da tawagar sa sai dai kaga dakaru, kuyangi,da bayi na
zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa Cikin ladabi,
Bayan an shiga ne sai a Kowa aka basa nasa masaukin,
Saurayi Hizmal, yaro Humair makaho da sunaila a bangare guda kowa da turakar sa,
Sarki shazwan, boka Dargas , sarkin yaƙi da tawagar bokaye a bangare guda,
Hushriba ,sarauniya Abidatul-auliya da sarauniya Nuwairat a sauki guda,
Sarki uslaim da tawagar sa,
Aljani Marhutul-Azab da boka Jadwar da matsafi shubairu da aljani Darmanu
Hibairu SARKIN SADAUKAI da budurwa Nihla,
Tare da tawagar dabbobi da aljanu da sukayi masa rakiya a masauki ɗaya ,
Sauki Baddadul-ulƙas kuwa masaukin sa daban,
Sai dai masaukin kowa yana bisa saman benayen ma bambanta,
Jim kaɗan sai ga waɗansu irin tsaka-tsalan kyawawan yan mata sun shiga rarraba abin kalaci
da abubuwan sha da tanɗe -tanɗe a Kowa ne masauki.
Sai da aka shafe tsawon kwanaki huɗu ana gudanar da shirye - shiryen tunkarar gasar
jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,
A iya tsawon waɗannan kwanaki soyayya mai karfi ta ƙullu tsakanin HUBAIRU Sarkin sadaukai
da budurwa Nihla,
Kuma Hibairu ya fahimci Yaren sauran mutane ainun, sai dai a Kowa ce rana sau ɗaya kacal
sarki Baddadul-ulƙas yake yadda Hibairu ya gana da mahaifin sa Barde Shabbaru,
Tun a daren ranar da za'a gudanar da gasar jarumtaka,
Birin madinatul-shaja'a ya cika ya batse da al'umma manyan sarakai, attajirai, jarumai da
bokaye sukayi cincirindo,
Kuka kuma a daren wannan rana ne aka aika da sunan dukkan tawagar dake tare da sarki
Baddadul-ulƙas zuwa ga sarkin yakin birnin wanda shine ke kula da harkokin gudanar da gasar,
Lokacin da sarkin yaƙi abu-Damraz yaga jerin sunayen tawagar sarki Baddadul-ulƙas tare da
jarumin da zai kasance wakilin sarki Baddadul-ulƙas wato SARKIN SADAUKAI Hibairu.
Sai ya shafe tsawon daƙiƙa goma yana nazarin sunayen,
Sa'adda ya ɗora idanun sa akan sunan hubairu sai yaji zuciyar sa ta buga da karfi, tsoro ya ɗari
su a cikin ta.
Al'amarin da yayi matukar ba shi mamaki kenan yace a cikin ran sa,
Shin wane ne wannan baƙon jarumi Hibairu mene ne yasanya dukkan binciken da na gudanar
bisa halarar tsafi bai bayyana mini shi ba.
Mene ne yasanya zuciya ta buga da na yi arba da sunan sa,
An ya kuwa wannan jarumi ba shi ne abin farauta ta ba?.
Amsar tambayar da ya ka sa bawa kan sa kenan,
Kawai sai ya dubi wani hadimi dake tsaye a gefen sa a durƙushe ƙasa bisa gwiwar sa cikin
kakkausar murya yace dashi "yakai amirul-bait shin wane ne wannan jarumi kuma daga wace
nahiya a ka taho dashi.
Ko da jin wannan tambaya sai Amirul-bait ya buɗi baki cikin ladabi yace"ya shugabana wannan
jarumi da ake kira da suna Hibairu nayi leken a siri akan sa,
Abin da binciken ya tabbatar mini shi ne jarumin ya rayu ne a cikin daji tun yana jariri har ya cika
saurayi,
Mutun ne mai ɗauke da abubuwan al'ajabi da jarumtaka,
Domin bokaye da matsafa haɗe da sarakai na yi ma shi laƙabi da SARKIN SADAUKAI
Domin bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu babu GWARZON MAYAKI kamar sa
Kuma dukkanninsu waɗannan sarakuna da ka gani da Jarumai sun biyo shi ne izuwa gasar
jarumtaka domin ya cika burikan su,
Wani abu na mamaki da na gano ga me da wannan jarumi shi ne yakasance ɗa ne a wajen
Barde Shabbaru wadda a duk shekarun da aka shafe ana gudanar da gasar jarumtaka ba'a
taɓa samun gwarzo tamkar shi ba.
Ko da jin sunan Barde Shabbaru sai Sarkin yaƙi abu-Damraz ya miƙe tsaye zumbur daga kan
kujerar sa a dubi amirul-bait yace dashi
Shin ya kayi Shabbaru ya kasance a raye har ya samu Haihuwar ɗa namiji,
Bayan cewa a sani na ya daɗe da mutuwa,
Tabbas wannan fa shi ake cewa ana wata sai ga wata,
Tabbas ba'a rabu da bukar ba an haifi habu yakai amirul-bait kayi sani cewa fiye da shekaru
talatin barde Shabbaru ya cinye mai girma shaibat a gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,
Sarki yayi kukan baƙin wanda sai da ya kamu da rashin lafiya
Tsawon shekaru domin ya ɗaukar wa mahaifin sa alkawarin cewa sai ya zamo GWARZON
MAYAKI na gasar jarumtaka,
Bisa hakan ya sanya ya bani wani sinadarin tsafi na sanyawa Barde Shabbaru a cikin barasa a
lokacin da ake gudanar da shagalin nadin sarautar GOGA SHA FAMA,
Nayi mamaki da ka ce mini Shabbaru na raye Tabbas koda wani ya canza sinadarin dana sanya
masa a cikin barasar ko kuwa waɗanda na umarta ne da aikin su ka ci amana ta,
Cikin biyun nan dole ɗaya ya faru.
Tsawon shekarun da aka shafe da faruwar wannan al'amari
Mai girma shaibat bai manta da wannan abu a zuciyar sa ba,
Bisa wannan dalili yasanya yasha alwashin cewa yar sa gimbiya haya'ul-nur
Ta sha alwashin sai ta cika wa sarki wannan buri na sa,
Yakai Amirul-bait kayi sani cewa ahalin yanzu gimbiya haya'ul-nur na cikin jerin sunayen
jaruman da zasu fafata a gasar GOGA SHA FAMA,
Tabbas a halin yanzu a cikin tarko guda biyu,
Na farko shine yayin da sarki ya gano cewa HUBAIRU ɗa ne ga Barde Shabbaru zai tuhume ni
akan aikin da ya bani na hallaka Shabbaru ya akayi ya rayu,
Abu na karshe shine tsoro na kada gimbiya haya'ul-nur ta faɗi a wannan gasa
Tabbas a tsakanin waɗannan abubuwa da na lissafa faruwar ɗayan su dai dai yake da na
rayuwa ta
Haƙiƙa zama bai same ni ba matsawar Hibairu na numfashi a doran ƙasa,
Sa'adda sarkin yaƙi abu-Damraz yazo nan azancen sa sai hankalin sa ya sake dugunzuma fiye
da ko Yaushe ya dubi hadimi Amirul-bait yace dashi ina so ka ɗebi dakarun leƙen asiri guda
dubu su bazama ko ina a wannan birni kuma su saka idanu akan duk wani motsi na sadauki
Hibairu,
Koda jin wannan umarni sai Amirul-bait ya miƙa tsaye ya fice daga cikin harabar.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya ciki da waje na birnin madinatul-shaja'a ya cika ya batse
da baƙi daga sassan duniya,
Domin halartar bikin gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA.
Tun ketowar alfijir jama'a suka fara cincirindo shiga filin gasa domin samun wajen zama,
Nan fa yazamana cewa duk inda Mutum ya kalla a wajen gasar dakaru ne shirye cikin
gagarumar shigar yaƙi hannayen su riƙe da miyagun makamai suna ta kai komo domin tabbatar
da cikekken tsaro,
Kuma duk wanda zan shiga filin gasar sai an buga masa wani hatimi a tafin hannun sa
Idan kuwa mutum guda ne yake ɗauke da tawagar mutane a bayan sa zai bayyana takardar
shaidar halartar sa gasar,
Daga cikin wajen gasar kuwa tuni an tsara komai yadda ya kamata wajen zaman sarakuna
daban,jaruman gasa, attajirai da sauran su.
Kowa dai an tanadar masa wajen zaman sa dai dai da matsayin sa,
A cikin wannan hali ne aka hango tawagar wani basarake ta shigo filin gasar,
BASARAKEN yakasance gabjejen kato mai kirar samudawan farko,
Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cewa yana da karfi na Allah ya isa,
Sanye yake cikin ado na sarauta a gefen hannun sa na hagu wata irin tsaleliyar kyakkyawar
budurwa ta gaban kwatance kai kace ita ce ta tsara kanta yadda take bukata domin tsayawa
masalta kyawun ta ya huce hankali.
Tana sanye cikin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke, tun daga ƙasa har sama.
A gadon bayan ta ta rataya waɗansu zaratan takubba,
A gefen hagu da dama dakaru ne gami da hadimai ke take musu baya
Ba waɗansu ba ne waɗannan sarakai ba face
Sarki shuraih ibn shaslam na birin Iskandar tare da yar sa gimbiya Rumaisat,
Fiye da shekaru goma sha biyar sarki shuraih ya shafe yana sanya ana bawa yar sa gimbiya
Rumaisat rohon yaƙi a can birin Kisra domin dai jiran wannan rana da zata shiga gasar
jarumtaka ta GOGA SHA FAMA domin ta kafa tarihi a can nahiyar su ta gabashin duniya.
A lokacin da gimbiya Rumaisat ke karɓar horon yaƙin sai da yazamana cewa ta zarce kowa ne
jarumi karfin damtse gami da sanin dabarun yaƙi,
Har yazamana an bata lambar girma mawa ta gwarzon mayaƙi,
Lokacin da mahalarta gasar su kayi arba da sarki shuraih ta tawagar sa fadar ta ruɗe da shewa
masoyan sa nayi masa jinjina.
Waɗansu ma tsananin kwayun surar gimbiya Rumaisat ne ya ruɗe su.
Har sa sarki shuraih da tawagar su ka je suka zauna abisa kujerun da aka tanadar musu
sannan fadar ta ɗan samu nutsuwa,
Haka dai tawagar sarakuna suka dunga shigowa fadar rukuni-rukuni kafin wani lokaci filin ya
kammala cika maƙil,
Ana cikin wannan hali ne aka hango tawagar sarki Baddadul-ulƙas ta shigo filin gasar nan take
fadar ta ruɗe fiye da ko yaushe kuma mutane suka cika da matukar al'ajabi bisa ganin yadda a
wannan karon tawagar ta sa har da miyagun dabbobi su ma sun samu halartar gasar.
A wannan lokaci sarkin sadaukai Hibairu ya rufe fuskar sa da rawani idanun sa kaɗai ake gani
don haka babu wanda ya shaida cewa wane ne gwarzon mayaƙi acikin tawagar sarki
Baddadul-ulƙas,
Bayan Baddadul-ulƙas sun zauna bisa kujerun zaman su,
Sai mai girma shaibat ya miƙe tsaye ta hanyar ɗaga hannun sa sama fadar tayi tsit tamkar
mutuwa ta gifta
A wannan lokaci yana sanye cikin shigar alfarma ta hamshakan sarakai,
Sannan daga bisani ya buɗi baki yayi gyaran murya yace
"Da farko ina yiwa dukkan mahalarta wannan GASAR jarumataka Barka da zuwa wannan birni
mai albarka.
Nayi matuƙar farin cikin yadda manyan sarakuna, bokaye, attajirai,sadaukai haɗe da talakawa,
Su ka fito kwan su da kwarkwatar daga ko ina a sannan duniya domin halartar wannan gasa
mai ɗumbin tarihi da ake gudanarwa tsawon shekaru,
Da wannan nake yiwa dukkanin mahalarta Barka da zuwa tare da fatan ayi taro lafiya a tashi
lafiya,
Yanzu sai a samu nutsuwa a saurari sauran bayanin yadda gasar zata kasance daga bakunan
alƙalan gasa.
Koda Gama faɗin hakan sai sarki shaibat ya koma bisa kan karagar sa ya hakimce,
Kawai sai sarkin yaƙi abu-Damraz ya miƙe tsaye yayi gyaran yace
"Bayan jawabin mai martaba yanzu abinda ke gaban mu shine gabatar da dokokin gasa ga
dukkan jaruman da zasu fafata,
Amma kafin hakan yanzu za'a kira wo sunayen jaruman domin su wajen wajen zaman su dake
daf da filin fama.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Sarkin yaƙi abu-Damraz ya sanya hannun sa na dama ya
ɗauki wata jimammiyar fata dake ajiye a bisa teburin dake gaban sa,
Ya ɗora idanun sa akan ta sannan ya fara karanto sunayen jaruman kamar haka
Gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat
Koda jin an ambaci sunan yar mai girma shaibat sai fadar ta ruɗe da shewa,
Lokaci guda ta sauko daga kan karagar ta ta durfafi wajen zaman alkalan gasar,
Nan da wasu da ya wa daga cikin mazaje suka ɗimauce bisa ganin tsananin kyawun sura da
diri nata,
Haka dai sarkin yaƙi ya cigaba da kiran sunayen sadaukan ɗaya bayan ɗaya
Jama'a nayi musu jinjina,
Har yazamana an ambaci sunan Jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI
Koda jama'a suka yi arba da Hibairu sai fadar ta kaure da ihu da shewa fiye da ko yaushe,
Zukatan al'umma cike da matukar mamaki da al'ajabi suna masu cewa wai shin dama Barde
Shabbaru yana raye bai mutu ba,
Amma kuma ai Shabbaru ai a halin yanzu dattijo ne kuma ma labarin mutuwar sa ya watsa ko
ina a duniya
Haka dai hubairu ya cigaba da tafiya har ya zamana ya zaune a bisa kujerar sa,
Koda ya zauna sai ya hangi wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ta ƙura masa idanu ko ƙiftawa
baya yi,
Ba wata ce wannan kyakkywar budurwa ba face gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih,
Koda gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat taga yadda Rumaisat ke ƙuruwa hubairu idanu
sai ta daka mata harara kuma tace a cikin ran ta tabbas idan kin kamu da soyayyar Hibairu ne
to kin so gawa mara amfani,
Domin na rantse da darajar iyaye na sai na hulakanta hubairu kamar yadda mahaifin sa ya
wulakanta Abbana.
Kuma tabbas Ni ce zan zamo ajalin sa bayan na cinye wannan gasa ta GOGA SHA FAMA.
Sarkin yaƙi ya kira sunan jaruma ta karshe wacce ake kira Amirat bintu Hamza ta birnin
madinatul-barnawiy.
Koda fitowar jarumar sai kowa ya cika da mamaki Bisa ganin jarumar bata ɗauke