Showing 9001 words to 12000 words out of 30696 words
Chapter 4 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf
Cikin ruwan sanyi ka damƙa mini yaro Humair domin na yanke maka hukunci cikin lumana ta
hanyar daddatsa sassan jikin ka,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai saurayi Hizmal ya bushe da dariyar ƙarfin
hali sannan daga bisani ya murtuke fuska yace"kaicon ka yakai wannan azzalumin sarki da bai
damu da darajar ran ɗan adam ba face buƙatar kansa,
Ai a halin yanzu yaro Humair yayi maka nisa, domin bazaka taɓa samun nasarar hallaka sa ba
matsawar ruhina yana tare da gangar jiki,
Da jin wannan batu sai takaici ya turnuƙe sarki Shazwan jikin sa ya kama tsuma,
Har ya sake buɗar baki da nufin ya furta wani abu sai aka ga wani haske na ratsowa daga
sararin samaniya
Koda kowa ya mayar da duban sa zuwa ga wajen take aka yi ido biyu da wata tsaleliyar
kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance tare da wani dattijo mai tarin shekaru zaune abisa kan
wata dardumar sihiri,
Mu haɗu a GOGA SHA FAMA littafi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Mansur Usman Sufi
GOGA SHA FAMA 2
BABI NA BIYU
Littafin yaki
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Free book
Ba wasu ba ne face sarauniya Nuwairat tare da boka Jadwar dake farautar Budurwa Nihla
domin su hallaka ta,
Domin Nuwairat ɗin ta samu nasarar kasance mace ta farko da Hibairu zai fara gani a rayuwar
sa kuma ta samu soyayyar sa.
Nan fa sabon kallon kallo ya fara guda na tsakanin sarauniya Nuwairat da budurwar Nihla
dake tsaye hannun ta riƙe da takobi,
Bisa mamaki a wannan karon sai sarauniya Nuwairat taga Nihla ta ƙura mata idanu babu tsaro
ko fargaba a tare da ita duk kuwa da irin kwarjinin ta,
Abangaren jaruma Husnaila kuwa koda ta gama faɗin hakan sai yar uwar ta gimbiya Hushriba
ta zare waɗansu tagwayen takubba guda biyu a gadon bayan ta ta falfala da azababban gudu
izuwa kan ta, tana mai ihu da kururuwa mai firgitar wa, Koda ganin hakan sai sunaila ta falfala
da gudun izuwa kan ta riƙe da takobi domin tarar juna,
Tamakar haɗin baki a lokaci guda jaruman kowane bangare sukayi kukan kura domin yin karon
battar karfe,
Sarki shazwan da boka Dargas suka ruga izuwa kan saurayi Hizmal, Sarauniya Nuwairat da
boka Jadwar suka ruga izuwa kan Budurwa Nihla,
Aljani Marhutul-Azab da aljani Darmanu suka tari juna,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sai suka tari tawagar sarki uslaim domin ganin sun tseratar
da yaro Humair domin shine abin buƙatar su.
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin jaruma sunaila da Hushriba,
Sarauniya Nuwairat,boka Jadwar da budurwa Nihla,
Saurayi Hizmal, boka Dargas, da sarki shazwan,
Aljani Marhutul-Azab da aljani Darmanu, sarki
Sarki uslaim, boka ƙarzum da tawagar sarki shazwan,
A gabar shiga dajin Baitul-shamshan,
Sai yakin yazamo abin tsoro kuma tashin hankali ga kowa ne bangare.
Jaruman suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta
tagaban kwatance,
Ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihun mazaje ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin
samaniya,
A bangaren jaruma sunaila da yar Uwar ta Hushriba kuwa,
Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi ta hanyar kaiwa juna sara da takubban su,
Cikin ɓakin zafin mama juriya da nacin tsiya,
Duk sa'adda takubban su suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da kara
marar daɗin sauraro,
Babu abinda zai burge ka ga zaratan matan biyu sama da yadda suke kaiwa juna sara da suka
tamkar jikkunnan su ba su kasance na jini da tsoka ba,
Abangaren sarki shazwan,boka Dargas da saurayi Hizmal labari yasha bamban,
Domin duk karfin damtsen zaratan sarakunan biyu sai yazamo ya tashi a banza.
Domin kuwa sun kasa koda lakutar jikin saurayi Hizmal da makaman yakin su.
Sai dai ga wanda yake kallon yadda artabun ke wakana zai iya fahimtar cewa ƙarfin damtsen
Sarki shazwan da boka Dargas ya nun ka na Hizmal sau goma,
Saboda wasu lokutan idan su ka kai masa hari da takobin sa,
Idan ya sanya takobin sa ya kare sai kaga har durkushewa ƙasa yake yi,
Amma saboda da juriya da bajinta irin ta JARUMAN DUNIYA sai kaga ya taso sama ya mayar
da martani.
Duk wannan fafatawa da akeyi tsakanin su Hizmal, yaro Humair makaho dake goye a gadon
bayan sa yana jin duk irin fafatawar da akeyi,
A bangaren manyan aljanu biyu kuwa aljani Darmanu da Marhutul-Azab,
Sun wanzu suna ba wa hammata iska yazamana cewa,
Suna yin ragas idan Darmanu ya samu nasarar kaftawa Marhutul-Azab sara a hannu sai kaga
shi ma ya mayar da martani ,
Ko iya hargagin su ma ya isa ya firgita lahittun
Dake wajen ,
Amma a bangaren sarki uslaim da boka ƙarzum da tawagar sarki shazwan kuwa,
Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi,
Duk inda sarki uslaim ya sanya gaba sai kaga dakaru na zubewa ƙasa magashiyan ,
Ita kuwa budurwa Nihla ta zamo tamkar wata shaiɗaniya a tsakanin sarauniya Nuwairat da boka
Jadwar,
Domin sun kasa samun nasarar murƙusheta
Al'amarin daya fusata sarauniya Nuwairat da boka Jadwar kenan, zukatan su suka kama
tafarfasa tamkar zasu ƙone
Abu na farko da ya dugunzuma hankalin su shine yaushe Nihla ta samu wannan gagarumin
karfin damtse,
Har su gaza samun nasara akan ta a matsayin su na zaratan Jarumai masu juriya da bajinta,
Sannan idan har aka cigaba da wannan artabu a haka zasu iya yin biyu babu,
Domin abinda zai faru shi ne dazarar ɗaya daga cikin abokan gaba ya samu nasarar kashe a
bikin faɗan sa zai iya rigasu saduwa da SARKIN SADAUKAI,
Kai ga kenan sunyi aikin banza, kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,
Sa'adda suka zo nan a tunanin su sai suka canza salon faɗan su.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa
ta canza.
Faruwar hakan keda wuya sai yazmana cewa a wannan karon su boka Jadwar suna haɗawa da
bugu da kafa da kai sara da takobi,
Nan fa suka fara haɗawa Nihla jini da majina,
A cikin wannan fafatawa ne Nihla ta kai musu wani sara da takobin ta a kirjin su,
Adai dai lokacin ne sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka kai mata duka da ƙafafuwan su
ɗia ɗin,
Bisa Sa'a sai suka dake ta a kirji da dukkan karfin su,
Saboda karfin dukan sai da Nihla tayi katantanwa a sama sau uku sannan ya kife ƙasa da ruf
da ciki,
Kawai sai sarauniya Nuwairat ta zare takobin ta ta durfafi inda take tana mai yi mata murmushi
mugun ta,
Tana isa ta ɗaya takobin ta domin ta sare mata wuya.
Dai dai lokacin da jini ke kwaranya daga bakin. Budurwa Nihla kuma numfashin ta na sarkewa.
Kwatsam ! Bazato babu tsammani sai sarauniya Nuwairat taji an dankara mata wawan naushi
a dagon bayan ta saboda karfin naushin sai Nuwairat ta tayi gundumbala sau uku sannan ta
kife a ƙasa,
Amma sai ta miƙe tsaye zumbur cikin matuƙar fushi da zafin nama,
Ta wai ga bayan ta domin taga wane ne ya dake ta ɗin,
Ai kuwa koda juyawar ta sai tayi Turus, bawa Ni ta gani ba face,
Wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa zaune a bisa kan wani tsuntsun tsafi tare da wani
zabgegen kyakkyawan saurayi,
Ba wata ba ce wannan budurwa ba face sarauniya Abidatul-auliya ta birnin Tehran tare da
matsafi shubairu,
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin sarauniya Nuwairat da sarauniya Abidatul-auliya,
Tsawon wani lokaci sai daga bisani Abidatul-auliya ta a dubi Nuwairat ta daka mata tsawa
sannan ta buɗi baki cikin kakkausar murya tace"yake tsohuwar azzaluma kuma abokiyar gaba
tun iyaye da kakanni ina fatan a halin yanzu kin shaida Ni ko?
Dajin wannan tambaya sai Nuwairat ta bushe da dariyar ƙarfin hali sannan tace "Ai kuwa ni na
gane domin na sanki fiye da yunwar ciki na,
Abidatul-auliya bintu shafwaz ta birnin Tehran,
Ban taɓa tsammani cewa akwai sauran zuri'ar mahaifin ki a doran ƙasa ba,
Abidatul-auliya ta ce"Idan barci kike sai ki farka a yanzu ne zuri'ar mahaifi na take gab da
yaɗuwa a duniya,
Hakika ke da zuri'ar gidan ku kun dade kuna aiwatar da mulkin zalunci,
Amma ina so ki sani cewa a waje zan hallaka ki na tsira kokon kan ki,na tsire sa da mashi na
ajiye sa a fada ta domin ya zamo inza ga sarakunan azzalumai,
Kuma ina mai tabbatar miki dacewa bazaki taɓa burin ki na saduwa da SARKIN SADAUKAI,
Ballantana ki cika burin ki, na sarrafa sa yadda kike so har ki sanya duniya a cikin musiba,
Koda jin wannan batu daga bakin Abidatul-auliya sai Nuwairat ta bushe da dariyar mugun ta
sannan tace"Fiye da shekaru ashirin baya mahaifin ki yayi wannan furuci amma sai da Abba na
yaga bayan sa don haka,
Wannan bayani naki tamkar a zuba ruwa a faifai,
Ina mai tabbatar miki dacewa a yanzu zan hallaka na zare ruhin ki daga gangar jiki,
Kuma na hallaka budurwa Nihla da kika ceci rayuwar ta a halin yanzu,
A bangaren matsafi shubairu da boka Jadwar kuwa koda suka yi kallon kallo
Sai boka Jadwar ya dubi matsafi shubairu yace"yakai shubairu kayi sani cewa zuwa wannan
waje domin saduwa da SARKIN SADAUKAI Hibairu domin ya tafi izuwa fadar Sarkin bokaye ya
ɗebo maka Tsumin tsafi
Kayi maganin lalurar tsagin jikin da ta addabe ka,
Ka sani ya tashi a banza domin kuwa matsawar ina numfashi a doran ƙasa bazaka taɓa cika
wannan buri maka ba Ballantana ka zama dodon bokaye na wannan nahiya,
Koda jin wannan batu sai matsafi shubairu yayi murmushi ya dubi boka Jadwar cikin kaskanci
yace "Ai kuwa ina da tabbacin cewa zan cika wannan buri na wa domin dai masu iya magana
na cewa
In da rai da rabo! Kuma tabbatar mai nema yana tare da samu,
Kuma ita karya fure take bata yaya tabbas rana dubu ta barawo ce rana ɗaya ta kai kaya
Na tabbata cewa da ace sarauniya Nuwairat tasan cewa ka shafe tsawon shekaru kana cin
amanar ta da ta daɗe da sheƙaka barzahu,
Na sani cewa a duniya baka da burin da ya huce kaga ka mallake ta a matsayin abokiyar
rayuwar ka domin a halin yanzu a duniya samun wata ya mace mai kyawun sura kamar ta abu
ne mai wahala,
Baka san cewa hatta mafarkin da sarauniya Nuwairat tayi ba akan dole ne ta fara arba da
SARKIN SADAUKAI domin tazamo mace ta Farko da zai gani yaji yana kaunar ta ba,
Duk kai ne. Ka shirya sa domin kawai ka yi amfani da ita wajen mallakar ta dashi kansa
SARKIN SADAUKAI, domin ka kwashe sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN sa domin ka
zama Sarkin bokaye na wannan nahiya,
Hatta zaluncin da sarauniya Nuwairat ke aiwatar wa kai ne ke sarrafa ta ta hanyar wani bakin
aljani,
Na sani cewa Nuwairat ba zata taɓa gano wannan sirri ba face an karya sirihin dake tsakanin ta
da masarautar su,
Abinda ba ka sani ba shine babban kuskuren da kayi shine,
Matsawar Nuwairat tayi arba da SARKIN SADAUKAI take dukkanin sirrikan tsafin dake jikin ta
zasu lalace su daina aiki,
Domin bisa tsarin sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN Hibairu duk wanda yafara arba da shi
sai ya rasa nasa sirrikan tsafin,
Wannan shi ne fa abin da masu iya magana ke cewa karyar ƙasa wai malamin duba ya dubo
ranar mutuwar sa,
Kuma idan za ka gina ramin mutunta to gina sa gajere,
Sa'adda matsafi shubairu yazo nan azancen sa sai idanun boka Jadwar suka kaɗa sukayi jajur
har wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita kai da gani kasan aiki ne na sihirin tsafi,
Kawai ya buɗi baki yace"Na rantse da kushewar mahaifina boka sahibul -ƙarnas sai na mai
sheka gawa domin a halin yanzu kai ne kadai kasan sirri na,
Koda gama faɗin sai boka Jadwar ya ɗaya daga hannun sa izuwa sama,.sai ga wani narkeken
Gatari ta bayyana a hannun sa mai matukar kaifi tamkar takobi,
Tamkar hadin baki a lokaci guda jaruman huɗu sukayi kukan kura suka afkawa juna ta hanyar
ɗaga makaman yaƙin su,
Wato sarauniya Nuwairat ta afkawa sarauniya Abidatul-auliya,
Boka Jadwar kuwa ya afkawa matsafi shubairu,
Aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro,
A dai dai lokacin ne akaga sararin samaniya tayi duhu dunɗum,
Kwatsam sai wata runduna ta bayyana mai ɗauke da dakarun bil'adama da aljanu haɗe da
miyagun dabbobi.
Ba wata bace wannan runduna ba face rundunar Sarki Baddadul-ulkas na birnin Rum,
Daga cikin dajin Baitul-shamshan kuwa sai kaji wani kara ya cika wajen kuma wata irin guguwar
iska ta bayyana ta dunga sanyawa bishiyoyi na karairayewa suna zubewa ƙasa,
Duwatsu suna karo da juna suna yin bindiga,
Wata irin walkiya na bayyana a sararin samaniya tamkar hadari ne ya hadu ake shirin ɓarkewa
da ruwan sama,
Alamun dake nuna cewa HUBAIRU SARKIN SADAUKAI na gab da bayyana Daga cikin dakin
Baitul-shamshan .
Kwatsam bazato babu tsammani sai akaji wani irin gurnani na fitowa daga dajin haɗe da
waɗansu irin sauti ka da kunnawa ba su taɓa jin su ba,
Al'amarin daya sanya budurwa Nihla dake kwance a ƙasa ta ɗimauce kenan,
Bata san sa'adda ta kama rarrafe ba ta shiga izuwa dajin Baitul-shamshan saboda da ɗimauce
wa,
Tsaye tayi arba dashi sanye da kayan fata riga da bante iya kaurin sa,
Kyakkyawan saurayi ne nagaban kwatance wanda kallon farko zai ɗimauta zuciyar duk wata ya
mace mai hankali,
A gadon bayan sa yana rataye da wata rantsattsiyar kwari da baka hannun sa riƙe da wani
dogon mashi mai baki biyu,
A gefen sa na dama wani irin tsuntsun tsafi ne mai ɗauke da siffar mikiya da girman sa bai huce
na jakin dawa ba,
A gefen daman sa kuwa wani murgujejen zaki ne mai kwarjini daban tsoro,
Tsaye a bayan sa kuwa nau'ikan miyagun halittun daji ne gasu nan birjik har da ma waɗanda
idanu basu taɓa gani ba,
Ba wani bane wannan saurayi ba face jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Sa'adda budurwar Nihla ta yi arba dashi sai ta sake ɗimauce wa bata san sa'adda jikin ta
Yakamata tsuma yana kyarma ba,
Saboda tsananin tsoro, shi kuwa jarumi Hibairu sai ya ƙura mata idanu ko ƙiftawa baya yi,
Abu na farko da ya daɗo masa arai shine shin dama akwai wata halitta a wannan sararin dake
ɗauke da halitta irin ta sa,
Sannan mene ne abin da ya kawo wannan halitta izuwa cikin dajin Baitul-shamshan,
Amsar tambayoyin da Hibairu ya kasa bawa kansa kenan a karon farko kawai yaji ya kamu da
ƙaunar halittar wato Nihla,
Har yaji yana son yaga yaksance da ita a rayuwar sa har abada,
To amma mene ne ya janyo yaji ya damu da wannan halitta a cikin ran sa,
Koda wannan murgujen zaki dake tsaye a hannun sa na dama ya hango sunaila sai kawai ya
dako wawan tsalle domin ya turmushe ta ya hallaka ta,
Kafin ya kai ga aiwatar da hakan Hibairu SARKIN SADAUKAI ya daka masa tsawa tayi yin wani
furuci cikin wani irin yare,
Kawai sai zakin ya dawo da baya ya tsaya cikin ladabi,
Al'amarin daya sanya Nihla ta sake faɗuwa ƙasa a sume,
Cikin hanzari Hibairu SARKIN SADAUKAI ya riga izuwa inda take kwance ya busa mata wata
iska daga cikin bakin sa,
Jim kaɗan sai Nihla ta fara buɗe idanuwan ta ,
Sai gashi ta mike tsaye zumbur cikin koshin lafiya tamkar Banu wani abu daya faru gare ta,
Kuma ta ƙurawa Hibairu idanu,
A karon farko taji Ta kamu da matsananciyar kaunar HUBAIRU,
Kuma dukkan tsoro da fargaba sun fita daga zuciyar ta,
Hakika so na da matukar tasiri wajen canza zuriyar bil'adama cikin kankanin lokaci,
A can bakin shiga dajin Baitul-shamshan kuwa,
Yaƙi yayi tsamari tsakanin kowa ne bangare,
Bangaren sunaila da yar uwar ta Hushriba kuwa,
Sun wanzu suna kaiwa juna hare - hare cikin zafin nama