Showing 30001 words to 30696 words out of 30696 words

Chapter 11 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf

07 Aug 2025

615

tare da tawagar aljani Marhutul-Azab sai dukkan jama'ar gari da suka bayyana a
wajen,

A wannan waje ne wani abu ya faru domin kuwa bayan sarauniya Abidatul-auliya da
masoyinta matsafi shubairu sun faɗi kalmar shahada nan take suka ji wannan cutar kuturta
dake tsagin jikin su ta daina yi musu ciwo yayin da suka duba kuwa sai suka ga babu komai
tamkar cutar bata taɓa wanzuwa ba, yaro Humair makaho kuwa shi sai yaga idanunshi yana iya
ganin kowa alamar ya samu lafiya.

Nan fa suka ji sun ƙara imani da ubangijin musulunci.

Kashe gari tun da duku-dukun safiya fadar margayi shaibat ta cika ta batse da jama'a babu
masaka tsinke domin yin naɗin sarautar hubairu sarkin sadaukai tare da ɗaurin aurenshi da
Budurwa Nihla, sarauniya Nuwairat, jaruma Amirat da gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat
tare gumbiya Rumaisat yar sarki shuraih,tare naɗin wazirin shi sarkin yaƙi abu-Damraz bayan
shima ya karbi addinin Musulunci,

Saurayi Hizmal suka zai auri jaruma sunaila da baƙuwar jaruma ba wata bace wannan
baƙuwar jaruma ba face amrita wacce suka kasance Hassana da Husaini ga jaruma Amirat,
lokacin da fuskar ta ta bayyana a fili sai da kowa ya cika matuƙar al'ajabi bisa ganin yadda
kamannin baƙuwar suka zo ɗaya sak da na Amirat tamkar an tsaga kara.
Sarki shazwan kuwa zai auri gimbiya yar uwa ga jaruma sunaila,

Sarauniya Abidatul-auliya kuwa da matsafi shubairu masoyin ta.

Sarki Hamza mahaifin jaruma Amirat ne ya zamo waliyin amaren, wani hadimin shi mai suna
Salman kuwa ya zamo waliyin angwaye.

Bayan anyi shagin ɗaurin aure da naɗin sarauta dukiyar da za'a bawa hubairu ta nasarar
cinye gasar GOGA SHA FAMA kuwa sai yayi umarni aka dunga rabawa talakawan gari tare
bawa dukkanin bayin kurkuku da aka 'yan tasu.

Haƙiƙa anyi gagarumin shagalin da ba'a taɓa yin kamar shi ba iya Tsawon wanzuwar birnin
madinatul-shaja'a, domin kowa ya wadata da arziki mai tarin yawa.

Bayan mako guda ne da faruwar hakan sai sarki Hubairu yayi umarni ga waɗannan aljanu yan
uwan aljani Marhutul-Azab suka ɗauki Sarauniya Abidatul-auliya da angwanto, sunaila da nata
aka kai su izuwa kasashen su,

A inda matsafi shubairu yazama sabon Sarkin birin Tehran,saurayi Hizmal kuwa yazamo sabon
sarkin birin Baitul-mausul, bayan ya warkar da sarki ishwar mahaifin jaruma sunaila daga lalurar
dake damunshi bisa ikon Ubangijin musulmi batare da anyi amfani da tsumin tsafin dake fadar
sarki bokayen Duniya ba , yarima ubaiyu ya zama wazirinshi, yarima zaiyum kuwa ya zama
shugaban majalissar sarki bayan sun karɓi addinin Musulunci, kuma suka janye gabar dake
tsakanin su da yar uwar su jaruma sunaila.

Sarki shazwan da amaryar shi Gimbiya Hushriba yar uwata ga sunaila suka kasance cikin
aminci,

Lokacin da aljani Darmanu ya ɗauki sarki uslaim, boka ƙarzum da gimbiya Zarifa bai zame ko
ina sai tsakiyar birnin baharen ya sauka a turba,

Nan fa farin ciki ya kama jama'ar bisa dawowar gimbiya Zarifa da sarki, kuma a wannan rana
aka ɗaura auren boka ƙarzum da gimbiya Zarifa

Sarki Hamza mahaifin jaruma Amirat ya koma izuwa birnin madinatul-salam bayan ya aika da
malaman addini izuwa dukkan kasashen daban-daban.

Yaro Humair makaho ya ci gaba da kasance tare da sarki Hubairu, daga wannan rana hasken
musulmi ya mamaye ko ina a duniya, a kawo KARSHEN ZALUNCI da azzalumai, adalci ya
cigaba da wanzuwa.

ƘARSHE

Alhamdulillah



Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da Koyaushe
Sarkin marubuta littattafan Yaƙi
MANSUR USMAN SUFI
08137237071

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login