Showing 15001 words to 18000 words out of 30696 words
Chapter 6 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf
cikin zuri'ar ka,
Koda jin wannan batu sai hawayen bakin ciki suka zubo daga idanun Shabbaru
Ya sake ƙurawa Hibairu idanu nan take yaji cewa tamakar matar kuwailat ce yake tare da ita ,
Sarki Baddadul-ulƙas ya yi nuni da hannun sa izuwa inda yaro Humair makaho yake nan take
wata iska mai karfi ta jimimiyo sa ta kawo sa izuwa daf da inda SARKIN SADAUKAI Hibairu
yake tsaye,
Sannan sarkin sadaukai Hibairu ya dubi yaro Humair ya buɗi baki ya fara yi masa Magana da
irin nasa yaren,
In da yake cewa dashi "yakai wannan yaro ɗan baiwa shin wane ne wancan mutumin mai
matukar kama da Ni,
Kuma me yasa wannan azzalumin sarki yake son hallaka sa
Haƙiƙa ina ji a zuciya ta cewa wannan mutumin wani ne na musamman a cikin rayuwata.
Koda jin waɗannan tambayoyi sai budurwa Nihla ta matsa daf da in da Humair makaho yake da
ya ke taji dukkan abinda sarki Baddadul-ulƙas da Barde Shabbaru ke tattaunawa,
Nan take ta zayyane wa yaro Humair dukkan abinda ya wakana tsakanin su,
Shi kuma ya shiga yi wa HIBAIRU bayani tun daga farko har ƙarshe,
Sa'adda Hibairu yaji bayanin abinda yafaru tsakanin sarki Baddadul-ulƙas da dattijon,
Kuma dattijon ba wani bane face Mahaifin sa Barde Shabbaru
Da irin zalunci da cin amanar da yayi masa har ya yi sanadin mutuwar mahaifin sa,
Kawai sai a kaga Hibairu ya fashe da kuka mai tsuma zuciya,
Tsawon daƙiƙa goma yana zubar da hawayen,
Sai daga bisani ne ya sanya hannun sa na hagu ya murza zoben dake hannun sa sai ga wani
irin koren haske ya fita daga zoben ya bayyanar da wani Hoto wanda dukkan wanda ke wajen
yana iya gani,
Majigin wata mata ne ya bayyana ɗauke da juna biyu ya bayyana ta na cikin tafiya a dajin
Baitul-shamshan ta yanke jiki ta fadi kasa
Kallo ɗaya zaka yi matar ta kamu da matukar tausayin ta har ka zubar mata da waye,
Saboda yadda raunukan dake jikin ta ke zubar da jini,
A wannan hali ne nakuda ta kamata tasha wahala sosai matuka kafin ta haife abin da ke cikin
ta,
Bayan ta Haihu ne numfashin ta ya ɗauke ta mutu nan take sakamakon jinin ta da ya zuba a
jikin ta
Jim kaɗan da faruwar hakan sai wani aljani ya bayyana a wajen a lokacin da jaririn da matar ta
haifa ke tsala kuka,
Kukan na sa ya amsa amo izuwa cikin dajin
Aljanin ya sunkiya ƙasa ya ɗauki jaririn sannnan ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Haka dai Hoton ya cigaba da bayyana yadda Hibairu ya rayu a cikin dajin Baitul-shamshan tare
da dabbobi da aljanu,
Daga farko har ƙarshe ya bayyana,
Sa'adda Barde Shabbaru yaga wannan al'amari sai ya sake fashe da kuka a karo na biyu,
tamkar bazai daina ba,
Shi kuwa SARKIN SADAUKAI Hibairu yana zubar da hawaye ne bisa halin da yaga mahaifiyar
sa da Yadda akayi ta rasa rayuwar ta
Kusan dukkan jama'ar dake wajen sai kwallar takaici da tausayi ta zubo musu,
Ina ban da boka Jadwar da aljani Darmanu
Da Hushriba,
Ita kan ta sarauniya Nuwairat da ta kasance azzalumi tagaban kwatance sai taji tausayin ya
kamata,
Tsawon daƙiƙa hamsin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne,
Sarki shazwan katse shirun da ya wanzu ta hanyar duban yaro Humair makaho ya ce" yakai
Hibairu matsawar kana son ka tsira da mahaifin ka wanda a halin yanzu shi kaɗai ne ya rage
maka a duniya to ya zama wajibi ka bi dukkan sharuddan dana bayyana wa mahaifinka na
shiga gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA.
Da kuma bin umarnin dukkan abinda nake da buƙata,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulƙas sai yaro Humair ya dubi Sarkin sadaukai
ya bayyana masa abinda sarki Baddadul-ulƙas yake nufi da irin nasa yaren,
Dajin wannan batu sai hawaye suka sake zubowa HUBAIRU,
Sannan ya dubi Humair makaho yayi masa magana da irin nasa yaren shi kuma ya juya ya dubi
Baddadul-ulƙas yace "A bin da Hibairu yake nufi shine zai bi dukkan umarnin ka matsawar zaka
bar mahaifin sa a raye,
Amma bisa sharaɗin cewa bazaki yaudare sa ba, matsawar hakan ya faru zai yaƙe ka,
Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yaji wannan batu sai ya bushe da dariyar farin ciki maral
misaltuwa
HUBAIRU ya tako da kafafun sa har izuwa inda mahaifin sa yake yazmana tazarar dake
tsakanin su bata huce ta ku ɗaya ba,
Sa'adda suka ƙurawa juna idanu sai Hibairu yaji wani irin abu ya roki zuciyar sa,
A karon farko yaji gaba ɗaya yanayin ɗabi'ar sa ta sauya,
Nan fa ya cika da mutukar mamaki da al'ajabi
Abin da Hibairu bai sani ba shine wannan abu daya ji a zuciyar sa bakomai ba ne face
Akwai wani sirrin tsafi na musamman dkaek da ke ɗauke a cikin idanun Shabbaru wanda ya
gada tun iyaye da kakanni,
Bisa tsarin tsafin Dazarar mutum ya kai Shekaru hamsin shafin zai rabu dashi ya tafi izuwa jinin
sa,
Sinadarin tsafin na ɗauke da dukkanin sirrikan nasara, adalci, tausayi da sauya al'amura,
Wani abu da Hibairu bai sani ba shine a halin yanzu yana dauke da dukkanin yaren mutanen
duniya na kowa ne jinsi ,
Bisa mamaki koda Hibairu ya buɗi baki da nufin yace wani abu sai yaji yana magana da Yaren
irin na jama'ar dake wajen,
In da ya dubi mahaifin da Barde Shabbaru Yace"ya abbana kayi sani matsawar ina numfashi a
doran ƙasa bazan taɓa bari na rasa ka ba kamar yadda na rasa ummana,
Zan bi dukkan umarnin da sarki Baddadul-ulƙas yake buƙata,
Koda jin wannan batu daga bakin Hibairu sai Barde Shabbaru yayi murmushin karfin hali,
Sannan yace "ya ɗana abin alfahari kayi a halin yanzu kana ɗauke da dukkan sirrikan tsafin mu
na gado,
Don haka ina da tabbacin zaka samu nasara akan dukkan abin da ka sanya a gaba,
Yanzu abin da kawai nake bukata a gare ka shine.
Dukkanin waɗancan mutane dake wannan waje sun zo gare ka ne domin ka share musu
hawaye,
Don haka dukkanin su zaka cika musu burikan su bayan ka samu nasarar cinye gasar
jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,
Domin kuwa cika burikan nasu tamkar shafe duk wani zalunci ne da azzalumai a doran ƙasa,.
Wanda ke bukatar ya bi ka izuwa birnin madinatul-shaja'a zai iya yi,
Wanda kuma zai koma izuwa birnin sa ya jira har izuwa lokacin da zaka dawo daga gasar
jarumtaka ta GOGA SHA FAMA to ,
Koda jin wannan batu daga bakin Shabbaru sai Sarkin sadaukai yace "An gama ya abbana
dukkan abinda ka faɗa shi za'ayi.
Dajin hakan sai Barde Shabbaru ya cika farin ciki jin Hibairu ya kira da Abban sa,
Hibairu ya juya izuwa inda sarakuna bokaye da matsafa suka yi cincirindo suna kallon abin da
ke wakana,
Ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace"ya ku jama'ar dake wannan waje kuyi sani nasan
cewa dukkanin ku kun taru ne anan domin na cika muku burikan ku,
To na amince zan biya kowannen ku buƙatar sa, amma sai bayan na dawo daga birnin
madinatul-shaja'a,
Duk wanda zai biyo ni zai iya wanda kuma zai jira na dawo shi ma zai iya,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin sadaukai sai kowa dake wajen ya cika da matukar
mamaki Bisa jin Hibairu na magana da Irin Yaren su,
Shin Yaushe Hibairu ya iya wannan Yaren
Amsar tambayar da dukkanin su suka kasa bawa kansu kenan.
Nan take kowannen su ya amince cewa zai bi Hibairu izuwa birnin madinatul-shaja'a domin
yaga irin wainar da ake toya wa,
Domin idan suka bari sarki Baddadul-ulƙas ya tafi da SARKIN SADAUKAI yaushe suke da
tabbacin zai dawo gare su bayan cewa dukkanin su sun shaida azzalumi ne nagaban kwatance
bayan dukkanin su sun amince da hakan sai sarki Baddadul-ulƙas ya sake nuna Barde
Shabbaru da ɗan yatsan sa na hagu nan take ya dawo izuwa cikin wannan keken doki
Sannan sarkin sadaukai yaje inda tsuntsun tsafin sa yake yakama ya hau,
Tare da goya yaro Humair makaho akai cikin hanzari ya bi bayan Sarki Baddadul-ulƙas a
lokacin da tawagar su suka fara cigaba da tafiya,
Koda ganin hakan sai budurwa Nihla zaune bisa kan wannan zaki, tare da tawagar namun dajin
Baitul-shamshan suka mara masa baya,
Saurayi Hizmal da sunaila suka hau bisa kan Aljani Marhutul-Azab,take kowa ya hau bisa kan
abin hawan sa aka karawa sarki Baddadul-ulƙas baya a ka fara tafiya , domin durfafar hanyar
da zata Sada su da birnin madinatul-shaja'a,
Mu haɗu a littafin GOGA SHA FAMA na uku domin jin cigaban wannan ƙayataccen labarin.
Dagaa mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Goga Sha Fama 3
Littafin yaki
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Hausa
Wthapp Number
08137237071
Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas,ya jagoranci tawagar matsafa,sarakuna bokaye da jarumai,
Tare da SARKIN SADAUKAI Hibairu,
Domin isa izuwa birnin madinatul-shaja'a don halartar gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,
Sai aka wanzu ana ratsa dazuka da tsaunuka
Babu sassauci,
Kai idan kaga yadda tawagar suke tafiya sai kayi tsammanin cewa gaba ɗaya sarkaunan duniya
ne suka taru waje guda suke shirin yakar duniya baki ɗaya,
Ana cikin wannan tafiya ne sarauniya Abidatul-auliya ta dubi matsafi shubairu cikin alamun
matukar damuwa tace "ya amini na shin yanzu mene ne makomar mu a wannan tafiya,
Yanzu muna ji muna gani haka sarki Baddadul-ulƙas zai dunga sarrafa musu kamar yadda zai
sarrafa Hibairu,?
Wai shin ma Wane ne a cikin mu yake da tabbacin cewa Baddadul-ulƙas bazai ci amanar
Hibairu ba?
Ko da jin wannan batu daga bakin SARAUNIYA ABIDATUL-AULIYA sai matsafi shubairu yayi
murmushin karfin hali sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye yace"ya sarauniyar kyawawan
duniya kiyi sani cewa Ni kai na na yiwa kai na waɗannan tambayoyi sai dai ban iya bawa kai na
amma sa ba,
A halin yanzu bamu da wani zaɓi da ya huce mu bi sarki Baddadul-ulƙas domin ta wannan
hanya ne zamu samu nasarar bayyana cika burin mu,
Domin a halin yanzu Hibairu tamkar farin ingarman doki ne a tsakiyar bakaken dawakai,
Abin nufi anan shi ne farautar sa abu ne mai matukar wahala da rabo,
Saboda kowa muradin mallakar sa yake a
Kawai dai abin da zamu yi riƙe a wannan tafiya domin samun nasara shine
Rike amana,gaskiya da tausaya wa ga wanda muka sani da ma wanda ba mu sani ba,
Sannan ƙoƙarin mu yakasance kullum cikin taimakon Hibairu,
Waɗannan abubuwan sune tabbatar nasarar mu idan mun riƙe su.
Lokacin da matsafi shubairu yazo nan azancen sai sarauniya Abidatul-auliya ta cika da matukar
farin ciki,
Daga wannan batu kowannen su yayi shiru suka shiga hirar da ta shafi rayuwa,
Kamar yadda ya wakana tsakanin su shubairu haka al'amarin yaksance,
Abangaren jaruma sunaila da saurayi Hizmal a in da sunaila ta dubi Hizmal tace"yakai Hizmal
har yanzu kayi sani cewa har yanzu ina ji a jikina cewa tabbas zamu samu nasara a wannan
tafiya,
Domin dai babu wani mahaluki da zai iya zuwa fadar Sarkin bokaye face yana ɗauke da
taswirar dake hannun aljani Marhutul-Azab,
Duk da cewa a halin yanzu Ban San mene ne abin da zai kasance a birnin madinatul-shaja'a
ba,
Shin Hibairu SARKIN SARAKAI zai iya cika sharaɗin da sarki Baddadul-ulƙas ya ginda ya masa
ya cinye gasar jarumtaka,
Har ya yan mahaifin sa Barde Shabbaru Daga KANGIN BAUTA,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hizmal ya ce "Naji a jiki na cewa HUBAIRU zaiyi
nasara a gasar jarumtaka
Hujja ta na faɗin hakan shi ne kada fa ki manta cewa HUBAIRU shine SARKIN SADAUKAI na
duniya a halin yanzu babu wani jarumi mai karfin gaske kamar sa,
Sunaila ta ce"Ko da hakan amma kasan cewa Sa'a da rabo ake bukata a Kowa ne al'amari ba
wai tarin karfi ko sihiri ba,
Komai karfin damtsen ka idan baka da Sa'a da rabo kenan kayi aikin banza,
Hizmal yace"Tabbas zancen ki dutse yake sunaila,
Amma ai Sa'a da rabo na tare da gaskiya da adalci,
Sunaila"tabbas zancen ka haƙƙun ne yakai Hizmal.
Amma a ɓangare sarauniya Nuwairat da boka Jadwar kuwa,
Nuwairat ce ta dubi boka Jadwar cikin damuwa da ɓacin rai tace "yakai abin dogaro yanzu
gashi dukkanin shirin mu ya tarwatse yanzu ina amfanin tafiyar mu tare da tawagar sarki
Baddadul-ulƙas,
Tun da budurwa Nihla ta samu nasarar fara yin arba da SARKIN SARAKAI,
Kuma a yadda alamu suka nuna tuni ya kamu da matukar kaunar ta,
Koda jin wannan batu daga bakin Nuwairat sai boka Jadwar yayi ya mai sunkiyar da kan sa
ƙasa daga bisani ya ɗago da kansa ya dube ta cikin girmamawa, da kakkausar murya yace
"Ya sarauniya kyawawan mataye kiyi sani cewa har yanzu kina da damar mallakar HUBAIRU
har ma ki sarrafa shi yadda kike so
Matsawar kina bukatar hakan to wajibi ne ki mallaki zoben sihirin dake hannun jarumi Hibairu ki
sanya shi a hannun ki,
Domin duka sirrin zuciyar sa ya tattara a cikin wannan zobe,
Daga nan har izuwa lokacin da za'a kammala gasar jarumtaka a birnin madinatul-shaja'a,
Dole kisan hanyar da zaki bi domin ki ga kin raba Hibairu da zoben,
Ko da wasa kada kiyi yunkurin cewa za ki hallaka Nihla domin hakan zai iya kawo miki cikas
wajen mallakar zoben,.
Sannan dole ne mu kasance a cikin shiri domin tayi a cikin abokanan gabar mu akwai masu
muradun zoben.
Musamman abokiyar gaɓar ki sarauniya Abidatul-auliya,
Nan gaba zan sanar dake waɗansu muhimman abubuwa game da zoben.
Sa'adda boka Jadwar yazo nan azancen sa sai sarauniya Nuwairat ta cika matukar farin ciki
maral misaltuwa
Har bata san sa'adda murmushi mai taushi ya suɓuce mata ba,
Amma a bangaren sarki shazwan kuwa ya shiga tattaunawa tsakanin sa da gimbiya Hushriba
da sarkin bokaye Dargas akan hanyar da zasu ba wajen mallakar sarkin sadaukai a wannan
tafiya,
Haka dai tafiya taci gaba da wakana kwanaki banin kwanaki, Mako banin mako,
Sai a wuni cire ana tafiya batare an yada zango ba,
A iya tsawon wannan tafiya soyayya da shaƙuwa ta kara shiga tsakanin sarkin sadaukai Hibairu
da jaruma Nihla, sarauniya Abidatul-auliya da matsafi shubairu,
Sunaila da saurayi Hizmal,
Kuma ba a haɗu da waɗansu abubuwa masu cutar wa,
Koda yan fashi da darun sunane da miyagun dabbobi,
Domin tsananin yawa da kwarjinin tawagar kafin su haɗu da su suke cika wandon su da iska,
Kuma a wannan tafiya ne dukkan sarakunan suka samu nasarar bayyana bukatar su ta hanyar
kamun ƙafa da yaro Humair makaho
In da kusan dukan bukatun sarakunan ya dogara akan tafiya izuwa fadar Sarkin bokaye,
Sarki uslaim domin ceto yar sa gimbiya zarifa,
Jaruma Sunaila, Hushriba, sarauniya Abidatul-auliya da matsafi shubairu dake buƙatar su shine
mallakar tsumin tsafi domin samun waraka,
Aljani Marhutul-Azab kuwa domin ta ceto ruhikan kabilar su dake ajiye a cikin akwatin baƙin
ƙarfe dake hannun Sarkin bokaye.
Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas ya cigaba da jagorantar tawagar sarakuna,bokaye,jarumai
haɗe da matsafa domin halartar bikin gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA da za'a gudanar a
birnin madinatul-shaja'a,
Sai yazamana cewa ana tafiya dare da rana Babu sassauci da yake harka ce ta gawurtattun
matsafa cewa tafiyar da za'a iya a cikin kwana ashirin, an yi ta a cikin kwana shida kacal,
A ranar kwana na sha takwas ne da la'asar sakaliya aka iso kofar birnin madinatul-shaja'a
Nan fa kowa ya cika da matukar mamaki,
Abin da ya ba su mamakin shine yadda kofar shiga birnin madinatul-shaja'a takasance cike da
zaratan dakarun tsaro na jinsin mutum da aljan, ɗauke da miyagun makamai.
Saboda da kwarjinin su bazaka iya tantance dakarun mutum da aljan a cikin su ba,
Duk inda Mutum ya kalla daga saman kofar da katangun birnin dakarun birjik Babu adadi,
Nan take wani gabjejen kato mai tsawo da kwarjini tamkar toran Giwa ya dako da kafafun sa
izuwa inda suke.
A lokacin da sarki Baddadul-ulƙas ya fito daga cikin keken dokin sa,
Ya dube sa cikin ladabi kansa a sunkuya yace"marhaban da zuwa BIRNIN MAZAN JIYA ya
Dodon sarakai, hadari ma'anar duniya,
GOGA SHA YAƘI"gagarau uban kan garau,
Ka ci dubu sai ceto , ANNOBA DARI mai saukar da GOBARAR DAJI,
FARGABAR SADAUKAI,
Lokacin da badakaren yazo nan a kirarin sai sarki Baddadul-ulƙas ya sake jin izza gami da
ƙasaita ta ƙara shiga cikin ƙoƙon kan sa,
Har jikin sa na tsuma
Ya dubi badakaren yace"An gaisheka yakai
Himaru haƙiƙa ka cancanci kyauta mai tsoka,
Bayan na samu nasarar lashe gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA.
A wannan karon zaka samu adadin dinaren da baka taɓa samun kamar su ba,
Koda Gama faɗin hakan sai Baddadul-ulƙas ya yiwa wani badakare inkiya ta wutsiyar idanu.
Badakaren ya gabato da wata jakar fata,
Ya risina a gare shi,
Sarki ya umarce sa ya miƙa wa badakare Himaru ya karɓa ya buɗe jakar, aikuwa sai yayj arba
da dinare masu yawa a ciki,
Nan take ya sakarwa sarki Baddadul-ulƙas wani ƙeƙashasshan murmushi wanda babu abinda
ya ƙarawa fuskar sa face muni,
Kuma ya zube ƙasa ya