Showing 6001 words to 9000 words out of 30696 words
Chapter 3 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf
ta
farautar budurwa Nihla wanda ke tare dasu yaro Humair makaho,
---
Kamar yadda gimbiya Hushriba ta tsara haka al'amarin yaksance wato tun da duku-dukun
safiya fadar sarki shazwan ta cika ta batse da al'umma maza da mata yara da manya suka yi
cincirindo babu masaka tsinke,
Duk inda Mutum ya kalla babu abin da zai gani face kawunan bil'adama rututu,
Tamkar dandazon kiyasai, tsawon daƙiƙa Ɗari biyu da ɗoriya ana jiran fitowar sarki shazwan
tare jama'ar sa,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka jiyo bugun tambura da bushin algaita,
Sai aka hango sarki shazwan tare da bakuwar jaruma Hushriba da tawagar bokaye,
Nan take fadar ta rude da shewa da jinjina kuma kowa ya mike tsaye daga wajen zaman su
domin girmama ga sarki,
Sai da sarki tawagar sa suka zauna abisa kujerun su,
Bayan yan majalissa sun kammala kwasar gaisuwa,
Sai sarki shazwan ya mike tsaye daga kan karagar mulki ya fuskanci jama'a kuma fadar tayi tsit
tamkar mutuwa ta kawo ziyara
Sannan daga bisani ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace"Da farko ina yiwa dukkan
waɗanda suka hallara a wannan fada mai albarka barka da zuwa
Bayan haka kuma ina taya al'ummar kasa ta alhinin abinda yafaru damu na ibtila'in GOBARAR
DAJI,
Yaku jama'a ta kuyi sani cewa ina mai farin cikin sanar ɗaku cewa a yau ne zanyi gagarumar
tafiya domin samo maganin dazai kare wannan birni namu daga sharrin bayyanar SARKIN
SADAUKAI,
Sannan ina muku albishir dacewa bakuwar jaruma Hushriba zata baku wani muhimmin sirrin
tsafi dazai kare ku daga sharrin GOBARAR DAJI har izuwa lokacin da zamu dawo daga abin da
suka fita ne ma
Sa'adda sarki shazwan yazo nan a jawabin sai fadar ta sake rudewa da shewa a karo na biyu
kuma jama'a suka cika da matukar farin ciki maral misaltuwa.
Batare da bata lokaci sarki shazwan ya ɗora waziri Rufyan a matsayin halifan sa,
Bayan ya shiga izuwa gidan sarauta yayi bankwana da yar sa gimbiya sulairat,
Sai aka dunga aka fito izuwa wajen fada, batare da bata lokaci jaruma Hushriba ta buɗe bakin
ta takaranto waɗansu dalasiman tsafi,
Tsawon daƙiƙa goma, tana gama rufe bakin ta nan take wani irin haske kore ya bayyana a
wajen ya duka shiga jikkunnan jama'a,
Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa Ɗari ba ya shiga jikin duk wani mahaluki dake wajen,
Sannan haske ya dawo ya cure waje guda ya tashi izuwa sararin samaniya ya tsaya cak,
Sai gashi yana bayar da wani irin haske tamkar fitila,
Koda kammala hakan sai sarkin bokaye Dargas ya kwalla wa aljani Haulatul-infal,
Jim kadan sai ga sa ya bayyana a wajen ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa,
Cikin azama sarki shazwan ya hau kansa ya zauna,
Sarkin bokaye Dargas, gimbiya Hushriba, sarkin yaƙi tare da tawagar bokaye biyar suka yi koyi
dashi,
Cikin sadaukantaka aljani Haulatul-infal ya naɗa fuka-fukan sa ya luluƙa izuwa cikin gajimare,
Tun jama'a na hango su har yazmana sun ɓace ɓat tamkar basu taɓa wanzuwa,
Wannan shi ne yafaru da su sarki shazwan bayan su saurayi Hizmal sun samu nasarar shiga
gidan tsira,
Turƙashi ana wata sai ga wata, yanzu dai gashi manyan sarakuna
Sarki shazwan na birin zawatul-ifdal, sarki uslaim na birin Istanbul, sarauniya Abidatul-auliya ta
birnin Tehran, sarauniya Nuwairat ta birin Garul-mausul.
Da matsafan duniya sun bazama farautar yaro Humair makaho domin saduwa da SARKIN
SADAUKAI Hibairu,
Tabbas farautar wadannan abubuwa biyu dai dai yake da neman jaki mai ƙaho.
---
A birnin Rum dake yammacin duniya anyi wani gawurtaccen sarki da ake yiwa laƙabi da
Baddadul-ulƙas
Sarki Baddadul-ulƙas yakasance gabjejen kato mai kirar samudawan farko mutum mai tsananin
jarumtaka tagaban kwatance,
Ya bunƙasa a sihirin tsafi da da tarin dukiya,
Bokayen duniya da masu hasashe sun tabbatar dacewa a wannan ƙarni babu wani sarki mai da
ya kai sa tarin dukiya dangin lu'u lu'u da zinare gami da dabbobin ni'ima,
Baddadul-ulƙas ya samu nasarar tara wannan dukiya ne saboda wata gasar jarumtaka da ake
shirya wa a wani birni mai suna madinatul- shaja'a ma'ana BIRNIN MAZAN JIYA,
Fiye da sukaru goma sarki Baddadul-ulƙas ne ke cinye wannan gasa saboda jaruman da yake
kawo wa sun kasance hatsabibai a fagen fama,
Duk jarumin da labarin jarumtakar sa ya shahara sai sarki Baddadul-ulƙas ya mallake sa kodai
ta hanyar siyan sa da dukiya mai tarin yawa ko kuwa ta karfin tsiya,
Domin dai kawai ya saka sa a cikin gasar jarumtaka,
Duk sarkin da ya lashe gasar ana naɗa jarumin sa a matsayin GOGA SHA FAMA na shekara,
Wata rana sarki Baddadul-ulƙas na zaune a lambun shaƙatawar sa,
Sanye yake cikin shiga irin ta sarauta zaune abisa kujera ta ƙasaita gudanar da bincike bisa
halarar tsafin sa abisa madubin tsafin sa,
Kwatsam sai yaga wani al'amari da ya sanya shi farin ciki kuma ya dugunzuma hankalin sa
Abin da ya sanya sa farin cikin shine akwai wani boyayyen jarumi da ake kira da suna Hibairu
SARKIN SADAUKAI,
Wanda yake a halin yanzu babu wani gwarzon mayaki kamar sa,
Abin da ya dugunzuma hankalin sa kuwa shi ne ta wace hanya zai mallaki SARKIN SADAUKAI
Hibairu domin ya shiga gasar jarumtaka dashi,
Bayan cewa A halin yanzu Hibairu baya jin Yaren mutanen duniya baki ɗaya shi yana amfani ne
da wani yare na musamman,
Wani abu da ya fi dugunzuma hankalin sa shine haƙiƙa sauran Yan uwan sa sarakuna abokan
gaba zasu iya cin nasara akan sa matsawar su ka riga sa mallakar SARKIN SADAUKAI,
Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin sa sai ya sake zurfa fa izuwa cikin Kogin
tunani domin samun mafita,
Daga bisani ya samu mafitar, mafitar kuwa ita ce tun da a halin yanzu saura kwanaki ɗari biyu
SARKIN SADAUKAI ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIn sa sannan
ya fito daga dajin Baitul-shamshan to yazamana wajibi na yi ma za na ɗebi runduna ta domin na
je bakin dajin Baitul-shamshan na kafa sansani har izuwa lokacin da SARKIN SADAUKAI zai
bayyana
Fatana shi ne Hibairu ya samu nasarar cinye gasar jarumtaka ta duniya ya zamo GOGA SHA
FAMA,
Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin sai ya sake nutsawa bisa halarar tsafin sa
domin yakara samun haske akan al'amarin,
Yana cikin wannan bincike ne sai kawai ya a bushe da dariyar farin ciki maral misaltuwa tamkar
ba zai taɓa daina wa ba,
Bakomai ne yasan ya shi a cikin wannan farin ciki ba sai domin ya gano cewa HUBAIRU
yaksance ɗa a wajen babban maƙiyin sa Barde Shabbaru
Wanda a halin yanzu yake bauta a ƙarƙashin masarautar sa,
A salin Shabbaru mutumin ƙasar Misra ne kuma sarki Baddadul-ulƙas ya farauto sa ne bisa
yarjejeniyar cewa idan ya samu nasarar lashe gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA zai raba
dukiyar da ya samu ya basa kaso biyu kuma zai nada shi wazirin sa,
Bayan Barde Shabbaru ya samu nasarar cinye gasar ne, sarki Baddadul-ulƙas ya ci amanar sa,
Kuma yayi umarni a hallaka matar sa domin bincike ya tabbatar masa dacewa jaririn da zata
haifa ne zai kawo karshen mulkin sa,
Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas yaga wannan al'amari sai ya sake cika da mamaki,
Amma sai ya tambayi kansa a cikin ransa yana mai cewa ya a kayi matar Barde Shabbaru ta
rayu har ta haifi abinda ke cikin ta ?
Wani ɓangare a zuciyar sa kuma na cewa dashi yanzu ai zaka yi amfani da wannan dama ne
wajen jifar tsuntsun biyu da dutse ɗaya,
Wato zakayi amfani da Barde Shabbaru wajen mallakar SARKIN SADAUKAI,
Koda cewar bata ganin bil'adama ballantana ya tuna wane mahaifin sa,
To amma soyayyar uba da ɗa ba wasa ba ce tilas zata yi tasiri,
Zaka samu nasarar sarrafa Hibairu yadda kake so har ya kai ga lashe maka gasar jarumtaka ta
duniya,
Dazarar ka cimma burin ka sai ka hallaka su baki ɗaya da uba da ɗan na sa,
Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yazo dai dai nan a tunanin sa sai ya sake bushe da dariyar farin
ciki tamkar bazai daina ba.
Tun a daren wannan rana sarki Baddadul-ulƙas ya fara shirya rundunar mayakan sa ta haɗar da
dakarun bil'adama da aljanu haɗe da miyagun dabbobi
Alfijir na ketowa ya tashi hankalin rundunar sa ya durfafi dajin Baitul-shamshan,
Tirƙashi gaskiya masu iya magana da suka ce ba'a rabu da bukar ba an haifi habu,
Gashi duk waɗannan sarakuna da jarumai sun bazama farautar Hibairu tare da nasu
hukumomin,
Jaruma Husnaila, saurayi Hizmal da aljani Marhutul-Azab suna tare da yaro Humair wanda
shine kaɗai ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Sarauniya Nuwairat kuwa tana son kasance mace ta farko da Hibairu zai fara arba da ita domin
ya kamu da ƙaunar ta domin ta iya sarrafa sa yadda take so,
Yanzu kuma ga sarki Baddadul-ulƙas wanda ya tawo tare da Barde Shabbaru mahaifin Hibairu
SARKIN SADAUKAI,
Domin yayi amfani da mahaifin na sa wajen mallakar sa,
To masu saurare sai muje zuwa Littafin na gaba domin muji yadda zata kaya tsakanin
sarakunan duniya
Lokacin da tawagar sarki Baddadul-ulkas suka dauki hanyar da zata kai su izuwa dajin
Baitul-shamshan,domin da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI.
Sai suka wanzu suna tsala Azababban gudu a bisa dawakansu,
Daya ke tafiyar ta manyan sarakai ce da suka yi shura a halarar tsafi sai ya zamana cewa,
Tafiyar da za'a yi ta a cikin kwanaki shida sai ayi a kwana biyu,
Kasancewar masu iya magana na cewa sarkin yawa yafi Sarkin Karfi dai yazamana cewa komai
yawan abokan gaba da dakarun sumame,
Cikin abin da bai huce dakika ashirin ba ake hallaka su,
Wadansu ma cika wandonsu ke da iska domin tsira da rayukan su domin sun san cewa ko ba'a
gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza.
Haka dai wannan tawagar ta wanzu tana ratsa duwatsu koramu haɗe kwazazzabai gami
sarkakiyar bishiyoyi,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarki Baddadul-ulkas ya birnin Rum.
Gaskiyar masu iya Magana da suka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba.a je
ba.
Akwana a tashi sai gashi jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI ya cika kwanaki ɗari uku da
sittin da biyu,
Ma'ana saura kwanaki ɗaya kacal ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN
SHIRI,
A daren wannan rana ne aljani Marhutul-Azab ya sauke su saurayi Hizmal a bakin kofar
shiga dajin Baitul-shamshan,
Bayan ya sauka a turba ne sai kowa ya yunkura ya sauko ƙasa,
A sannan ne kowa yasha jinin jikin sa bisa yin arba da yadda farkon shiga dajin
Baitul-shamshan yakasance,
Duk da kasancewar a wannan lokaci dare ya tsala babu abinda kunne keji face kukan
tsuntsaye da kananan dabbobi,
Jaruma Husnaila ta katse shirun da wanzu ta hanyar buɗar baki tayi gyaran murya a karo na
farko tace"ya abokanan tafiya ta ahalin yanzu gashi mun iso dajin Baitul-shamshan domin
saduwa da jarumi Hibairu,
Kuma na ji a jikina cewa muna halitta ta farko da muka riga kowa zuwa wannan waje,
Shin yanzu mene ne abin yi?
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai ce kala'.
Sai daga bisani aljani Marhutul-Azab yayi''''' gyaran murya yace "yaku abokan tafiya kuyi sani
cewa wannan waje da muka iso shine waje mafi haɗari fiye da ko ina ,
Domin kuwa duka burikan sarakunan duniya, bokaye,da jarumai ya dogara da dajin
Baitul-shamshan,
Ku sani cewa a subahin gobe ne nan da Sa'a uku Hibairu SARKIN SADAUKAI zai fito daga
wannan daji na Baitul-shamshan,
Shawarar da zan ba mu ita ce mu dole mu kasance a cikin shirin ko ta kwana domin kowa ne
lokaci sauran abokan gaba na iya iso nan,
Idan bamu mai da hankali ba zai zamo abin nan da masu iya magana ke cewa
Kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai kowa yayi na'am da shawarar.
Nan take kowa ya zare takobin domin shirin ko ta kwana,
Aljani Marhutul-Azab ya zare wani zabgegen Gatari a gadon bayan sa,Hizmal goye da yaro
Humair makaho,sunaila da budurwar Nihla suka zare waɗansu takubba a damtsen su,
Kuma aljani Marhutul-Azab ya dunga rangadi yana kai komo a harabar wajen domin tabbatar
da cikekken tsaro,
Ana cikin wannan hali ne sunaila ta dubi budurwa Nihla tayi gyaran murya tace da ita"yake
wannan jaruma shin mene ne labarin rayuwar ki kuma mene ne dalilin daya sanya wannan
azzalumar sarauniya ke farautar rayuwar ki? .
Ko da jin wannan tambaya daga bakin sunaila sai idanun Nihla suka suka ciko da kwalla,
Har ta buɗe baki da nufin ta ba wa sunaila amsar tambayar sai kawai a ka ji wani gurnani
daga sararin samaniya,
Cikin hanzari kowa ya ɗaga kan sa izuwa sama domin ganin abin da zai wakana,
Nan take akayi arba da waɗansu halitta na sauka daga sararin samaniya,
Sannu a hankali halittun suka dunga sauko ƙasa,
Lokacin da suka sauka a turba sai aka fara kallon- kallo tsakanin su da su saurayi Hizmal,
Ba wasu ba ne halittun ba face aljani Haulatul-infal dauke da gimbiya Hushriba,sarki
shazwan,sarkin bokaye Dargas,da tawagar matsafa biyar,
Halitta ta biyu kuwa ba wata ba ce aljani Darmanu ibn kauƙas dauke da sa sarki uslaim da
boka ƙarzum da tawagar su
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma sunaila da yar uwar ta Hushriba,
Sarki sarki shazwan kuwa da saurayi Hizmal,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sa aljani Marhutul-Azab,
Gimbiya Hushriba ta taka da kafafun ta ta durfafi inda Sunaila ke tsaye yazmana tazarar dake
tsakanin su bata huce taku goma sannan taja ta tsaya,
Kana ta buɗi baki cikin matukar ƙiyayya tace"yake yar uwa ta kuma babbar abokiyar gaba ta
har abada kiyi sani cewa nayi matuƙar baƙin ciki da na gano cewa mahaifin mu ya sanar da ke
maganin da zai warkar dashi daga shirin da muka yi masa domin ki samu nasarar hawa Bisa
karagar mulkin kasar mu,
Gashi Ni da dan uwana yarima zufair har kin riga mu mallakar yaro Humair makaho wanda
shine kaɗai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Kuma kina tare da aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye inda anan
ne za'a ɗauko tsumin tsafi da mahaifan mu zai sha ya warke,
Duk da waɗannan nasarorin da kika samu Ina mai tabbatar miki dacewa sun tashi a banza
domin a yanzu batare da ɓata lokaci ba zan hallaka ki kuma na mallaki yaro Humair makaho da
taswirar fadar Sarkin bokaye,
Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai jaruma sunaila tayi guntun murmushi mai tattare
da takaici yace"kaicon ki yake yar uwa ta haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kike tunanin cewa
zaki samu nasara akai na kwatar yaro Humair tare mallakar taswirar fadar Sarkin bokaye,
Ki sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA basa taɓa haɗuwa a waje guda, Domin kuwa
keda ɗan uwan ki kuna kwaɗayin mulki ne domin ku zalunci talakawa,
Wanda akan dalilin hakan ku kayi yunkurin hallaka mahaifin mu, Ni kuwa ina so na warkar da
mahaifin mu ne daga sihirin da kuka yi masa domin na samu nasarar hawa Bisa karagar mulki
domin na gaji mulkin adalci irin na mahaifin mu,
Sannan da kike iƙirarin cewa za ki samu nasara akai na shin kin manta ne cewa a halin yanzu
ina ɗauke da dukkan sirrikan tsafin mahaifin mu,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hushriba ta cika da matukar baƙin ciki zuciyar ta
kama tafarfasa tamkar zata kone,
Abangaren sarki shazwan kuwa bayan ya kammala karewa saurayi Hizmal dake goye da yaro
Humair makaho kallo sai ya dube sa cikin matukar fushi yace "yakai Hizmal kayi sani cewa
haƙiƙa ka aikata mini laifi mafi munin gaske sanadiyyar tseratar da rayuwar yaro Humair
makaho da kayi wanda sanadin hakan ya jefa al'umma ta cikin gagarumar tashin hankali
sakamakon GOBARAR DAJI,
Ina mai tabbatar maka da cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne,