Showing 12001 words to 15000 words out of 30696 words

Chapter 5 - GOGA SHA FAMA Book by Mansur Usman Sufi .pdf

07 Aug 2025

608

nagaban kwatance tamkar waɗansu
ifritai,

Sai dai a wannan karon labari yasha bambam domin kuwa idan Sunaila ta kaiwa Hushriba hari
da takobi idan ta yanke ta sai ka wajen ya dare jini ya zuba,

Sai kaga ita ma Hushriba ta mayar da martanin,

Kafin cikar daƙiƙa hamsin sun yiwa juna raunuka fiye da goma kuma kowanne na zubar da jini,

Har jiri yana ɗibar su suna faɗuwa ƙasa amma saboda nacin tsiya sai su miƙe tsaye zumbur su
sake afkawa juna,

Kaji faɗan MAZAN JIYA masu tarwatsa maza a filin daga,

A bangaren sarki shazwan,boka Dargas da saurayi Hizmal kuwa,

Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi a wannan karon sai yazamana cewa dakyar saurayi Hizmal ke
iya kare hare haren da su ke kawo masa,

A wasu lokutan har faɗuwa ƙasa yake amma sai ya miƙe tsaye zumbur kuma bai taɓa yarda
yaro Humair makaho ya daɗo daga gadon bayan sa ba,

Haƙiƙa inda ace mutum ya tsaye a wajen lokacin da ake wannan artabu Dole ne ya jinjina wa
Hizmal ya tabbatar da cewa ya cika gwarzon sadaukai,

Amma a bangaren boka Jadwar da matsafi shubairu kuwa ba a cewa komai domin komai kallon
ƙurillar mutum bazai iya gane wane gwani a cikin artabun ba domin kowannen su yana yaƙin ne
cikin baƙin zafin nama tamkar jikin sa bai kasance na jini da tsoka ba,

Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas da rundunar mayakan sa suka ja daga suna masu kallon
fafatawar da ake yi tsakanin sarakuna bokaye da matsafa da suka kafa sansani a dajin
Baitul-shamshan,

Sai Baddadul-ulƙas ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki,

Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa wasikar mutuwa ya dubi wani hadimin sa
dake tsaye a hannun sa na dama yace dashi cikin kakkausar murya

"Yakai zawatu ban taɓa sanin cewa wadancan sarakuna, bokaye da matsafa da suka fafatawa
yaƙi su na da taɓin hankali ba sai a yau domin in ban da rashin tunani yanzu idan suka hallaka
kawunan su wane zai iya saduwa da SARKIN SADAUKAI Hibairu,

Da ace sun haɗa kansu kowa ya ajiye buƙatar sa a gefe sai kaga kowannen su ya samu nasara
dazarar an samu haɗin kai.

Jira nake yi su kammala kashe kawunan su sannan na ni kuma na mallaki Hibairu cikin ruwan
sanyi,

Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulkas sai hadimi zawatu ya jinjina kai yace
tabbas maganar ka haka take yakai sarkin sarakuna mai duniya,

Ana cikin wannan fafatawa ne kwatsam bazato babu tsammani sai a kaga Hibairu SARKIN
SADAUKAI ya Bayyana a bisa kan tsuntsun tsafin sa hannun sa riƙe da wani dogon mashi,

Abangaren hannun sa na dama budurwa Nihla ce zaune a bisa wani murgujejen zaki

Sauran tawagar dabbobi da aljanu na take masa baya,

Wani irin koren haske na fita daga jikin ZOBEN SHIRIn dake hannun sa,

Lokacin da duka ɓangarorin sarakuna, jarumai, bokaye,da matsafa suka yi arba da SARKIN
SADAUKAI Hibairu sai kowa ya tsaya cak da yakin da yake yi da abokin gwamin sa,

A kayi cirko cirko aka rasa wanda zai fara tunkarar sa yayi masa wata magana,

Ita kuwa sarauniya Nuwairat Sa'adda ta yi arba da budurwa Nihla tare da SARKIN SADAUKAI
sai takaici da baƙin ciki suka mamaye zuciyar ta domin kuwa,

Ta tabbatar dacewa bazata taɓa samun soyayyar Hibairu tun da har Nihla ta fara arba dashi
kuma a yadda alamu suka nuna sun kamu da soyayyar juna tun da gashi har ya ɗora ta a bisa
kan ɗaya daga cikin dabbobin sa,

Koda Nuwairat tazo dai dai nan a tunanin ta

Sai hawaye suka kwaranyo daga idanun ta ,

Kuma a sannanne tsananin kyawun diri da sura na jarumi Hibairu ya sake bayyana a gare ta,
nan take taji ta sake kamuwa da matukar begen sa,

Hibairu ya cigaba da bin jama'ar dake wajen da kallo yana mamakin yadda ake yi a kasa samu
halittu masu siffa irin tasa,

Wai shin dama akwai wata halitta mai irin sura ta a wannan duniya,

Amsar tambayar da Hibairu ya kasa bawa kan sa kenan,

Kawai daga bisani sai ya juya ya dubi budurwa Nihla da wani irin kallo mai ɗauke da tsnatsar so
da kauna,

Kuma ya buɗi baki da wata irin magana wacce shi kaɗai ce ke fahimtar abinda yake cewa,

Koda jin wannan batu daga bakin Hibairu, sai budurwa Nihla ta yiwa su saurayi Hizmal nuni da
su gaba to da yaro Humair makaho izuwa gare ta,

Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa jaruma sunaila da Hizmal goye da Humair suka taka
sannu a hankali suka durfafi inda SARKIN SADAUKAI ke tsaye,

Ko da ya rage saura kamar taku goma a tsakanin su

Sai suka ja suka tsaya Nihla ta sauko daga kan zakin da take akai,

Bayan Hizmal ya sauke yaro Humair daga gadon bayan sa sai taja hannun sa har izuwa daf da
inda SARKIN SADAUKAI yake,

Har a wannan lokaci namun dajin dake take wa Hibairu baya suna ta hargagi jira kawai suke a
basu umarni suka afkawa sarakunan,

Hibairu ya ƙurawa yaro Humair makaho idanu ko ƙiftawa baya yi,

A karo na farko yaji ya kamu da matukar tausayin sa bisa ganin cewa yakasance karamin yaro
kuma makaho wanda baya gani,

Nan take ya tuna sa'adda wani daga cikin halittun dake dajin Baitul-shamshan ya makan ce, ya
shaƙu matuka ainun da halittar gami da jin tausayin ta,

Nan take Hibairu yaji cewa a ransa tamakar wannan halitta ne ke tare da shi,

Hibairu ya sake buɗar baki a karo na biyu ya dubi Nihla yayi mata magana da Yaren sa,

Bisa mamaki caraf sai suka ji yaro Humair makaho ya mayar wa da Hibairu amsar maganar da
irin Yaren na sa,

Al'marin da yayi matukar bawa Hibairu mamaki kenan kuma ya ɗaure masa kai bisa makahon
Yaron na magana da irin Yaren,

Su kansu su jaruma sunaila sun cika da matukar mamakin Bisa jin yaro Humair makaho na
magana da Yaren Hibairu,

Bata de wani bata lokaci ba yaro Humair makaho ya zayyane wa SARKIN SADAUKAI Hibairu
dukkan abinda ke tafe dasu saurayi Hizmal izuwa gare sa dama bukatar da suke nema

Koda jin wannan batu daga bakin Yaro Humair sai Hibairu ya yi shiru yana mai dogon nazari,

Daga bisani ya dubi Nihla, sunaila da Hizmal sannan ya dawo da duban sa ga Humair makaho
yayi masa bayani abinda zai faɗa

Sannan Humair makaho ya juya ya dubi su sunaila yace

"Ya abokan tafiya ne kuyi sani cewa abinda sarkin sadaukai yace a cikin bayanin sa shine ya
amince da dukkanin bukatun ki kuma zai biya muku su,

Amma bisa sharadi guda ɗaya sharaɗin kuwa shine bazaku taɓa cutar da wata dabba ba,

Kuma zaku taimaka masa wajen kare martabar su da kuma zaku masa wajen yaƙar dukkanin
bil'adama dake doran ƙasa,

Koda jin wannan batu daga bakin Yaro Humair makaho sai hankalin kowa ya dugunzuma ainun,

Kuma cikin su ya ɗuri ruwa , tsawon daƙiƙa goma babu wanda ya ce ƙala a cikin su,

Sai daga bisani ne,

Jaruma sunaila tayi gyaran murya sannan tace"yakai Hizmal kayi sani cewa a halin yanzu ba
lokaci ne da zamu tilasta Hibairu ya janye ƙudirin sa na yakar bil'adama ba tare da shafe su
daga doran ƙasa ba,

Domin kada ka manta cewa akan hakan ya rayu, bai san cewa akai wasu bil'adama ba,

A can gaba za mu samu nasarar canza masa ɗabi'un sa ta hanyar Budurwa Nihla da a halin

Yanzu ya kamu da matukar kaunar ta,

Tare da yaro Humair makaho da shi kadai ne ke iya jin Yaren sa a halin yanzu,

Sannan wani abu da baka sani ba shine,

A lokacin da Hibairu ya fito daga dajin Baitul-shamshan na fara arba dashi naga ɗumbin tausayi
da jin kai a tattare da fuskar sa,

Wanda hakan ya tabbatar mini dacewa mahaifan sa sun kasance mutanen kirki masu adalci,

Haƙiƙa dole ne Hibairu ya kasance yana tare da wannan dabi'u kyawawa nasu domin kuwa
masu iya magana na cewa,

"kyan ɗa ya gaji uban sa

Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hizmal ya cika da farin ciki yace "yanzu zai mu ce
masa mun amince ko

Koda jin hakan sai Humair makaho ya juya ya dubi Sarkin sadaukai Hibairu yace "yan uwa na
sun amince da sharaɗin ka sannnan dukkanin wadancan mutane da ka gani,

Su ma sun zo gare ka ne domin bayyana maka nasu bukatun,

Kafin yaro Humair makaho ya gama rufe bakin sa sai kawai gani akayi a suri yaro Humair anyi
sama dashi,

Sai ga zaune a daf da keken dokin da sarki Baddadul-ulƙas ke zaune,

Sarki Baddadul-ulƙas ya bushe da dariya mugun ta,

Sannan bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa yace

"ya ku masu jiran gawar shanu kuyi sani ceqa a halin yanzu gashi na mallaki yaro Humair,

Tare wani abu da gaba ɗayan ku baku dashi,

Wanda yazama dole saboda shi

HIBAIRU ya zamo mai biyayya a gare Ni,

Sa'adda sarkin sadaukai Hibairu yaga cewa sarki Baddadul-ulƙas ya kwace yaro Humair
makaho,

Sai ya fusata ainun kawai sai ya zare kwarin dake gadon bayan sa,

Ya ciro kibiya ɗaya daga cikin kwanson ya saka a cikin bakan sa ya taɓe take ya harba kibiyar
izuwa kan dakarun sarki Baddadul-ulƙas,

Kibiyar ta tafi cikin matsanancin gudu a iska,. Ya yin da ta sauka akan dakarun take wata irin
guguwar Wuta ta bayyana

Kafin dakarun suyi wani yunkuri wutar ta hallaka dakaru dubu biyu cikin abin da bai gaza daƙiƙa
Ɗari ba sun ƙone ƙurmus,

Al'amarin daya fusata sarki Baddadul-ulƙas kenan ya takarkare ya kwarara wawan ihu irin na
hamshakan sarakai da suka saba gwagwarmaya da maza a filin daga,

Ya nuna yaro Humair makaho da ɗan yatsan sa na hagu,

Take wadansu irin sarkokin tsafi suka ɗaure sa tamau hannu da ƙasa a jikin keken dokin Da
yake akan sa

Kawai sai ya dako tsalle daga kan keken dokin sa tamkar an janye sa kungiya, yana tafiya a
cikin iska ya durfafi inda SARKIN SADAUKAI

Yana saman ya saman ya zare wata sharbebiyar adda a damtsen sa,

Koda ganin hakan sai Hibairu ya zunguri cikin tsuntsun tsafin sa da kafafun sa biyu,

Take tsuntsun ya kaɗa fuka -fukan ya durfafi Sarki Baddadul-ulƙas domin tarar juna yana aman
wuta daga bakin sa,

***

Lokacin da SARKIN SADAUKAI Hibairu da da sarki Baddadul-ulƙas suka ruga izuwa kan juna
suna ihu da kururuwa mai firgitar wa,

Lokacin da suka haɗu da juna sai suka kacame da azababban yaƙi mai matukar kwarjini, muni
ban tsoro da tashin hankali,

Ga dukkan mai kallo.

Wohoho haƙiƙa idan BABBAR GIWA ta fito filin fama babu wanda ke tunkarar ta face GOGA
SHA FAMA da ya saba gwagwarmaya a DUNIYAR MAYAKA

Tabbas faɗa yan MAZAN JIYA na JARUMAN DUNIYA ne,

Ana fara wannan artabu ne fa kallo ya koma sama,

Domin du ka bangarorin sarakuna bokaye da matsafan da suka hallara a wajen sun zuba idanu
domin su ga abinda zai wakana,

Duk sa'adda sarkin sadaukai ya kaiwa sarki Baddadul-ulƙas hari da kashin sa idan
Baddadul-ulƙas ya zillewa harin sai kaga duk inda mashin ya sauka a ƙasa wajen ya rufta idan
bishiya ce ko duwatsu sai su kama da wuta

Idan kuwa makaman nasu suka haɗu da juna sai kaga wata irin tartsatsin wuta yana tashi haɗe
da walkiya,

Nan fa dawakai suka firgice suka dunga jefar da mahayan su suna nausawa izuwa cikin daji
saboda firgita,

Sa'adda da halittun dake bayan Hibairu suka ga cewa shugaban su ya garƙame da azababban
yaƙi da sarki Baddadul-ulƙas sai kawai su kayi kukan kura suka afkawa dakarun sarki
Baddadul-ulƙas,

Nan fa waje ya sake rincaɓewa da ɗauki ba daɗi,

Nan fa halittun suka zamo tamkar guguwar annoba a tsakiyar dakarun,

Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa hamsin ba gawarwakin dakarun sun watsu a ko ina,

Waɗansu kuma na faɗa wa izuwa cikin wannan rami ka dake faruwa sakamakon nutsewar
makamin Sarkin sadaukai,

Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas yaga cewa an shafe tsawon Sa'a Arba'in ana wannan fafatawa
batare da ya samu nasarar lakutar koda jikin sarkin sadaukai da takobin sa ba,

Sai takaici ya turnuƙe sa ya faɗa izuwa kogin tunani,

Abu na farko da ya faɗo masa arai shine mene ne dalilin daya sanya ya kasa samun nasara
akan Hibairu,bayan cewa a kaf jinsin sarakunan duniya babu sarki mai karfin damtse kamar sa
gami da karfin sihirin tsafi,

Sannan idan har a ka cigaba da wannan artabu miyagun halittun dake fafatawa yaƙi da dakarun
sa zasu iya samun nasarar hallaka Barde Shabbaru mahaifin Hibairu

Don haka dole ya samu mafita

Koda kammala tunanin hakan sai sarki Baddadul-ulƙas ya yi yuf ya kaiwa HUBAIRU wani
nagartaccen sara da kafaɗa,

Cikin zafin nama Hibairu ya zille tare da mayar da martani Cikin zafin nama,

Bisa Sa'a sai gashi ya soke Baddadul-ulƙas a cinyarsa saboda karfin sukar sai mashin ya fasa
sulken yaƙin dake jikin sa ya jini yayi tsayuwa

Baddadul-ulƙas yayi taga taga zai fadi amma sai ya turje,

Kawai sai ya shafi wani gurun tsafi a damtsen sa kawai sai riƙiɗa izuwa wata baƙar guguwa,
guguwar ta tashi izuwa sama ta nufi keken dokin dake tsakiyar dakarun yaƙi,

Daga bisani guguwa ta bayyana a daf da inda SARKIN SADAUKAI ke tsaye sai ta riƙida izuwa
sarki Baddadul-ulƙas tare da wani dattijo ya ɗora kaifin takobin sa akan wuyan dattijon yana mai
yi Hibairu murmushin mugunta,

Sa'adda HIBAIRU yayi arba da Dattijon sai ya tsaya cak yana mai ƙura masa idanu ko ƙiftawa
baya yi,

Bakomai yagani ba face yadda kamannin sa dana dattijon suka zo iri ɗaya sai tamakar an tsaga
ƙara,

Nan take yayi tausayin Dattijon yakama sa bisa ganin yadda aka ɗaure dattijon da sarkokin tsafi
kuma Baddadul-ulƙas ya ɗora kaifin takobin sa akan wuyan sa,

Abangaren su jaruma sunaila,sarki uslaim,sarki shazwan, sarauniya Abidatul-auliya, Nuwairat
da su aljani Marhutul-Azab kuwa,

Sa'adda da suka yi arba da wannan dattijo mai matukar kama da sarkin sadaukai sai suka cika
da ɗumbin al'ajabi da mamaki,

Su na masu cewa a cikin ran su an ya kuwa wannan dattijo bashi ne mahaifin Hibairu ba lallai
tsananin kamannin surar su yayi yawa!

Idan kuwa har haka ne tabbas wannan baƙon sarki da ya bayyana zai iya samun nasarar
mallakar HUBAIRU cikin ruwan sanyi

Shin wane ne wannan sarki, menene alaƙar sa da Hibairu?

Amsar tambayoyin da su ka kasa ba wa kansu kenan,

Kawai su ka zuba idanu suna kallon abin da zai wakana

Kallo ne ya wakana tsakanin sarkin sadaukai da dattijo na tsawon daƙiƙa talatin daga bisani sai
hawaye suka zubo daga idanuwan dattijon yana mai sakarwa Hibairu murmushi mai taushi

Bisa mamaki HUBAIRU bai san sa'adda da ya mayar masa da martanin murmushin ba,

Sarki Baddadul-ulƙas ya katse shirun daya wanzu ta hanyar buɗar baki cikin kakkausar murya
mai kama da haniniyar doki ya dubi dattijon a lokacin da kara rikon wuƙar dake kan maƙogaron
sa yace

"Ya kai Barde Shabbaru bin sha'asanul-haibar kayi sani cewa ban kawo ka nan ba sai domin na
nuna maka ɗan ka na cikin ka tsawon shekaru ashirin kenan yau

Wato Hibairu nasan cewa ko ba'ayi maka bayanin komai ba

A halin yanzu gaji a jikin ka cewa HUBAIRU ɗan ka ne wanda matar ka layizat ta haifa wannan
daji mai ban al'ajabi,

Ka sani cewa ban fito dakai daga kurkukun Darul-barzak ba sai domin na yan taka daga
KANGIN BAUTA a karkashi tsahon shekaru masu yawa,

Amma fa hakan bazai tabbata ba face ka amince ka biya mini wata buƙata guda biyu

Kamar haka.

Da farko Wajibi ne ka janyo hankalin ɗan ka HUBAIRU akan lallai ya amince ya zai shiga gasar
jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,

Idan yayi nasara ne kawai zai sanya na yan taku kai da ɗan ka daga KANGIN BAUTA a
karkashi na,

Sannan tilas ne ka sanya Hibairu ya zamo mai biyayya a gareni,

Yakai Shabbaru kayi sani cewa matsawar ka cika mini waɗannan to bayani ya zo karshe,

Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulƙas sai fuskar Shabbaru ta canza daga
walwala izuwa ɓacin rai,

Ya daga kai sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai ɗauke da karfin zuciya yace"ya kai
Baddadul-ulƙas kayi cewa nafi kowa sanin wane ne kai,

Kai mutum ne maci amana kuma mayaudari nasan cewa ko da na cika maka waɗannan
sharudda ko ban cika ba baza ka taɓa bari na da rai ba,

Kuka kuma tilas ne sai ka ci amanar ta shin ka manta da zaluncin da kayi mini,

Ka raba ni da kasar mu, yan uwana, sannan ka zo ka raba ni da mata ta da na fi kauna fiye da
komai,

Ai har abada ba'a taɓa canzawa tuwo suna kuma mai hali ba ya canza halin Sa,

Koda jin wannan batu daga bakin Barde Shabbaru sai sarki Baddadul-ulƙas ya bushe da dariyar
mugunta,

Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa wasikar mutuwa yace"shin yanzu ka zaɓi ka
rasa rayuwar ka da ɗan ka guda ɗaya jal ai ko babu komai kaso zuri'ar ka su ci gaba da wanzu
a doran ƙasa,

Kada ka manta cewa HUBAIRU shi kadai ne ya rage maka a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login