Showing 24001 words to 27000 words out of 35201 words
da hayaniyar jin daɗi ta kauraye hall ɗin hakan yasa seda
aka ɗauki 3mins kafin gurin yayi tsit Adam ya cigaba da cewa"sekuma abu na biyu kuma muna
me farincikin sanar daku an kammala komai na babban branch ɗin pharmacy na Namijin duniya
wanda za'ah cigaba da haɗa magunguna ranar asabar za'ah buɗesa in Allah yakaimu akwai a
cikinku akwai wasu tsiraren mutane da muka ɗaukesu wanda matakin karatunsu ne yakaisu ba
zaɓenmu ba zasu koma can da aiki ga sunayensu kamar haka zamu fara faɗowa tundaka
sabbin canje-canje da aka samu ciki kuwa harda sakatarorinmu da aka canza su zamu fara
kira".
tafi gurin yaƙara ɗauka da hayaniya.
Daɗa gyarawa Sakatariya Feenerh tayi ta kalli ƙawarta Zaby daketa ƙara shafa powder danta
siye zuciyar Namijin duniya cikin kishi tace"mezan gani haka Zuby kike wani shafa powder
sekace me ƙoƙarin yimun snatching".
cikin muryar riƙaƙun ƴan bariki Zuby tayi dariyar da iya kacinta fatar baki tace"haba ƙawata inani
ina yiwa babbar aminiyata snatching ai Namijin duniya ni yafi ƙarfina wane ni dashi ai seku
manyanmu inadai gyarawa ne domin ba'ah ga ƙawar Mrs Namijin duniya ba kamar wata
mahaukaciya ba saboda banaso a rainamun ke ". cikin jin daɗin kalaman Zuby tace"da wasa nike miki dama ƙawata nasan bazaki taɓa cin
amanata ba aiko gwara ki gyara dakyau kinyi tinani mekyau kodon waccan berar da tin ɗazu
suke kallonmu inkin gama ki bani nayi na gyara domin nasan ni za'ah fara kira da alama Oga fa
kamar yafara kamuwa da soyayyata domin a sati biyunnan ni yike sawa inyimasa komai na
office".
sosai ran Zuby yaɓaci da aminiyartata amma dake ƴar duniya ce seta dake kamar bataji komai
ba tace"masha Allah kice aiki dai yafara kyau ".
"sosaima kuwa".
nanta cigaba da abinda take tana gamawa ta miƙawa Feenerh powder tashiga shafawa .
Tin fara shafa powdernsu Feenerh Hauwah ta lura dariya shiga yi hakan yasa Inteesar kallonta
cikin ƙasa da murya tace"lafiya kiketa dariya".
"wani abu ne yabani dariya mutanenki nagani anata aikin wahalar da aka saba kallasu can ita
da aminiyar nan tata".
taƙarasa zancenta tare da nunawa Inteesar su Feenerh dakyar tayi control ɗin dariyar data kusa
suɓucemata taita dariya ƙasa-ƙasa seda tayi me isarta ɗaga idonnan da zatayi sukayi 4 eyes
da Namijin duniya yana kallonta saurin janye lulu eyes ɗinta tayi domin gabanta dataji ya buga
da ƙarfi tashiga karanto duk addu'o'in da suka zo bakinta tace da Hauwah gaskiya iska na
wahalar dame kayan kara mutum yayita abu a inda ba'ah san yanayiba".
"wallahi kuwa ni yanzu dariyama suke bani".
"nima haka dukkansu fa yadda na fahimta sonsa sukeyi amma da alamu ɗaya ke ha'intar ɗaya
inda zasu dena saka wa'innan kayan da suke fitomusu da shegen ƙirjinnan nasu me kama da
lawashin albasa daya fimusu alheri ƙila ya kulasu ni banga abun so a wannan mutumi ba da
mata suke zubar da ajinsu da darajarsu ta ɗiya mace suke cemasa suna sonsa yana ɗisgasu
amma dukda haka suyita liƙemasa yana yabasu ba".
"hmm wallahi kina bani dariya da ƙirjinnan nasu me kama da silifas da kike cewa mutuniyas ƙila
fa harda ke a cikin wa'inda zasu koma pharmacy ɗin Namijin duniya ".
"hmm kema kinsan yadda mutuminnan ya tsaneni baze taɓa sakawa dani ba wallahi kima
dena wannan tinanin ƙila dai kiga masu goga powder a gaba-gaba".
Hauwah zatayi magana kenan sukaji muryar Adam a laudspeaker yana cewa"zamu fara da
sakatariyar Namijin duniya mesuna Aisha Muhammad Ahmad ".
dammm gaban Inreesar yabayar sakamakon jin full name ɗinta dataji Adam ya anbata basu
ƙara tabbatar da abinda sukaji taji muryar Adam a laudspeaker yace"Malama Inteesar idan tana
kusa zamu so ganinta a step tazo ta gabatar da kanta".
ƙululu taji cikinta yabayar cikin yanayin damuwa tace"Hauwah anyako ba wata kitumurmurar
suka shiryamunba kuwa saboda mutanen nan basu da mutunci".
"ki kwantar da hankalinki Besty insha Allahh bakomai kedai kiyi addu'ar duk data zo bakinki
kinji insha Allahu ba abinda zefaru se alkhairi basu isa suyimiki abinda Allah bemiki ba".
jiki a sanyaye tace "toh".
jiki a sanyaye ta miƙe tafara tafiya yayinda zuciyarta tashiga bugawa da sauri-sauri!!!!!!!!!
Votes and comments
Plz share to others
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_ ƴar Mutanen Gwarzo.*_ *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
_Wannan shafin kyauta ne ga masoyan MAN OF THE WORLD a duk inda kuke Real eeshow
na alfahari daku._
*BOOK 1*
*PAGES* 2️⃣3️⃣➡️2️⃣4️⃣
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka take tafiya domin idanun mutanen gurin
gabaki ɗaya na kanta jiki a sanyaye taƙarasa step ɗin kanta a ƙasa ɓangaren Namijin duniya ko
tunda ta fito ya kafeta da mayun idanunsa dake mugun bata tsoro harta tsaya a step ganin
yadda tayi ƙasa da kanta ne yasa Namijin duniya taɓe baki a zuciyarsa yace"wai ita ala dole
ace tanada kunya da tarbiyya".
a hankali ta ɗaga golden eyes ɗinta dake masifar tafiya da zukatan mutane taɗan saci kallon
inda yike caraf suka haɗa ido gani tayi ya taɓe baki saurin janye idanunta tayi daga garesa
zungurarsa Ahmad yayi yace"bakaga yadda mutuniyarka tayi bane dubeta a haka kamar
mutuniyar kirki se rashin tarbiyya kala-kala a cikinta kamar kuɗin cizo batasan munkusa zuwa
ƙarshen game ɗinba".
wani killer smile ya saki nan Adam ya cigaba da kiran sauran mutane ba sunan Feenerh ko
ɗaya sede canzamata muƙami da akayi takoma sakatariyar Adam .
Ɓangaren Sakatariya Feenerh da Zuby ko mutuwar zaune sukayi ganin abubuwan da suke
faruwa sosai ran Feenerh yakai ƙololuwar ɓaci tana huci ta zunguri Zuby da kamar zatayi kuka
tace"nidai na rasa mena tsarewa wannan tsinanniyar yarinyar ne da bata da wani burin daya
wuce taga bayana ƴar kujerar da nike taƙama da itama seda ta rabani da ita a tinanina da
wannan kujerar yakamata nayi amfani gurin shawo kansa shine saboda ita tambaɗaɗɗiya ce
tayimun haka dole wannan karon ta ɗanɗana kuɗarta domin sena nunamata na rigata zuwa
duniya ko ta halin ƙaƙa senaga bayanta tsinanniya ƴar gidan masu dattin hula ƴar matsiyata ko
nawane a shirye nike dana kashe matsawar zanga bayan wannan ƴar iska yarinyar".
"amma gaskiya kinyi sake wallahi Feenerh banyi zaton abun yayi ƙamari har haka ba aida nina
ɗauki matakin dakaina amma ko yanzu bamu makaraba itaɗin banza duka yarinyar nawa take
dako da ƙissa baki koreta ba saboda sakarci irin naki yanzu gashinan ta nunamiki ɗan hakin
daka raina shike tsokalemaka ido domin koke kinƙi ɗaukar mataki akan wannan ƴar iskar
yarinyar doleni naɗauka dan bazan taɓa barin wannan cin kashin data yimana ya tafi a banza
ba wallahi".
taƙarasa zancenta cike da tsananin fusata hakan yasa Feenerh jin wani mugun sanyi a
zuciyarta dan ita a tinaninta Zuby baƙaramin sonta take ba ganin yadda hankalin Zuby yayi
mugun tashi hakan yasa Feenerh cike da kulawa da sigar lallashi tace"ki kwantar da hankalinki
ƙawata muje gida muyi shawara da Ummah muga ta inda za'ah ɓullowa al'amarin". wani shu'umin murmushi taƙara yi tare da cewa"kidena ma tinanin zanƙi ɗaukar mataki akan
duk wani abu da yike niyyar yimun shamaki da samun farincikina muradin zuciyata wanda
nikejin kamar danni akayisa a shirye nike dana kauda duk wani abu dake niyyar nisantani dashi
ko ƙanwata Zarah ce tayimun haka wallahi senasa anɓatarmun da ita daka doron ƙasa domin a
yadda nike jina yanzu haka na ƙuna bana tsoron ƙaure akan Namijin duniya banƙi inɓata da
kowa ba".
cikin sigar kwarewa da harkar bariki Zuby ta ware ƙananun idanunta da suke kamar ankwantali
duma tace"ƙawata kina nufin kenan zaki iya rabuwa dani".
"gaskiya Zuby baki da hankali kefa nacemiki ko iyayenane sena raba gari dasu bare wata ke tin
yaushe da zanmanta dake infara sabuwar rayuwa matsawar zan mallaki Man of the world da
dukiyarsa".
sosai maganganun Feenerh suka ɓatawa Zuby rai dake ƴar bariki ce seta nunamata kamar
bataji komai ba ta ƙaƙalo wani munafikin murmushi wanda iyakacinsa fatar bakinta tace"maida
wuƙar aminiyata nima da wasa nike miki aini ko da baki kika nuna abu kinaso bazan taɓa son
abunba ko nawane abun ni me iya barmiki ce kinji tawan". murmushin jindaɗi Feenerh tayi tace"godiya nike babbar aminiyata ".
wani shu'umin murmushi Zuby tayi wanda ita kaɗai tasan ma'anarsa suka cigaba da hira.
Ana tashi daga taron Inteesar ta nufi gurin Hauwah jiki a sanyaye tace"anyako Besty ba wani
abun suke shirya ba kuwa mutuminnan ba alheri a tare dashi inaji a jikina kamar wata muguntar
suka shiryamun".
"banaso Besty kina munanawa mutum zato banajin sun baki wannan muƙamin dansu tozar taki
face sedan kin cancanta ki kwantar da hankalinki tawan ki cigaba da addu'ah ba wanda ya isa
yayimaka abinda Allah bemaka ba".
"hakane kam Bestyna nagode sosai da kulawarki gareni Allah yabarmu tare".
"Ameen ya Allah muyi mu tafi mu shirya kar Uncle Zaid yazo yayita jiranmu".
"toh aiko kinsan shi sede ya jiramu badai mu jirasa ba bara naje na tambayesa koda abinda zan
masa".
"ok hakan yanada kyau nidai nariga da munyi sallama da Oga Ahmad bara injiraki a can".
taƙarasa zancenta ta maimata nuni da wata ƴar rumfar shaƙawata.
"toh".
nan kowaccensu ta tafi.
Bakinta ɗauke da sallama tashiga office ɗin jin shiru se ƙarar a.c daketa aiki yasata ɗagowa
tashiga bin ko ina na office ɗin da kallo har lulu eyes ɗinta ya sauka kan wani tanƙamemen
hofonsa sanye da wata haɗaɗɗiyar black arman suit sumar kansa tayi luf-luf da ita se ɗaukar
ido take ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya bazato taji murmushin ya suɓucemata a hankali tashiga
tafiya harta isa gurin ɗage tashiga yi ko hannunta zekai kan hoton dake hoton yaɗanyi sama
sosai yasa dukda ɗagen datayi hannunta bekai ba shiru tayi harta juya sekuma ta fasa ta nufi
gurin wata haɗaɗɗiyar resting chair ɗinsa me tayoyi ta turata daidai saitin photon ta tuɓe
takalminta ta taka tsayinta yayi daidai da tanƙamemen photon lallausan hannunta tasa tashafa
hoton cikin wani irin yanayin da batasan kona menene ba takai bakinta daidai saitin bakinsa
tasakarmasa wani hort kiss tasaki wani sansanyan murmushi tare da ƙara kai lallausan
hannunta kan photon daidai saitin hancinsa tace"sturborn kaidai baka da girma ko kaɗan sena
jikinka".
taƙarasa zancenta tana mai ƙara sakarmasa wani hort kiss zata janye bakinta daga jikin photon
kenan taji lion voice ɗinsa ta daki dodon kunnenta yace"inkin gama kiss ɗin kya iya sakkowa
anga ɗan sangiri saurayi ba kamar ƙolon saurayinki ba ".
a ruɗe ta juya jiki na rawa zata sakko hakan yasa kujerar da take ta tafi zuuu zata faɗi sauri rife
golden eyes ɗinta tayi domin tagama sadaƙarwa da zata faɗi tajita a jikin mutum ƙamshin
turarensa ne ya tabbatar mata da shine a hankali tashiga buɗe oily eyes ɗinta ta saukesu kan
kyakyawar fuskarsa kallon-kallo suka shiga yi na tsawon 5mins yayinda iskar damuna tashiga
kaɗawa hakan yasa gabaki ɗayansu suka tsunduma cikin duniyar tinani buɗo ƙofar da akayi ne
yasasu dawowa daga duniyar tinanin da suka shiga ganinsu a haka yasa ran Meemah yayi
mugun ɓaci .
Ɓangaren Namijin duniya ko kallo ɗaya yayiwa Meemah data banko musu ƙofa ya ɗauke kansa
jin Inteesar nata mutsu-mutsun ya sauketa yasashi ƙara matseta a faffaɗan ƙirjinsa gefe guda
kuma cike da mugunta ya takemata ƙafa da haɗaɗɗen takalminsa sosai taji azabar yadda ya
takemata ƙafa amma hakan be hanata mamakin abinda yikemata ba a zuciyarta tace"anyako
wannan mutumin kanshi ɗaya kuwa".
lokaci ɗaya bugun zuciyarsa su yaƙaru saboda yadda ƙirjinsu ya haɗe guri ɗaya tana cikin
zancen zuci taji muryarsa cikin wani shegen salo da batasan yanada shiba yace"sannu My
Angel kiriƙa yimun a hankali da jikinki kinsan banaso kina wahalarmun da kanki saboda keɗin
rayuwata ce badon nazo a lokacin daya dace ba daya kike tinanin za'ayi". yaƙarasa zancensa tare da kashemata sexy eyes ɗinsa baki buɗe Inteesar ke kallonsa fuskar
ɗauke da tsananin mamaki ganin yadda tayine yasashi gyaramata zama a ƙirjinsa yashiga
caring ɗinta kamar kwai yayinda gefe guda kuma yaketa mitsitsikemata ƙafa ɓangaren
Inteesar ko ba abinda take se al'ajabin abinda yike mata.
Ganin ƙofa a buɗe bakowa ne yasa Zuby cewa"yauwa Feenerh mushiga kawai ki basa haƙuri in
wani abun kika yimasa yayi haƙuri ya maida ke muƙamunki ina ganin hakan zefi kuma a ganina
wannan shine stage na farko da yakamata mubi domin se muna haɗawa da ƙissa Allah ma ya
temakemu wannan makirar yarinyar bata nan komai zezomana da sauƙi". "mu wuce kawai gobe na shawo kwalliya speacial domin bashi haƙuri".
cike da zaƙuwa Zuby tace"a'ah muje yanzu".
"toh tunda kin matsa mushiga ɗin".
Feenerh taƙarasa zancenta suna shigewa cikin office ɗin sandarewa suka yi sakamakon ganin
Namijin duniya rungume da Inteesar yana caring ɗinta itakuma tayi luf a faffaɗan ƙirjinsa kamar
wata ƴar baby yayinda daka ƙasa kuma yake ƙara mutsitsike mata ƙafa.
Ɓangaren Namijin duniya ko yi yayi kamar besan da mutane a gurin ba hakan baƙaramun ƙara
ɓatawa su Meemah da sukayi mutuwar tsaye rai yayi ba shiko ɗan gogan cigaba yayi da caring
ɗin abarsa kamar wata matarsa saurin yin baya su Feenerh sukayi cikin tsananin ɓacin rai
yayinda Meemah ma tabi bayansu zuciyarta na tafarfasa ta buga musu ƙofa da ƙarfi .
Mutsu-mutsu takeyi cike da tsananin ɓacin ran abinda yayimata a gaban mutane yayinda wasu
hawaye suka shiga sintiri a kumatunta a zuciyarta tashiga tinanin wanne irin kallo mutanen nan
zasu yimata ƙin sakinta yayi hakan yasa ta ƙara lafewa a ƙirjinsa wani ƙasaitaccen murmushi ya
saki ganin yadda ta sakankance taƙara lafewa a jikinsa hakan yasa cike da mugunta ya
hankaɗata ta faɗi ƙasa jikake ƙass ƙarar kashin ƙafarta yayi ƙara yayinda lokaci ɗaya ƙafar ta
kaure da zugi ga tsamin da tayi cikin yanayi na jin zafi tace"ochhhhhh".
murmushin mugunta a gadarance yace"matsamun da wannan ƙazamun jikin naki dayasha
taɓawar ƴan bariki kin wani lefe jikin mutum kina yin pretending kamar wata ta Allah bayan
kuma a zuci ba haka bane kina wani kakkare jiki kamar wata uwar mata mezan gani abu kamar
kwan kurciya". yaƙarasa zancensa tare da ƙara shan mur kamar bashi yayi maganar ba ya wani ƙara haɗe rai
ɗaga idonnan da zeyi sukayi ido huɗu da!!!!!!!!!
*Sorry my fans kuyi haƙurin da rashin typing yafaru ne saboda wani uzuri daya tasomun me
ƙarfi amma yanzu na dawo normal zamu fara wasa kullum insha Allahu zaku fara samu update
sau ɗaya ko biyu a rana matsawar zaku bani haɗin kai ta hanyar suburbuɗamun comments and
votes zaku sha mamaki domin yanzu zan tsoma hannu cikin labarin dan shimfiɗa mukayi
yanzu zamu fara wasan.*
Votes and Comments
Plz share to others
_*Daga Alƙalamu *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
*BOOK 1*
*PAGES* 2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣
Dasu Ahmad da sun daɗe suna kallon ikon Allah abinka da miskilin mutum se ya wani
basar kamar besan abinda ke faruwa ba ya wuce ya zauna a kujerar office ɗinsa yashiga duba
takardun dake aje akan table ɗinsa jawo system ɗinsa dake gefe guda yashiga operating
juyawa su Adam sukayi cikin sauri ɗinta ɓangaren Inteesar ko kasa motsi tayi saboda tsananin
azabar da ƙafar kemata lokaci ɗaya hawaye suka wankemata fuska cikin office ɗin ba abinda
kakeji se shashekar kukanta ɓangaren Namijin duniya ko jin kukanta yike har cikin ransa ya
rasa dalili a zahiri seka ɗauka wani mahimmin aiki yikeyi a system ɗinsa a cikin zuciyarsa ko jin
wani irin abu yakeji dangane da kukan da takeyi .
Jiyayi duk be kyautaba abinda yayimata zuciyarsa ce tashiga rayamasa idan Rahamansa wani
yayiwa haka zeji daɗi zuciyarsa ce tabashi amsa da"a'ah ".
wata zuciyar ce tace"to ita meyasa kake yimata haka?".
wata zuciyar ce tace"ka rabu da ita ai rashin kunyarta ce ta jamata cigaba da aikinka kawai".
yana cikin wannan zancen zucin yaji sallamar su Ahmad ba tare daya ɗago ya kallesu ba
yace"wa'alakumus salam".
yaƙarasa amsa musu tare da duba wani file dake gabansa kamar da gaske ya wani ƙara haɗe
rai dan karsu yimasa magana ganin haka yasa suma basu bi takansa ba suka nufi inda Inteesar
take cikin nuna basu ga duk abunda yafaru ba Adam yace"subahanallah Aishatu meya samu
ƙafar taki haka naga ta kumbura Abdallah meyafaru da ita haka". ba tare daya ɗago daga danna system ɗin da yike ba kamar wanda yake wani abu me
mahimmanci yace"ka tambayeta man nima yadda kaganta haka na ganta".
saurin juyawa Adam yayi gun Inteesar cike da takaicin amsar rainin hankalin da abokinsu ya
bashi karo na farko a rayuwarsu da sukaji tausayinta cikin tausayin halin da take ciki Adam
yace"meyasameki Aishatu ".
cikin siriryar muryarta dake nuni da tasha kuka tace"gurɗewa nayi Sir".
taƙarasa zancenta kuka na niyyar cin ƙarfinta yayinda takejin wata muguwar tsanarsa na ratsa
zuciyarta ganin shi yajimata ciwo amma shi ko ajikinsa sosai tabasu tausayi cikin sigar lallashi
Ahmad yace"sannu kinji bara na kira Hauwah ta temakamiki semu kaiki asibiti naga ƙafar ta
kumbura sosai". cikin sanyin murya tace"toh Sir nagode".
"bakomai".
nan yashiga dialing number Hauwah bugu ɗaya ta ɗauka cikin girmamawa tace"salamu
Alaikum".
"wa'alaiki salam ki sameni a office ɗin Abdallah".
"toh sir".
nan ya kashe ko minti goma ba'ah yiba Hauwah tayi knocking buɗemata Adam yayi haɗe da
cewa"temaka mata kisamun ita a mota mukaita asibiti naga ƙafar ƙara kumbura takeyi".
yaƙarasa zancensa yana mata nuni da inda Inteesar