Showing 3001 words to 6000 words out of 35201 words
har ya ƙaraso inda yike Namijin duniya kasan
cewa yayi zurfi a cikin tinani domin ko sallamar da Ahmad yayi be amsaba taɓashi Ahmad yayi
da sauri ya ɗago ya kalli Ahmad dafashi Ahmad yayi tare da cewa"Abdallah meyasa koda
yaushe kakeson ɓoyemana damuwarka ne tin muna yara baka da abokan da suka fimu inbaka
faɗamana damuwarkaba wazaka faɗawa".
sauke numfashi Namijin duniya yayi tare da cewa"bakomai Ahmad inda dashi dana faɗamaka".
"ohk to meyasa kasa na kori mutum haka kurum ba dalili dafa wannan aikin sukecin abincifa
shida iyalansa".
sauke numfashi Namijin duniya yayi tare da labartawa Ahmad komai da Inteesar tayi masa
murmushi Ahmad yayi tare da cewa "haba My Man aiba haka yakamata kayiba ai kan yarinyar
yakamata ka huce ".
kallonsa namijin duniya yayi alamun yana san sanin mezaiyi mata murmushi Ahmad yayi tare
dakai bakinsa saitin kunnensa yayimasa raɗa wata magana wadda nima kaina Real eeshow
bansan meya faɗamasa ba lokaci ɗaya namijin duniya yasaki wani murmushin gefan baki tare
da furta "amma Ahmad kana ganin ba raini a wannan shawarar taka kuwa ?". "wanne irin raini My Man ai wannance kawai hanyar da zaka rama kenan a ganina".
shiru Namijin duniya yayi kafin daga bisani ya saki wani ƙayataccen murmushi saboda se yanzu
yagane abinda Ahmad yike nufi cikin jindaɗin shawarar Ahmad ya furta "shiyasa nike
ƙara ƙaunarka saboda kai akwai kawo light".
dariya su dukansu sukayi sai a sannan namijin duniya yaɗanji ranshi yayi sanyi nan suka koma
hirar bikin Adam daga bisani Ahmad ya ɗaga waya yayi sai kuma ya aje naga yayi murmushi
Babu ɓata loƙaci sakataren Ahmad yashigo shida wani ɗan dattijon mutum abayansa.
Zama sukayi a ƙasan carpet cikin girnamawa sakataren Ahmad yace"ranka yadaɗe gashinan".
"ohk we can go".
nan yafice yabarsu da Abbah daketa ƴan kalle-kalle saboda tinda yike bai taɓa ganin
tsararren guri ba kamar wannanba saboda falon yagaji da haɗuwa komai na more rayuwa
akwaisa a falon gefe guda kuma tanƙama-tanƙaman photunan Namijin duniyane a kowanne
bango na falon dakyar ya ɗauke idanunsa daga kalle kalle yamaida ƙasa cikin rawar jiki ya gaishesu Ahmad
ne kawai ya amsa namijin duniya kuwa kallo ɗaya yayi masa yakauda kai ya taɓe baki a
zuciyarsa yace"dama wannan ne mahaifin dirty girl ɗinnan yarinyar nan mara tarbiyya dubeshi
wani iri". yana cikin wannan zancen zucin yaji Ahmad yace "dama abinda yasa kaga
na sallameka agurin aiki babu laifin dakayi dama wata sabuwar dokace tafito mun dena ɗaukar
tsofaffi da wa'inda basuda kwalin degree amma idan kana da wanda zaka kawo mai kwalin
degree tom ka kawo sai yamaye gurbinka ko mace ko namiji amma bada Comphany ɗina za ai
aikiba na Namijin duniya ne zasu ɗaukesa".
Cikin farin ciki yaɗago ya kallesa yana washe baki Abbah yayi tare da cewa"to ranka yadaɗe
Allah yasaka da alkhairi nagode Allah yaƙara arziƙi amma banida wani namiji dayayi wannan
karatun sai dai mace zan iya kawota?"
Murmushi Ahmad yayi tare da cewa "ai babu komai Baba kakawota inhar tana da degree".
shiru Abbah yayi daga bisani yace"ammafa wani hanzari ba guduba ita da ƙawarta suke komai
Alhaji Zannah ne yayiwa yarinyar tawa komai be kamata na samarwa tawaba itakuma tashi nayi
musu hakaba koba komai be taɓa ware tawaba abawa tashin kawai se a kyale Inteesar ɗin".
damm ƙirjin Namijin duniya yabayar daketa shan ƙanshi jiyayi kamar yasamusu baki amma
saboda tsabar girman kai da izza bazaka gane yaji wani abuba yacigaba da operating ɗin
phone ɗinsa jiyayi Ahmad yace"a'ah Babah ka kawosu kawai gabaki ɗayansu a kawosu sesuyi
interview in Allah yakaimu gobe". Wani farincikine ya lulluɓe Abbah nan yadungi zabga godiya yatafi yana tafe yana murna ganin
aikinsa yadawo bai suɓucemasa ba.
Murmushi namijin duniya yayi wanda shikaɗai yasan ma'anarsa yabawa Ahmad hannu suka
kashe Ahmad yace"to tazo hannu saura plan ɗinmu na biyu ita harta isa taja da ɗaya daga cikin
ɗan cliff ɗinmu Tripple A saura shawarar Adam shima aji tabakinsa daganan semuyi
tsare-tsaren biki". "toh tashi muje".
nansuka tafi yayinda ran Namijin duniya yayi fess ji yike kamar yajawo gobe tayi.
Washe gari tin safe Namijin duniya ya shirya ko breakfast be tsaya yayiba yafito yana ɗaura
agogon rolex a hannunsa yaga Abbih ɗinsa zaune a dining gefensa Mummy zaune ƙarasawa
yayi gurin Abbih ɗinsa yayin ɗinsa sannan yace"Abbihna ka tashi lafiya".
"lafiya ƙlau Babana harka sakko da wuri haka".
"eh sauri nike zanyi wani abu".
"okay yanaga yau kana cikin farincikiko ko suruka aka yimun".
wani smiling Namijin duniya yayi wanda ko Abbih ɗinsa rabon dayaga yayisa harya manta yaji
yace"Abbih the weather is so nice today".
murmushi Abbih yayi nanya gaida Mummy data tsaya kallonsu sannan yayimusu sallama yafita
ba tare dayaci komaiba.
Yana isa ya wuce Office ɗinsa direct koda yashiga yaja kujera yazauna tare da lumshe ido yayi
shiru yashiga dunuyar tinani jiyayi anbuɗe ƙofa
sakatariya ce tashigo sai faman karai-raye karai-raye take da jiki dukda ƙamas take ga shegun
riga da wando data saka sun matseta rabin breast ɗinta da suka zube kamar silifas a waje
tasha heavy makeup sai taunar cingam take kamar karuwa baki ta saki ganinsa zaune akan
kujera har yazo gani tayi shikaɗai se murmushin gefan baki yake lokaci ɗaya taƙara cigaba da
karairayarta dan ita a tinaninta ita yikeyiwa taƙarasa gabanshu cikin yauƙi da iyayi irin na ƴan
bariki tace"yallabai
barka da hut meza'ah kawo maka bayan coffee".
taƙaraasa zancenta tana ƙuresa da kallo
Gyara zamansa yayi ba tare daya kalleta ba a daƙile yace"yau bana buƙatar komai".
yafaɗa sai kallonta yaƙarasa zancensa tare da ƙara sakin wani murmushin
Ganin yanamata murmushi ne saitaga kamar da ita yake tako ƙara gyara gaban rigarta tana
tsaida shafaffun nonuwanta wa'inda suka kwanta kamar lawashin albasa tana tunkarosa gani
yayi tana matsowa gabdashi dan-danan yatattaro ɓacin rai yaɗorawa fuskarsa yahaɗe rai
murtuke kamar bashine yagama murmushi yanzuba tana ganin haka tayi saurin wayencewa
taƙarasa cikin freidge taɗauko cups tatafi dasu zata wanke tana fita taja dogon numfashi "yau
danayi gisgirin taɓa oga dana shiga uku ashe murmushin danaga yanayi badani yakeba to
dawa yike danni dai bazan taɓa bari Oga ya airi wataba koda zan rasa zanin ɗaurawa wallahi
dole inƙara zuwa gurin boka na bayan tsauni yayimun maganinshi yau naso na gwadamasa
irin tawa soyayyar".
take faɗa aranta nanta wuce tazauna tana maida numfashi ta ɗauki wayarta tashiga dialing
number ƙawarta bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa!!!!!
*Idan naga ruwan comments da votes zakuga cigaban kullum ta Allah har sau biyu a rana idan
ban ganiba daka wannan na dena wannan book ɗin.*
Votes and Comments
Plz share sisters and brothers to others fisabilillah
_*Daga Alƙalamun ƴa *THE WORLD MAN*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 0️⃣5️⃣➡️0️⃣6️⃣
"Lafiya irin wannan kira haka da sassafiyar nan kota warune".
"hmm ai dole na kiraki hankalina ne Zuby yayi mugun tashi".
"faɗamun mana Feenah".
"yau ina zuwa na tadda Oga harya zo yanata murmushi da farko na zata dani yike Allah yasoni
da harnaje in rungumesa nayi saurin wayancewa saboda kingako yadda ya haɗe rai lokaci ɗaya
da tini nasamu matsala bakiji yadda naji ba saboda tsoro nike Allah yasa dai ba wata ya haɗu
da itaba dan wallahi Zuby bazan taɓa jurar ganin Abdallah da wata ba ko zan rasa zanin
ɗaurawa sena nisantashi da mata matsawar bani ze aura ba".
"kece Feenah tin yaushe nike cemiki koda muna yin amfani da maganin Bokanan to dole kema
ki riƙa nunamasa kefa kina sonsa akwai wasu kaya danaga Hajiya Riga ta ɗakko ƴan
gumamane masu kyau anjuma kizo muje gidan ki zaɓa zakisha mamakin yadda ze riƙa kallonki
kamar wani magnet haka ze riƙa binki da ido saboda zasusa sha'awarsa ta motsa kinga
dakanan kekuma sekisan yadda zakiyi har yayi sex dake dakanan zamu kamashi a hannu ta
hanyar cemasa kinada ciki kamar yadda yike popular once bazeso ace zamu tonamasa asiriba
duniya tasani kinga semuyi amfani da wannan damar muce masa sede ya aureki inba hakaba
mu tona masa asiri".
"wow gaskiya ƙawata kinyi dogon tinani sosai yanzu zan cigaba da nunamasa inasonsa dukda
nasan ya gane hmmm inyazo hannu ze gane kurensa dan yadda yabamu wahala semun
fanshe".
"ai dole yagane kurensa Allah yasa karki samu duniya ki manta dani danke ɗan tsakoce samu
kaƙi dangi kina samun abun duniya zaki yimun ƴan ta waye".
"haba Zuby aina dena yimiki haka ai anzama ɗaya tare dake zamuci duniyarmu a tsinke ko
banza a riƙa nunomu a mujallu".
"toh ƙawata bara na tashi tunda kin tasheni ".
"toh dan Allah da kinjemun gurin bokan danni banga alamun aikinnan yanayiba ƙinji ta
bakinsa".
"aiko kema kince wani abu bara na shirya senaje gurin wani Bokan danaga su Mum ɗina suna
zuwa aikinsa kamar yankan wuƙa haka yike ammafa sekin kawo wani abu".
"kema dai ƙawata kinsan da wannan Bokan kikasa mukaita kashe kuɗi gurin wannan da aikinsa
bayayi bara inyimiki transfer kiyi sauri dan Allah".
"toh aikeɗince ƙawata bakya sakin kuɗi sosai tayayako zankaiki gurin wannan da manyan
mutane ke zuwa shiyasama ban sanar dakeba".
"kinsan dai ko nawane zan iya kashewa matsawar Namijin duniya ze aureni a riƙa kirana ta Mrs
Namijin duniya ai zan bada ko nawane yanzu bara nafara turamiki idan bazasu isaba ki kirani".
"toh ina jiranki dan inyi maza indawo".
"toh".
nansukayi sallama ta gyara zamanta ta cigaba da haɗa files ɗin da zata shigarwa da Namijin
duniya.
Ɓangaren Zuby ko tana kashe waya ta tintsire da dariya mahaifiyarta dake kusa da itace ta
kalleta alamun dariyar metake tsagaitawa da dariya Zuby tayi tare da cewa"yanzu karyar zata
turon da kuɗi Mum semuje gurin bokannan da kikeso muje ita inbanda itama tinkiyace ta ina
zan bari inaji ina gani ta auri Namijin duniya bayan nina fara nunamata shi a rayuwarta
tasameni ina sakatariyata tasa aka koreni a tinaninta kyaleta zanyi to wallahi yanzune ko
zatasan wutsiyar raƙumi tayi nisa da ƙasa zan nunamata na rigata zuwa duniya koya kikace
Mum".
washe baki Mum tayi tare da cewa"aiko yanzu zanzo inkira Hajiya Mansura ta shirya muje
ayimiki aikinnan dama kuɗine sukai tsaiko to yanzu Allah ya kawo na banza bara naje na wanki
bayan tukunya a ɗaura a leda seki kaimata a matsayin maganin sede taga anayi Namijin duniya
mijinkine ke kaɗai Zubyna". "yauwa Mum".
nan Mum takira Hajiya Mansura tasanarmata suka cigaba da harkokinsu.
Zaune take akan kujera tana wanke-wanke Khadijat na ɗaurayemata Abbah yashigo
fangan-fangan ya wuce ɗakin Uwar Gwarama zaune yasameta tana ƙullin magungunan mata
zama yayi kusa da ita tare da cewa"yaufa yakamata suje yarannan shine nace bara
insanarmiki". "toh kayimata magana ammafa albashin gabaki ɗaya namune kasansu da baƙin hali kar wani
lokacin ace sun faɗi".
"toh".
nanya fita kallo ɗaya yayimusu ya kauda kai tare da cewa"kee".
cikin ɓarin jiki Inteesar ta miƙe dantasan da ita Abbah yike cikin ladabi taƙarasa inda yike ta
duƙa tare da cewa"gani Abbah".
"ki shirya yanzu kutafi keda Hauwa kuje ma'aikatar Namijin duniya zakuyi interview yike kome
saura kuma ki nuna baƙin halin naki a canma".
gaban Inteesar ne yayi mummanan faɗuwa jin sunan da Abbah yafaɗa dakyar ta saita
nutsuwarta cikin sanyin jiki tace"toh Abbah angode Allah yasaka da alkhairi".
jin muryar Uwar Gwarama tayi akanta tace"bar wani saurin godiya munafuka Malam baka
faɗamata ni za'ah riƙa kawowa kuɗin bane".
taƙarasa zancenta tare da jifan Abbah da wani banzan kallon daya hautsinamasa ƴan hanji cikin
rawar murya yace "ayi haƙuri ai bankai ga sanar da ita bane".
"ka gama munafuncinka".
suna wannan zancen wata mata tashigo tashigo gidan da sauri Uwar Gwarama na ganinta
tace"Hassatu badai Jummalar bace kikaga ta wuceba".
"ita ce kuwa yanzunnan tashiga gidanta".
"to bara naje yau koni ko ita wallahi".
nanta wuce ta tafi tana isa gidan Jummala sukayi kaciɓus a zaure zata fita saurin riƙota Uwar
Gwarama tayi cikin masifa tace"wallahi sekin bani kuɗina ina dalili ina ɗan mafari tunkan inhau
ruwan cikinki ki bani kuɗina".
"kiyi haƙuri idan nasamu zan aikomiki dasu inzo inyimiki godiya".
"wuce muje cikin gidan kome kike dashi kibani na daidai kuɗina".
nanta tasa ƙeyar Jummai suka shiga ta buɗemata ƙofa ganin akwati uku a ɗakin yasa Uwar
Gwarama ta ɗauka tare da cewa"naɗauki wa'innan dukda nasan kuɗina basukai wannanba
dama akwai ɗan tala dayace inhaɗamasa akwati zeyi aure idan na haɗamishi se inbaki sauran
canjinki". zaro ido Jummai tayi tace"ki rufamun asiri Uwar Gwarama kayan Nura ne ya siyo ze fara haɗa
lefe".
"ko kayan waye naɗauka ɗin".
nanta ɗauka ta tafi abinta.
Tin fitowarsu Inteesar taga yanayin Hauwa'uh kamar mara lafiya gashi tayi shiru cikin kulawa
Inteesar tace"Hauwa'uh lafiyarki kuwa naga duk jikinki yayi sanyi kamar wadda wani abun ke
damunta".
"hmm Inteesar tinani nikeyi saboda Comphany ɗin da zamufa na Namijin duniya ne bakya
tinanin idan yaganmufa inajin tsoron abinda zemikine".
tsaki Inteesar tayi saboda ita harta manta da abinda yafaru tsakaninsu tace"hmm halinki yana
bani mamaki Hauwa'uh mufa sukayiwa laifi ba mumuka musuba bana taɓa regreting ɗin abinda
nayimasa kuma ko yanzu yakuma yimana wani abun wallahi sena rama be isa yayimana
abinda Allah bemana ba irin kune marasa kishin kansu da se a takasu su kyale". suna wannan zancen suka ƙaraso titi suka tsaya jiran napep basu daɗe da tsayuwaba suka
samu adaidaita suka hau suka tafi.
Suna sauka Inteesar taji gabanta yayi mummunan faɗuwa dakyar ta tattaro sauran nutsuwar
data ragemata da jarumta ta dake suka shiga inda akeyiwa mutane interview suka zauna.
Namijin duniya dake zaune a Office ɗinsa yana ganinsu Inteesar ne yasaki wani ƙasaitaccen
murmushi me cike da ma'anoni kala-kala yace"yarinya kin shigo hannu zakisan wanene Namijin
duniya zaki tantwncemun waye me ƙazamun hannu cikin ni dake waye mara tarbiyya cikin ni
dake". ya miƙe yafita bin bayansa sakatariya tayi tana tinanin ina Ogan nata zeje gani tayi sunyi hanyar
inda akeyiwa mutane interview mamakine yakamata tasan ogannata baya zuwa irin wa'innan
guraren bata ƙara tsinkewa da al'amarinba seda taga Ahmad da Adam suma tsaye bayansu da
sakatariyansu suma tana wannan mamakin har suka ƙarasa inda su Adam suke cikin
girmamawa aka shiga gaida Namijin duniya cikin takun isa suka jera Tripple Apple suka jera
kallo ɗaya Namijin duniya yayiwa su Inteesar ya ɗauke kai kamar be gansuba sunzo dafda su
Inteesar ganin mutane hadda tsofaffi nata duƙawa har ƙasa suna gaidasu kamar zasuyi sujjada
sukuma sun wani ɗauke kai ko amsawa basayi hakan baƙaramun ɓata ran Inteesar yayiba taja
tsaki karaf a kunnen Namijin duniya dake side ɗinta suna haɗa ido ta taɓe baki cikin ƙasa da
murya tace"mara tarbiyya kawai da rashin sanin darajar ɗan adam".
baƙaramun ɓaci ran Namijin duniya yaƙara yi da Inteesar ba be nuna yaji komaiba har suka
shiga theater da za'ah fara interview ɗin suka zauna lokaci ɗaya idanunsa dake cikin baƙin
glass suka canza kala fuskarnan taƙara haɗewa kamar hadarin kaka aka fara kiran mutane
suna shigowa.
Se yamma liƙis sannan akayi kiran sunan Hauwa'uh aka kira na Inteesar a tare suka shiga
theater suna shiga sun zauna kenan su Namijin duniya suka miƙe cikin gadara Ahmad
yace"muntashi gobe kuzo da wuri ayimuku Muh'd ɗauki sunansu gobe dasu zamu fara".
"toh ranka shidaɗe".
nansuka wuce suka barsu nan sosai ran Inteesar ya ɓaci domin wa'inda sukazo
bayan-bayansuma ammusu amma su saboda rainin hankali sukacemusu sun tashi Hauwa'uh
ce ta faɗawa Muh'd sunansu sannan suka tafi rai ɓace.
Zaune suke a falo suna hirarsu Ahmad yace"My Man kadena damun kanka kan wannan Babe
ɗin domin tarigada ta shigo hannu yanzu zata gane kurenta".
buɗe idonsa yayi yasaki murmushin gefan baki a zuciyarsa yace"zan koyamiki hankalin da har
abada bazaki sake yiwa wani makamancin abinda kikayimunba ".
dariya Adam yayi tare da cewa"akan wannan Babe ɗin nafara ganin Namijin duniya yafara
tinani dolene muyi maganinta ta yadda sunansa taji seta suma".
"wallahi kuwa ai yanzu zata fara gane kurenta".
nansukaita hirarsu Namijin duniya ya miƙe ya nufi pridge yaɗauki bottle water yashiga bedroom
yana zuwa yazauna gefan haɗaɗen italian bed ɗinsa yasa hannu yajawo loka dake kusa sa
gadon yaɗauki ledar drugs ɗinsa yazauna sannan ya ɓaɓɓala yasha ya mayar loka ya kwanta
tare da lumshe ido yashiga tinanin wani mugun tausayin kansa ne yakamasa lokaci ɗaya wasu
hawaye masu zafi suka silalomasa yasa hanky ɗinsa ya share yanajin wani irin nauyi a
zuciyarsa idan ya tino da irin ƙaddarar dake tare dashi tashi yayi yashiga toilet ɗinsa ya ɗauro
alwala yashiga yin nafila yana kaiwa Allah kukansa kan Allah ya yayemasa lalurar dake
damunsa.
Washe gari tin bakwai su Inteesar sukaje Comphany ɗin Namijin duniya amma har yamma
ba'ah yimusuba sedaka baya sannan aka yiwa Hauwa'uh Inteesar na shiga suka miƙe Adam
ya kalleta tare da cewa"Madam muntashi sede gobe ki dawo da wuri".
ko kallonshi Inteesar batayiba cikin ɓacin rai tace"Hauwa'uh mutafi".
"toh mungode ranka shidaɗe".
Hauwa'uh batayi aune ba se ganin Inteesar tayi fuuu tayi waje kamar zata tashi sama
kallon-kallon suka shigayi Ahmad yace"saura step two da alama wannan ya amsu".
"amma Ahmad baka ganin a zuciya irin ta wannan yarinyar zata iya ƙin zuwa gobe".
"hmm bazataƙi zuwaba saboda ninacemaka wannan Adam saboda da wannan aikin zasu
dogara kagako dolenta tazo".
"hakane amma wannan mugune yasan kan tsiyar ".
namijin duniya dai becemusu komaiba nan suka tafi.
A bakin titi Hauwa'uh tasamu Inteesar tsaye murmushi Hauwa'uh tayi ganin