Showing 9001 words to 12000 words out of 35201 words
fita tadda shi sukayi tsaye gaisar dashi sukayi sannan suka
hau motar suka nufi Comphany Namijin duniya dalilin traffic da suka samu basu suka isa ba se
wuraren 10 yana saukesu sukayi sallama suka nufi cikin ma'aikatar a compound ɗin gurin suka
rabu kowa ya nufi gurin aikinsa.
Tana isa ƙofar da sakatariya take zaune taji mararta tashiga tsunkunamata cikin dakiya da
dauriya ta buɗe ƙofar haɗa ido sukayi da sakatariya daketa shan ƙamshi tana ganin Inteesar ta
haɗe rai tsaki Inteesar tayi tare da wucewa fuuu danna ƙofar tayi ta buɗe shiga tayi kanta a
ƙasa tace"Salamu Alaikum". ba tare daya amsa sallamartaba ya ɗago sexy eyes ɗinsa da sukayi kamar na mejin bacci ya
zubamata cikin gadara da isa yace"yakamata kisan gurin aiki ba gurin nanaye bane da zaki riƙa
hawa motar wani ƙato yana kawokiba sannan dama irin wannan lokaci yakamata cleaner yazo
yayi aikinsa?". sosai ciwon mararta ke ƙara ƙaruwa cikin sanyin jikin da ita kanta batasan tana dashi ba
tace"kayi haƙuri traffic muka samu ne".
a gadarance yace"traffic ba uzuri bane da kin fito da wuri traffic ɗin ze tsaidake ne dan haka
wannan ba uzuri bane dama ke ba albashi ɗaya zan riƙa biyanki da cleaners ba su dubu
hamsin ne ke kuma dubu ashirin na zari kuɗin makarar da kikayi zan baki dubu sha shida
gobema kinga bazaki ƙara bari ki makara". yana ƙarasa faɗar haka ya miƙe ya fita tashi tayi dakyar saboda ciwon yafara cin ƙarfinta
tashiga share gurin dukda taga alamar anyi shara ta goge tana cikin goge wata haɗaɗɗiyar farar
kujera fara tass da ita ta miƙe kenan taji tana jin jiri saurin zama tayi kan kujerar tana maida
numfashi bazato taji anbuɗe ƙofa saurin miƙewa tayi ganin Namijin duniya waigawar nan da
zatayi taga duk tayi staining ɗin inda ta zauna da jini!!!!!!!
*Daka wannan update ɗin zaku jini shiru saboda zamu fara exam bani zan koma rubutuba se
18/1/2022 dan Allah ku tayani share dan masu karatu su sani ngd.*
Votes and Comments
Plz share to others fisabilillah
_*Daga Alƙalamun ƴ *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 0️⃣9️⃣➡️1️⃣0️⃣
Cikin matsanancin tashin hankali tayi saurin komawa ta zauna lokaci ɗaya zufa yashiga
ketomata a zuciyarta tace"nashiga ukuna ni Aishatu na ɓatawa wannan jarababben mutumin
kujera yazanyi wayyo Allah na Allah ka temakeni karya gani Allah kaɗaine yasan irin hukuncin
dazemun wayyo Allah na haka nanma ya alah cika da wannan masifaffen mutumin bare na
ɓatamasa farar kujerarsa Allah kaɗai yasan irin muzantani dazeyi Allah ka temakeni nashiga
uku".
tana cikin zancen zucinnan ɗaga idonnan da zatayi caraf suka haɗa ido da Namijin duniya yana
jifanta da wani
irin wulaƙantaccen kallo me cike da zallar ƙyama da ƙasƙanci Step biyu zuwa uku ya taka zuwa
inda take kafin ya tsaya tare da harɗe hannuwansa aƙirji yayinda sexy eyes ɗinsa suka kaɗa
sukayi jawur dasu saboda tsananin ɓacin rai se huci yike kamar wani mayunwacin zaki ya tsaya
a gabanta .
Cikin lion voice ɗinsa wadda taƙara tsorata Inteesar yace"How dare You ?Waya baki izinin
zama akujerata ke wacece da har kika samu damar zama akan kujerar da nike zama da
wannan ƙazamun jikin naki wanda ba lallai banema yataɓa ganin ruwabama ko kina tunanin
wannan wajen zama ƙasƙantattun mutanene irinkine duk ki wuce sauran chairs ɗin office
ɗinnan ki rasa wadda zaki zauna se privet chair ɗina ".
yaƙarasa maganarsa cikin ɗan ɗaga murya Kasa furta komai tayi se ƙasa da tayi da kanta wani
irin matsananciyar kunyarsa na shiganta dukda begani ba amma jitake kamar ƙasa ta tsage ta
shige dan kunya shin taya zata iya tashi wannan mutumin ya ganta ahaka" Ya rabbi kada ka
bari wannan bawa naka ya muzantani ". tafaɗa a ƙasan ranta shiko Namijin duniya ganin tayi banza dashi yasashi ƙara hassala gani
yike wani salon iskancin taƙara tsiromasa dashi hakan yasa yasaki wani guntun tsuka cikin
ɓacin rai ya bugamata wata razananniyar tsawa wadda har seda ƴan cikinta suka kaɗa lokaci
ɗaya jikinta yahau rawa batasan lokacin data miƙeba .
A hankali sexy eyes ɗinsa suka sauka akan kujeran data ɓatamasa Wara shu'uman idanunsa
yayi yana kallon wajen wani irin baƙin cikinta ne yazo ya tokaremata maƙoshi dakyar ya iya
haɗiye wani ƙullutun baƙin ciki daya tsayamasa lokaci ɗaya yaji yaƙarajin wata muguwar
tsanarta na ƙara ƙaruwa a cikin zuciyarsa lokaci ɗaya kanshi yafara juyawa ga wata irin
tsananin kyamarta dake damunsa ya buɗe baki da niyyar yimata magana kenan idanunsa ya
sauka akanta .
Takurewa Inteesar tayi ajikin kujeran jikinta yashiga rawa saman goshinta da hancinta yafara
fitar da zufa tamkar babu a.c a office ɗin kanta ta fara juyawa tana shura ƙafarta cikin tsananin
azaban ciwon da cikinta ke mata a take idanunta suka shiga tsiyayar da hawaye ga jikinta dake
karkarwa tamkar mazari cikin yanayin ficewar hayyaci ta janye hijabin dake jikinta tare da
tasani ba ta dafe ƙasan maranta tana kuka.
Da sauri ya rintse idanunsa sakamakon ganin yanda saman breast ɗin ta suka bayyana ta
saman doguwar rigar jikinta da sauri yaja baya tare da rintse sexy eyes ɗinsa dukda bawani
abu dayaji a jikinsa kome ya tuna kuma yayi saurin buɗe wa yana kallon yanda hawaye ke
ambaliya a idanunta kamar wani famfo dakyar ya saita kansa jiyayi a zuciyarta tabashi tausayi
amma dake ya iya wanke allonsa bazaka ganeba saboda ƙara shan kunu daya ƙarayi cikin
muryar zaratan maza yace"keeeeh".
tsabar firgita tafara ja baya yana binta har suka isa inda ta fara mofewa luuuu ta tafi zata faɗi
hakan yasa cikin zafin nama yasa hannu ya jawota bazato ta faɗo jikinsa hakan yabawa
ɗankwalinta damar saɓulewa ƙasa yalwataccen gashinta ya sauka a gadon bayanta bazato
sukaji tsawa ƙara shigewa tayi jikinsa ta inda ƙirjinsu ya haɗe dana juna gam .
Ɓangaren Namijin duniya ko ba'ah cewa komai saboda ya shagala da kallon zara-zaran eye
lashes ɗinta da suka kwanta sukayi luf dasu yanayin iskar da akeyine yasa yalwataccen
gashinta kaɗawa ya rifemata fuska bazato taji lallausan hannunsa a fuskarta yana gyaramata
dogon gashin sun daɗe suna kallon juna eyes to eyes saurin dawowa yayi daga dogon tinanin
daya shiga bazato taji ya hankaɗeta ya saki wata uwar tsuka kallon farar suit ɗinsa yayi meze
gani suma sun ɓaci da jini sosai cikin ƙololuwar ɓacin rai ya buɗe baki zeyi magana kenan yaji
muryar Abbih ɗinsa na cewa"Son buɗe nine".
damm ƙirjinsa yabayar sakamakon ganin Inteesar dashi duk sun ɓaci da jini murya kamar
ammasa dole yace"toh Abbih ganinan zuwa".
wani ƙasƙantaccen kallo ya watsawa Inteesar tare da yin tsuka bazato taji lallausan hannunsa a
nata ya nufi toilet ɗinsa da ita!!!!!
*Kuyi manage da wannan saboda kwana biyunnan da banyin typing yasa na sangarce nasan
insha Allahu nanda gobe zan dawo normal saboda akwai labari a bakina sosai*
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_ar Mutanen Gwarzo.*_ *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣
Ba abinda take se aikin rawar jiki domin wani sabon tsoronsa ne ya dirarmata dan gani
take wata muguntar ya shiryamata domin tasan baze taɓa barinta ba tunda ta ɓatamasa guri
ɓangaren Namijin duniya ko yana shiga da Inteesar toilet ya cire ƴar saman suit ɗinsa ya fita.
Dukda tana cikin firgicin abinda ya fitar dashi amma hakan be hanata bin ko ina na toilet ɗin da
kallo ba a zuciyarta tace"amma gaskiya ankashe kuɗi a banɗakinnan kamar baza'ah mutu ba
ace duk toilet aka tsaya ƙawatawa haka kamar mutum ya zuba abinci yaci dan kyau".
tana cikin wannan zancen zucin taji buɗe ƙofar Namijin duniya ƙara raɓewa tayi ɗan nesa dashi
kamar wata munafuka ƙarasa shiga yayi ya zauna kan kujerar wanka yashiga tinanin irin rashin
mutuncin da zewa Inteesar a zuciyarsa yace"haka kurum Ahmad kasa nabi shawararka kan
wannan ƙasƙantacciyar yarinyar aiko dole kazo asan mafita dan seta gane kurenta bazan taɓa
bari abinda takemun ya tafi a banza ba wallahi jibi yadda tasa na tsaida mahaifina a waje duk
saboda iskancinta dole na gyaramata zama ".
yana cikin wannan maganar suka haɗa ido da Inteesar daketa faman zare ido kamar wadda
tayiwa sarki ƙarya wani kallon tsana da ƙasƙanci da nunamata zaki gane shayi ruwane yike
binta dashi tare da yin tsaki yace"kin dena kallona da wannan idanun naki kamar na mayu ko
senazo nan na tattakaki mara mutunci kawai ". yaƙarasa zancensa tare da sakin wani uban tsaki yana yamutsa fuska sakamakon zuciyarsa
dake tashi saurin duƙar da kanta ƙasa tayi jiki a sanyaye zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ga
wata tsananin faɗuwar gaba dake damunta.
A zuciyarta tace"nashiga ukuna Allah kaɗai yasan irin muzantani da wannan mara tarbiyyar
mutumin zeyi haka nanma ya lafiyar kura bare antaɓota na ɓatamasa kujera yanzufa wannan
mara sanin darajar ɗan adam ɗin duk wani fishinsa kaina zeriƙa hucesa".
duk wannan zancen zucin da Inteesar take batasan a fili takeyinsa ba kaf Namijin duniya yajita
bazato taji ya bugamata tsawa yace"keeeh dawa kike".
saurin dawowa tayi daga zancen zucin da takeyi batasan lokacin data ce"ba magana nayiba".
hakan yayi daidai da buga ƙofar toilet ɗin kwafa yayi tare da tashi cikin tafiyarnan tasa ta isa ya
nufi ƙofa rakashi tayi da uwar harara tare da yin tsaki tace"abanza man kare ko ƙarya nayimaka
kanada tarbiyyarne oho stupid kawai ji da Allah wata irin tafiya da yike kamar wani wahainiya
waishi isashe". jin abinda take cewa ne yasashi sakin murmushin dabe shirya yinsa ba ya girgiza kai tare da
wucewa yayi kamar bejitaba buɗe ƙofar yayi ya anshi wasu leda guda biyu na store sannan ya
mayar ya rife a hankali seda yazo gabda Inteesar yace"heey you ƙasƙantacciyar cleaner ga
kaya nan wa'inda ba'ah taɓa sawaba sede a gansu a t.v ko a jarida asa nasandai kan wa'innan
kika ɓatamun kujera base kin nunamun kin balaga ba har kin fara period ba".
yana gama faɗin haka ya wani watsamata kayan a jikinta ya buga tsaki ya nufi can cikin toilet
ɗinsa yana murmushin gefan baki domin yasa ya gama da ita.
Wasu zafafan hawayene suka zubomata saboda tinda take ba'ah taɓa cin mutuncinta kamar
yadda Namijin duniya yaciba ko wanda Uwar Gwarama take musu bekai wanda yayimata ba
saboda ba wanda ya taɓa kiranta da ƙasƙantacciya se Namijin duniya gashi ba yadda za'ayi
tabar aikinnan Abbansu ya kyaleta a fili ta furta "wallahi bazakaci banzaba indai nice sena rama
mara tarbiyya kawai inbanda tsabar jahilci meyakawo maganar wani period banda ɗan iska
neshi banda kayana sun ɓaci wallahi da bazansa wa'innan ƴan iskan kayan ba da har akemun
gori kansu ".
ta daɗe tana wannan maganar taji buɗe ƙofarshi dukda taji haushi cin zarafinta dayayi amma
hakan besa ta ɗago ta kalleshiba sema ƙasa data ƙarayi da kanta saboda tinda yaga jinin nan
taji tana masifar jin kunyarsa ko rashin kunya zata yimasa bata yadda su haɗa ido har yazo
dafda ita bata ɗagoba sema wasa data riƙayi da zara-zaran ƴan yatsunta taji muryarsa cike da
rashin mutunci yace"saura kuma idan kin gama ƙazantar taki kiƙi wanken toilet kinji".
yanayin yadda yayi maganar kamar yaga kashi hakan baƙaramun ƙara sosa zuciyar Inteesar
yayiba ya fara tafiya abinsa bazato yaji tayi tsaki ta wuce fuuu cikin inda ya fito murmushi yayi
danyasan ya ɓatamata rai ya fice.
Ɓangaren Inteesar ko tana shiga wanka taji ta tsaftace jikinta sannan ta buɗa ledar daya jefeta
da ita pad tagani dozen se pant dozen da breziya dozen se kuma wata haɗaɗɗiyar abaya
maroon taɓe baki tace "kome zakayimun kayimun lokacinka ne maratarbiyya kawai oh ni
Aishatu wannan mutumi shiya yankewa iskanci cibi banda ƙasurgumin ɗan bariki ne meye na
wani haɗowa da breziya ",.
ɗaukae pant tayi guda ɗaya da pad tasa ta da bra ɗaya ta shirya jikinta tsaf cikin haɗaɗiyar
abayarta data sha adon stone se walwali take baƙaramun ansar jikinta kayan sukayiba tayi
rolling da ɗan kwalin abayar sosai farar fatarta tafito tayi wani mugun kyau tamkar balarabiya
kallonta a madubi tayi taga tayi kyau sosai tinowa datayi da waye ya siyo kayan yasata jin wani
ɓacin rai lokaci ɗaya ta haɗe rai tayi tsaki tace"shegun kayanma da akemun gori kansu ko kyau
basu dashi".
tatattara sauran ta zubamasa kayansa tashiga wanke toilet ɗin.
Ɓangaren Namijin duniya ko yana fita ya tadda su Ahmad zaune da Abbih ɗinsa suna hira
murmushin gefan baki yayi tare da cewa"sannu da zuwa Abbih".
"yauwa Son mekakeyi ne a toilet".
zeyi magana kenan Adam yace" sabuwar Cleaner ɗinsa yike nunawa yadda zata kunna kayan
toilet ɗin saboda kartayi ba daidaiba".
saurin sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya yayu saboda banda Adam yayi saurin magana besan
mezeceba zama yayi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yace"Abbih anyini lafiya".
"lafiya ƙlau Son dama wucewa zanyi nace bara na shigo na kawomaka ziyarar bazata".
"aiko naji daɗi nagode Abbih Allah yaƙara girma".
"Ameen Son Allah yayimuku albarka".
haɗa baki sukayi da "Ameen".
suna cikin wannan hirar Inteesar tafito tindaka ƙafarta har zuwa kanta kwanne cikinsu yabita da
kallo a hankali take tafiya ganin yadda hankalin kowa yike kanta yasa Namijin duniya yaji wani
abu yazo ya tsayamishi a maƙogoro harta iso inda suke cikin girmamawa ta duƙa har ƙasa
tace"Ina yini ranka shidaɗe". "lafiya ƙlau daughter ya aiki".
"Alhamdulillah".
tana gama faɗin haka ta miƙe da niyyar tafiya Abbih yace"ɗiyata da wanne matakin karatu kike
amfani".
zatayi magana kenan Namijin duniya daketa gumi yayi saurin cewa"batayi karatu ba tausayi
tabani datazo neman aiki dankar inbarta haka yasa nabata cleaning ".
sosai tayi mamakin abinda Namijin duniya yace nan ta shiga tinanin itako meta tsaremishi a
duniya da harya tsaneta haka wasu hawayene masu zafi suka zubomata tayi saurin sharewa
taji Abbih yace"ka kyauta kuwa Son Allah yayimiki albarka ungo wannan".
ya miƙamata bandir ɗin yan dubu-dubu da farko taƙi ansa hakan yasa Abbih cewa"ki ansa ki
ɗaukeni tamkar mahaifinki kinji".
"toh nagode Allah yaƙara buɗe da ɗaukaka".
"Ameen ".
nanta fita kallonsu Namijin duniya Abbih yayi tare da cewa"amma yarinyar nan tanada nutsuwa
hakanan naji ta kwantamun a rai wallahi anyako ba surukata bace ba cleaner ba kuka ɓoyemu
naga kwata-kwata batayi kama da masu sharaba".
kallon juna su Namijin duniya sukayi tare da cewa "wallahi Abbih cleaner ce".
murmushin manya Abbih yayi tare da cewa"to ni zan wuce".
nan suka miƙe dan yimasa rakiya seda suka fitar dashi har gurin motocinsa sannan suka juya.
Ɓangaren Inteesar ko tana fita ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya tare da dafe ƙirji waigawar
nan da zatayi sukayi ido huɗu da sakatariya nata bankamata harara tsaki Inteesar tayi tare da
cewa"andaiyi asara zuwa duniya mutum yayita ɓata lokacinsa kan wanda bemasan yanayiba
dama hijabinki kika fara sawa kina rifawa wannan kwantaccen ƙirjin naki da yike kamar farantin
fawa asiri ƙila yasan kinayi".
"oho dai a haka ake ganin ake sha'awa kuma ba'ah kula na masu miƙaƙƙen se inzonan in
zauna kanki da ubanki inga ƙaryar fitsara ".
dafa kwankwaso Inteesar tayi a zuciyarta tace"wai wannan me ɓaka-ɓakan duwawun tazauna
kaina aina shigesu".
a fili kuma taɓe baki tayi tace"waya gayamiki dama ni inaso asoni ai abu me tsada binsa ake
yana wulaƙanci abu me arha ko kullum buɗesa ake ana tallarsa kamar dai wannan ɗan silifas
ɗin ƙirjin naki me kama da takalmi ɗan madina saboda taushi".
taƙarasa zancenta tare da niyyar fita Sakatariya Feenerh ko cikin jin ɓacin ran maganganun
Inteesar tace"inkin isa ki tsaya inbaga tsoro ba dasekin gane ke ƙaramar mara kunyace
wallahi".
gabda zata fita ta juya tace"Allah ya kyautamun na tsaya ina goga jiki da wannan ƙazamun jikin
naki dayasha taɓawar ƴan bariki".
taƙarasa zancenta tare da saurin ficewa da gudu dankarta cimmata tasan duka zatayimata
sosai abinnan yaƙara ɓatawa Sakatariya rai taji taƙara tsanarta.
Zaune suke suna hira Ahmad ya kalli Adam tare da cewa"ammafa yarinyar nan ɗazu
baƙaramun kyau tayiba kasan Allah seda ta matso nagane wacece Allah yayi halitta anan
gurin".
"gaskiya tayi kyau sosai wannanfa da a gidan hutu take zatayi yaya wallahi".
cikin ɓacin rai Namijin duniya yace"ban kiraku nan dan kuzauna kuyita yimun surutan banza
ba".
yaƙarasa zancensa cike da ɓacin rai kallonsa Adam yayi yace"abokina lafiya naga duk ranka
yaɓaci kamar wata girlfriend ɗinka abinda kakeyifa like kishifa anya abokinmu ko be zurma ba
kuwa Ahmad ".
"nima tinanin da nikeyi kenan".
cikin tsananin ɓacin rai Namijin duniya ya miƙe ya fice a fusace binsa sukayi da kallo gabaki
ɗayansu sannan suka tafi suma.
4:00pm
Zaid na tsaye jikin motarsa suka fito daga cikin comphany ɗin bakinsu ɗauke da sallama suka
ƙarasa inda yike murmushi yayi tare da cewa"wa'alakumus salam sannunku da aiki".
"yauwa ina yini Uncle Zaid".
"lafiya ƙlau Hauwa'uh".
"ina yini".
"lafiya ƙlau My heart ya aiki".
"Alhamdulillah ya naka".
"lafiya ƙlau".
nan suka shiga motar yajasu suka nufi Suleja.
Yana gama daidaita parking suka fito gabaki ɗayansu kallon Inteesar Hauwa'uh tayi tare da
cewa"sena shigo Uncle Zaid ka gaida gida mungode".
"toh Hauwa'uh se Allah yakaimu".
"Ameen".
taƙarasa faɗa tanaiwa Inteesar inkiya da ido ta wuce ƙasa Inteesar tayi da idonta tana tinanin ta
inda zata fara faɗawa Zaid maganar mahaifinta taji muryar mahaifinta na tunkarosu batace
ƙalaba harya ƙaraso inda suke Zaid ya duƙa cikin girmamawa yace"Babah ina yini ".
"lafiya ƙlau ɗannan ya magabatanka".
"lafiya ƙlau Babah".
"masha Allah