Showing 18001 words to 21000 words out of 35201 words
matsawa gefe tayi tare da cije ɗan pinky lips ɗinta murya na rawa sabo da
kukan daya fara taho mata ta ce"nagode sir".
Tana gama faɗan haka tashiga tafiya cike da jarumta duk da irin yadda take jin ƙafafun na mata
azaba haka ta daure ta tafi abunta tana kuka.
Ji ya yi duk beji daɗin yadda ta fita ba tana kuka domin jin kukanta yike har cikin zuciyarsa be
san meya saba ji ya yi beyi mata adalci ba kome ya tino kuma ya ɗaga kafaɗa alamar
matsalarta ce ya cigaba da aiki a system ɗinsa ɓangaren Inteesar ko tana fita taga wani
gangarumin hadarine a garin ga wata irin iska da akeyi ba alamun abun hawa ko kaɗan ta daɗe
tana jiran abun hawa kafin dabarar kiran Zaid ta faɗo mata saurin zaro wayar da Zaid ya bata
tayi daga cikin jakarta tashiga dialing no Zaid a kashe taji wayar a kashe hakan yasa hankalinta
mugun tashi tashiga rage tafiya ko Allah ze sa tasamu abun hawa har tayi tafiya me nisa amma
bataga masu napep ba samun guri tayi ta raɓe ta tsugunna kamar wata marainiya ta fashe da
wani marayan kuka.
Bazato taji ana mata horn ɗago sexy eyes ɗinta tayi da suka rine sabo da kukan da take yi ta
saukesu akan wata haɗaɗɗiyar farar G-box tasha tintac se ɗaukar ido motar take yi mai da
kanta tayi ta cigaba da kukanta dan tasan da Zaid ne ze kirata ta cigaba tana cikin kuka taji
muryar wani mutum akanta ya ce"ki taso mutafi inji sir". Ɗago jajayen idanunta tayi ta saukesu akan mutumin wan da daka ganin shi kaga security ta
ce"waye ogan naka?".
Zai yi magana kenan ya ji wayarsa na ƙara ɗagawa ya yi tare da ce wa"okay sir".
Ya kashe wayar tare da kallonta ya ce"ya ce in ba zaki taho mutafiba inkyaleki".
Waigawa tayi taga unguwar kwal ga duhu ya ɗan fara yi bako mutum ɗaya hakan ya sata
miƙewa jiki ba kwari tabi bayan mutumin ƙofar baya ya buɗe mata tashiga ya mai da murfin ya
rufe sannan ya zaga ya shiga mazaunin driver ya jasu.
Tana shiga daddaɗan ƙamshin turarensa ya daki hancinta satar kallonsa tayi ta wutsiyar idonta
gani tayi yana karatun daily trust ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya saurin juyar da kanta wajan
window tayi tare da ɗan tsuke ƙaramin bakinta a zuciyarta ta ce"shi dai ko a ina zamansa kenan
sabo da isa". Tana cikin wannan zancen a zuciyarta taji lion voice ɗinsa ta daki dodon kunnenta ya ce"me
yasa baki kira wannan faƙirin saurayin naki ya ɗauke ki ba? Ko yau be aro motar bane?".
Sosai maganganunsa suka ɓata mata rai amma seta make tayi kamar ma bata san da ita yi
keba jin tayi banza da shi yasa ran shi ɓaci ya yi kwafa ringing wayarta tashiga yi ɗauka tayi
tare da ce wa"tun ɗazu nayi ta kiranki baki ɗauka ba".
Sorry besty ina wanka ne kin taho muna gurin me make-up ki wuto kawai na faɗawa Umma na
tafi miki da kayan da zamusa".
Anya zanyi make-up ɗin nan ma ni kuwa kin san bana son a cika mun fuska kin tafi da Khadijah
ko".
Ai ko dole kiyi kin san Asma'uh bazata ji daɗi ba ki daure kawai kiyi eh na taho da ita amma fara
yi mata make-up ɗin Uncle Zaid ya yi mana siyayya sosai ki kira shi kiyi mishi godiya kowacce
cikinmu yasiya mata gown da takalmi da pos se kuma dalleliyar waya ƙirar iphone 13pro daya
bani in ajiye miki". Cikin farin ciki ta ce"dan Allah".
Wallahi kinga ko dole kiyi kwalliyar nan ko dan kiyi masa hotuna".
Sosai ma kuwa aiko bara in kira shi in yi masa godiya kuwa".
Ya dai kamata sekin ƙaraso muna gurin Reality ".
"toh sena ƙaraso".
"yauwa".
Nanta kashe cike da zumuɗi tafara lalubar no Zaid taji muryarsa ya ce"ki faɗa masa unguwar da
za'ah kaiki".
Se lokacin ta tina a in da take hakan yasa fara'ar dake kan fuskarta saurin gushewa ta katse
kiran da take yiwa Zaid ta ce"kusa da Garki akwai wata me make-up a tsallaken titi nan zan
sauka".
Toh ranki shidaɗe".
ce war security nan ya juya akalar mota suka nufi Garki shiru ne ya biyo baya har suka isa suka
yi parking a ƙawataccen gurin tanƙamemen shagon make-up ɗin Real Eeshow juyawa tayi ta
kalli Namijin duniya cikin girmamawa ta ce"thank you sir".
Ba tare daya ɗago daga karatun daily trust ɗinsa ba ya yi banza da ita buɗe mata mota security
ɗin ya yi ta fita tare da shigewa gurin driver yaja motar suka bar gurin.
8:30Pm
Suka iso gurin dinner kallon Inteesar Hauwa'uh tayi ta ce"amma gaskiya besty kinga yadda kika
yi kyau kuwa kamar bake ba kodon bakya make-up shiyasa yau da kika yi ya yi mugun yi miki
kyau".
Hmm besty kenan niko kunyar fita nike yi cikin mutane da wannan kwalliyar sabo da idan naga
ana kallona duk se in tsargu bakiga yadda kika yi kyau ba Wallahi besty".
"au nice banyi kyau ba kenan ko Aunty?".
Sorry my Khady nina isa in ce da wannan shagaɓaɓɓiyar ƙanwar tawa bata yi kyauba? Kinfi
kowa yin kyau".
Yauwa Auntyna muje".
nan suka fita Inteesar ji take kamar tsirara take sakamakon rashin saka gyale da batayi ba
kanta a ƙasa sabo da wata irin kunya da take ji haka sukabi layin da akai na shigar da amarya
suka shiga tanƙanemen hall ɗin da ya gaji da haɗuwa suka fara tafiya kiɗa na tashi har suka
raka amarya da ango mazauninta dafa Inteesar Hauwa'uh tayi cikin ƙasa da murya ta
ce"kinsanko waye angon Asma'uh".
"a'ah waye".
"Sir Adam ne".
dammm ƙirjinta ya bayar lokaci ɗaya zuciyarta tashiga bugawa da sauri-sauri ga yawun bakinta
daya ƙafe ƙaf murya na rawa ta ce"what?".
"Eyi".
Wani gumi ya shiga ketomata suka samu seat suka zau na ta ce"amma baku kyauta mun ba da
kuka hanani saka gyale ko wanne tom and jerry ya gama kallemun jiki a banza".
Nan Hauwa'uh taita kwantarmata da hankali aka shiga gabatar da program.
Suna cikin hirarsu da Khadija taji muryar m.c na ce wa"muna buƙatar aminiyar amarya me suna
Aishatu domin tazo ta gabatar mana da tarihin amaryar".
a gigice ta ɗago ta ce"Hauwa'uh kinga irin abin da nike gudu ko da kun barni nasa gyalena ai da
duk haka bata faru ba".
"Sorry besty gani muka yi idan kika sa zaki lalata kwalliyarki kiyi haƙuri kije kiyi kin san Asma'uh
bazata ji daɗi ba".
"Ba bu 'in da zani ".
Ji suka yi m.c ya ƙara kiran sunan Inteesar hakan yasa Khadija ce wa"Aunty dan Allah kiyi in
baki yi ba kamar kin watsawa Aunty Asma'uh ƙasane a ido ta wuce kowa ta zaɓeki plz Aunty".
taƙarasa zancenta tare da saka hannunta alamar roƙo kamar zata yi kuka hakan yasa Inteesar
ce wa"sorry my Khady karkiyi kuka bara naje".
"yauwa Auntyna maganin kukana".
nan Inteesar tafara tafiya cikin nutsuwa take tafiya kanta a ƙasa hankalin kowa kanta ya koma
sakamakon m.c daketa koɗata tun daga nesa ya kafeta da shanyayyun idanunsa da sukayi
kama dana me bacci gani yike kamar ita kamar ba itaba hakan yasashi tanfatsar da glass cup
ɗin dake hannunsa hakan yaja hankalin mutanen dake kusa da gurin yi ke suka kalle shi ba
tare daya sani ba a zuciyarsa ya ce"why zuciyata da zaki dameni da tunanin wannan kucakar
yarinyar ne da kowacce nagani ganinta nike kamar ita why anyako wannan yarinyar ba mayya
bace takamani".
yana wannan tunanin harta ƙarasa gurin m.c ta tsaya saurin dawowa ya yi daga tunanin daya
tafi gani ya yi ba Imergination ɗinta daya saba yi bane ita ce tasha gayu tagaji da haɗuwa se
ƙamshi take bazawa!!!!!!!!!
meson shiga group ɗin wannan novel ɗin tayimun magana ta wannan number 08108362334
Votes and Comments
Plz share
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_r Mutanen Gwarzo.*_ *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣
Cikin amsa kuwwa m.c yace "masha Allah ga babbar aminiyar amarya amma gaskiya
tahaɗu kwarai dagaske bara muji taƙaitaccen tarihin babbar aminiyartata".
yaƙarasa zancensa tare da miƙawa Inteesar laudspeaker amsa tayi tare da ɗago da kyakyawar
fuskarta wadda tayi mugun kyau domin inba farin sani kayimataba ba lallai bane ka ganetaba
saboda kwalliyar tayi mugun amsar jikinta kamar ka saceta ka gudu jin abinda m.c yafaɗane
yasashi ƙara tabbatarwa da kansa tabbas ba gizo tayimasa ba itance dai zuciyarsa ce
tacemasa"to a ina tasamu kuɗinda harta iya saka wannan tsadadden material ɗin domin nidai a
iya sanina bamasu hali bane".
wata zuciyarce tace"wataƙila saurayinnan natane ya siyamata".
tsaki yayi saboda lokaci ɗaya yaji wani mugun ɓacin rai yadirarmasa lokaci ɗaya yaji duniyar
tayimasa zafi Mimah dake zaune kusa dashi ce tace"wow Hubbi ammafa ƙawar amaryarnan
kyakyawace ajin farko".
taɓe baki Namijin duniya yayi kamar wanda yaga kashi ya waigar da kansa gefe yadda bama
zaka ɗauka yaga Inteesar ba.
Cikin zazzaƙar muryarta me tafiya da zuciyar duk wani ɗa namiji me lafiya tashiga zazzaga
speach kamar wata baturiya yadda take ba kowacce kalma haƙƙintane yasa taƙara burge
mutanen gurin uwa uba kuma a natse take komai nata bayan ta gama da yaren turanci ta juya
larabci yadda take fitar da harufa bazaka taɓa ɗauka ba balarabiya bace tana gamawa gabaki
ɗaya gurin ya kaure da tafi saboda baƙaramun tafiya da hankalin mutane tayiba ta juya zata tafi
m.c yace"ranki shidaɗe kitsaya babban abokin ango yazo yabada biography ɗin ango sannan
ku zauna a seat ɗin da aka tanaza dominku munason ganin babban abokin ango ɗaya tamkar
da dubu uban gayya Sir Abdallah Namijin duniya ".
damm ƙirjin Inteesar yabayar jin sunan wanda aka kira lokaci ɗaya hankalinta yayi mugun tashi
amma dayike miskilace bazaka taɓa fuskanta ba tafi gurin ya ɗauka alamun Namijin duniya ya
miƙe a hankali ta ɗago lulu eyes ɗinta da suka cika da tsoronsa ta saukesu akansa ɓangaren
Namijin duniya ko yanajin abinda m.c yafaɗa yaƙara shan kunu ya ɗauki glass cup ɗin dake
kusa dashi kenan yaji wasu abokan kasuwancinsu ɗaya na cewa ɗaya"wow amma gaskiya
wannan babe ɗin ƙarshe ce anyako bazan raɓa ba kuwa".
"gaskiya dai Muhseen kayi maza ka raɓa domin tahaɗu yarinyar tunkafin wani ya rigaka domin
irin wa'innan sune irin matan da ake layi gurin neman aurensu se me tsananin rabo kesamun
aurensu kagafa ga kyau ilimin addini da boko ga nutsuwa uwa uba hankali kai Muhseen inka
sameta kagama morewa wlh ga dirin jiki". "ai da wuri zanyi sauri inje ana tashi zanje insanarmata da kudirin zuciyata ko Allah zesa
insamu shiga da aduniya zanga nafi kowa sa'ah".
lokaci ɗaya yaji wani ɓacin rai ya lulluɓesa idanunsa sun canza kala saboda tsananin ɓacin
ransu yayi saurin ɗaukar glass cup ɗin ya shanye ruwan tas kozeji sauƙin zugin da zuciyarsa
kemasa amma wani canji ga wani abu daya tsayamasa a zuciya na ganin irin shigar dake jikinta
.
Sanye yake da white arman suite wanda sukayi matuƙar amsar jikinsa se necktiet ɗinsa data
kasance baƙa sumar kansa kamar kullum se sheki takeyi anyimata irin askinnan na zamani
wanda an aske gefe da gefe anbar tulun suma a tskiya wadda taketa ɗaukar ido da sajensa
tamkar wani balarabe kunnensa sanye yike da ɗan kunne me matuƙar ɗaukar hankali ga wasu
shegun sarƙoƙi daya saka suka zubomasa har ciki cike da isa da izza yike tafiya yayinda
hankalin ƴammatan gurin gabaki ɗaya yayi kansa saboda a ƙasarma gurin ƴammata haka suke
cemasa burin kowacce ɗiya mace ƙarasawa yayi inda Inteesar ke tsaye a hankali ta ɗago
fararen sexy eyes ɗinta da niyyar satar kallonsa caraf idanunsu ya sargafe cikin na juna saurin
janye idanunta tayi a nasa tare da yin ƙasa da kanta ta ƙarasa inda yike cikin ladabi ta
miƙamasa laudspeaker ɗin hannunta bazato taji lallausan hannunsa ya haɗa da hannunta wani
irin shock ne ya ziyarci gabaki ɗayansu hakan yasa tayi saurin janye lallausan hannunta a nasa
cike da izza gami da taƙama yashiga bada biography ɗin ango yana gamawa gurin ya ɗauki tafi
jin yagama sanya Inteesar fara tafiya ba zato taji hil ɗin takalminta ya tafi luuu zata faɗi saurin
rife zara-zaran eye lashes ɗinta tayi saboda tarigada tagama sadaƙar da zatajita a ƙasa bazato
tajita a jikin mutum wata wawuyar ajiyar zuciya suka sauke a tare sexy eyes ɗinsa da suke
kamar na me bacci ya sauke akan zara-zaran eye lashes ɗinta da suka kwanta kamar na kanti
sunsha lining da baƙin kwalli ga eye shadow da suka sha lokaci ɗaya yaji tsigar jikinsa ta tashi
yarrrr idanunsa sun wani ƙanƙance irin na wa'inda suka kai ƙololuwar buƙatuwa a hankali
yashiga yawo da sexy eyes ɗinsa kan kyakyawar fuskarta ya shagaltu da kallonta ɓangaren
Inteesar ko jin bata faɗi a ƙasa bane yasa tashiga buɗe oily eyes ɗinta ta saukesu kan
kyakyawar fuskar Namijin duniya lokaci ɗaya gurin yaɗauki tafi domin baƙaramun bada style
sukayi ba idan kagansu seka ɗauka couples ne saboda matching ɗin da sukayi kallon-kallo
suka shigayi hakan yayi daidai da ɗauke wutar gurin bazato taji ya manneta da faffaɗan ƙirjinsa
da kowacce ɗiya mace ke burin jinta a gurin saurin haɗe fuskarsu yayi gurin ɗaya yayinda
dogayen hancinansu suka haɗe guri ɗaya a tare suka saki wata nannauyar ajiyar zuciya jikinta
ne yashiga rawa saƙala kansa yayi ta jikin wuyanta yashiga shinshina wuyanta da kamar
anyimasa ɓarin turare akaikai yashiga sauke ajiyar zuciya wadda daga ita seshine kawai sukeji
bazato taji saukar numfashinsa daidai kunnenta cikin narkakkiyar muryar dabata taɓajin yayi
magana da irinta ba kamar yana yimata raɗa yace"waya baki izinin saka irin wa'innan banzayen
kayan keko kunyar fitowa a haka bakijiba jibi wata kwalliya kamar wata aljana kewai a tinaninki
kinyi kyau dama zuwa kikayi kika wanke dayafimiki alheri domin mutane dariya suke tayimiki a
hakan kike cewa wani bashi da tarbiyya ke ai itan gareki domin dai duk mace me aji datasan
darajar kanta bazata saka irin wannan kayan ta fito cikin taron jama'ah ba jibeki kamar wata one
ko lankwasa babu".
sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci dashi ta matsar da bakinta daidai kunnensa zatayi magana taji
yayi saurin haɗe bakinsa da nata seda ya shanye jambakin bakinta tas sannan ya zame
bakinsa a nata cikin muryar raɗa yace"da kinwani saka jambaki kamar wata buranya ke dan
bakiga irin munin da kikayi bane temakonkifa nayi domin banaso ina ganin mutane suna miki
dariya keko bikiyardaba se wani yanga kikeyi ala dole gani kike kinyi kyau".
a zuciyarta tace"kodai banyi kyau bane dagaske shiyasa naga mutane nata kallona ne bara zan
tambayi Khady naji".
a filiko sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci dashi ganin yadda yaketa tattaɓamata jiki bako sisi a
sanga hakan yasa tasa hannuwanta da iya ƙarfinta ta tureshi ta sassauta murya yadda iya
shikaɗaine zejita tace"to ina ruwanka idanma banyi kyanba kokai ka biyamun" .
"wayema zeyi ɓarnar kuɗinsa kan wannan mummunar fuskar taki dako taushi bata dashi
ƙabe-ƙabe take kamar bayan kada ayimiki kwalliya sede wannan ɗan asaran saurayin naki
dayaga ze iya".
sosai ran Inteesar yakai ƙololuwar ɓaci idanunta suka fara kyallin fito da ruwa zatayimasa
magana kenan wani diff haske me circle yafito a inda suke yayinda wani cool music yashiga
tashi bazato taji hannunsa a waist ɗinta yashiga yin rawar nan ta turawa ya wurnata can yayi
can da ita kamar wata ƴar baby ganin mutane na kallonsu ne yasa ba yanda ta iya tabishi
sukayi rawar bayan sun gama aka dawo da haske ɗaukar tafi gurin yayi lokaci ɗaya suka nufi
high table suka zauna yayinda Inteesar tazauna nesa da Namijin duniya.
"Feenerh wai wannan wacce tsinanniyar yarinyarce dahar ta haɗa jiki da Namijin duniya kina
zaune Feenerh".
" hmm Zuby kenan to itace sabuwar cleaner ɗinnan danake baki labari kike ganin kamar bata
da abinda zata siyi zuciyar Namijin duniya to gadaishi kingani da idanunki har rawa yayi abinda
nike burin inyi da Namijin duniya shi wannan kwailar tayi to kindai gani da idanunki keda dabiki
ɗauki zancennan serious ba ni dama tunda tazo gurinnan naji na tsaneta wallahi". sosai ran Zuby yaɓaci a zuciyarta tace"dole inyi maganin duk wanda ze kawomun cikas a
rayuwata dakai Abdallah domin kai nawane ni kaɗai ba wata ɗiya mace data isa inyi sharing
ɗinka da ita ban kauda itaba".
a filiko sosai ta nuna ɓacin ranta ta dafa kafaɗar Feenerh cikin nuna alhini tace"aiko ƙawata
dole muɗauki babban mataki akanta bata isa tazo da rana tsaka ta rabaki da abu mafi soyuwa a
garekiba ko itaɗin banza kinkoyi amfani da maganin dana kawomiki kuwa".
"sosaima kuwa amma kinga shiru anyako maganin bokannan kuwa yanayi Zuby domin ni
banganin wani canji ko ɗaya".
damm ƙirjin Zuby yabayar amma dake ƴar duniya ce seta make tace"yikai domin bokannan kaf
inda su Ummanmu suke zuwa ba wanda yakaishi aikinsan irin wannan aikin ba'ah yimasa
garaje kibari mugani nanda sati uku".
"toh mujira amma yanzuma semunje munyiwa wannan kwailar kashedi".
"toh kibari a tashi".
nan sukaita tsinewa Inteesar.
Ɓangaren Mimah ko sosai rawar dayayi da Inteesar ta ƙonamata rai hakan yasa takira Mum a
waya kamar zatayi kuka ta zayyanemata abinda yike faruwa daga ɗaya ɓangaren Mum tace"ki
kwantar da hankalinki duk duniya Abdallah bashi da wata mata data wuceki ko ubansa be isaba
bareshi me akai akayisa dazaki tsaya kina zubarmun da tsadaddun hawayenki ki kwantar da
hankalinki karki nunamasa kinji haushin abinda yafaru kinjini ninasan yadda zanyi dashi".
"to Mum".
nanta kashe ta goge hawayenta tayi kamar ba abinda ke damunta.
Sosai aka shiga gabatar da program yayinda gawurtattun masu kuɗi sukaita