Showing 27001 words to 30000 words out of 35201 words

Chapter 10 - Man Of The World Book 1 by Real Eshow.pdf

28 Sep 2025

685

ke yashe se lokacin ta lura da Inteesar
daketa faman kuka cikin tashin hankali ta nufi gunta tana cewa"meya sameki Besty".
kasa magana Inteesar tayi kuka ya kuɓucemata se nuni takemata da ƙafarta sosai Hauwah taji
tausayin halin da aminiyarta take ciki tashiga ƙoƙarin temaka mata .



Kasa ɗagata tayi hakan yasa Ahmad nufar gurin yana cewa"bara na temaka miki".
be ƙarasa zancensa ba yaji Namijin duniya ya bangajesa ransa a mugun ɓace yayinda yaketa
faman huci yace"muharramarka ce da zaka taɓatamata jiki meye alaƙarka da ita ?".
cikin tsananin ɓacin rai ya nufi gurin da Inteesar take yashe tana kuka wani guntun tsaki yayi
sannan yasa lallausan hannunsa ya ɗauke ta cak kamar wata baby ya wuce fuuu baki sake
suke kallonsa har ya ɓacewa ganinsu sauke numfashi gabaki ɗaya sukayi Adam ya kalli
Ahamad suka saki wani shu'umin murmushi wanda su kaɗai sukasan ma'anarsa Ahmad ya kalli
Hauwah gani yayi duk tashiga damuwa yace"ki kwantar da hankalinki ba abinda zemata nasan
asibiti zekaita kya iya tafiya gida nasan shima idan sun dawo kaita zeyi".
"toh Sir".
nanta fice tabarsu ba abinda sukeyi se aikin murmushi.

Ɓangaren Namijin duniya ko yana fita ya nufi gurin haɗaɗiyar Bugatti ɗinsa sabuwa dal da ita
kafin yaƙarasa securities ɗinsa sun buɗemasa motar back seat ya ajeta jin yadda take kukane
yasashi sakin wani dogon tsuka ya juya ya nufi gurin driver security ɗin dake niyar shiga
mazaunin driver ya dakatar da hannu yace"nizanja ku zauna ku". "okay sir".
nan security ɗin ya matsa ya shiga harya fara tada motar sekuma ya kashe yayi tsaki ya fita ya
zagaya inda take yasa lallausan hannunsa ya ɗauketa cak ya buɗe gefan me zaman banza
yasata ya zaga yashiga mazaunin driver yaja motar da gudu ya cilla hancin motarsa titi shiru
ne ya biyo a tsakaninsu kowanne da abinda yike saƙawa a cikin zuciyarsa ita tana tinanin itako
meta tsarewa wannan mutumin dahar ya tsaneta haka shikuma yanajin duk beji daɗiba ganin
yadda tayi ƙasa da kanta tana shashekar kuka ta wutsiyar ido ya saci kallonta gani yayi tana
nan dai a yadda take sosai tabasa tausayi amma dake miskilin gaskene se ya nuna be damu
da halin da take cikiba sema taɓe baki da yariƙa yi a haka har suka isa wani tanƙamemen na
masu faɗa aji a ƙasa me suna A2 bakin tanƙamemen parking space ɗin hospital ɗin yayi
parking tare da juyar da kansa ya kalleta tana nan a yadda take tsaki yayi ya buɗe mota ya
zagaya inda take ya ɗauketa kamar wata baby yayinda ƴan hospital ɗin se bashi respect suke
ya nufi wani room da ita yana shiga haɗaɗen room ɗin ya kwantar da ita akan wani haɗaɗen
sick bed wanda inkana kai seka ɗauka na gidane gidanma wanda ya amsa sunansa gida
mamakine ya kamata seta make gefe guda kuma wani mahaukacin tsoro ne ya dirarmata ganin
irin aljannar duniyar gurin da take yana nan tsaye kanta sega wani Doctor yashigo bayan sun
gaisa yayimasa bayani abinda ya sameta amma becemasa shiya jimata ba nan yashiga bata
emergency care domin ƙafar ta kumbura sosai.



*FEENER POV*


Suna fitowa daka Office ɗin Namijin duniya Zuby ta dafe shafaffen ƙirjinta tare da kallon
Feenerh cikin tsananin baƙin ciki tace!!!!!!!!!




Votes and Comments
Plz share to others



_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_n ƴar Mutanen Gwarzo.*_ *MAN OF THE
WORLD*

(NAMIJIN DUNIYA)



*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*



*BOOK 1*


*PAGES* 2️⃣7️⃣➡️2️⃣8️⃣



"Gaskiya wannan tsinanniyar yarinyar anyi tambaɗaɗiya daka gani sede in gurin boka taje
banda haka banga abinda Namijin duniya ze kalla a jikinta ba bare har yayi sha'awar aurenta
muna ganinta saida kaji saida kaji ashe har shanu ma siyarwa take".
"aina faɗamiki dama ƴar iskar yarinyar nan ta wuce duk inda kike tinani domin ba Allah a tare da
ita dakanan direct mu wuce gidan Ummah mu tafi gurin Boka".
"aiko dai kema kince wani abu domin abunnan gagarumi ne".
"eh mana hatsabibiya ce yarinyar ga kuɗin dana ciro zankai gidan adashi mutafi dasu kawai
gobe na ciri wasu inkai".
"toh muje ammafa yarinyar nan koda ansamu anɓan bareta daka jikinsa aciki wasa tunda ita
yafara runguma kafinke amma dai nima zaki bani passentage ɗina daiko".
"gaakiya baki da haƙuri Zuby kinsan dai ai zanbaki ungoni".
"ai gaskiya ce najiɗin bani da haƙurin indai akan kuɗine gwara kibani haƙƙina".
a zuciye Feenerh ta dankawa Zuby kuɗin tace"gashinan sarkin zalama".
"naji ɗin kome zaki ce kice ɗin ina ganin kawai mu kira Ummah ta fito titi mu ɗauketa mu wuce
kawai ina ganin tafiyar zata fimana sauri".
"ok kirata da hanzari dan Allah".
kamar yadda Zuby tace hakan sukayi suka kira Umman Zuby suna isa bakin layinsu suka
ɗauketa suka tafi.




"Ummah gaskiya ni nagaji da wannan ƙailular taki kinsanko irin san da nikewa mejan kunnenan
kuwa da kika wani ƙi maida hankali kan zancen".
"kefa Jameelah daɗina dake rashin haƙuri ki kwantar da hsnkalinki indai ina numfashi baki da
wani mijin se mejan kunne domin yau ko gobe zansa Malam yasa Zaidu mejan kunne yazo
gaidashi semu samu kafar saka maganin boka Tsula kai waye nafiki son kiyi aure gidan daula

kodon inriƙa zuwa inaɗan yago abinkaiwa a bakin salati".
"yanzu naji duka ".
"kedai abinda nike so dake kiɗanje ki wankemun ɗan wanke-waken can domin yau waccan
tsinanniyar yarinyar batayiba ta tafi yawon tazubar ɗinta".
ƙin tashi tayi dakyar ta tashi tana zumɓure-zumɓuren baki ta fita.


Ɓangaren Namijin duniya ko Doctor na gama gyarawa Inteesar ƙafa cikin yanayin caring
Doctor Shahid yace"princess gaskiya kinada dauriya da watace da yanzu tana nan ta cika
ɗakinnan da ɓararrako".
wani sansanyan murmushi Inteesar tayimasa wanda yayi mugun tafiya da zuciyar Doctor
Shahid tace"nagode".
"ba godiya a tsakanin princess kedai kawai ki kula da shan maganinki insha Allahu nanda
kwana uku zakiji ƙafar ta saki".
yaƙarasa zancensa yana sakarmata wani shu'umin murmushi ,murmushin itama ta mayarmasa
itama cikin siriyar muryarta dake tafiya da zuciyar ɗa namiji tace"insha Allah zankiyaye".
wani ƙullutun baƙin cikinsu ne ya tokarewa Namijin duniya maƙogoro ganin yadda Inteesar
keyiwa Doctor Shahid murmushi tsaki yayi a karo na uku sakamakon jin Doctor Shahid na
niyyar ƙara jan Inteesar da hira murya aɗan daƙile cikin basarwa ya katse Doctor Shahid tare da
cewa" Mallam kayi abinda ke gabanka". "sorry Sir".
nan Doctor Shahid ya tsuke bakinsa saboda yana ɗagowa yaga Namijin duniya na jifansa da
kallon kashiga taitayinka beƙara cewa da Inteesar komai ba ,ɓangaren Inteesar ko wani ƙullutun
baƙin cikinsa taji tashiga itako metayiwa wannan mutumin da bayason yaga wani ya raɓeta
bayason yaga wani yana nunamata kulawa tana farinciki tana cikin tinani taji muryarsa a ɗan
daƙile yana cewa da Doctor"thanks".
saurin dawowa tayi daga duniyar tinanin data tafi taji ƙamshinsa a gabda ita waigawa tayi
taganshi befi saura taku biyu ya iso inda take ba saurin miƙewa tayi dukda zafin da ƙafarta
kemata ta haɗe girar sama data ƙasa dan karya kaimata wargi tashiga aikamasa da harar
wutsiyar ido tafara tafiya tana ɗingishi murmushin gefan baki yayi ganin yadda ta wani haɗe rai
yabi bayanta yarigata zuwa gurin mota hakan yasashi yana isa ya buɗemata murfin motar har
tayi niyyar wucewawarta taga idanun mutanen gurin gabaki ɗaya yadawo kansu hakan gefe
guda kuma wata zuciyar tace mata"kishiga har yanzu kina ƙarƙashin ikonsa tunda baku tashi
daka gurin aikiba".
hakan yasata jiki a sanyaye ta shiga ya mayar ya rife ya zaga yashiga mazaunin driver yaja
motar suka bar gurin yana fita daka get ɗin gurin ya cilla hancin motarsa titi ya ware a.c ɗin
dake motar ya kunna karatun Alqur'ani megirma ƙira'ar Sudais tashiga tashi a cikin motar
suratul Muhammad ba tare daya ƙara bi takanta ba yashiga bin ƙira'ar da daddaɗar muryarsa
me daɗin sauraro .



Ɓangaren Inteesar ko juyar da kanta tayi tana kallon titi hakan datayine yabashi damar ƙarewa

fuskarta kallo ɗan motsawa tayi hakan yasashi saurin ɗauke kansa daga gareta cikin nutsuwa
yake tuƙi ganin hankalinsa ya karkata akan tuƙin taga ya nufi hanyar cikin gari da ita saurin
kallonsa tayi gani tayi ya wani make kamar besan metake nufiba sosai ranta yakai ƙololuwar
ɓaci da abubuwan da yikemata ta aro jarumta cikin tsiwa tace"Malam ajeni anan". yi yayi kamar badashi take ba hakan daya yimata baƙaramin ƙara tunzurata yayiba a harzuƙe
tace"Malam ka ajeni anan".
ƙara banza da ita yayi hakan yasa takai hannu cikin ɓacin rai zata murɗa handle ɗin motar kafin
taƙarasa taji ƙarar sa lock ɗinsa hakan yasa ta koma ta zauna tare da jingina da jikin kujerar ta
lumshe oily eyes ɗinta cikin kwanciyar hankali ya cigaba da tafiyarsa harya isa wani
tanƙamemen mall mesuna MAN OF THE WORLD SHOPPING MALL da manyan baƙi ƙarasa
shiga gurin yayi tare da yin parking a tanƙamemen parking space ɗin gurin yana daidaita
parking ɗinsa yaɗan saci kallonta gani yayi har bacci ya ɗauketa a haka jiyayi wani murmushin
dabe shirya yinsa ba ya kuɓucemasa ganin yadda ta duƙunƙune ne yasashi gane a.c tayimata
yawa yaɗan ragemata haɗe da kwantar mata da kujerar ya gyaramata kwanciyarta ya buɗe ya
fita tare dasa lock ta waje ya nufi cikin gurin bejima da shiga ba yafito bayansa da masu aiki a
gurin sanye da riguna da kaya niƙi-niƙi a bayansa danna key ɗin motar yayi har zasu zuba a
boot ya dakatar dasu yayimusu nuni da gidan baya cikin girmamawa suka zuba yashiga motar
yaja seda sukayi tafiya me nisa rasa hanyar dazebi yakaita gidane yasashi juyawa ya kalli inda
take gani yayi ta tashi taɓe baki yayi haɗe da cewa"ina zankaiki".
ba tare data kalli inda yike ba tace"Suleja amma a titi zan sauka".
ba tare daya tankamata ba ya juyar da kansa ya cigaba da tuƙinsa cikin kwanciyar hankali
yaƙara volume yashiga bin karatun Alqur'ani taɓe baki tayi a zuciyarta tace"ashe su wa'eeh an
iya abun mutane".
jin muryarsa tayi kamar a mafarki yace"keeeh dawa kike".
se lokacin tagane a fili tayi maganar tsuke bakinta tayi har suka isa bakin titi kamar yadda tace
dashi yayi parking gefan titi ba tare daya kalleta ba yasa hannu ya jawo ɗaya daka cikin ledojin
da yasa aka saka a baya ya buɗa ya fito da wasu rantsatsun abayas masu ɗaukar hankali ya
zaro ɗaya daga ciki ya buɗa ba tare daya kalleta ba yace"daka yau wa'innan kayan zaki riƙa
sawa da safarsu da niƙab ɗinsu dan bazan lamunci saka wannan banzan gyalen da kikeyi ba
domin Comphany ɗina ba gurin nanaye bane da mutum zaki riƙa saka wa'innan fugaggun
gyaluluwan naki masu kama da matacin koko a ciki akwai hijabs kowanne kowanne kaya da
kalar niƙab ɗinsa da hijab ɗinsa su zaki riƙa sawa".
wata dariyar rainin hankali tayimasa tare da taɓe baki ta aro jarumta tace"waikai meyasa kake
son takurawa rayuwata ne sekace wani mijina ina ruwanka da kayana kuma da kake cewa
gyalena kamar matacin koko meye naka a ciki naga tundaka gidanmu nasawo kayana meyasa
su basu yimun maganaba sekai kuma kai bakaga irin shigar da Sakatariyarka take ba se tawa
saboda ni kaɗai ka tsana to bazan dena sawa ba banason kayan kakaiwa matarka tasa domin
ni a ganina ita zakaiwa wannan kullen baniba".
taƙarasa zancensa tare da ture rigar daka jikinta cikin isa yace"ke wacece da zanyimiki kyauta
ki mayarmu dame kike taƙama baki isa kin karyamun record ba dole ki ansa".
wani kallon tara saura kwata tayimasa cikin tsiwa tace"mutum ce kamarka kai waye da baza'ah
mayarmaka ba masha Allah kaga seka aje record akaina anyi rejecting ɗin kyautarka domin ni
wallahu bazan ansa ba ka adana zasu yimaka amfani gun matarka".

taƙarasa zancen tare da saurin murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa'ah tajishi a buɗe tayi saurin fita
ganin ya kawo hannunsa da niyyar cafkota tafice cikin sauri dukda tanajin zafin ciwon da ƙafarta
ke mata karo na farko a rayuwarshi daya yi murmushi dukda rashin kunyar data tayimasa beja
motar ba har seda yaga ta tsallaka titi tahau napep sannan ya tada motarsa yabar gurin a guje.


8:30pm
Tsaye yake a ƙofar gidansu yanata dialing number ta amma amsar ɗaya switch off sosai
hankalinsa yayi mugun tashi ɗaga kannan da zeyi yaga Hauwah ta fito daka gidansu tunkaro
inda yike tsaye sosai yaji wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa bakinta ɗauke da sallama taƙarasa
murmushin daya ƙara masa kyau yayimata cikin girmamawa Hauwah tace"Uncle Zaid anyini
lafiya".
"inafa lafiya banji zuciyata ba ina zakijini naga ta lafiya".
sosai Hauwah daɗin kalamansa akan ƙawarta nanta labartamasa duk abinda yafaru a iya
yadda tasani sosai hankalinsa ya tashi sosai takejin daɗin yadda yake caring ɗin ƙawarta tace
"Uncle ka kwantar da hankalinka bara inshiga insanar musu seka shiga ka ga jikinta".
"aiko da kin temakeni domin bakiji yadda hankalina yayi mugun tashiba dukda kin faɗamun
amma hankalina yaƙi kwanciya in naganta hankalina yafi kwanciya".
"tom bara naje".
nanta shiga .



A tsakar gida tasamu Abbah da Uwar Gwarama zaune Abbah yana cin tuwo Uwar Gwarama
tana ƙuƙula magungunan mata da take siyarwa abinka dame sana'ah goma maganin me gasa
ƙarasawa tayi inda suke cikin girmamawa tace"Abbah sannunku da hutawa".
"yauwa Hauwah ya mutanen gidan naku".
"lafiya ƙlau Abbah dama Zaid ne yazo zamuje gidansu shine nike faɗamasa Inteesar ɗin batada
lafiya ……".
bata ƙarasa abinda take son cewa ba cikin zalama Abbah ya tari numfashinta da cewa
"meyasa to baki ce yashigo ciki yagaida itaba aida kince ya shigo aishima yanzu yazama ɗan
gida ko Tsahare".
tsilum Uwar gwarama tace"aiko dai Malam".
jin abinda Uwar Gwarama tace sosai yabawa Hauwah mamaki tace"ai Abbah nacemasa bara
inyimasa iso yashigo".
"toh! toh!! toh!!! kin kyauta ki sanar dasu suɗan gyatta seki shigo dashi".
"toh".
nanta nufi ɗakinsu Inteesar zaune tasamesu Khadijat na karantawa Inteesar wani littafin Real
eeshow mesuna ZANJIRATA sosai suke jin daɗin littafin domin yana kaimusu Umman su kuma
tana kan sallaya tana lazumi hararsu Hauwah tayi tace"yanzu nan saboda rashin mutunci shine
kuka cigaba da karantawa koku kirani inason jin yadda zata kaya tsakanin Amatujjabar da
Yayah Mahmud saboda dramar su nakaimun ".

"ya haƙuri Aunty Hauwah zan karantamiki kema seda nace tabari kizo taƙi kinsan Aunty da
gauƙa yanzu ma kuma muka fara".
"toh ƴar ƙanwata takaina ".
taƙarasa zamcenta ta nufar gurin Ummah duƙawa tayi ta sanar da ita zuwan Zaid sannan tasa
suka ɗan kintsa dukda ɗakinsu fes-fes yike basu da lalaci nanta fita tashigo dashi.



Uwar Gwarama na ganin fitar Hauwah ta kalli Abbah daketa sukurkuta lomar tuwo yana santi
tace"Malam bara inɗanje inɗan kunna turaren wuta sirikinmu bayazo yanaɗan jin bashi -bashi
ba kadai sanni da iya karramar baƙo bare kuma babban sirikinmu".
"aiko dai da kin kyauta".
wani shu'umin murmushi tayi ta wuce ɗakinta tana shiga ta iske Jameelah tana waya da
saurayinta cikin azama tace"ke banza kina nan kina shashsnci Allah yakawo mana dama Zaidu
yanzu ze shigo ya duba waccan tsinau ɗin ki tashi ki ɗebo rushi kizuba magain nan".
tsalle Jamilah ta buga tare da miƙewa cikin jin daɗi tace"I love you Mamah na maganin kukana".
ta fice cikin sauri murmushi Uwar Gwarama tayi ta tafi ta ɗakko maganin da boka yabata ta fito
waje a tsakar gida suka haɗu da Jameelah ta ebo wuta a marfin langa nanta jiki na rawa ansa
Uwar Gwarama tayi tana murmushi tace"yimaza kije kiɗan kintsa jikinki karya ganki kamar wata
ƴar jaka". "toh".
nanta wuce ita kuma ta buɗe maganin ta zuba .



Zaid na shigowa ƙamshin turarennan ya bugu hancinsa lokaci ɗaya yaji kansa yashiga
saramasa dakyar yake iya ɗaga ƙafa yake tafiya har suka isa!!!!!!!!




Votes and Comments
Plz share to others



_*Daga Alƙalamun *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)



*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…


*BOOK 1*


*PAGES* 2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣


Inda Abbah ke zaune yaƙarasa tare da zama kan sallayar da aka shimfiɗamasa ya zauna
cikin girmamawa yace"Abbah ina yini".
"lafiya ƙlau ya wajen iyayen naka".
"lafiya ƙlau Abbah suncema suna gaisheku".
"masha Allah Hauwah yimasa jagora zuwa gurin mejikin".
"toh Abbah".
taƙarasa faɗa tana kallon Zaid da bashi da niyyar miƙewa ɓangaren Zaid ko ji yayi duk bayako
son ganinta daurewa yayi ya miƙe da nufin bin bayasan sukaji muryar Uwar Gwarama dake
fitowa daka ɗaki cikin shiga ta alfarma jiki na rawa Zaid yayi saurin duƙawa yace"Ummah ina
yini". ganin yadda jikinsa yaketa faman tsuma baƙaramun daɗi taji ba a zuciyarta tace"kai gaskiya
Boka Tsula aikinka na kyau jibi yadda jikin wannan shu'umin yaron daya wulaƙantani yaketa
faman karkarwa kamar mazari kaɗanma kagani ɗan shegiya zaka kwashi kashinka a hannu
domin seka gane shayi ruwa ne seka zama tamkar raƙumi da akala domin Jameelah se yanda
tayi dakai badai kai ƙaramin tsageraba hadda wani cewa dani ni Inteesar nike itakuma har wani
gwalli takeyi wai ita zatayi aure gidan jindaɗi maga yadda za'ayi ayi auren matsawar ina
numfashi bazan taɓa barin ɗiyar Aminah taji daɗin duniya ba kamar yadda na hanasu jin daɗin
gidannan haka bazan taɓa barinku kuji daɗin gidan mijiba sede ku ƙare a bauta matsawar ina
numfashi ".
katsemata zancen zucin da takeyi Zaid yayi murya na rawa yakuma cewa"Ummah ina yini".
wani gauron numfashi ta sauke haɗe da dawowa daga duniyar tinanin data lula tace"lafiya ƙlau
yaron kirki ya wajen magabatan naka".
baki har ɓari yikeyi yace"lafiya ƙlau Ummah sunama gaisheku",.
a wani yatsune Uwar Gwarama tace"muna amsawa ɗiyar kirki ƴan makaranta kifito ga yayanku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login