Showing 1 words to 3000 words out of 39022 words

Chapter 1 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

1 A.M. Xanzaki

Gawa ta qi rami
1 A.M. Xanzaki

GAWA
TA KI RAMI
















Ayuba Muhammad Xanzaki

Gawa ta qi rami
2 A.M. Xanzaki

Copyright © Ayuba Muhammad Xanzaki
Haqqin Mallaka (m)
Ayuba Muhammad Xanzaki

Shekarar Bugu
2024

GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu wata’ala
Mai kowa Mai komai da Ya ba ni ikon rubuta wannan
littafi da na fito da shi. Tsira da aminci su tabbata ga
Shugaban halitta Annabi Muhammadu Sallallahu
Alaihi Wasallama da Alayensa da Sahabbansa.

GARGAXI
Ba a yarda wani ko wata qungiya su kwaikwayi
wannan labarin ta kowacce siga ba sai da cikakken
izni daga Marubucin. Sannan labarin ciki qirqira ne
wanda bai faru a gaske ba, idan an ji suna ko gari sun
zo xaya da naku ba da kowa ake ba illa iyaka arashi
da aka samu.

SADAUKARWA
Ga Aminina Marubuci Lawan Muhammad PRP,
da Ibrahim Muhammad Indabawa, da kuma Ilyasu
Garba Minjibir, yadda suka tsaya wajen tace min
labarin gami da gyare-gyare. Na gode.

Gawa ta qi rami
3 A.M. Xanzaki

TUKUICI
Ga matata Madeena da ‘yata Afnan, Allah Ya
qara musu lafiya da nisan kwana.

GAISUWA GA;
- Faisal Haruna Hunkuyi
- Zubairu M. Balannaji
- Bilkisu M. Sani Balare
- A’isha A. Bello (Fulani)
- Hassana Abdullahi Hunkuyi
- Dalhatu S. Mai Sharifiya
- Adamu Yusuf Indabo
- Abdussalam Musa Hotoro (Barista)
- Mubarak Idris Jiqamshi
- Sani Tahir

GAISUWA TA MUSAMMAN GA MALAMAN
ADABI:
- Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau
- Farfesa Ibrahim Malumfashi
- Farfesa Yusuf Adamu
- Malam Ibrahim Sheme
- Ado Ahmad Gidan Dabino (MON)
- Habibu Hudu A. Darazo

Gawa ta qi rami
4 A.M. Xanzaki

MABUXI
duk lokacin da al’amura suka cakuxewa
mutum yakan bi duk hanyoyin da yake
ganin sun kamata ko waxanda ba su
kamata ba don ya ga ya samu sauqi, wannan zavin
sa ne. idan mutum ya gaza samun mafita yakan yi
fatan a ce ba shi kaxai ba ne a cikin matsalar.
Alhaji Haruna bai tava samun kansa a
matsalar rayuwa ba sai wannan karon, yana daga
cikin mutanen da suka xauki kuxi a matsayin wani
makami na qare dangin matsalolin rayuwar
duniya. Mai kuxi ne na gaske haka nan kuma yana
tare da ‘yan siyasar da ludayinsu ke bisa dawo a
halin yanzu, ta yadda ba ya kukan alfarma, kusan
duk kowacce gwamnati da ta kafu da shi take
tafiya a matsayin xan baranda ko kuma mai aiki ta
qarqashin qasa saboda gogewarsa a fannin siyasa.
Hulxarsa da mutane irin su Alhaji Tanko
Bara’u da Alhaji Kawu Maitangaran ya sauya
masa rayuwa ta yadda ba ya fargabar yin komai
matuqar dukiyarsa za ta qaru. Ya tsani abu biyu;
asara da faxuwa a kasuwanci, haka nan kuma yana
son abu biyu; dukiyarsa da dukiyar wasu. Yana da
rauni guda xaya wanda ita ce matarsa da yake
mutuwar so.
A

Gawa ta qi rami
5 A.M. Xanzaki

Alhaji Haruna ya shirya wani gagarumin
kasuwancin voye da su Alhaji Tanko Bara’u inda
suka yi amfani da damarsu ta shiga siyasa suka
samar da hanyoyin safarar kayayyaki waxanda
haramtattu ne a doka. Sun yanke shawarar ba wa
Alhaji Haruna ajiya ne saboda shi ne mutumin da
bai yi shuhura ba a cikinsu, ta yadda ko da wani
bincike ya zo zai yi wahala dogon hannu ya iso
kansa. Alhaji Haruna ya ba wa matarsa ajiyar
kayan ba tare da ya sanar da ita ko mene ne ba.
Matarsa ta adana masa ajiyar a inda hannu ba
zai kai ba, sannan tunani ba zai hasaso ba domin
kuwa ita kanta ta yi nesa da ajiyar da ba zai yiwu
ta iya fito da ita cikin qanqanin lokaci ba.

Gawa ta qi rami
6 A.M. Xanzaki

______________BABI NA 1____________

FARKON LABARIN
lhaji Haruna Tinqwal na zaune a falonsa
na karvar baqi yaronsa Sani direba ya
shigo cike da tashin hankali a fuskarsa ya
tsuguna a gabansa.
Alhaji Haruna ya kalle shi cike da mamaki,
“Lafiya kuwa Sani na gan ka a wani hali?”
Sani ya girgizakai kafin ya iya furta, “Ranka
ya daxe Hajiya ce ta yi hatsari.”
Cikin alamun razana da damuwa ya gyara
zama, “Wacce Hajiyar? Matar da yanzun nan
muka gama waya da ita?”
Sani ya girgiza kai, “Alhaji da gaske ne,
yanzun nan na ji ana sanarwa a rediyo, kuma bisa
kwatancen da aka yi na tabbatar ita ce, domin har
sunanka aka ambata cikin sanarwar.”
Hankalinsa ya dugunzuma,, ya miqe tsaye a
fusace, “Tana ina?”
Sani ya ce, “Tana asibitin cikin gari, amma
dai jikin nata da sauqi.”
Alhaji ya miqe yana save malum-malum,
“Wanne irin zance ne wannan kake yi Sani?” ya
xauko wayarsa ya sake dannawa ya saka a kunne
A

Gawa ta qi rami
7 A.M. Xanzaki

amma sai ya riski kamfanin layinsa yana sanar da
shi cewa lambar da yake kira a kashe take.
Ya zari makullin mota da ke bisa tebur ya
riqe, “Mu je ka kai ni asibitin.”
Sani wanda ke cike da tunani iri-iri ya miqe
tsaye ya shige gaba yayin da Maigidansa ya bi shi.
A yadda ya san Ubangidan nasa yana matuqar
son matarsa bai yi tsammanin ba zai faxi ba in aka
ba shi labarin, duk da cewa kuwa bai gaya masa
ainihin abin da ya faru ba, amma sai ga shi garau
har yana iya takawa.
Lokuta kaxan suka taimake su wajen shiga
mota, yayin da gomomin mutanen da ke tsaye
suna jiran fitowar Alhaji don ya ba su abin miya
suka bi su da kallo, su kansu sun san Maigidan
nasu (na maula) yau yana cikin wani hali, duk
yadda aka yi wani abu ne ya faru maras daxi, a
yadda suka ga babban direbansa ya shigo a firgice
Allah Ya sa ba wata asara ce ta samu Maigidan
nasu ba, domin sun san shi farin sani, abu qanqani
sai ya xaga masa hankali ya hana shi sukuni.
Duk waxannan tunane-tunanen da mutanen
ke yi bai damu Alhaji ba, hankalinsa na can kan
tunanin a wane hali zai samu matar tasa, matar da
yake matuqar so haka kuma taskar ajiyar
sirrikansa, akwai abubuwa da yawa da ke tsakanin

Gawa ta qi rami
8 A.M. Xanzaki

sa da matarsa Hajiya Abu, wanda mutane ba su
sani ba, muhimmi a ciki shi ne voyayyiyar sana’ar
da yake yi wadda ke kawo masa kuxi da gaggawa,
ta san abubuwa da yawa game da haka, ita wata
jigo ce mai qarfi a tafiyar sa ta voyayyen
kasuwancinsa, yanzu in aka ce ta mutu ko ta yi
raunin da ba za ta moru ba akwai matsala! Tabbas
akwai matsala.
Yana cikin tunane- tunane da fata a zuciyarsa
sai ji ya yi Sani yana yi masa magana a sanyaye,
“Maigida mun iso.”
Alhaji Haruna ya sauqo suka bi sahun masu
shiga asibitin ta hanyar bin dogon koridon da zai
sada su da vangaren ‘yan taimakon gaggawa
(emergency) bai yi mamaki ba da ya ga wasu daga
mutane suna gaishe shi, abin da bai sani ba shi ne,
duk masu gaishe shi idan ya wuce sukan bi shi da
kallo suna girgiza kai.
Ganin za su wuce vangaren da ake kwantar da
marasa lafiyar sai ya kalli Sani cikin mamaki, “Ina
za mu je ne?”
Sani ya yi gyaran murya, “Likita ya ce in ka
zo mu same shi a ofis.”
Suka miqe zuwa ofishin likitan.
Akwai ‘yan sanda guda biyu a tsaye a bakin
qofar suna fuskantar juna suna hira, ganin Alhaji

Gawa ta qi rami
9 A.M. Xanzaki

Haruna ya nufo wurin sai suka dakata da magana
suka qura masa ido.
Cike da ladabi suka gaishe shi sannan xaya
daga cikinsu ya kalle shi cikin ba shi tabbaci ya yi
magana, “Yana ciki.”
Suka buxe qofar suka shiga yayin da ‘yan
sandan suka ci gaba da tattaunawa.
*** *** ***
Ofishi ne mai madaidaicin faxi wanda ya
mallaki wani makeken tebur daga can quryar
gabas na ofishin, tayil ne ya mamaye ofishin babu
masaka tsinke yayin da a kowanne bango akwai
takardu ko fastoci masu kala da ke nuni da
matakan kula da lafiya ko kariya ga wata cuta
musamman cututtuka masu yaxuwa.
Dakta Hamza Xorayi na zaune bisa kujera
yana faman rubutu akan wasu takardu, ya xago kai
ya kalle su sannan ya ci gaba da rubutunsa. Lokaci
kaxan ya ajiye alqalaminsa ya kalli Alhaji Haruna
fuskarsa ba yabo ba fallasa ya xan yi miqa ba laifi.
Alhaji ya qurawa Dakta Hamza ido yayin da
ya nemi wuri ya zauna a wata kujera da ke
fuskantar likitan.
Dakta Hamza ya jawo wani fayil da ke gefe
ya buxe cikinsa ya xan duba wani shafin sannan

Gawa ta qi rami
10 A.M. Xanzaki

ya tura wa Alhaji Haruna fayil xin wanda ke ta
kallon sa fuskarsa cike da alamun tambayoyi.
“Me zan yi?” Alhaji Haruna ya tambaya.
“Hannu za ka sa, ko ba su yi maka bayani
ba?”
Alhaji ya qanqanta idanuwansa cike da
mamaki, “Wanne bayani? Ni babu wanda ya yi
mini bayani. Me ya faru ne likita?” ya cire hula
saboda gumi da ya ji ya fara jiqa masa riga ta
wuya.
Dakta Hamza ya xan nuna mamaki a fuskarsa
yana kallon Alhaji Haruna, Ba su sanar da kai
Allah Ya yi mata rasuwa ba?”
Alhaji Haruna ya ruxe, a take cikin ruxewa ya
kalli likitan, “A’a an dai gaya mimi ta yi hatsari
tana cikin mummunan hali.”
Dakta Hamza ya yi gajeriyar miqa tare da
nuna alamun gajiyawa a jiki da fuskarsa ya yi
wata hamma doguwa mai haxe da qwalla, “A
gaskiya sun rufe ka ne ba su gaya maka gaskiya
ba, amma mu nan ba a kawo mana ita da rai ba
ma, tun a hanya ta rasu.”
“Hajiya ta rasu ka ce? Inna lillahi wa’inna
ilaihi raji’un…”
Daga nan bai qara cewa komai ba sai faxuwa
ya yi a qasa rigija!

Gawa ta qi rami
11 A.M. Xanzaki

*** *** ***
Labarin mutuwar Hajiya ya bugi zukatan
mutane da yawa a unguwar, sai dai a lokacin da
ake rurumar yi mata jana’iza, Alhaji Haruna na
kwance a asibiti yana karvar magani.
Bai farfaxo ba sai sha biyun dare tun qarfe
huxu na yamma, a wannan lokacin ne kuma ya
samu damar sanya hannu a takardar karvar gawar
da amincewa da dalilin mutuwar matarsa.
An ci gaba da karvar gaisuwa a qarqashin
jagorancinsa. Mutane da yawa sun zo yi masa ta’a
ziyya a cikinsu har da wasu hamshaqan abokansa
kuma shahararrun ‘yan siyasa; Alhaji Tanko
Bara’u da Alhaji Kawu Mai tangaran.
Bayan sun gama yi masa ta’aziyya ne Alhaji
Tanko ya kalle shi, “Duk da kana cikin alhini
amma wannan ba zai hana mu yi magana ba,
domin an ce ana bikin duniya ake na qiyama, ko
ba haka ba Alhaji Kawu?” ya qarasa maganarsa
yana kallon Alhaji Kawu.
Alhaji Kawu ya gyara zama, “Qwarai kuwa.”
Alhaji Tanko ya ci gaba, “wato tun watannin
baya muka yi maka magana game da kayan da
muka ba ka ajiya cewa watan nan muke son karva,
to ga yadda al’amari ya kasance, matarka ta rasu,
yaya ake ciki ne?”

Gawa ta qi rami
12 A.M. Xanzaki

Alhaji Haruna ya gyara zama, “Kaya kam
suna nan sai dai sai an yi bincike kafin a gane
yadda za a vullowa al’amarin.”
Alhaji Kawu ya kalle shi da mamaki,
“Bincike kamar yaya?”
Alhaji Haruna ya yi shiru yana tunani
fuskanrsa cike da damuwa.
“Ka yi magana mana Alhaji Haruna, ka yi
shiru ba ka ce komai ba,” cewar Alhaji Tanko.
Da qyar Alhaji Haruna ya iya yin magana,
“An xan samu akasi ne game da kayan, wato
sadda na karva saboda amincin da ke tsakaninmu
sai na ba wa Hajiya ajiyar kayan? To kuma tun da
ta karva ta sanar da ni za ta ajiye su a wurin da
hankali ba zai tava kaiwa ba ballantana wani
mahaluqi ya gane, ban sake waiwayar ta ba, da ma
tun da ta ce min za ta yi tafiya sai na yanke
shawarar idan ta dawo yau da daddare za mu
zauna mu tattauna mu ga ina ya kamata a adana
kayan ta yadda ba za su samu matsala ba
musamman saboda zarge-zarge na neman kunno
kai daga jami’an tsaro.”
Tun da ya fara maganar gaba xaya abokan
nasa suka xauke wuta suna kallon sa levvansu a
sake.

Gawa ta qi rami
13 A.M. Xanzaki

Wurin ya xan yi tsit da fari. Alhaji Tanko ne
ya fara magana, “Mu duk wani bayanin jami’ai ba
ya gabanmu tun da ka fi kowa sanin su wane ne
mu, amma dai ba mu qarasa fahimtar ka ba, kana
nufin ko kai ba ka san in da ta yi ajiyar ba ne ko
yaya abin yake?”
“Wannan shi ne babban tashin hankalin, shi
ya sa ma na ce sai na yi bincike mai xan tsawo.”
Alhaji Haruna ya mayar da amsa.
Suka jinjina kai gaba xayansu suna wani
tunanin, Alhaji Tanko har da cije leve. Ganin
Alhaji Kawu zai yi magana sai ya xaga masa
hannu ya dakatar da shi, sannan ya kalli Alhaji
Haruna ya ce, “Sa’arka xaya kana cikin alhinin
rashin iyalinka amma da a yau xin nan za a kashe
bos xin nan amma wannan ba zai hana mu ba ka
dama ka yi bakin qoqarinka ba, saboda ka san
haxarin da ke tattare da fitar bayanai a kan kayan
nan, kuma ka san yadda ba ma son sakaci da
dukiya musamman irin wannan mai tattare da
abubuwa masu yawa.”
Ya miqe tsaye ya kalli Alhaji Kawu, “tashi
mu tafi Alhaji.”
Alhaji Kawu ya miqe yana save babbar riga
tare da kallon Alhaji Haruna a fusace.

Gawa ta qi rami
14 A.M. Xanzaki

Suka nufi wurin motocinsu suka shiga suka
tafi.
Ya daxe a wurin yana tunani har sai da ‘yan
uwan marigayiyar suka zo ya tashi ya je don ci
gaba da amsar gaisuwa.
Da dare ya yi Alhaji Haruna ya kasa barci sai
yawan tunani akan yadda ya kamata ya nemi
mafitar wannan al’amari, a cikin daren ya tashi ya
fara binciken wurare masu muhimmanci in da
hankalinsa zai iya halartowa da inda hankalinsa ba
zai iya halartowa ba, sai dai kash! Duk vata
lokacinsa yake yi, domin bai samu riskar inda
takamaimai Hajiya Abu ta yi ajiyar nan ba.
Har ya haqura zai koma ya kwanta sai wani
tunani ya zo masa, da sauri ya koma ya zauna
jikinsa a sanyaye yana tunani, lokaci guda
qwaqwalwarsa ta fara halarto da abubuwa da
yawa.
Ya shiga zirga-zirga a xakin barcinsa yana kai
gwauro yana kai mari, gaba xaya tunaninsa ya
koma baya ya xebo abubuwa masu dama ya dawo
masa da su.
Tabbas! Biri ya yi kama da mutum, ya dafe
kai sannan ya saki kan ya kuma dafe kan cikin
tunani da kokwanton yadda abubuwan suka koma
haka.

Gawa ta qi rami
15 A.M. Xanzaki

Ya tashi tsaye ya ciro hotonta na bango ya
qura masa idanuwa, ya haura mintuna goma yana
kallon hoton sannan ya zaro idanuwa yana cije
leve a fusace.
“Makira, ki gama naki makircin ni ma nawa
yana nan tafe, kifi na ganin ki mai jar koma.”
Ya yi jifa da hoton gefe ya tarwatse, gilashin
hoton ya bayyana a fili, a sannan ne takardar ta
bayyana ta faxi, ya kalli takardar cike da mamaki.
Wannan ne mafarin al’amarin da ya haifar da
rikice-rikice da dama a wannan labarin, ciki har da
asarar rayuka.

*** ** ***
A qauyen Xansarai yayin da mazaje ke
kokawar cika rumbunansu da amfanin gona, wasu
kuma na qoqarin cashe wani sashe na amfanin
gonarsu da xurawa a buhu don kai wa kasuwa , a
wani gida kuma murna ce ta cika gidan da xokin
dawowar Hajiya Abu daga Saudiyya, yau
shekararta uku rabon ta da garin, tun sanda ta zo
musu da labarin mijinta ya rasu kuma har an raba
mata gado ta samu nata rabon, don haka Saudiyya
za ta tafi neman abin arziqi, domin ita da aure sai
ta samo abin huce takaicin wulaqancin da Maigari
ya yi wa mahaifinta a sanadiyyar neman aure ya

Gawa ta qi rami
16 A.M. Xanzaki

haxa su, tun daga wannan lokacin ba a qara samun
labarinta ba sai yanzu da ta dawo daga tafiyar da
ta yi.
Duk wanda ya san Abu a shekarun baya
(wadda a yanzu ta koma Hajiya Zainab) idan ya
kalle ta yanzu zai iya rantsewa ba ita ba ce, domin
ta yi qiba ta yi vulvul ta yi matuqar kyau, fatarta
har wani sheqi take yi. sannan ga haqoran Makka
guda biyu da ta jera ko yaya ta yi murmushi sai
haqoran su haskake fuskar wanda take kalla, duk
da ba ta dawo da kayayyaki masu yawa ba amma
mutanen gidan da danginsu na matuqar mamaki
da yadda suka gan ta, domin ita ce mace ta farko
da ta fara zuwa Makka (aikin Hajji) a faxin
qauyen, ko da Maigari da ake ganin ya tava zuwa,
umra ya je ya yi, shi ma albarkacin wani xan
majalisa ne da ya yi masa alqawarin kai shi
matuqar ya taimaka masa ya ci mazavar qauyen
da ake ganin yana da yawan jama’a a mazavun
qaramar hukumar da zai wakilta a tarayya.
Nan da nan labarin dawowar Abulo ya cika
garin aka yi ta zuwa ana taya ta murna, ‘yan
uwanta na hura hanci da alfaharin ‘yar uwarsu ta
je Makka ta dawo lafiya, yayin da ita kuma kan bi
yara da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login