Showing 21001 words to 24000 words out of 25520 words

Chapter 8 - INDA RAI B 3 end Book True Wallafar A'isha Aliyu Garkuwa .pdf

kika halicce ta ne?”.
Cikin zafin nama Addawa ta shiga tsakiyarsu tare da fara faɗin.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun, aoozubillahi mina sharrin shaidan.
Tajjuddeen kada fa ka lizimci muguwar ɗabi'a akan fushi”.
Cikin zubda hawayen Ishmah ta fara mgnar cikin murya mafi rauni tace.
“Addawa barshi ya dakeni ai ya saba! baya jin daɗin rayuwarsa sai ya dakeni yake samun yayi
numfashi mai daɗi!.
Barshi ya dakeni hakan shine riƙon amanar da Abbana ya bashi”.
Sai kuma tasa rafin hakan ta sharce hawayenta da wani ke korar wani murya a disashe taci ga
da cewa.
“Abba na ya haifa ya bashi ne ai don ya daka kamar ya samu ganga.
Hakan shine yarda da yaƙinin da Daddey na tayi mishi kafin barinta duniya”.
Haka nan Addawa taji tuni kalamanta sun sa idonta cikowa da hawaye.

Shi kuwa Tajj jin kalamanta yake suna zubo mishi wani irin suka da suya a ranshi ji yake yi
tamkar haɗashi da Allah takeyi kallon da take mishi ido na zubda hawayene yasashi yin ƙasa da
kansa.
Ita kuwa Ishmah tana mai gyara riƙon da tayiwa Daddey tace.
“Ya ɗaukoni ya kawoni ƙasar da bani da kowa nawa domin yaci zarafina,

Dan haka barshi ya nuna ƙarfin ikonsa a kaina.
Na sani Ubangiji na zai min Sakayy..”.
Sai kuma sheshsheƙan kukan ya kubce mata.
Da sauri kuma tasa tafin hannunta ta rufe bakinta tayi shiru sabida shigowar Hamisu da Laylah.
Shi kuwa Tajj ruggume Afishi yayi kan guiwowinsa tare da shafa kanta yana mai jin kalaman
Ishmah dake fita cikin tsananin rauni da rawan murya suna hukunta ruhinsa da jikinsa da ransa
baki ɗaya.

Ita kuwa Ishmah da sauri ta share hawayenta jin Hamisu na cewa.
“Ammey ga Ummeey da Yah Abana tare muke dasu fa.
Kuma sunƙi shigowa.
Please Addawa zo ku shigo dasu“.
Wani irin Ni'imataccen murmushi mai nuna tsananin jin daɗi Addawa tayi tare da komawa ta
zauna bisa kujerar dake bayanta tana mai sakin numfashi dake nuna tana da manufar zaman
alamun bazata jeba dan tasan rashin zuwanta kamar akalar jawosu cikine.

Ita kuwa Ishmah da sauri ta miƙewa Laylah Daddy tare da juyawa ta nufu waje da sauri tana
ƙara goge fuskarta.

Shi kuwa Tajj tamkar an dasashi haka ya kasa cewa komai sai shafa kan Afisha da yake yi
yanajin kalaman Ishmah da na Hamisu na haɗe mishi.

A waje kuwa cikin wani irin mabayyanin so da girmamawa Ishmah ta buɗe marfin motar gefen
da Ummeey take cikin Sassayan murya tace.
"Alhamdulillah yau gidanmu zai samu cikekken ma'anarsa na masu albarka da samun haske da
darajar ziyarta iyaye mafi girma da daraja da ƙololuwar iya bada tarbiyya a duniya, yau muma
zamu samu cikekken yaƙini da samun tsammanin albakar Ubangijin talikai tunda ga al'barka
iyayenmu mafi soyuwa a garemu. Bismillah Ummey ku shigo”.
Wani irin sassayan numfashi Yah Abana ke fesarwa tare da zuba mata idanunsa masu cike da
sonta da yaranta.
Ita kuwa Ummey murmushi takeyi tamkar zata haɗiyi haƙorinta.
Sai kuma ta nunawa Ishmah inda Yah Abana yake alamun izininsa take buƙata.
Da sauri Ishmah ta zagaya daya gefen.
Cikin yin ƙasa da murya da girmama tace.
“Barka da zuwa Yah Abana, dan Allah Yah Abana shigo ko dan Addawa muma muci darajar
Manzon Allah”.
Cikin kulawa Yah Abana yace.
“Sallallahu alaihi Wasallama”.
Ya faɗa tare da fitowa daga cikin motar”.

Wani irin sassayan numfashi mai haɗe da ruwan hawaye Ummeey ta fesar lokacin da suka
shigo cikin corridor ɗin.

Ita kuwa Ishmah da sauri ta fara haura saman steps ɗin zuwa sashi mafi girma da daraja a
gidan wato side ɗin Tajj.

Taka step ɗin forko tayi tare da buɗa muryarta cikin sauti mai cike da farin ciki take cewa.
“Addawa Laylah Ayeed Ayaan kuzo sama Addawa kuzo da sauri.”
Sai kuma ta kalli Yah Abana da Ummiey da idonta keta zubda hawayen.
“Bismillah Yah Abana Ummey ku taho”.
Cikin wani irin yanayi mai ratsa zuciya suka fara haurawa.

A parlor kuma da sauri Addawa ta kamo hannun Tajj da har yanzu yake tsaye,
Jawo shi tayi suka nufi wurin da Ishmah ke kiransu.

Yayinda ta yafito Laylah da Hamisun dasu Zulaihat da ta fito dasu Ayeed cikin shigar Jallabiyar
sky blue color.


kusan duk a tare suke taka steps ɗin.

Su kuwa Yan Abana da Ummeey kan 3 sitter suka zauna tare da sakin numfashi a tare suna
masu kallon tangamemen hotonsu dake kafe a tsakiyar falon wanda yafi tv falon girma.

Wani irin rawa da karkarwa jikin Tajj ya saki lokacin da yayi arba da Yah Abana da Ummeey a
parlornshi a cikin gidansa a zaune a kan kujera.

Wasu irin zazzafan hawaye ne suka fara kwaranyowa mishi saboda ganin yadda Yah Abana ya
buɗe masa hannayensa duka biyu alamun yazo ya ruggumeshi.
Cikin wani irin sassarfan da yafi kama da gudu gudu sauri-sauri, yazo ya faɗa jikinshi.
Cikin wani irin tsananin tausayi, ƙauna so, bege, kewa, rauni, gami da nadama mai zurfi Yah
Abana ya ruggumeshi.......






By
*GARKUWAR MARUBUTA**INDA RAI*
Part 3 page 5
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu
son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai
musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones
din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa
mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke
taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida
sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima
wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba
sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar
musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu
yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani
na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato
cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai
daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta
whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa
bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin
shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu
karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine
karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account
number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar
da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan ce nasunesayan na gari meda
kudi gida....

Ƙam-ƙam ya ruggemishi cikin jikinsa tamkar wanda yake tsoron kada a kwace masa shi.
Shi kuwa Tajj sai kawai ya fara sakin wani irin sheshsheƙan kuka mai tsanyi da rauni wanda yafi
kama da Ajiyan zuciya.
Ummey kuwa kawai sai ta zame ƙasa da durƙushe tayi sujulshukur kamar yadda taga Addawa
tayi.

Suna ɗagowa kuwa kawai sai suka ruggume juna.

Afisha Ayeed da Ayaan kuwa da sauri suka isa inda Tajj ɗin yake suka kwanta a jikinsa da sauri
Yah Abana ya ƙara buɗa hannayensa ya ruggumesu duka, sai kuma ya miƙawa Laylah hannun
alamun ta miƙo mishi Daddeey, da sauri ta muƙa mishi tare da zamewa ta zauna kusa dashi
inda ya nuna mata.

Haɗesu yayi kab a jikinsa ya ruggemesu, tamkar wanda yake tsoron kada a kwace masa su sai
wani irin dogon numfashi da Ajiyan zuciya yake sauƙewa.
Hawayen da yake riƙewane suka kwance mishi, hakan yasa yayi saurin sunkuyar da kanshi.
Sai kuma ya fara shafa kan Tajj tare da ɗan bubbuga kafaɗarsa cikin Sassayan murya yace.
“I miss you so much Abbana, Allah yayi maka al'barka ya rufa maka asiri duniya da ƙiyama ya
raya maka ahlinka. Allah ya ƙara dawwamar da kai cikin farin ciki da kwanciyar hankali Allah ya
dauwamar da zaman lfy tsakaninka da Matarka yariyar kirki mai mutunci da karanci.”
Cikin murmushi mai tafe da hawaye Ummey da Ishmah da Addawa suke Amsawa da.
“Amin Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil alamin”.
Cikin sauri kuma Ummey ta koma ta zauna gefen Yah Abana tare da yafito Ishmah.
Da sauri Ishmah tazo ta durƙusa gabanta tare da ɗaura kanta bisa cinyoyinta.
Hamisu kuwa mai raunin zuciya kamar mace tuni hotuna da vidio yake musu yana share
hawayen dake zubo mishi.

Ita kuwa Ishmah cikin farin ciki mara misaltawa dan ji takeyi ta samu surka me zame mata
madadin uwar data rasa.
Ummeyy kam shafa kanta take da sumbatar goshinta.
Sai kuma ta zuba idonta kan kuncin Ishmah da ya sha tarine Tajj, wanda har yanzu shatin
yatsunsa ke kwance kana jan da fatar tayi bai washeba, cikin tsananin kula daso tasa tafukan
hannunta duka biyu ta tallabo fuskar Ishmah tare da cewa.
“Ɗiyata meya ya sameki a fuska!?”.
Tayi tambayar ne cikin tausayawa.

Tambayar da tasa Addawa zuwa Tajj Ido shi kuwa Tajj da sauri ya kalli Ishmah cikin wani irin
salon kallon da yafi kama da na ta rufa mishi asiri.

Wani irin kallon da yafi kama da bata son kallonshi ta watsa kishi tare da tsuke fuska kana ta
dawo da kallonta kan Ummeyy murmushi tayi tare da kauda zance, ciki jin dadi tacewa Zulaihat.
“Zulaihat tashi muje mu kwaso basket ɗin abinci su Ummeey da ma sauran duk womars ɗin
abincin”.
Cikin girmamawa Zulaihat ta fice da sauri kuwa ta fara kawowa.

Ummeyy ido ta kuma dubawa Ishmah ta buɗe baki da nufin ƙara tambaya sai kuma taji Ayeed
ya faɗa jikinta, haka yasa ta jawosu jikinta tare da cewa.
“Jikokina ababen so da alfaharina”.

Shi kuwa Tajj cikin sauƙe numfashi farin ciki ya ɗago kanshi tare da kallon Yah Abana sai kuma
ya kalli Ummeyy, cikin jinsa tamkar yaron goye ya kwanta da kansa a tsakiyarsu cikin rawan
murya yace.
"Yah Abana, ka gafarceni ka yafe min, ka ƙara min addu'a da yafiya, al'barkar nan bata
isheniba, dan bazata goge fushin tsawon shekaru tara ba”.
Cikin sauri Yah Abana yace.
"Waya cema ina fushi da kai? Bana fushi da kai Abbana, Allah yayi maka al'barka ya ƙare min

kai da ahlinka baki ɗaya da muguwar ƙaddara”.
Da sauri ya zame ya zauna ƙasa tare da jawo ƙafar Yah Abana ya ɗaura kan cinyarsa tare da
fara yi mishi massaging sawunsa kamar yadda yake masa kullum in suna tare.
“Yah Abana ka yafe min? Ka amince inci gaba da alaƙantuwa da yan uwana? Ka yarje min
inyiwa Ummeyna magana? Ka bani dama in sake haɗa sunana da naka? Ka amince ince kai
mahaifinane? Ka dawo sani cikin yankaka? Ka janye sharaɗin da kai akan cewa in na matso
inda kake ko na kula ahlinka akan auren Ummeyy na? Ka bani dama inje Ethiopia? Ka yarda
in....”.
Da sauri Yah Abana yasa hannunsa kan bakin Tajj ɗin kana ɗaya hannun kuma ya fara sharce
masa hawayensa dake zuba cikin tsananin nadama yace.
“Na yafe maka komi da komai na yarje maka komi da kamai ɗana”.
Da sauri ya juya ya fuskanci alƙibla yayi sujulshukur sai kuma ya kife kansa kan cinyar
Ummeeynshi tare da ruggume sawunta sam.
“Allah yayi maka al'barka ya rufa maka asiri duniya da ƙiyama ya albakar yaranka”.
Wani irin yelwataccen murmushi ya saki wanda yasa Ishmah tsaida kallonta kanshi iya tsawon
zamanta dashi bata taɓa ganin irin wanan mashahurin farin ciki a cikin murmushinsa ba
kalamansa take juyawa na sharaɗin mahaifinsa akansa cikin ranta take jujjuya kalaman.

Gyaran murya Yah Abana yayi tare da ɗan zamowa ƙasa ya zauna bisa carpet ɗin dake wurin
cikin girmamawa ya gaida Addawa tare da cewa.
“Ki gafarceni a bisa hukuncin da na yanke kan Abbana, na kuma gode da kulawar da kika
bashi, Allah ya biyaki da mafi kyawun sakamako. Ki yafe min ki kuma samin al'barka, dan
darajar Manzon Allah”.
Cikin murmushi mai cike da tarin jin dadi Addawa tace.
“Ba komai Muhammad ai dama rayuwa ta gaji haka, kuma komai yayi forko zaiyi ƙarshe”.
Daga nan suka fara gaishe gashe, shi dai kam Tajj tamkar zai koma cikin iyayen nasa.

Ethiopia cikin kwaffa Mom Amal tace.
“Nifa tunda Malam ya tafi bamuyi magana ba, ko na kira layinsa na Saudia baya shiga.
Sai in ta Whatsapp na kirashi yana online kuma bai ɗaukaba, gsky na fara shiga ruɗani anya
kuwa Malam Umran ya tafi?”.
Cikin sauƙe dogon numfashi Kabeeru yace.
“Nima nayi zaton nan domin naga makar akwai abinda yake ɓoɓɓoyewa”.
Cikin sauri tace.
“Kai Malam dai akwai abinda yake ɓoyewa Amman zan bincika wlh sai na gano koma menene”.
Cikin lumshe ido Amal yace.
“Nifa ban damu da inda Malam yaje ba.
Kawai lamarin yarinyar nan Meymey ne nake jin tsoron sharrinta dan naga da taji tsarin plan C
ɗinmu akan Afif kamar ma ta fimu zaƙuwa a kai don ko ɗazu saida ta kirani”.
Cikin sakin makirin murmushi Aryan yace.
“No kada kuji komai wannan Meymey tuni na sauya mata hankali da tunani tana tare damu fiye
da zatonki”.
Daga nan sukaci gaba.

Qatar cikin sanyi Yah Abana ya shafa cikin Tajj.
“Zo zauna nan Abbana zo muci tare dan cikin nan da yunwa”.
Ya ƙare mgnar yana matso da plate ɗin da Ishmah ta zuba mishi cips da pepper chicken, da yaji
albsa da ƙayan ƙanshi.
Sai ɗaya plate ɗin kuma jolof ɗin Couscous ne da yasha kifi da jan nama, gami da dafaffan ƙoi.
Sai kuma wani ɗan bowl mai ɗan girma da ta zuba mishi ferfesun kifi na musamman.
Hakama ta sawa Ummeyy ma.
Sai kuma su Ayeed da Ayaan.
Murmushin mai cike da farin ciki Ummeyy tayi tare da kallon Laylah da Afisha tace.
“Kuzo muci tare to”.
Aiko da sauri Laylah da Afisha suka matsota.
Da sauri Ishmah tace.
“Ummey zasu dameki da suturu musamman wanan kabaran ke tashi a wurin”.
Ta ƙare mgnar cikin tsukewa Afisha fuska da watsa mata harara.

Da sauri Yah Abana yace.
“A'a Ishmah ai yau lokacin sune, barsu suci tare, Ayeed Ayaan kuma kuzo nan muci Hamisu
maza kaima taho nan”.
Aiko da saurinsu suka matso shima Hamisu cikin farin ciki ya matso.

Shi kuwa Tajj ido ya zubawa Ishmah cikin tsoron matakin da take shirin ɗauka akan Afisha na
hantara da kyara.
Jin kamar ana kallonta ne yasa ta ɗan watsa mishi kallon fushi da harara ƙasa-ƙasa.

Addawa kuwa cike da kunya ta surkai tace.
“To ni bari Inyi nan”.
Da sauri Ishmah tace.
“Addawa jirani. Zulaihat sakowa Addawa abinci da naki zo kici mu shiga kitchen”.
Sai kuma ta ɗan kalli Ummeyy cikin sakin fuska da girmamawa tare da cikar kulawa cewa.
“Ummeey me kuke so in dafa muku”.
Kai Tajj ya ɗago yana kallonta cikin mmkin yadda take sarrafa farin cikinta a kan kowa banda
shi da Afisha da take musu mugun kallo na cikar fusata da masifa.
Fuska ta tsuke tare da kauda kanta gefe tamkar wacce bata son ganinsa.
Kai ya sunkuyar fuska ɗauke da guntun murmushi gefen baki jin Yah Abana na miƙa mishi
spoon.

Cikin tsananin so Ummeeyy tace.
“Ishmah wannan ɗinma ai bamu cinyeba, ki huta yanxu kam”.
Da sauri Laylah tace.
“Ummmey yau kam ma ni zanyi muku girki kuji irin girkina”.
Sai kuma ta kalli Zulaihat dake cewa.
"Eh Ummey da nima ba da kina min dariya ban iya girkiba yanzu Ammeey ta koya min yau

zakisha mamaki”.
Cikin jin dadi Ummeyy tace.
“To ɗiyata kinji ko ki barsu sune su shiga kitchen.”
Cikin girmamawa tace.
“To Ummeyy na Amman zanyi muku abinci ƙasar mu Nigeria ko kala ɗaya ne ku faraci, in yayi
muku daɗi sai in rinƙa yi muku irinsa”.
Da sauri Yah Abana yace
“Yau mamana kiyi min tuwo da miyar kase in akwai kayan haɗin in babu kiyi min miyar ya
yakuwa yaji gyaɗa ko zogale”.
Cikin mmki Ishmah tace.
“Toh Yah Abana in sha Allah zan maka”.
Daga nan suka fice tana mmkin ya akayi yasan miyoyon Nigeria harma kase da tasan a Nigeria
ma a yankin Adamawa ne tushen miyar”.

Suna shaga falon suka zaunan Addawa da Zulaihat na cin abinci ita kuwa kitchen ta wuce dan
fara ɗaura miyar.

A can parlor Tajj kuwa cikin tsare Yah Abana da ido Ummeyy tace.
"Ni dai farin cikina bai cikaba”.
Da sauri suka kalleta shi kuwa Yah Abana cikin yin ƙasa da kai yace.
“Amman dai ba laifina bane ko?”.
Tana ɗan kurɓan tea tace.
“Naka ne mana”.
Murmushin Tajj yayi tare da sunkuyar da kansa.
Uwa kenan sai yau ya gane hikimar Addawa da ta nace dole Ummeyy ta zauna dashi gashi da
hikimarta ta uwa ta gyara komai da haƙurinta da addu'arta da juriyarta.

“To me kuma nayi Fatima ni Muhammad da bana rasa laifi”.
Tana tsuke fuska tace.
“So nake inga yayana mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login