Showing 24001 words to 25520 words out of 25520 words

Chapter 9 - INDA RAI B 3 end Book True Wallafar A'isha Aliyu Garkuwa .pdf

anan in ganni a tsakiyarsu a gidan dan uwansu su ganshi ya gansu
suga yaransa da matarsa”.
Yanzu kam murmushi Tajj ya kasa ɓoyuwa, Allah sarki uwa.
Shi ko Yah Abana cewa yayi.
"Daɗina da Fati gaggawa, in kinyi haƙuri ai Ethiopia gaba ɗaya zai koma yaga kowa, kowa ya
gansa ko Abbana”.
Da sauri tace.
“Kafin nan dai yarana su zo”.
Yana kai tsokan kifi bakinsa yace.
“Wata ƙil dai kin mance ba nine keda ikon basu izinin fitaba tun dai duk da aurensu da mazan
su suna ɗakunansu”.
Cikin sauri tace.
“Tun da safe da ka shiga Wonka na gaya musu muna Qatar kuma nace su tambaya in mazansu
sun barsu.

Shi ɗan uwansu zaiyi amfani da matsayin aikinsa na Pilot ya samar musu daman zuwa koda a
matsayin ganin doctor zasu zo yin dan shin zasu fi samin sauƙin zuwa yau ko gobe.
Kaga matsayinsa na Doctor mai girma da asibitin sa, asalinsa ɗan Ethiopia kuma shi Pilot abin
bazai gagaraba ko Afif?”.
Ta ƙare mgnar da tambayarsa da sauri yace.
“Sosai ma kuwa Ummeyy in dai mazansu sun barsu”.
Ya ƙare mgnar yana kamo hannun Afisha tare da cewa.
“My happiness kin gama ne?”.
Yayi tambayar cikin tausayinta, Allah ya sani bazai taɓa iya jurar hantar Afisha ba, da Ishmah ta
ɗauko dan yasan zafi da ƙuncin dake cikin zuciyar ɗa in itayensa na fushi dashi ko hantara.
Cikin sanyin da tunda Ishmah ta wasa mata harara ta gyaɗa mishi kai.
Sai kuma suka kalli Ummeey da ta.
Ta kalli Yah Abana tace.
“Tunifa mazansu kam sun barsu ma”.
Murmushin mai sauti Yah Abana yayi wanda yasa duk suka kallesa cikin raha yace.
“To wai waya gaya Miki dama zamu zo nan ne har kike gayyato tawagarki?”.
Tana shafa kan Afisha tace.
“Na gane son Afisha ya zame maka linzamin zuwa wurin iyayenta ai”.
Murmushin sukayi baki ɗaya har Hamisu dake haɗawa Tajj tea.
Laylah kuwa tana miƙe mishi tea ɗin da ta haɗa mishi tare da cewa.
“Gashi yayi sanyi yadda kakeso karɓi ka sha”.
Da sauri Ummeyy ta kalli Laylah tare da cewa.
"Wai ni kam Afif Laylah kam da Hamisu kam meke tafiya ne?”.
Yana murmushi yace.
"Ummeyy ai bikinsu saura wata shida, kai inaga ma bazai cikaba, kawai zan aurar dasu”.
Ya ƙare mgnar da jin tamkar akwai rauni a farin cikinsa da yake tunanin bashi da ranar farin ciki
kamar yau a duniya.

Cikin maganar girma da fahimtar Yah Abana yace.
“Eh to hakan zai fi, in sha Allah a Ethiopia za'ayi bikin nan kusa”.
Cikin sunkuyar da kai Hamisun yace.
“Ngd Yah Abana Allah ya ƙara girma”.

Ita kam Laylah tuni tayi ƙasa.

Shi kuwa Tajj fuska ɗauke da murmushi ya kamo hannun Afisha tare da miƙe tsaye tare da
jawota tsaye yace.
“Zo muje wurin Ammeey ko muga me zata dafa su Ummeey”.
Ya ƙare mgnar tare da janta suka nufi ƙasa.

Ummeyy kuwa da ya Abana hira sukeyi sosai dasu Ayeed.

A ƙasan kuwa, da ido Addawa ta rakashi lokacin da ya leƙa ɗakin Ishmah ganin bata cikine

yasa shi fotowa ɗan jujjuya kai yayi kamar mai neman abun da ya ɓace masa, sai kuma ya ɗan
shaƙi numfashi jiyo mai sanyi tare da jan hannun Afisha suka nufi kitchen ɗin.

Ita kam Addawa kai ta jinjina tare da ci gaba da cin abincinta.

Cikin tsuke fuska ta kauda kanta da sauri ta ta ƙarayin kici-kici da fuska tare da janye idonta
daga cikin nasa idanun taci gaba da motsa kayan miyan da take siyasa tamkar ba wani halitta a
wurin.
“Hmmmm”.
Ya fesar da ƙuntaceccen numfashi sai kuma ya sunkuyo kan Afisha bakinshi ya kai gab da
kunnenta cikin sanyi da yin ƙasa da murya yace.
“My Happiness”.
Da sauri ta amsa tana ɗago kanta tare da kallonsa da idanunta da sukayi tab da hawaye
saboda ganin kallon da Mahaifiyartan tayi mata, a hankali ya ɗan jujjuya mata kai cikin sanyi
yace.
“Meya sameki?”.
Sharr hawayenta suka kwaranyo cikin tsoro tace.
“Abeey Ammeyy na fushi takeyi, ban san me nayi mataba”.
Da ƙarfi ya rumtse idanunsa don jin wasu masofaffun hawaye masu ciwo na ratso mishi jijiyoyin
ido cikin sanyi yace.
“Kije gabanta ki durƙusa ki kama ƙarfata ki bata haƙuri kice ta yafe miki, ta daina fushi dake tayi
mana dariya”.
Cikin sauri tace.
“Abeey ina tsoro zata dakeni”.
yana ɗan turata zuwa gaban Ishmah yace.
“No je ki bata haƙuri kice mun tuba”.
Cikin ɗari-ɗari ta isa gaban Ishmah da tayi kamar bata san da ruwan tsironsu ba cikin sanyi ta
tsaya gabanta tare da sa hannun ta da nufin riƙota cikin daka mata hargitse tsawa tace.
“Ke kada ki yarda ki taɓani ɓace min daga nan”.
Cikin tsananin tsoro da rauni Afisha ta fashe da kuka mai cike da firgici tare da cewa.
“Please Ammey koyi haƙuri ki yafe min bazan dake Miki oyoyo ba tunda bakya so bazan ƙara
ce Miki i miss you ba tunda bakya so nayi alƙawarin bazan ƙaraba kinji kuyi haƙuri mun tuba”.
Sai kuma kawai ta durƙusa a gabanta tare da sakin maraitacccen kuka.
Cikin tsuke fuska ta sake watsa mata tsawa.
“Ke kinafa cika min kunne”.
Yah Salam shi kam Tajj tuni hawayensa ke kwaranya tausayin Afisha ya Barka mishi zuciya
haka yasa da sauri ya durƙusa gabanta tare da rungumota yana shafa bayanta.
Ita kuwa Ishmah baki ta taɓe tare da ficewa ta bar musu kitchen ɗin.

Tana fita Laylah na shiga hakan ne yasa Tajj ɗaukan Afisha ya koma sama da ita domin ji yake
tamkar zuciyar sa zata fashe ya sani ganin su Ummeyy a gidansa a tare da sune kawai zai sa
ya danji sanyin azabar suya da zuciyarsa keyi sosai kuwa zama tsakiyarsu yasa yaji sanyi
Afisha tuni ta sake wurin kakanni shima har yana murmushi.

Alhamdulillah ranar dai haka suka wuni cikin farin ciki.
A kuma ranar Tajj ya gamawa su Maryam, Rashida, Halima, da dama taxo tana Ethiopia da
Zakiya duk ya gama musu shirin su akan nanda kwana uku zasu taso.

Misasalin ƙarfe tara Yah Abana ya kalli Ummeyy tare da miƙewa tsaye yana meda kallonsa kan
Hamisun yace.
"Dare yayi fa, tashi muje Hamisu ya maidamu”.
Da sauri Tajj yace.
"Yah Abana ya maidaku ina? Please dan Allah kayi haƙuri ku zauna dan Allah kada ka hanani
samun wannan ladan”.
Sai kuma ya kalli Ishmah dake cewa Ummeyy Dan Allah.
Ummeyy kuyi haƙuri dan Allah ga ɗaki nan”.
Ta ƙare mgnar da nuna ɗaya bedroom ɗin dake gefen hagun daman wanda nanne turakan Tajj
ɗakine da babu abinda babu a ciki, dan bai dade da canza kayan ɗakinba kuma tunda aka
zubasu ko sau ɗaya basu kwana a cikiba.

Cikin lumshe ido Ummeyy tace.
"Yo ai ni babu inda zanima yau kam da Addawa na zan kwana shekara tarafa ba kwana taraba,,
wata ƙil shi kaɗai zai tafi zaka ɗauko mana kayanmu ne ko Malam?”.

Murmushin Ishmah tayi tare da tattare kwanukan da sukaci abinci ta aje kan dinnin table kana
ta ce Ayaan ya kirawo Laylah tazo ta tattare.

Sai kuma ta wuce bedroom ɗin Tajj wanda tsakaninsa da wannan kitchen da dinkin area yake.

Komai fes a ɗakin saboda shi ba irin hargitsatsun mazan nan bane.
Harara ta liƙawa gadonshi kamar shine a kwance a wurin.

Key ta ɗauko ka tazo ta buɗe wannan ɗakin ta shiga ba wani dadti ko kaɗan amman sai da ta
ƙara gyarawa tare da sauya bedsheet da blankets ta ƙara gyara bathroom kana ta ɗauko musu
dukkan abin buƙata ta kawo musu tare da sa musu turaren wutan.

A can parlor kuma cikin bada umurnin Tajj yacewa Hamisu yaje.
Hotel ɗin da suka sauƙa ya ɗauko musu kayansu, sannan ya biya su kuɗin in ma akwai”.
Cikin fesar da numfashi Yah Abana yace.
“Babu ma, dan dama kuɗin one week na biyasu”.
Cikin sauri Tajj yace.
“Rabonsu ne, Yah Abana”.
Sai kuma ya kalli Laylah data shigo tattara kwanu kan yace.
“Laylah tea”.
Da sauri tace to.

Dai-dai lokacin Ishmah ta fito daga ɗakin da yake ta baza wani irin Ni'imataccen ƙamshin.
“Sai kuma ta kalli Daddey dake hannun Ummeyy hannu ta miƙa da niyar amsarta da sauri
Ummeyy tace.
“Barta baccin baiyi nisa ba”.
Kai ta jinjina kana ta kalli Ayeed da yake ta jan hannun Yah Abana yana cewa.
“Yah Abana zauna in zauna a cinyarka”.
Murmushin Yah Abana yayi tare da cewa.
“To my Twins ina Ayaan ɗin kuma”.
Da sauri Ayaan yace.
“Gani ta nan”.
Dariya yayi ganin shima ya riƙe gefen alkebarsa”.
Shi kuwa Tajj cikin dadin ganin yadda suka zagaye iyayen nasa yasashi miƙewa tare da cewa.
“Ku bar min Yah Abana da Ummeyna sun gaji, Yan Abana zo muje kaga ɗakin in yayi maka, in
baiba a canza wani”.
Yana ƙarewa parlor kallo yabi bayansa.

Itama kuwa Ummeey bayan Ishmah tabi.

A Laylah kuma ta hauro da tray kayan tea da flacks a hannunta.
Da sauri tace Yauwa Ummey amshi kawo Daddey.
Kai Ummeey ta jinjina tare da cewa.
“A'a kai mishi”.
Daga nan suka sauƙa.

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login