Showing 6001 words to 9000 words out of 25520 words
Chapter 3 - INDA RAI B 3 end Book True Wallafar A'isha Aliyu Garkuwa .pdf
gwani,
wanda zai wakilci ƙasar su gasar rawar yara ta duniya da za'ayi a Dubai.
Cikin salo na ɗaukan hankali ya fara karairaya jikinsa tamkar babu ƙashi, tuni suka fara ihu da
ta'ujjibi hatta jojis ɗin mamaki suke suna sai sare ido suke tare da buɗe baki suna kallon ikon
Allah.
Tun da ya fara rawar wajan ya ruɗe matuƙa fiye da yadda aka ruɗewa sauran abokanansa na
fidda gwanayen da zasu wakilci tawargar gasar rawar.
Ganin ihun da kuma nuna yadda ya birge su ya ƙara masa ƙaimi wajan yin wasu salon rawar da
ba a saba gani ba musamman a wajan yara irinsa, tuni mutane suka miƙe tsaye suna tafi wasu
na tsalle suna kiran sunansa.
Yasir! Yasir!! Yasir!!!!!!
Tun kafin lokacinsa ya cika jojis uku suka danna masa likes wajan ya ƙara ruɗewa wanda ke da
tabbacin ya haye matakin gaba tabbacin dashi za'a wuce Dubai.
Lokaci na cika ya tsaya cikin salon rawar da sai da mutane suka bushe da dariya sai kuma ya
juya ya fuskanci jojis ɗin tare da ɗaura hannunsa na dama kan ƙirjinsa gefen hagu kana ya ɗan
sunkuyo alamun gaisuwa da girmama a yarensu na yan rawa.
Kana ya koma wajansa cike da tafiyar alfahari da jin ƙasaita domin ya san ya gama cinye
wannan ɓangaren.
Washe gari. QATAR.
Gidan cike yake da mutanen arziƙi masu zuwa sam barka, da taya su murnar lashe gasar
karatun Alkur'ani da yaran gidan suka yi musamman Afisha da acikin awanni ƙalilan vedios ɗin
ta ya ƙaraɗe media.
Rahma na zaune kusa da Ishma hannunta riƙe da yaranta ƴanbiyu, maza Shuraim da Shu'aib
Dr Farida da yarinyar ta Amani, da kuma yaron ciki da take da shi, sai Sister Nuraini da kuma
sauran maƙotansu.
Ƴar ƙaramar walima aka yi ta murnar nasarar da suka samu kana aka yi rabon gift na
al'qura'anil kareem da sauran hadisai da kuma ƙira'ar Afisha da ta yi kamar yadda babanta ya
yi, tun daga falaƙi har Kahf, cikin zazzaƙar muryarta, tuntuni ta yi, ya bari ne sai bayan sun
gama gasar ya fitar da karatunta, haka suka gama kowa ya watse bayan hotuna da vedios da
aka yi mata.
Ishmah ce ta ƙwace wayarta a hannun ƙaramar yarinyar ta Daddey da take ta tura ta a baki,
tana goge wayar kiran Arfah ya shigo, sai da ta yi murmushi kana ta ɗaga cikin jin kewarsa.
"Arfah, fatan kana lafiya.?"
Dariyarsa ta ji cikin muryarsa ta matasan maza ma su ji da kansu.
"Ammeyna, fatan kowa na lafiya har rabin raina Afisha."
Ɗan murmushi ne ya kufce mata ta gyaɗa kai cikin gamsuwa.
"Mutuniyarka tana lafiya, amma wanna son kai da yawa ya ke, kullum dai Afisha babu maganar
Ayan da Ayeed balle ƙaramar alhaki Daddey na duk ko kara baka min....."
Katse ta ya yi.
"Ana zancan rabin rai waya ke ta alewar zuciya?"
Dariya suka yi dukkansu.
"Afisha rabin raina ce, su kuma sweetheart ne kaɗai, kin ga banbancin bayyananne ne."
Afisha ce ta zo kusa da ita ba tare da ta sani ba.
"Ammeyna ki faɗa wa Ayeed ya daina taɓa min laptop, dan ai ba tashi ba ce."
Karaf Arfah ya ce.
"Yauwa Ammeynmu dan Allah bawa Afisha waya, sai na gama da ita kana zan miki murnar
nasarar da muka samu, na gani a media ana ta magana akan My happiness harda masu cewa
suna sonta Basu san Yah Arfah ya riga su ba."
Miƙa wa Afisha waya ta yi tana cewa.
"To me ya sa ya taɓa miki taki alhali shi ma yana da tashi?"
Amsar wayar ta yi ta kara a kunnanta.
"Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu."
Ya amsa cikin zakwaɗi kana ya ce.
"Ƙyale shi rabin raina idan ma laptop dubu kike so zan saya miki ai tunda kin cika mana
burinmu kin zama shahararriya a ɓangaren karatun Alkur'ani mai girma, ina taya ki murna
alfaharin danginmu, ina miki fatan alkairi nan gaba ki zamo gwarzuwa a na hizfi sittin."
Dariya da kyau ta yi kana cikin son shi da sabawa da shi ta ce.
"Amin yayanmu Arfah, Allah ya saka da alkairi ya cika maka burinka."
Sai kuma tai maza ta miƙa wa Ishmah wayar tana ta dariya.
Dariya Ishmah ta yi ta ce.
"Irin wannan washe baki haka."
Muryar Arfah taji yana cewa.
"Ba dole ba tunda tana waya da rabin ranta."
Girgiza kai Ishmah ta yi kana ta ce.
"To, rabin ran juna, Allah ya saka da alkairi dai."
Amin yace tare da ɗaurawa da cewa
"Yanzu fa, Afisha kaɗan ya rage ta kai babanta jama'a a duniya, kinga kuwa yadda media ta
ɗauka cikin ƙanƙanin lokaci, sai haɗa vedios ɗin karatunta ake yi dana babanta ana
comparison, abin dai sai wanda ya gani."
Cikin jin dadi Ishmah ta ce.
"Na gani nima, gaskiya na yi mamakin wanzuwar karatun cikin ƙanƙanin lokaci, domin cikin awa
ashirin da hudu zancan ya ƙaraɗe duniya, ƙanwar Yah Arfah kam Allah Ubangiji ya ƙarawa
rayuwa al'barka."
Cikin jin daɗi Arfah ya ce.
"Amin Ammeynmu, matar Sheikh Tajj Afif, mahaifiyar Sheikhiya Afisha, gaskiya ki godewa Allah
duk ke kaɗai wannan baiwa ga surku Arfah surutacce ga ƙani Hamisu mai mutunci."
Ranta ne ya yi mata tass kana ta sauke numfashi a hankali, bayan ta lumshe idonta cikin son
yaron tace.
"Alhamdulillah Arfah, kullum cikin godiya muke ga Allah."
Kamar yadda take jin daɗin shi ma haka yake ji dan tana jiyo sautin muryarsa yadda ta fallasa
sirrin ransa.
"To, Ammeynmu, sai mun sake magana dan yau ina da passingers duk da ba nisa zan yi ba."
Ɗan kwantar da kanta ta yi tan gyara zaman Amnah a kan cinyarta.
"To, Arfah Allah ya yi jagora sai na ji ka."
Asina ce ruggume da Yasir dake bacci cike da farin ciki, ido ta zubawa Adaya dake zaune tasa
boron kayansa da ta gama haɗa masa komai na tafiyarsu da zasu yi gobe jumma'a zuwa Dubai
jibi da safe za'a fara fafatawa.
Hankalinta duk na kan wayarta cikin cikowar hawaye ta ɗago idanunta tare da kallon Asina
murya cike da takaici tace.
“Asina wai meyasa wasu mutanen duniya basa son yan rawane, duk abinda zamuyi bazamu
burgesu ba, kigafa yadda wasu keta tsine mana a comments wai mun lalace kuma munzo
shima Yasir zamu lalata shi.
Sai kuma ta kalli Asina da tai kwaffa tare da cewa.
“Ni tsoro na ma kada tsinuwar da mutane suke mishi ta kamashi”.
Sai kuma duk suka juyo suka kalli Mamin Adayan data shigo tare da watsa musu mugun
harara.
“Ai gsky mutane ke faɗa muku, sam baku maida Yasir abin so ko ƙauna bare alfahari dashi ba
in dai a wurin mutanen kirki bane kuma lokacin nadama nan tafe gareku”.
Tura baki Adaya tayi tare da maida kallonta bisa wayarta.
Video gaba ta taurawa ido wanda Afisha ke tsaye tsakiyar malaman da duniya ke ji sasu a
babin Alkur'ani mai girma tana raira karatu tamkar wacce akewa wahayinsa.
Cikin ƙarfin mu'ujizar Alkur'ani ta kasa wucewa.
Koda video ya ƙare bata wuceba Saida ya sake daga forko haka tai takallonsa har sau uku sai
kuma ana huɗun ta shiga bin comments ɗin mutane ya Salam.
Shine abinda ta faɗa wanda yasa Asina kwantar da Yasir tazo suna kallon tare comments na
forko kan video cewa yace.
“Alhamdulillah wannan itace abar alfaharinmu mutanen Ethiopia ba irinsu Adaya da Yasir ba”.
Da sauri ta kalli na ƙasanshi da wani ke cewa.
“Wannan ɗin itama yar Ethiopia ce”.
Da sauri wani balaraben Qatar yace.
“A'a wannan ƴar Qatar ce”.
Kusan mutun dari ne suka bawa wannan balaben amsa da cewa.
“A'a wannan asalinta yar Ethiopia ce, in ma bai sani ba to ya sani yaji sunanta mana Fatima Afif
Tajj, shi kuwa Sheykh Afif Tajj ai kowa ya sani a duniya shi ɗan Ethiopia ne.”
Emojis sin murmushi da alamun so mafiya yawa suka rinƙa turowa sai kuma wani daga cikin
larabawan Qatar yace.
“Amman ai raininmu ce”.
Da sauri Hamisu dake bibiyar duk Comments ɗin a video da sakan yace
“A'a duk ma ba taku bace, tamu ce ta Nigeria.”
Cikin sauri wani Balaraben Jordan yace.
“A'a kam wannan batai kalar kuba”.
Murmushi Sheykh Afif ɗin dake bibiyar Handel ɗin Hamisu wanda komai nasu Afisha dama shi
kanshi Tajj din a handil nasa ake gani, cikin hikima da iya sarrafa harshe ih zuwa alƙalami yace.
“Afisha ta dukkan musulman duniya ne, duk inda kake in dai kai musulmine in Kai na mijine kai
yayantane ko babanta ko ƙaninta in macece ke yayartace ko ƙanwarta ko Auntynta. Duk
ƙasashen musulmai ita tasuce. Nigeria kuwa itace jigon raininta da tarbiyarta.
Ethiopia kuma itace tushenta jintan. Qatar kuma itace Mahaifarta kuma makarantar ta.
Yah salam kan wannan comment ɗin nashi an mishi like yafi 1.5m dan yasa dukkan musulmai
jin farin ciki.
Hamisu kuwa da sauri yayi falon inda Afishan ke zaune tana yiwa Daddey bita.
Jawota yayi tare da cewa
“My dear zo nan kiyi video kiyi godiya ga masoyanki na fadin duniya.”
Cikin murmushi tace.
“To My Uncle”.
Ishmah kuwa murmushi tayi tare da miƙewa da nufi kitchen tana cewa.
“Ku dai kula sabida baki in yayi yawa da illa”.
Da sauri Addawa tace.
“Mu da muke da Alqur'ani mai girma ai baki baida wurin sauƙa a jikinta”.
Da sauri Laylah dake fitowa daga ɗakin Ishmah tace.
“Sosai ma kuwa Addawa mu kam badai mutumba sai Allah”.
Murmushi Ishmah tayi cikin gamsuwa da in sha Allah ba abinda baki zai musu tunda sun lizamci
karatun Alkur'ani mai girma”.
Shi kam Hamisu sakin video yayi tare da komawa kan comments ɗin ganin Arfah yayi
comments kan na Sheikh Afif da cewa.
“Uncle Tajj ka manta baka gaya musu cewa.
mijinta ɗaya ne a duniya kuma Yah Arfah ta ne so kowa ya kama kansa”.
Murmushi Afif yayi tare da cewa.
“Toh ai ka faɗa”.
Da sauri Hamisu yace.
“To in dai fa kana so ka ƙara min biyayya”.
Alamun dariya Imran ya tura tare da ƙarawa da cewa.
“Ai Uncle Hamisu dole muyi mubaya'a tunda muna son Afisha da Minnat ni, yanzu hakama ina
shirin tafiya Nigeria ne.
Daga nan kuma sai duk suka bar TikTok ɗin suka koma Whatsapp group ɗinsu inda suke
hirarsu.
Wani irin nannauyan numfashi Adayan ta fesar tare da ƙurawa sunan Tajj ido.
Sai kuma ta kalli Asina tare da cewa.
“Mutumin nan kamarfa gasa yakeyi damu, kin tuna lokacin da muke kan gasarmuma kullum
dashi ake mana misali ana kushemu, Kinga yanzu kuma da wannan beautiful baby ɗinsa yake
daƙushe mana taurarin Yasir ɗinmu ana mana misali da ita”.
Da sauri suka kalli Umminta jin tana murmushi mai sauri tare da cewa.
"Ai ko a gaban Allah ya fiku, kuma yarsa ta fi ɗanku kuma bakuma kai yayi gasa da kuba, shi
bai ma san da ruwan tsironku ba”.
Tana ƙare mgnar ta juya zata fita sai kuma ta tsaya tare da juyowa ta kallesu tace.
“Af nafa mance shegen yaron nan Izzin ne yazo yana waje.
Kuyi sauri ku sallameshi kafin Abpu ku ya fito”.
Tana faɗin haka ta fice
Asina kuwa numfashi mai nauyi ta fesar tare da cewa.
“Barshi mu bashi nan da kwana biyar da za'ayi gasar nan, in sha Allah har abadan sunansa
bazai sake tasiri ko daraja ko kima a duniyaba daga abun so zai zama abun ƙyama, dan ko jiya
shine tattaunawar da mukayi da my Man”.
Cikin sauri Adaya tace.
"To Amman meyasa kikaƙi ki gaya min tsarin naku”.
Cikin yarda da kai tace.
“Kar ki damu nafi son sai naga Yasir yaci gasar zan gaya miki kafin nayi abin”.
Cikin takaici Adayan tace.
In kinga dama ma karki gaya min.”
Ta ƙare mgnar ta janta suka fita suka tafi.
Sai kuma ta ƙali part ɗin Abpu da sauri tare da cewa.
“Ke yi sauri mu fita kin san Abpu tunda ya samu lfy in Izzin yazo gidanan ji yake kamar ya hau
kanshi da mota”.
Murmushi Asina tayi tare da cewa.
“Nima in ya ganni kamar ya harbeni fa”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Nima ko gaisuwata fa baya amsawa”.
Daga nan suka fice suka tafi.
Ya Abana ne ya ƙurawa Afisha ido kamar mai son haddace fuskarta cikin sonta ya sa yatsansa
akan play ɗin vedion nan da nan sautin muryarta ya bayyana Wanda hakan ya tilasta shi sakin
ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi, ya lumshe ido yana jin daɗin ƙira'ar.
A haka bgajeran bacci mai nauyi ya fisge shi.
Mom Amal ce ta shigo ɗakin nasa hannunta rike da fruts da ta yanko ta kawo masa, tun daga
falonsa ta fara jiyo sautin karatun, cikin rawar jiki da tsananin faɗuwar gaba ta ajiye fruts ɗin ta
sunkuya ta leƙa fuskarsa taga yana bacci da sauri ta ɗauki wayar da take a dai-dai kunnansa,
cikin mamaki da ruɗewa take kallon fuskar Afisha.
"Ita ce."
Ta faɗa zuciyarta na rawa haka ɓacin ranta ya fito ɓaro-baro, da sauri ta katse karatun kana ta
fara ƙoƙarin deleting vedion cikin rashin sanin abin yi, gab da za ta goge ta ji gyaran muryarsa.
Da sauri tsoron zuciyarta ya taka mata burki, ta saki ajiyar zuciya tana jin kamar ta fashe da
kuka dan bakin ciki.
Cikin nannauyan baccinsa ya daina jin ƙira'ar da yake jinta tamkar tana wanke masa wani datti
a cikin ƙwaƙwalwarsa, cikin mamaki da tarin gajiya ya buɗe ido tare da gyaran murya yana
kallonta.
Kamar wata shashasha haka ta saki baki tana lashe leɓenta da yake a bushe, sai ta zauna
kusa da shi cikin mutuwar jiki tana son fassara kallon da ya ke jifanta da shi, kamar wata mutum
mutumi haka ta sadaƙar tare da ajiye wayar tana sunke kai cikin yanayin ƙunci da damuwa
miƙewa yayi tare da shigewa baruwanta jim kaɗan ya fito bisa alama alwala yayi. Cikin inda inda tace.
“Niko Malam yaushene tafiyar taku?”.
Da sauri tayi ƙasa da kanta saboda ganin wani irin futinennen kallon fahimtar sirrin zuciya da
tunanin ƙwaƙwalwar kanta”.
Kabbara ya tayar ba tare da yace mata komai ba.
Ummeey ce zaune tare dasu Rashida harma da Halima wacce yau kwananta biyar kenan da
zuwa.
Binafa ce ɗiyar Zakiya ke bisa cinyar Ummey cikin tsananin jin daɗi suke kallon Video Afisha
dasu Ayeed.
“Kai Allah na gode maka bisa ni'imar da kaimin da samun yara irinku da jikakiki kamar yaranku,
Amman tabbas mahaifinku ya tauye min farin cikin rayuwata daya nesantani da ɗana da
yaransa, ina son in ganni gani gasu Afishan Ayeed da Ayaan in ruggume Daddey kamar yadda
nake ruggume da Binafa haka”. Cikin rauni suke kallon fuskar ta dake zubda hawaye, sai kuma sukayi saurin kallon Imran da
Hamida dake shigo Hamida na cewa.
“Ke da akayiwa shigel ɗin layin zuwa Umrah dan a ɗan rage Miki raɗaɗin rashin Uncle Tajj
kuma shine kika tara mana Auntys ɗinmu a gaba zaki sasu kuka.”
Daƙuwa Maryam tayi mata.
Rashida kuwa murmushi tayi ganin Ummeynsu tayi murmushin tare da goge hawayenta.
Cikin wasa irin na yan auta da iyayensu Zakiya tace.
“Ato nima dai haka na gani su Ummey amare”.
Ɗan duka ta kaiwa Zakiya tare da miƙewa ta bar wurin.
Washe gari ranar juma'a.
Misalin ƙarfe tara na safe.
Meymey ce durƙushe gaban mahaifinta da mahaifiyarta.
Wani irin maraitacccen kuka mai cike da dana sani da nadama takeyi kuka ne mai tsananin
ciwo da zogi da radaɗi takeyi har numfashinta na yayyankewa.
Yayinda shima Uncle Jibiril ɗin hawayene suke malala a kuma tunsa tare da danne
sheshsheƙan kukan.
Mommy ta kuwa kukan takeyi harda majina.
Sai kuma ta kalli Meymey dake rarrafowa ta matso kusa da iyayen nata da kyau cikin
disashewar murya da rawan baki tace.
“Ya ku iyayena ku gafarceni, musamman ke Mommy da kikayi ta ƙoƙarin ganin kin fidda rashin
gaskiyata a lokacin da nake ƙullawa Yah Afif wannan sharrin da ƙazafin da nayi masa, Amman
son Zuciyata da ɗaurin gindin son da Abbana kemin ya hanaki samun damar bayyana
makircina, gashi a sannu duniya da sakayyar Yah Afif tasa yau ni da kaina na zauna na baku
labarin ƙazafin da nayi mishi”.
Sai kuma muryarta ta sarƙafe saboda tasowar wani sabon kuka.
Zuwa yanzu shima Uncle Jibiril kukan ya kwafce mishi cikin sauri kuma ya haɗiye kukan jin
Meymey na tari tare dacewa.
“Dan Allah Mommy keda Abba ku rakani gidan Yah Abana in tonawa kaina da kaina asiri in
bashi haƙuri in nemi gafararsa, ko Allah zai kawo min sauƙin wannan cutar damuwa da son
aure wata ƙil in Yah Afif ya yafe min in samu mijin aure.”
Cikin tsanani ƙunar rai Mommy ta miƙe tsaye tare da nuna ƙirjinta da yatsarta manuniya.
“Har abadan bazan taɓa rakaki gidan Malam dan ki tonawa kanki asari basu Mom Amal
makiran wofi dan ni idona da kunya kuma Zuciyata da tsoron Allah, so ke da kikayi amanki ke
kaɗai lokacin da kikayi ban saniba kuma dan haka ke kaɗai zakije, kuma wallahi a yau ɗin nan
zakije yanzun nan ma ba da jimawa ba.” Sai kuma ta koma da baya ta faɗi zaune bisa kujera cikin kuka tace.
“Meymey kin shiga uku ina zaki kai zunubin raba uwa da ɗanta ke ba mutuwaba, Meymey ina
zaki kai zunubin yiwa tsarkakekken mutum mahadaccin Alkur'ani ƙazafin zina da farraƙashi da
iyayensa, Meymey ina zaki kai zunubin zubda hawayen Hajia Fatima Mahaifiyar Afif ina zaki kai
zunubin sa mahadaccin Alkur'ani mai girma zubda hawayen. Shekara tarafa cib kenan kika
rabashi da kowa nasa, ina zaki kai zunubin fidda tsiraici mutum mai kunya da kima da daraja.”
Sai kuma kawai ta fashe da kuka tare da cewa.
“Ta ya zakiyi tunanin samun salama a rayuwarki kinsa marainiyar Allah Laylah a wahala”.
Da sauri ta rarrafa ta koma gaban Abban nata cikin tsananin kuka