Showing 18001 words to 21000 words out of 25520 words
Chapter 7 - INDA RAI B 3 end Book True Wallafar A'isha Aliyu Garkuwa .pdf
kuma Afisha
na can, Ummeynshi tace ya bar mata ita, Yah Abana kuma bai tsine mishi ba, kai ko mugun
kallo ma bai mishiba Kum...”
Sai kuma yayi shiru tare da juyawa da sauri ganin ta raɓa ta wuce shi, ta nufi sama wurin Afif
ɗin.
Kai ya jinjina cikin gamsuwa da so irin na kaka da jika.
Sai kuma ya nufi ɗakinsu Laylah inda yake jiyo alamun Muryar ta tana bitan.
Ƙofar ya tura tare da ɗan jingina ta gefe yana mai kallon Ayeed da Ayaan da sukayi bacci
ruggume da sawun juna, kan Ayeed na ta sawun Ayaan.
Da sauri Rahman ta ɗago kanta ganinshi tsaye ya dawo da kallonshi kanta ne yasata sauƙe
numfashi mai nauyi dake ƙara kafa sonshi a ranta tace.
“Ya dai ina Afisha, Abeey ya huce”.
Kwaɓe fuska yayi tare da cewa.
“Hayateeh Yunwa nakeji, kizo muje ki bani abinci kafin in amsa miki”.
Miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
“Ba'afa ɗaura aurenba tukun”.
Longoɓar da kansa yayi tare da cewa.
“To barni yunwa ta kasheni ki huta”.
Da sauri tace.
“Allah ya rufa min asiri, ai ciwon zaimin yawa a raina, na rasa uwa, uba, yayu, ƙani, yanzu kuma
kamin fatan rasa miji, abokin rayuwa, jigon farin cikina, uban yayana In Sha Allah”.
Ta ƙare mgnar a lokacin da suka zauna kan Dinning table ɗin.
“Allah ya bamu tsawon rai da lfy da zuriya ɗaiyiba mu samu irinsu Afisha”.
Tana zuba mishi abinci a plate tace.
“Amman dai kamin alkawarin ba kishi ya ko”.
Kai ya jinjina mata.
Da sauri tace.
“Yauwa kuma ga ƙarin wani alkawarin duk laifi banda mari irin na Abeey”.
Tsuke fuska yayi tare da tsareta da ido cikin isar matsayi irin na mijin gsky yace.
“Itama Ammeey ita ta jawo ya mareta, duk da nagartarsa saida ta ƙureshi tasa ya kai hannunsa
jikinta, Yah Afif ma yayi mari da akayi mishi wargi akan yaransa shi da yake ma nagarci mai
tsananin haƙuri gautsin bakinta da taiwarta yana faɗa tana faɗa ya ja ya mareta, bare ni
Hamisu da haƙurina bai kai nasaba, in bakya son mari kada ki kwatatanta yin abinda yar uwata
tayi a yau, dan in nine ya Afif ma sai na haɗa mata da Hangurɓar kumbura mata fuska da mari
in fasa baki da naushi in karya ƙafa”.
Da sauri ta miƙe tsaye tare da zazzaro idonta waje tsoronta ya fito a fili, sai kuma ta koma ta
zauna jin ya jawo hannunta ya zaunar da ita tare da cewa.
“Amman ke a ganinki abinda Ammey tayi ta kyauta?”.
Cikin sanyi tace a'a.
Murmushi yayi tare da sakin fuska kana yace.
“To kada kiga laifin Yah Afif. Hayateeh ke nasan ma bazakiyi min hakaba koma mun ɓata ba laifi
bane, dan tsaɓanin masoya hutune kuma in an shirya sai danƙon so ya ƙaru kiga anfi ji da juna,
yanzu mu zuba musu ido muga fushinsu da shiryawarsu zakiga bayan nan sai sun nemi haɗiye
juna a gabanmu. Amman kafin nan akwai zaman ƙunci a gidan nan dan naga duk sun fusata”.
Tana murmushi tace.
“Ai shi zaizo ya bata haƙuri”.
Da sauri yace.
“A'a itace zata bada haƙuri dan itace mara gsky”.
Cikin sauƙe numfashi tace
“Anya kuwa?".
Yana juya spoon ɗin hannunsa yace.
“Zamu gani dai”.
Addawa wace durƙushe gaban Tajj tayi sujulshukur saboda jin harda ɗiyarta aka zo kuma Yah
Abana bai tsine mushi ba, sai kuma ta zuba mishi ido ganin har yanzu hawaye ne ke kwaranya
a idanunsa lips inshi na rawa alamun so yake ya danne sheshsheƙan kukan dake son fuzgo
mushi. Idanun sunyi jazir jiyoyin kansa duk sunyi ruɗu-ruɗu more especially na kan goshinsa cikin
rawan murya yake cewa.
“Addawa sujjadar Godiya a tabbatar tsinuwar Yah Abana a kaina, Addawa sujjadar Godiya a
tabbatar mutuwar auren Ummeyna sujjadar Godiya a tabbatar Allah ya isan Yah Abana ya hau
kaina tunda yau duk na keta alfarmarta ƙa'idar da yasamin na kar ya ƙara ganina a duniya kar in
kuma zuwa inda yake”. Sai kuma yayi saurin kife kanshi bisa kujerar da yake zaune a gabanta tare da kubcewar kuka.
Da sauri Addawa ta zauna bisa kujerar, kanshi ta ɗago tare da ɗaurawa kan cinyarta tafinta ta
kife a kan kafaɗunsa tana ɗan bubbugawa, cikin Muryar tsammani tace.
“In sha Allah babu tsinuwa a kanka, kuma ba Allah ya isa a kanka, kuma da yardar Allah auren
mahaifiyarka na nan daram.
Tajj kayi shiru ka fahimta mana shine fa da kansa ya nemeka”.
Da sauri ya ɗago kanshi tare da cewa.
“No Addawa Afisha ya nemafa ba niba, kiɗima tasa na mance naje”.
Hannunta tasa tare da tallabe fuskarsa kana tace.
“To ai duk wanda ya nemi Afisha kai ya nema, duk wanda yaso ganin Afisha ai kai yaso gani.
Saboda duk wanda yaso ɗanka to kai yake so.
Tajju ai kaine Afisha”.
Da sauri yace.
“Ki fahimta Addawa nifa da naje har na bar wurin ko ɗago kanshi ya kalleni da idanunsa baiyiba.
Ina jin ƙamshin jikinsa da na rasa ji tsawon shekaru tara, ina ganin sawunsa da kullum in ina
kusa da shi yake ɗaura kaina a cinyoyinsa.
Ina kallonsa inaji bege da sha'awar ya jani jikinsa ya ɗaura kaina a cinyarsa yasa tafin
hannunsa na dama a tsakiyar kaina yayi min Addu'a yasa min al'barkar da nayi missing nata
tsawon shekaru tara in yi mishi massaging sawunsa da nayi shekaru tara ban mishi.
Addawa duk fa bai bari na samu wannan ladan ba, ko kallona baiyiba ko sunana bai kiraba, ina
son inji yace min.
Abbana Amman yaƙi.”
Sai kuma kawai ya fara bubbuga gefen kanshi da hannunsa na dama yana faɗin.
“Addawa nayi asarafa a rayuwata tsawon shekaru tara cikin fushin mahaifi kuma ba sa al'barka
uwa, kuna ga kamar na rabu da baƙin cikin rashinsu a kusa ko, yana raina fa”.
Da sauri tace.
"Innalillahi haba Tajju kayi Astagfirillah, na sani kullum Fatimana tana saka maka al'barka ta
kuma yi maka addu'a a cikin dukkan motsinta ai shiyasa kake samun nasara, shi kuma
mahaifinka ai bai tsine makaba bai kuma ja maka Allah ya isaba tunda yasa sharadin sai kaje
inda yake ne ko kayi alaƙa da yayansa da mahaifiyarka. Kuma ka kiyaye bakayi ba,
Wannan shine sirrin nasararka da rashin ganin masifa, ai ba don wannan ba ko da gskyarka
iyayenka suka fushi da kai sai kaga ba daɗi.
Kuma zuwa Yah Abana Qatar da neman Afisha ai duk shimfiɗar son ganinka ne.
Kuma zaka gani da idonka, Addu'ar da mahaifiyarka keyi kullum ne lokacin amsashi yazo, in
sha Allah asirin magauta zai tonu nan kusa inaji a jikina komai zai bayyana nan kusa gsky
zatayi halinta, jifan da sukayi yana gab da sauƙowa ƙasa bayan tafiya sama da yayi tsawon
shekaru tara, dan duk nisan jifa ƙasa zai faɗo”. Sai kuma ta ƙara tallaɓe kanshi da kyau tare da fara sharce mishi ruwan hawayensa.
“Kai da Allah ya baka ajiyar ƙura'ani mai girma a cikin kanka ai kuka bai canceka kaba, yi uziya
da basmala fara karatu nasan shine abi mafi daɗi da sauƙin samar da warakan ko wanne ciwo”.
Ai kuwa kamar mancewa yayi ta tunasar dashi.
Cikin lumshe idonsa ya fara karatun tun daga farkon Alkur'ani mai girma.
Da ƙarfi ya sauƙe wani zazzafan Ajiyan zuciya lokacin da ya dire ayar karshe ta Suratul fatiha,
kana ya ɗaura da suratul Baqara.
Gyara zama tayi har Saida taji ya kai tsakiyar surar kana ta miƙe ta fice.
Baima san ta fitaba dan falalar Alkur'ani tasa baya jin komai sai sautin muryarsa da kuma sauƙe
Ajiyan zuciya akai a kai.
Ita kuwa Ishmah tunda ta shiga ɗakin ta faɗa kan gado, ta ruƙume Daddey ta saki wani irin
maraitacccen kuka mari a gaban kowa da kowa na gida zai dakeki akan yar da kika haifa a
cikinki.
abinda shaiɗan ke karanta mata kenan haka ya ƙara ingiza fushinta da ƙunar ranta tai ta Kuka
har bacci yayi awon gaba da ita, tana mai jin raɗaɗin marin sai ajiyar zuciya take sauƙewa.
Shi kuwa Tajj ranar haka ya kwana karatun Alkur'ani ko na second ɗaya bai rintsaba.
Washe gari misalin ƙarfe takwas dai-dai tsaye take a dannin area cikin disashewar murya ta
kalli Laylah dake tsaye gefenta.
“Ki ɗauko mayafinki ki zo ku kaiwa su Yah Abana breakfast.”
Ta ƙare mgnar tana nuna mata basket har biyu da suke kan dinnin table ɗin.
Cikin sanyi Laylah tace.
"Toh Ammey”.
Sai kuma ta juya ta nufi ɗakinsu tana mai jin tausayin Ishmah sabida ganin yadda fuskantar ta
kumɓura tayi jazir more especially gefen hagunta inda nan ya bawa maruka biyu, ya kumbura
sosai hatta shatin yatsunsa na kwance ras, kana cikin gefen idon ya tara jini kamar irin wacce
aka tsole da ƙarfi haka. Gashi kuma duk idon suma sunyi jazir ga muryarta dake a disashe saboda kukan da rasha.
Haka nan taji hawaye na cika mata ido.
A inda ta barta a nan ta dawo ta same a tsaye.
Basket ɗin ta ɗauka duka biyu tare da cewa.
“Ammeey kice Ayeed yaje ya kira Yah Hamisu.”
Kai Ishmah ta jinjina tare da cewa.
"Muje in kira miki shi”.
Domin ƙa'idar gidan ne yara mata basa shiga ɗakin mazan.
Shiyasa Laylah barata jeba.
"Yauwa gashi nan ma”
Laylah ta faɗa lokacin da suka fito cikin corridor.
Da sauri ya amshi basket ɗin yana kallon yar uwar tasa.
Da sauri yayi ƙasa da kansa saboda ganin yadda fuskantar da idonta suke, lokaci ɗaya ƙauna
da tausayin yan uwan takan suka motso lip inshi na ƙasa ya ɗan taune tare da cewa.
“Adda muje in kaiki hospital ki samu magani”
Kai ta jujjuya cikin sanyi tace.
“Lafiyata ƙalau ɗan uwana kuje”.
Ta ƙare mgnar cikin kauda kai tare juyowa ta koma ciki.
Cikin sauƙe numfashi ya ɗan kalleta lokacin da suka fita daga harabar gidan.
“Hayateeh kuka kikeyi?”.
Cikin sanyi tace.
“Yah Hamisu kalli fuskar Ammey nafa”.
Kai ya ɗan kauda dan kar ta gane raunisa cikin sanyi da iya kar gsky yace.
“Kawai dai hannun Yah Afif nada tsananin zafine ita kuma abu da farar fata, shiyasa tayi haka,
da Ni ya mara da fuskata bazatayi hakan ba, kuma in sha Allah itama zai watstsake”.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah Ammeyna kusan kwana kuka tayi fa”.
Yana ɗaukar hanyar da zata dasu da hotel ɗin yace.
“Dama haka take da raki da saurin kuka”.
A can cikin gida kuwa.
Cikin kulawa da tausayi Addawa ke kallon Ishmah dake ƙoƙarin komawa kitchen tace.
“Me kuma zaki koma kiyi a kitchen”.
Murmushin ƙarfin hali tayi dan ciwon kai dake damunta ya fara sata jin bata son surutun a
hankali tace.
“Zan fara haɗawa su Ummey lunch ne”.
Cikin sanyi da tausayi Addawa tace.
“Kiyi haƙuri kizo kiyi breakfast, Kisha magani ki kwanta ki huta, ni da kaina zan shiga kitchen din
da Zulaihat in musu lunch ɗin”.
Da sauri tace.
“A'a Addawa barini in samu ladan mana”.
Miƙewa tayi da sauri tace.
“To naji Amman dai zo Kisha ko tea ne sai kisha maganin”.
Dole tabi Addawa tea ta haɗa mata da kanta kana ta bata tasha tare da maganin.
Cikin wani irin matsanancin farin ciki Ummeey ta rugume Laylah da ƙarfi tare da cewa.
“Allah sarki Laylah kece haka”.
Ita kuwa Laylah lip tayi a jikin Ummeeyn tana mai murmushin dake bayyana tsananin jin daɗin
ganinta.
Hamisu kuwa da sauri ya ajiye basket ɗin tare da rugume Afisha.
Dake tsalle musu oyoyo.
Cikin girmamawa Hamisu ya kalli Yah Abana da yace.
"To ai zaki kada Uncle ɗin, sakeshi ya zauna”.
Da sauri ta sakeshi sai kuma ta ruggume Laylah.
Shi kuwa Hamisu cikin girmamawa yace.
“Barka da safiya Yah Abana”.
Kan Hamisun ya shafa tare da cewa.
"Barka dai an turoku ɗaukan Afishane da sassafen nan?”.
Da sauri yace.
“A'a Yah Abana Adda Ishmah ce tace mu kawo muku breakfast”.
Ya ƙare mgnar yana nuna mishi basket ɗin da ya ajiye.
Kai ya ɗan sunkuyar ƙasa tare da cewa.
“Allah yayi mata al'barka.”
Cikin jin daɗi Hamisu da Laylah sukace.
“Amin Yah Allah”.
Yana jawo Afisha jikinsa yace.
“Ya baku kawo min Ayeed da Ayaan ba?”.
Da sauri Laylah tace.
"Sun maida bacci basu san zamu zoba.
Ayeed tun jiya fushi yake wai an hanashi zuwa.”
Ta ƙare mgnar tana tahowa inda yake dan yafitota da yayi da hannun sa.
Gefenshi ya nuna mata a ƙasa.
Da sauri ta zauna tare da kallon Ummeey da ke cewa.
“Ina Addawa na, ina Ammeyn naku da Daddey”.
Cikin yar sakekkiyar murya Yah Abana yace.
"kice ina Hayateeh Daddey na”.
Da sauri Afisha ta kwaɓe fuska tare da cewa.
“Daddey ne Hayateenka”.
Murmushin su Hamisu sukayi dan sun san Afisha kullum cewa take wai gani take da kamar
Dadeey akafi so.
Kanta Yah Abana ya shafa tare da cewa.
“Ke My happiness Daddy kuma Hayateeh”.
Da sauri tace.
“A'a ni dai Hayateeh nake so, ai sai an rayu kafin ayi farin ciki gwara dai ni in zama rayuwarka
ita kuma farin cikinka to su Ayeed fa”.
Dariya suka watse dashi har Yah Abana saida ya ɗanyi murmushi mai sauti kana yace.
“To Hayateeh haka za'ayi Ayeed da Ayaan kuma friends nane ai”.
Murmushin dake nuna wani irin mashahuran farin ciki ma bayyani Ummeey tayi tare da cewa.
“Wallahi ina son ganinsu fa Malam”.
Cikin lumshe idonsa yace.
“Zaki gansu in sha Allah”.
Da sauri tace to sai yaushe”.
Yana ɗan shafa kan Afisha yace.
“Verry soon”.
Dubai.
Tuni hall ɗin ya cika yayi maƙil.
Yaran ƙasar Japan da China aka fara haɗawa, suka goga a fagen rawan.
Inda Chaina ta kora Japan gefe.
Nan
Kuma aka haɗa Ethiopia kuma Mali.
Cikin abinda bai gaza awa biyu ba Yasir da sauran yan tawagar sukayi waje da ƴan Mali.
Haka dai suka ci gaba da fidda gwaneye, a ranar aka yi tantancewar forko gobe kuma za'a ci
gaba da rairarye gwanayen kasashe.
A hankali yake fesar da sassayan numfashi tare da shaƙan dadɗan ƙamshin da parlon ke
zubawa, idonshi ya ɗan lumshe kana ya buɗesu a hankali tare da tsaida kallonshi kan gefen
fuskantar da yake ɗauke da shatin yatsunsa da sukayi ruɗu-ruɗu sunyi jazir.
Lip inshi na ƙasa ya ɗan ciza ta gefe tare da ɗaura tafin hannunsa kan cikinsa da yakejin yana
kukan yunwa da rabonsa dasa abi a bakinsa tun jiya da asuba da zai taso, nanma iya tea
yasha.
Zura hannunsa ɗaya yayi cikin Jallabiyar dake a jikinsa sky blue color sai wani irin Ni'imataccen
ƙamshin da yake bazawa, wanda ya rigada ya kama jikinsa.
Ita kuwa Ishmah tunda ya shigo kanta ke sunkuye tanayiwa Daddey kitso duk da manyane,
sanye take cikin doguwar rigar material sky blue color sai ratsin Pink and red color.
Rigar tayi cas a jikinta duk da ba wata kwalliya tayi ba Amman tayi masifar kyau, sai ƙamshin
kullacar sirri da shu'umar humra take bazawa yanayin jikinta kuwa cike yake da rauni.
Hmmm! Addawa tayi gyaran murya don ganin tunda ya shigo bai zauna ba, kuma bai cire
idonsa kan Ishmah ba, ita kuma bata ɗago kai ta kalli inda yake bama.
“Zauna mana”.
Tace tana kallon Zulaihat da ta fito daga kitchen ta nufi ɗakinsu Ayyed dan tada su a bacci tayi
musu wanka.
Bisa alamun ta gama gyara komai na abinda Ishmah tayi amfani dasu wurin girkin rana da
wanda za'a kaiwa su Ummeey.
Yana mai rumtse idanunsa ya zauna gefen Addawa tare da amsa gaiduwarta.
“Muje kuyi breakfast ko?”.
Addawa ta faɗa tare da miƙewa.”.
Kai ya jinjina alamun to.
Da sauri Addawa ta kalli Ishmah data miƙe tsaye tare da tallaɓe Daddey a jikinta ta juya ta nufi
ɗakinta.
“A'a Ishmah ina kuma zaki tafi, ki kwantar da ita kizo muyi breakfast ko?”.
Ba tare da ta kallesu ba murya cike da rauni can ƙasa a narke tace.
“Bismilla kuci kawai Addawa bana jin yunwa”.
Cikin kulawa da jin tausayi Addawa tace.
“Me kikaci da zakice bakya jin yunwa, tun jiya da safe fa raban da kici abinci haka kika wuni kika
kwana da yunwa, dan Allah kada muyi haka dake Ishmah, kiyi haƙuri kizo ki kwantar da Daddey
anan muci abinci”.
Cikin murya mai tafe da rauni tace.
“Kiyi haƙuri Addawa ba ɗazu kin bani tea ba, wallahi Allah bana jin yunwa kuci kawai, bazan iya
cin komaiba”.
Miƙewa yayi ba temare da ya kallesu ba ya fara tafiya zuwa Dinning area.
Itama Addawa numfashi ta fesar tare da juyawa zata bishi dan tunda taji ta rantse tasan to ko
ya za'ayi bazata cin bane.
Ita ma Ishmah a hankali ta juya dan nufar ɗakinta.
Kamar daga sama haka suka ga Afisha ta shigo parlor a guje tare da rakadi tana faɗin.
“Hello Ammey! Ammey!! i miss you Ammey”.
Dai-dai lokacin kuma ta ƙaraso gaban Ishmah tare da rarumarta da ƙarfi ta ruggume ta.
Irin ruggumar nan ta yara da take sa Mutun faɗuwa.
Da sauri Ishmah tayi taga-taga tare da dafe kujerar dake bayanta saboda saura ƙiris ta faɗi.
Cikin fusata ta hankaɗata gefe tare da yarfa mata wani irin zazzafan marin da yasa Afisha yin
taga-taga ta faɗi gami da sakin wani irin maraitacccen kukan da yasa.
Addawa da Tajj da suka tsaya saurin nufowa kanta.
Cikin sauri Tajj ya tallaɓota jikinsa tare da miƙewa tsaye wani irin kallon ido cikin ido sukayiwa
juna shida Ishmah cikin tsanani fusata da huci ya nuna ta da yatsa cikin fusakatacciyar murya
yace.
“Ke wai meke damunki kanki ne?.
Me tayi miki da zaki daketa?”.
Cikin watsa mishi wani irin kallo idonta na cikowa da hawaye tace.
“An daketa ɗin! Ko zaka rama matane? tunda kai kayi min dakon cikinta wata tara da kwana
tara, ka kuma yi min naƙudarta da nishin haifa min ita kaji min zafi ketani da tayi ta fito duniya
kuma ka shayar min da ita nace zaka rama matane?”.
Da sauri ya nufo kanta yana faɗin.
“Dan ke kika haifeta, sai aka ce Miki kece