Showing 3001 words to 6000 words out of 25520 words
Chapter 2 - INDA RAI B 3 end Book True Wallafar A'isha Aliyu Garkuwa .pdf
taya
su murnan wannan abun farin ciki.
Zama Hamisu ya yi ya ce wa Tajj.
"Malamansu fa suna falon waje suna jiranka."
Cikin mamaki Tajj da Ishmah suka kalli yaran.
Laylah ta kama baki ta ce.
"Laaaa! Mantawa na yi, Ayaan me ya sa baka tuna mun ba."
Ayaan ya ƙara kwanciya jikin mamnsa ya ce.
"Taɓ! Ni ma mancewa na yi tare mu ke da su."
Afisha ce ta kwashe da dariya ta ce.
"Kowa na murna ina ma za ka tuna da su, ai ni tun da akace nice wacca ta cinye na ke da burin
zuwa na faɗa wa Abeyna."
Ayeed da yake ta tsalle-tsallen murna ya ce.
"Ni kam ma na mance da kowa sai farin ciki."
A ɗan hanzarce Tajj ya miƙe yana faɗin.
"Dukkanku dai Allah ya yi muku albarka, ku shiga ciki ku faɗa wa Addawa dan jiranku take ta yi
tun ɗazu."
Ya fice dan ganawa da malamansu.
A cikin nutsuwa ya shiga suka gaisa cikin girmamawa dan suna matuƙar girmama shi.
Cikin nutsuwa shugaban makarantar ya fara magana.
"Alhamdulillah, kamar yadda aka tsara an gama gasa lafiya yaranka su ne suka yi nasara
makaranta da mu kanmu muna alfahari da hakan, kuma mun zo yi maka murna da kuma kawo
musu kyautukan da suka samu."
Sauke numfashi Tajj ya yi yana jin zuciyarsa wasai kamar an wanke ta tass da babu sauran
wani datti.
"Alhamdulillah, Allah mun gode maka, na gode sosai Sheikh Khalilullah, Allah ya sa ka da
alkairi."
Murmushi suka kana ɗayan ya ce.
"Ai mu ne da yin godiya, domin dai ba dan jajircewarka ba, tabbas da makarantar mu ba ta yi
sunan da a yanzu ta yi ba, kaga dalilin yaranka kowa zai so kawo yaransa makarantar, ai mu
tsakaninmu da kai sai addu'a dan mun san bawai iyakar karantarwar mu bane harda
jajircewarka da bitarsu a gida."
Cikin tsananin farin ciki
Suka miƙa dan nuna wa Tajj kyautukan, bayan motar su fall cike da kaya kala-kala dan
dukkansu sun samu kaya masu yawa.
Cikin tsananin murna Tajj ya amshi kyautukan amma banda kuɗi ya ce malaman su riƙe, suka
ce sam babu wannan zancan da ƙyar dai suka daidaita akan sai dai a raba kuɗin biyu su ɗau
ɗaya ya ɗauki ɗaya kana ga kwaitar kujerar hajji wa Afisha.
Lokacin da suke jigilar shigar da kayan cikin gida zuciyar Tajj sai haske da farin ciki take yau
Allah ya nuna masa ranar da zuri'arsa ta sama masa farin cikin zamowa ƙololuwa a harkar
Alqur'ani.
Ita kanta Ishmah saddar da kanta ƙasa ta yi tana ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta taru cikin
idanuwanta.
Hotunan da Laylah ta ɗauka lokacin ba su kyautuka ta turawa Arfah da yake ta faman yi mata
magiya akan ta yi wa Allah ta tura masa hoton Afishansa na amsar kyautar gwarzuwa a karatun
Alkur'ani, tana turawa ya ce ta makaro domin tuni ya samu vedios ɗin a media dan yanzu babu
inda vedion karatunta bai je ba a duniya.
Ethiopia.
Shi kenan yanzu ruwa yana ƙoƙarin karewa ɗan kada? Ya Abana ya faɗa yana kallon hotunan
da Arfah ya turo masa wai ƴaƴan Tajj sun yi nasarar zama gwarazan hafizai.
Ya sauke numfashi yana kallon Afisha da ta buɗe baki tana amsar awards sai ya lumshe ido
yana jin azababbiyar soyayarta kana ya buɗe vedion karatunta.
Lokacin da ta zo ayar ta biyun ƙarshe cikin suratul yaseen innama amruhu iza arada shai'an an
ya ƙulu lahu kun fayakum.
Sai ya lumshe idonsa yana jin zazzaƙar muryarta cikin nata salon karatun da ƙira'ar mai
ɗaukan hankali.
Ban da yana kallon lasifikan da bakinta tabbas da ya ce, wannan karatun nata, sai da aka kai
shi computer aka gyara saboda daɗinsa da yadda yake kwantar da hankali.
Alƙalin gasar ne ya ƙara janyo mata aya a cikin suratul shu'ara'i nan ma ta ɗauke tamkar wata
na'ura ta fara biyawa cikin gwaninta da ƙwarewa.
Cikin tsananin jin daɗi da son kusanci da yarinyar
Ya sake lumshe ido yana jin karatun zuciyarsa na kwaɗaita masa son ta da ƙaunarta.
Lokacin da ta gama sai ya ƙara dawo da vedion farko ya ci gaba da sauraren ta yana lumshe
ido.
Shi kam Tajj rayuwarsa ta yi kyau, duk da baya tare dani Allah ya albarkace shi ta inda ban yi
tsammani ba, samun zuri'a irin wannan babbar kyauta ce daga Allah wannan kuma baya rasa
nasaba da riƙo da Alqur'ani mai girma da bin tafarkin dai-dai.
Sai kuma ya buɗe lumsassun idanunsa. Yanq ji wani irin tsananin farin ciki na ratsa shi, ya saki
murmushi kana ya miƙe, ya na kokarin kiran waya, cikin mintina biyu aka ɗaga ya ce.
"A saye ƙaton Sa babba yanzu a kawo a yanka shi a yi lafiyayyan abinci a soya naman a bayar
sadaka muyi kiyafa."
Ya faɗa cikin bada ubarni
Ya kashe yana jin wannan sadakar ta yi kaɗan dan nunawa Ubangijin sa farincikinsa ga ni'imar
da yayi masa a cikin zuriyarsa, fitowa ya yi waje, masu zama ƙofar gidansa ya hau rabawa kuɗi
cikin fara'a da jan su a wasa, kana ya bi dukkan ƴaƴansa da alert ɗin bank dan shi bai san wane
kalar daɗi yake ji na a cikin ransa, abin da ya sani duk ya tuna da zaƙin Muryar Afisha da yadda
take karatu sai ya ji zai iya bayar da komi nasa dan farin cikin kasancewarta jikarsa.
Ƴaƴansa kam sun yi mamaki matuƙa don har tambayar junansu suka dinka yi akan sauyin ya
Abana da kuma kyautarsa ta ban mamaki a ranar.
Washegari ma haka ya farka cikin farin ciki, kana ya ci gaba da sauraron karatun da ke sanyaya
masa rai da korar da ƙuncin cikin ransa.
A hankali gabansa ya faɗi da ya tuna waskataccan mafarkin da ya yi jiya wanda ya zame masa
masifa, a kodayaushe dai mafarkin ne ke ta nanata kansa.
Cikin jurewa takaicinsa akan rayuwarsa ta yanzu ya miƙe yana tunanin kai ziyarar bazata asibiti
dan haka kawai hankalinsa ke karkato masa shi.
Driver ya kira ya shiga ya fashi umarnin su tafi asibitin ko Allah zai sa ya ci karo da wani abun
da zai haska masa abinda ke faruwa a asibitin duk da har yanzu sautin ƙira'ar Afisha na kai
komo cikin kunnuwansa shi ya taimaka wajen tabbatar da farin cikin sa a zuciyarsa, a hankali
ya ɗauko wayarsa ya kunna karatun yana gyaɗa kansa cikin jin alfaharin jikarsa ce ke wannan
karatun tamkar ƴar larabawa mai na'ura a cikin maƙogoro.
Tun daga bakin asibitin ya fara cin karo da abun mamaki, domin wayam ya gan shi babu
mutane, ya sani yanzu babu patients sosai dan kuɗin shiga na asibitin da ka so sittin cikin ɗari
babu, wani zubin a aljihunsa ake cikawa Doctors ɗin kuɗin albashi yana kawo hakan da yadda
yanzu mutane ke matuƙar kulawa da kawunansu wajan gujewa cin ko yin wani abu da zai saka
su cikin wata lalura.
Bai tsinke ba sai da ya shiga farfajiyar asibitin, tamkar wanda aka yi kora, kai tsaye wards ya
shiga babu patients sai wasu da ba su fi mutum biyar ba, takaici ya sa ya runtse ido yana hasko
shekarun baya lokacin da Afif ke kula da asibitin.
D asauri ya buɗe idonsa ya shiga ɓangaren office ɗin Doctors ɗin wasu a rufe har sun yi yana
cikin mamaki ya kira wani Nurse da ya zo wucewa.
"Dan Allah Ina doctors ɗin nan suke."
Wani irin kallo ya yi masa kana ya ce.
"Amma kai baƙo ne ko nace ka jima baka shigo asibitin nan ba, ai ko ni da ban daɗe ba, ban zo
na same su ba, kawai office ɗin fanko ne babu kowa a ciki."
Har ya juya zai tafi ya dakatar da shi.
"Dan Allah dana tsaya na tambaye ka."
Cikin ƙaguwa ya tsaya.
"Ka yi sauri ka tambaye ni don ina da aikin yi."
"To korarsu aka yi ko me ya sa suka bar asibitin alhali nasan da Asibitin nan ba baya ba wajan
kula da majinyaci."
Kallonsa Nurse ɗin ya yi kana ya gyaɗa kai.
"Ada Kam a yanzu mai asibitin kamar taɓi-taɓi haka yake, babu mutunci lamarinsa, don yau zai
ɗauke ka aiki, da kaga kuskure ka yi masa gyara sai ya ce baka isa ba ya baka sallama ko
kuma ya tattara albashinmu na wata biyar ya hana, daga baya sai ya baka na wata ɗaya ya ce
zai cika maka sauran, ba ma wannan ba, babu ingantattun kayan aiki ko nagartaccan maganin
daya dace....
Kash bai kamata na faɗa maka haka ba, amma gaskkiya ɗaya ce, ni ma nan jira nake na samu
wani asibitin na koma can dan ba zan iya ba...."
Yana kaiwa na ya juya ya tafi.
Bango Malam ya dafa kana ya sulale ya durƙushe kan kujerar dake gefenshi dan yana da
tabbacin ba zai iya jure tsayuwar nan ba dan tabbas zai iya yanke jiki ya yi mummunan faɗuwa.
Gabansa na falfala faɗuwa haka zuciyarsa na ƙara hasa wutar baƙin ciki da takaicin wannan
al'amari.
Sai da ya kwashe kusan minti goma kana ya lallashi zuciyarsa ya miƙe ya yi injection room,
babu kowa, labor room nan ma mace ɗaya ya gani da ya tambaye ta ta ce su biyu ne kacal, ita
da wacca take aikin dare, yanzu babu ma'aikata, sai ya wuce sauran rooms ɗin nan ma duk
sammakal.
Da sauri ya koma mota ya ce wa driver ya tsaya a waje har sai ya kira shi.
Yana shiga ya fashe da kuka, rabonsa da kuka irin wannan tun yana matashin saurayi.
Kuka ya yi yana dafe zuciyarsa cikin ƙunci da ɗacin rai.
"Kabiru ne ko Aryan? Waya cuce ni a cikinsu?" Sai ya dafe kai ya ci gaba da kukan mai sauti.
"Haka rayuwata zata ƙare cikin baƙar ƙaddara yara su yi ta zalunta ta suna yaudarata, na ɗora
su akan tafarkin Allah su watsa min ƙasa a ido, su cutar da ni, Yah Allah na tuba menene na yi
wanda wannan masifa take bibiyata a yanzu? Me na aikata?"
Sai ya kuma fashe wa da kuka, cikin kukan ya ci gaba da magana.
"Iya sanina ban taɓa zaluntar kowa ba amma me ya sa ni ake zaluntata kuma masu zaluncin
yarana na cikina?".
Wayarsa ya ciro hannunsa na karkarwa ya kira Aryan.
Bata jima ba tana ringing ya ɗaga.
Sai da ya yi ƙoƙari matuƙa wajan saita kansa kana ya ce.
"Aryan ya Asibiti kuwa yana nan dai komai na tafiya ƙalau."
Muryar Aryan ɗin ta karaɗe kunnuwansa.
"Sosai kusa Ya Abana asibiti na nan yadda ake so, ina kula maka da shi da Kabirun ma yanzu
kam sai hamdala."
Cikin cijewa da takaici ya kashe wayar yana ƙara fashewa da kuka.
Lallai ba ƙaramin masifa ba ce wannan Allah ya jarabce ka da ƴaƴa irin nasa Aryan da Kabiru
masu son ganin bayansa.
“Allah na tu ba nasan Tajj bazai taɓa haintata hakaba koda kwatankwacin hakaba”.
Dole ya yi kuka mai sauti dan rage raɗaɗin bakin cikin munafurtarsa da ƴaƴan cikinsa suka yi
Sai kuma ya saki tattausan murmushi tunowa da Afisha lokaci ɗaya kaso tamanin na baƙin
cikinsa ya fice daga zuciyarsa sa bege da son ganin ahlin Tajj ɗin suka cike mishi gurbin da
zumuɗi da maraji ji yake dole ya kasance gaban Afishan dasu Ayeed suji ɗuminsa a matsayin
kanku, cikin farin ciki ya goge ƙwallar kana ya ƙara dai-dai-ta kansa sannan ya kira Driver ya zo
su tafi.
A kan hanya karatun Afisha ya kunna ya lumshe ido yana saurare zuciyarsa na raya masa
samun ta kaɗai matsayin jika ya ishe sa duk da irin mummunan zaluncin da ƴaƴan cikinsa ke yi
masa.
Zaune yake a falonsa yayinda duk manyan yaransa ke zaune hakama matansa.
Cikin tura baki Arfah da Imran da tuni yanzu sun zana cikakkun pillots masu kamala.
“Nifa sauri nake zan fita, dan ina da parsingers ɗin Pakistan.”.
Arfah ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Imran ma miƙewar yayi tare da cewa.
“Ni kuwa da tun juya da dare ina saman gajumare sai yanzu da na iso zan huta kuma ka wani
kiramu kuma kaƙi cewa komai”.
Da sauri suka koma zaune saboda ganin kallon da Yah Hafiz yake musu.
Shi kuwa Yah Abana E passport ɗinsa ya miƙewa Arfah tare da juyowa ya kalli Ummey cikin
tsuke fuska da yace.
“Kuje da Arfah ki bashi E passport ɗinki.
Kai kuma Arfah ka kaiwa Siddiq mun gama mgna dashi zai samo mana sahalewar barin ƙasar
nan”.
Cikin sauri ya kuma tsuke fuska tare da yin kici-kici da ita ya watsawa Mom Amal wani irin
kallon rufe min baki sabida jin tana cewa.
“Barin ƙasar kuma? To kuma ina zakuje? Kuma ai ma wannan karon ba tafiyarta bace”.
Cikin sauri Ummu Aryan tace.
“Ni tafiyatace kuma nasan Malam bazaiyi hakan a wofiba.
Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy yasa ayi Umrah karɓeɓɓe, ni na yafe duniya da ƙiyama
dama mun gama magana da Malam ɗazu da rana”.
Wani irin kallon tashin hankali Aryan ke yiwa Yah Abana tare da cewa.
“Toh Yah Abana? Umaran kenan zaku tafi?”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“Inda ka aikeni”.
Murmushi Hajia Babba maman su Yah Hafiz kenan tayi tare da miƙewa tana kallon Ummeey
tace.
“Ni dai dama zam-zam ɗina ya ƙare in kunje ki kawo mana da yawa”.
Ita kam Ummey sai binsu da ido takeyi cike da aminci yarda dasu a kanta duk da tasan wannan
karon bada ita zaije Umaran ba kamar yadda yake binsu layi layi amman tayi farin ciki da tafiyar
ko ba komai zata ƙara samun daman kai kukanta ga mai kowa mai komai.
Ita kuwa Ummey tare suka fita da Arfah.
Shi kuwa Yah Abana Imran ya kira suka shige har can uwar ɗakansa.
Mom Amal kuwa da sauri ta fice Aryan da Kabiru na biye da ita a baya.
Ganin shiru-shuru Yah Abana da Imran basu fito bane yasa duk su Yah Hafiz suka watse.
Washe gari da yamma Arfah ne ke kwance a masauƙinsa a Pakistan yana waya da Imran cikin
tarin ɗaurwar kai yake cewa.
“Oga Siddiq dai yace min ya gama musu komai na tafiyar jibi jirginsu zai tashi.”.
Cikin sauri Imran yace.
“To wai ina zasu kebe?”.
Kai Arfah ya ɗan mirgina tare da cewa.
“Ohon masa ni dai ban tambaya ba kuma ma ai kaima kasan bazai wuce Umrah zai je yi ba.
Numfashi mai sarƙafe da nazari Imran ya sauƙe kana sukayi sallama...
Wajan cike yake maƙil da mutane haka gefe jojis ne da ke zauna kan manyan kujeru suna
kallon mai gabatar da rawar wata yarinya Najisa, banda shewa da kida da kuma rawar da
yarinyar ke yi babu abin da ke ta shi a wajan, sai da ta gama aka yi mata shewa da tafi jojis ɗin
suka tambaye ta sunanta da kuma burinta akan nasarar da idan ta yi.
Can gefe Adaya ce da Yasir da ta saka masa wasu shegun fitinannan kaya, sai ƙura masa ido
da ta yi cikin ƙarfafa masa gwiwa.
Sauke numfashi ta yi a hankali kana ta ɗauke fuska ta ce.
"Wannan ita ce ranar da na jima ina zumuɗi da saurare, Yasir ka cika min burina, Yasir ka zama
kaine gwarzon wannan gasar kamar yadda na zama gwarzuwa a dukkan gasar rawa ta duniya."
Izzin ne ya katse ta.
"Duk yadda za a yi Yasir a yi ka yi nasara, burin mu ace ka yi gadon mamanka na zama gwani
na gwanaye."
Sai ya waiwayo ya kalli Asina.
Ya ce.
"Kina da abin cewa."
Sunkuyawa Asina ta yi ta ce.
"Yasir mamanka tun kana jariri ta ɗau alwashin zamowarka gwani, dan Allah ka cika mata
burinta kada ka ji gazawa kasawa, ka ƙarfafa kanka za ka zama gwani in sha Allah kuma bayan
ka cinye gwajin yau dole duniya tasan sunanka da mahaifinka yake fata da burin ka fito duniya
ta sanka dashi."
Gyaɗa kansa ya yi ya kalli lasifikan da take kiran sunansa dan gabatar da rawar sa zagaye na
ƙarshe wanda daga shi sai faɗin result.
Cikin wata tafiya da Izzin ya koya masa ya tunkaro wajan, tafiyar da ta tafi da imanin mutanen
wajan suka saka sowa, kana wasu na ƙara zuzuta kyawunsa da haibar yaron yana zuwa aka
miƙa masa lasifika domin amsa tambayoyi kafin ya fara rawar.
Ɗaya daga cikin jojis ɗin ne ya ce.
"Kyakkyawan yaronmu menene burinka idan ka samu nasarar cin gasar nan?"
Shiru Yasir ya yi yana kallon mutanen wajan yana jin tsananin farin ciki da zaƙuwa wajan
cikama mamansa burinta na zamowarsa gwarzon rawa.
Cikin zazzaƙar muryarsa ya ce.
"Ina son gina gidan koyar da rawa na yara irina, sannan ina son na zama babban ɗan rawa da
babu kamar sa a duniya kamar yadda mamana ta zama ƴar rawa na duniya!"
By
*GARKUWAR MARUBUTA**INDA RAI*
Part 3 page 2
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Wajan ne ya ɗauki shewa, da tafi.
Lokaci ɗaya jojis ɗin suka ba shi umarni ya fara gabatar da rawar gwaji dan fitar da