Showing 18001 words to 21000 words out of 70225 words
Chapter 7 - Amnoor Complete Romantic Hausa Novels by Aysha JB.pdf
tare da musu iso zuwa É—akin shi da ke wajen
gidan. Ɗakin fess yake kasancewar shi mutum ne me tsafta ɗan ƙwalisa domin ya ƙawata ɗakin
da kayan ƙyale-ƙyale na zamani cike da shaƙiyanci yake magana tare da gabatar musu da
kayan motsa baki kana ya ce "Har yanzu ban gane wane ne angon ba" Kallon Alh Aminu da ke
ta murmushi yaƙe Baban Amrah yai kana yai masa nuni da cewar "Ga shi nan" Sunkuyar da kai
Alh Aminu yai ganin yadda Baban su yake ƙare mishi kallo yana gyaɗa kai. "Madalla bari na
turo muku ita" Yana fita Baban Amrah ya ce "Amma da ganin wannan sirikin naka É—an duniya
ne" Shi dai bai ce masa komai ba. Lokacin da Babban su Nuriyya ya shigo ya yi daidai da zura
ƙatuwar hijjabinta tana ƙoƙarin yin Sallar la'asar da ya wuce ta domin yau da zazzaɓi ya wuni,
"Nuratu ki shirya kina da baƙi a ɗaki na, ki yi sauri domin ba jimawa za su yi ba"
"Ai ka bari ta yi Sallah ko kuwa?" Maman Nafisa ta faÉ—a tana hararar shi. Jiki a sanyaye ta yi
Sallar tana sallamewa ya azal-zala musu wuta ta yi ta fito Fiddoh da fitowarta kenan daga
banÉ—aki ta kalle shi tare da faÉ—in "Ai ta amsa za ta zo, ka je mana, ka tsaya kana surfawa
mutane ruwan bala'i haka za ta je ba tare da ta shirya ba?" Fita yai yana masifa. "Dalla ke ma
ki shirya kin yi tsaye se rawar jiki kike ba dole a cika mutane da surutu ba" Fashewa kawai
Nuriyya tai da kuka domin ta rasa ya ma za ta yi. ÆŠauke kai Maman Nafisa tai domin wannan
ba maganar da za ta saka musu baki ba ne. "To ni me zan yi? Dan Allah shirya mu je tare.."
Zaro mata ido Fiddoh ta yi tana faɗin "Wa? Taɓɗi! Ai ki shirya kawai ki je wurin mijinki ba inda za
ni"
Juyowa ta yi tana kallon Mamansu da ke zuba turare a kwalba, "Ayya Mamanmu dan Allah ki
ce mata muje tare" Ba tare da ta É—ago kanta daga abinda take yi ba ta ce "Ku je tare da Zaliha"
Zaliha da ke taya ta zuba turaren ta zunɓuro baki tana mita ita tana aiki za a ɗaga ta. "Ai ko na
je wallahi ba zama zan yi wurin mata da miji ba" Ta faÉ—a tana share hannunta a jikin hijjabin da
za ta saka, kallon yadda Nuriyya ke shirin fita ba tare da ta shafa mai ko turare ba "Eyye! Dama
haka ake zuwa wurin miji bagajan-bagajan ba shafa mai bare hoda ko turare? Kuma da wannan
uban hijjabin za ki tafi sai ka ce matar malam?" Dakatawa Nuriyya ta yi tare da juyowa tana
kallon yanda take hijjabin da take Sallah ne, ba shi da wani ainu. Bata aune ba ta ji Fiddoh ta
buÉ—e turare tana zuba mata. Cikin faÉ—a Maman su ta ce "Wai Firdausi lafiyar ki ? Turaren nan fa
an riga da an biya na gama musu haÉ—in kayan amare ne fa.."
"To ai ita ma amariyar ce" Fiddoh ta faÉ—a tana dariya tare da kallon yanda Mamansu ta haÉ—e
fuska "Yi haƙuri Mamanmu ni zan biya sai a musu wani shi ke nan? Ku kuma tsayuwar me
kuke? Ko se Baba ya dawo ne za ku tafi?" Hannun Zaliha ta riƙe suka fita Zalihar ce ta yi
Sallama sai da aka amsa musu sannan suka shiga. Zama suka yi kan ledar da ke malale ƙasan ɗakin cike da ladabi Zaliha ta gaishe su da
murmushi suka amsa domin yabawa da nutsuwa tare da tarbiyyanta abin ya burgesu ƙwarai.
Nuriyya kam har yanzun kanta na ƙasa da murmushi Baban Amrah ya kalli Nuriyya tare da taɓa
Aminin nasa nan shima ya É—ago yana duban inda take, mutuwar zaune yai yana sake kallonta
"Ita ce fa!" Ya faɗa yana kallon Baban Amrah wanda ya miƙe tare da yafito Zaliha suka fto tare
da nufar wurin mota yana tambayarta sunan ta.
"Suna na Zaliha Hamisu Saleh"
"Ni ce name amma kina mace na ji ki da turaren maza kuma haÉ—i na musamman" Turo baki ta
yi tana faÉ—in "To ba aiki É—urawa nake yi ba, shi ne Mamanmu ta ce se na rako Aunty Nuriyya"
Dariya domin yanayin da yarinyar take magana ya burge shi sosai haka suka ci gaba da hira
tana zuba mishi surutu da shirme shi kuwa yana biye mata can dai ya tambaye ta game da
karatu shuru ta yi masa ba tare da ta ba shi amsar ba.
"Turaren na siyarwa kuke yi?"
"Eh kuma harda haÉ—in amare Mamanmu ta iya da na maza ma duka ana yi"
"Je ki kawo min su na gani" Da gudu ta shiga gida ta É—auko mishi kwandon da take zuwa talla
da shi.
"Lallai Mamanmu ta iya turare masu kyau zan so mu yi magana da ita domin haÉ—in ya yi min
kyau, kodayake zan turo Amrah sai su yi magana.."
"Amrah? Aunty Amrah dai da na sani ƙawar Auntyna?"
Murmushi yai mata gwalo ido ta yi tana faɗin "Taɓ! Abun da mamaki wallahi to shi wancan mijin
Aunty na ya alaƙarku yake da shi?"
"Alh Aminu shi É—in Amini na ne tun yarinta komai namu tare muke yin sa" Daga haka hira ya
ɓarke tsakaninsu Zaliha nata zuba mishi shirme yana murmushi.
"Bisimillah ta so ki zauna a nan" Ya faÉ—a tare da nuna mata gefen sa. Girgiza kai ta yi tare da
ƙara takurewa da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce "Ina yini.."
Maƙalewa sauran maganar tata yai jin ya zauna gab da ita, ɗagowa ta yi da sauri tare da watsa
mishi Lulu Eyes ɗinta da ya tara ruwa, murmushi ya sakar mata tare da riƙe fuskarsa da hannun
biyu yana kallon kyakkyawan siririn fuskanta. "Kina mamaki ko? A baya na sha neman ki kamar
zan yi hauka, domin an ƙidaya min lokaci na fito da matar aure har wa'adi ya cika ba tare da na
ganki ba, lokacin da muka haɗu sai na ga gabaɗaya tsoro ne ke ɗawainiya da ke, da na tuntuɓi
É—iyata 'yar wajen Aminina Amratullah ita take sheÉ—amin cewar ke matar aure ce domin an É—aura
miki aure watanni baya, na ji babu daɗi nan na yanke shawarar zan amshi zaɓin da mahaifiyata
ta yi mini sai gashi a she ke ce, ina ta cika ki da surutu ba tare da na sanar da ke waye ni ba.
Sunana Alh Aminu ni haifaffen nan garin Abuja ne, ina da mata É—aya wacce ta kasance
'yar'uwata ce, yaranmu biyu Hisham shi ne Babba wanda a yanzu yana ci gaba da karatunsa a
ƙasar waje, se Suhaima. Matata tana matuƙar so na kuma tana da kishi sosai bana wasa da
duk wani abun da ya shafi iyalina musamman Ummata ina son su.
Ni ɗan kasuwane ina ƙasuwanci har ƙasashen ƙetare, anan ina da shagunan sarƙoƙi, ni kaɗai
nake ta magana ba tare da kin ce min komai ba"
Ɗan matsawa ta yi ganin yadda suke gab da juna, sake ƙanƙame jikinta take yi domin
gabaÉ—aya a takure take "Babu abinda zan yi miki" Ya faÉ—a tare da matsowa ya kamo hannunta
ƙara ta saka tana ƙoƙarin fisgewa nan da nan ta shiga rawar jiki "Subhanallahi!" Ya faɗa tare da
riƙe ta sosai a jikinshi yana mamakin wannan lamarin nata. Wayarshi ya ɗauka tare da kiran
Baban Amrah yana faÉ—in ya tura mishi Zaliha. Kallon Zalihar yai tare da faÉ—in "Har ka gama
shan love É—in ne da wuri haka?" Tsaki Alh Aminu yai tare da kashe wayar sannan ya É—auketa ya
É—orata akan kujera kana ya zauna kusa da ita.
Kuɗi masu yawa Baban Amrah ya miƙa mata tare da faɗin "Ki bawa Auntyn ki, domin zuwan
gaggawa ne bamu samu munyi tsaraba ba" Maƙe kafaɗa ta yi tare da ƙin karɓa "Wallahi idan na
amsa duka Mamanmu za ta yi min" Cike da yabawa da tarbiyyanta ya ce "Idan kika ce mata
mijin Auntyn ki ne ba za ta yi komai ba, in kuma taƙi ki ajiye min" Da ƙyar dai ta amshi kuɗin
sannan ta nufi É—akin.
Kallonta yai tare da faÉ—in "Zan tafi amma zan dawo dole zan kaiki asibiti domin a duba lafiyar ki,
ki kula da kanki" Ya faÉ—a tare da kai bakin shi goshinta yai mata kiss yana gyara gaban rigar
tasa. Shigowar Zaliha ya ba shi damar fita kanta har yanzun a sunkuye yake sai da ya kusan
fita sannan ya juyo ya yi daidai da É—agowar da ta yi, nan idanunsu ya faÉ—a cikin na juna, da
sauri ta ɗauke kanta daga kallon shi sannan ta miƙe ita ma jiki a sanyaye ba ta san ya ajiye
mata kuɗi ba sai da taga Zaliha ta ɗauko tana miƙa mata. "Laa Aunty ga kuɗin ki manta da su"
Juyowa ta yi tare da kallon kuÉ—in wanda ya kusan talatin. Haka suka shigo cikin gida nan
Maman su ta dinga faÉ—a ganin kuÉ—i har dubu hamsin "Mamanmu wallahi ban san ya aje min
kuÉ—in ba.."
"Ke ba ni kuÉ—in tun da ba ta so.." Baban su ya faÉ—a tare da kai hannu zai amshe, da sauri Zaliha
ta faÉ—a kan Maman su tana faÉ—in "Wallahi ba zan bayar ba, ai ina kallo Baban Amrah ya ba ka
kaima" Fita yai a É—aki yana faÉ—in yara duk babu me tarbiyya da zai dinga faÉ—ar magana cikin
ladabi da biyayya.
"Ji nai kana ƙamshi da alama dai sai da ka angwance.." Taka burki yai da ƙarfi yana kallon shi
tare da faÉ—in "Allah zanci abu kazan ka.. Haba! Duk ka isheni da surutu da ke ni na rako jaraba
duniya dole daga zuwa na hmm" Sai kuma yai shuru domin idan ya biye masa haka zai yi ta
zolayar tasa a haka suka nufi gidan Aminu suna tattauna yanda tariyar zai kasance anan ne
yake sanar mishi halin da take ciki wanda ya rasa gane mene ne, sun tsayar da maganar akan
zai samu Amrah su tattauna yayin da Hon. Sa’id ya ce ya sanar da Larai halin da ake ciki.
A gefen guda kuwa É—aya daga cikin 'yan group É—in su ne ta samu labarin Alh Aminu ya yi aure
ba tare da sanin matarshi ba nan fa aka kafa mitin tare da laluɓo number Hajiya Larai wacce
take can Legas tana duba shagon kayan ta Fiddoh ce ta yi kiran a É—aya daga cikin wayar da
suke amfani da shi. Ganin baƙuwar number ya sa ta ɗauka tare da kara wayar a kunnenta tana
faɗin "Hello!" Daga ɓangaren Fiddoh ta ce "Ki duba mun tura miki account ɗin mu ki turo da
miliyan ɗaya mu kuma za mu faɗa miki abinda ke shirin faruwa daga ɓangaren mijinki" Tana
gama faÉ—ar haka ta kashe wayar jiki na rawa ta tura musu kuÉ—in murmushi Fiddoh ta yi tare da
miƙawa Na'ilah wayar don ita ta gama aikin ta. "Ki yi gaggawar barin Legas ki dawo gida domin
mijinki na shirin angwancewa domin tuni an É—aura aure" Tana kawowa nan a zancen nata ta
datse wayar tare da kashewa bayan ta ajiye layin a ƙasa. Zubur Hajiya Larai ta miƙe tana faɗin
"Jar uban can! Ni ce za a yi wa kishiya? Duk yaushe aka yi wannan ban sani ba?" Jiki na rawa
ta É—auki waya tare da kiran layin shi sai dai baya shiga, haka ta siyi tikiti ba shiri ta kamo hanyar
Abuja.
***
Yana ɗaya daga cikin ɗalibai masu hazaƙa da malaman ke ji da shi, nutsuwa haɗe da tarbiyya
gami da biyayyarsa ne ya ƙara mishi ɗaukaka da farin jini, duk inda ya gifta nuna shi ake tare da
yabon ƙwazo da hazaƙar sa. Mata da yawa suna bin sa daga fararen fata zuwa ga 'yan'uwansa
'yan Nigeria da suke tare a wurin sai dai ko É—aga kai ba ya yi balle ya kulasu. Mace É—aya ce ta
tsaya masa wacce a kullum cikin mafarkinta yake kuma kullum cikin da-na-sani abin da ya
aikata mata yake, kusan kullum suna waya da abokansa wanda su ma tun faruwar lamarin
iyayensu suka ɗaga su a ƙasar kasancewar ta'asar da suke yi wa 'ya'yan mutane sai gaba yake
yi, duk da haka ba su daina ba, domin sex ya zame musu tamkar ruwan shan su wadda in har
ba su sha shi ba ba su jin daÉ—i iskancin na su ya shahara ne ya yi da suka samu gurbin karatu a
jami'ar London inda suka haɗu da gogaggun tatattun 'yan iska wanda suka yi ƙaurin suna a
harkan 'SEX GAME' idanunsu ya BuÉ—e fiyye da baya dan suna iya kwanciya da mace fiye da
É—aya a lokaci É—aya duk da haka ma maneji suke yi dan har yanzu ba su samu mace kamar
yarinyar can ba. Juyi yai a gadon da yake tare da runtsa idanunshi hoton abinda ya faru yana
sake dawo masa tamkar yanzu aka yi sa ihu da magiyar da take mishi ne ya sake cika dodon
kunnen shi.
Saura ƙiris free page zai ƙare.
Wannan Littafin na kuɗi ne domin kasancewa cikin group za a tura ₦500 ta wannan account ɗin
2389596965 Aisha jubreel Zenithbank. Sai a tura shedar biya ga wannan Number 09079740079
#Amnoor
#Sadstory
#Destiny
#Hotlove
#Romance
[5/9, 11:43 PM] FARHATULƘALBí ½í²”í ¾í´—: *♡AMNOOR...!*
_A romantic story_
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATIONí ½í³š
★F. W. A★
H-P Place Group.
Free page 23_24
Kuje ku yi Subscriber Channel É—i na a YouTube. FARIN JINI HAUSA TV. Domin sauraron
ƙyatattun littafanmu.
*Following me on Wattpad: ayshajb*
*Arewabooks: ayshajb*
Kuje Arewabooks za ku samu littafaina a can.
A kasalance ya sake buÉ—e idanun nasa wanda ya fara sauya launi saboda yanayin da yake
ciki, wayarshi ya laluɓo tare da kiran Hajiya Larai wacce take ƙoƙarin saukowa daga matakalan
jirgi ƙarar wayar tata ba ƙaramin kiɗimata ya yi ba, nan take zuciyarta ya fara dukan tara-tara
buÉ—e jakarta ta yi sannan ta É—auko wayar hannunta na rawa a hankali kuma ta sauke gwauron
numfashi ganin Hisham ne me kiran nata zama ta yi a kujeran da ke kusa da ita kana ta kara
wayar a kunnenta ba tare da ta ce masa komai ba, dan ta san maganar tasa ba zai wuce
wannan yarinyar da suka hake mata ba, ita ta rasa wane irin masifa ne yake bibiyarta É—anta
yana neman haukacewa a kan yarinyar da bata san wace ce ba, shi ma kanshi bai san wace ce
ita ba, amma duk ya damu a kan lallai sai ta binciko mishi ita, bari yau za ta yi maganin abun.
"Barka da warhaka Mome ya gida da su Hajiya?" Amsa mishi ta yi da faÉ—in "Kowa lafiya ya
karantun naka ina fatan kana mayar da hankali?" Tamkar yana gabanta ya gyaÉ—a mata kai kafin
ya ce "Mome wai har yanzu ba a samo inda yarinyar nan take ba ne.." Miƙewa ta yi daga
zaunen da take ganin drive ya ƙaraso tare da faɗin "Zan ci mutuncin ka muddin ka sake min
wannan maganar! Hisham ka fita idona na rufe daga kai har uban nan naka kun saka ni gaba
da fitina to wallahi ba za ku kashe ni da raina ba karka sake kirana muddin wannan maganar za
ka yi mun" Tana kawowa nan ta kashe wayar tana jan tsaki tare da da ka ma driven tsawa
"Dalla taka mota mu tafi ka wani tsare ni da ƙananun idanu kaman fincen ƙuma!" A gefen
Hisham kuwa bin wayar ya yi da ido yana jin wani abu ya tokare masa ƙahon zuciyarsa. Hamdala ta yi a ranta ganin motar tasa a gida da sauri ta fito ta nufi cikin gidan a falo ta jefar
da jakarta kana ta nufi ɗakin sa. Daidai ya fito toilte ɗaure da towel a ƙugunsa kenan ta shigo
kamar wacce aka jeho ta ba tare da ta yi sallama ba, É—auke kanshi yai daga kallonta ita kuwa
ganinsa a haka ya sa ta ji wani yanayi matsowa ta yi kusa da shi ba tare da ta ce komai ba
bayan idanunta da ke yawo a jikinsa kaucewa yai domin ya lura so da abin da take son yi, sai
dai duk yanda ya so ƙin abin sai da ta samo kanshi domin ta yi matuƙar kewarsa da ma shima a
'yan kwanakin nan haƙuri yake musamman ma idan ya je gurin Nuriyya duk sai ya ji shi a takure
nan fa suka lula duniyar sama sai da ta fara mishi ƙananun mita kafin ya ƙyaleta tare suka shiga
wanka sai da ya sake kimtsawa sannan ya zauna yana kallon yanda take ta murmushin yaƙe ga
dukkan alamu kuma akwai abin da take son faÉ—a masa sai dai yanda ya yake É—auke kai tare da
sake tamke fuskarsa ne ya hanata yin magana. Abinci ta zuba mishi tana kallon yadda yake
komai a nutse wannan yanayin nasa ba ƙaramin burgeta yake yi ba. Wani murmushi ne ya
suɓuce mata wadda ita kanta bata san na mene ne ba, ɗagowa yai yana kallon yadda take
murmushi har sautin sa yana fita wanda rabon da ya ga irin haka a É—au shekaru masu yawa "To
fa! Wannan murmushin fa?" Ya tambaye ta tare da ajiye cokalin gyara zama ta yi tare da faÉ—in
"Ina kallon kyakkyawan fuskar mijina mana, gani na yi ka ƙara kyau da cikar haiba, nutsuwarka
ya sake ƙaruwa fiyye da na baya gaskiya ba ƙaramin dace na yi ba.."
"Dacen me?" Ya katse ta da faÉ—in haka "Samun gwarzon kamar ka mana" Wani murmushi yai
tare da ture abincin gefe yana fuskantar ta ganin haka ya sa ta nutsu sosai tare da ƙura masa
ido.
"Tun kwanaki na so in faɗa miki abin da ke faruwa sai dai kika ƙi ba ni damar hakan duk yanda
na so mu yi maganar sai ki kauce da kawo min uzirin kina busy" ÆŠan dakatawa ya yi tare da
fesar da numfashi
07, December 2025
Habib Musa abdulkadir
We love ur book