Showing 39001 words to 42000 words out of 70225 words
Chapter 14 - Amnoor Complete Romantic Hausa Novels by Aysha JB.pdf
Suhaima ta kan kawo musu ziyara domin dai ya ƙi yarda ta dawo gidan
ganin yadda Amnoor take da fara'a kuma suna zaune lafiya da mahaifiyarta ya sa ita ma ta
sake har suke gaisawa da 'yar hira tana girmamata a matsayinta na matar mahaifinta domin sai
da Hajiya Umma ta ja mata kunne sosai tare da gindaya mata kashedi na ba ruwan ta da
Nuriyya bare ta ce za ta taya uwarta kishi, da ke tana tsoron kakar tata shi ya sa ta nutsu take
mata biyayya. Yanzu tana ɗan fita yawon daren ta ganin Hajiyar ba ta takura mata Lil ne dai ya
ƙi saukowa tun faɗar da suka yi da Fiddoh duk inda ta samu labarin yana zuwa bin shi take yi.
Amma ko kallo ba ta ishe shi ba.
“Amnoor ya dai na ga kin yi wani yanayi na daban a kwai wani abun ne?” Ya faɗa tare da kamo
hannunta, ɗan murmushi kawai ta yi tare da juyawa tana ƙoƙarin shafa mai towel ɗin da ke
jikinta ya kai hannu zai kwance mata, ba ta hanashi ba, domin ta san ba abin da zai iya yi mata
wanda ya wuce ya jagwal-gwalata tana jin shi ya fara taɓe-taɓe ita dai ba ta ce komai ba bayan
shurun da ta yi. “Ki yi haƙuri wallahi ni ma ban san abin da ke damuna ba”
“Uhm ka ji na ce wani abu dangane da rashin kafiyarka? Ko na ce maka na gaji da..” Rufe
mata baki ya yi da sauri yana faɗin “Baki faɗa ba, amma alamu sun nuna kina kewata ko? Na
sani ni ma ina kewarki” Danne damuwarta ta yi tare da haɗe fuskokinsu kissing lips ɗin shi ta
yi. “Hubby karka damu In Sha Allah za ka ji sauƙi” “Kin tabbata babu damuwa?” Juyowa ta yi tana kallon shi tare da faɗin “In sha Allah babu
komai” Jan karan hancinta yai tare da faɗin to ki gama shiryawa sai mu je asibitin tare ko?”
Gyaɗa mishi kai ta yi, yana tsare har ta gama shiryawa kallonta kawai yake yana haɗiyar miyau
shi dai wannan ciwon ya katse mishi jin daɗi. Har za ta shafa man baki sai ta ajiye domin ta san
ko ta shafa haka zai lashe, yana riƙe da hannunta har wurin mota Hajiya Laraba ta rako su tana
musu a dawo lafiya, motarshi na fita a gida ta kwashe da wani mugun dariya tana faɗin “Haka
za ka yi ta gantalin neman magani ba za ka taɓa samu ba” Suna zaune gaban likitan da ta duba
shi hannunshi na cikin nata ya ji likitan na faɗin “Alhj ni kam wannan lamarin naka yana ba ni
mamaki, duk da an yi aiki a wurin kuma kana shan magani amma dai har yanzu fa sai a
hankali...”
“Kamar ya ya sai a hankali?” Likitan ta ce “Batun iyalinka nake nufi sai...”
“Dalla dakata malama ban fahimce ki ba?” Kallon shi likitar ta yi ganin yadda ya fusata.
“Duk kuɗin da na ba ku? Ke kisan abin da nake ji kuwa? Matana biyu fa? Ki kalleta da kyau kina
nufin haka zan zauna ina kallon ta da kuruciyarta?”
“Sau nawa kake yi? Kallon Amnoor ya yi sannan ya sake kallon likitar “A sati ko a rana?”
Sunkuyar da kai na yi domin na fahimci a kan me suke maganar duk sai na ji kunya ta baibaye
ni amma shi ko a jikinshi likitar ta ce “A rana”
“Ke sau nawa kike yi?” Ya wurga mata tambayar dan ya lura tambayar renin hankali take mishi
“A'ah Alhaji ba ka ba ni amsar tambaya ta ba”
Riƙe mishi hannu na yi tare da matsewa ina mishi alamar rarrashi domin na lura ya fusata da
maganar likitar. “Idan na faɗa miki adadin da nake yi a rana tsorata za ki yi, domin tun ba ta
saba ba haka har ta saba tana nema da kanta, shi ne yanzu za ki faɗa min wani zancen banza
ina ga ba ku san aikin ku ba ba zan iya zuba ido ina kallo mace ba tare da na juye mata abin
da...” Riƙo shi na yi tare da faɗin “Ki yi haƙuri Dr tun da aka ce mafitsarar shi ya samu matsala
yake a fusace, musamman ma idan aka ce ba zai iya tarawa da iyali ba” Na faɗa ina kallon
ƙwayar idonshi “Ni na ce miki ba na jin ƙarfin da zan..”
“Mu je gida lokacin shan maganinka ya yi” Dariya kawai Dr ɗin ta yi domin daga shi har matar
tashi dariya suke ba ta ganin yadda ta ɓata rai tana cewa su je ya sha magani shi kuwa sai
faɗin “Ni na ce miki ba ni da ƙarfin da zan yi wani abu? Wato kin raina ni yanzu saboda kin ga
ba ni da lafiya ko? Ya yi kyau!” “Dan Allah duk wannan rigimar ka ajiye shi har mu ƙarasa gida tukun na lokacin ne zan kulaka
amma ban da nan domin idon jama'a na kanmu” Suna ƙarasawa gida ya fisgota da ƙarfi kamar
zai ɓalla mata hannu “Saboda ba ni da lafiya shi ne kike min haka? Kin gaji da ni ko kina son
rabuwa da ni dan ba na biya miki buƙatar ki...” Hannunshi ta riƙe har cikin falonta Zaliha ta iske
zaune. “Aunty Noor kun dawo? Daddy ya jikin ka? Na zo Maman Suhaima take cewa kun je
asibiti” Da sakin fuska ya amsa mata sannan ya fita zuwa nashi ɗakin. Zama Nuriyya ta yi tana
faɗin “Ai na manta yau za ki zo ga shi ban girka mana komai ba ko za ki shiga ki mana girkin?”
Miƙewa ta yi tana faɗin “To” Kayanta Amnoor ta adana mata sannan ta nufi ɗakinsa yana
kwance ta ɗauko magani da ruwa tana miƙa mishi karɓa ya yi tare da ƙure ta da ido, ɗauke
kanta ta yi sannan ta miƙe ta fita a ɗakin.
Da yamma suka haɗu dukkansu a falo suna cin abinci suna kammalawa Laraba ta yi ɗakinta
domin tun da Amnoor ta tare ta sallama mata shi tun da ta san abin da ta ƙulla musu. Kwana
biyu Zaliha ta yi ta tattara ta ce za ta koma gida dan masifar da suke yi kullum dare ya ishe ta
ɗan kullum da dare sai sun yi faɗa yau da wuri ma suka fara rigimar ta su. “Daddy mai ya sa
kake min irin haka? Kana ganin ƙanwata na nan amma kullum sai ka ta da rigima ka bari ta
koma mana in ya so koma mene ne sai ka yi tun da ka zama mafaɗaci..”
“Ni kike faɗawa wannan maganar? Amnoor zan mare ki...” Da mamaki ta matso tana faɗin
“Daddy ai ba sai ka faɗa ba, daman na daɗe da fahimtar kana son kai hannu jikina wallahi na
gaji da wannan fitinar naka haba dan Allah sai ka ce wani ƙaramin yaro kullum sai an jiyo
muryan mu...” Kallon hannun shi ta yi tare da faɗin “Shi kenan ka mare ni ko wutar da ke cin zuciyarka zai
ragu” Fitowa ta yi a ɗakin zuwa nata ɗakin dan kusan sati basu kwnaciya tare tun da ya tsiro da
faɗar dare. Kallon Zaliha ta yi tare da faɗin “Ke lafiya na ganki da jaka?” Zaliha ta ce “Aunty
Noor gaskiya ni gida zan ta fi wallahi ba zan iya da diraman ku ba” Ɗauke hawayen da ke zubo
mata ta yi sannan ta ce “Shi kenan ki gaishe da Mamanmu ki ce mata ina kewarta” A haka suka
yi sallama. Zama ta yi tare da fashewa da kuka dan ta rasa abin da ke jawo musu wannan
fitinar kullum dare babu kwanciyar hankali sai sun yi faɗa sun koma tamkar karnuka tun ba ta
kula shi har ya fara kaita maƙura.
#Paidbook 500
09079740079
[5/9, 11:45 PM] FARHATULƘALB: *♡AMNOOR...!*
_A romantic story_
Wattpad: ayshajb
Arewabooks:ayshajb
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION
★F. J. W. A★
Free page 33_34
Ku je YouTube ku yi Subscriber Channel ɗi na FARIN JINI HAUSA TV. Domin samun ƙayatattun
littafanmu.
H-P Place Group.
“Ya Nuriyya suke.?” Maman Nafisa ta yi mata tambayar bayan ta ajiye jakar Zaliha da ta karɓa.
“Gaskiya babu lafiya Maman mu, dan kullum Aunty faɗa suke yi da mijinta...” Dakatar da ita
Maman Nafisa ta yi da faɗin “Hajiya Laraba ke haɗa su faɗar ko? Dan na san za ta aikata fiye
ma da hakan in dai a kan mijinta ne..” Cikin sauri Zalihar ta katse ta da faɗin “Ko ɗaya Mama
mu, ai Maman Suhaima tana da kirki kuma suna zaune lafiya sai ma kinga yadda suke komai
tare tamkar ma ba kishiyoyi ba tsakaninta da Daddy ne ban san me ke faruwa wanda kullum
yake haddasa musu rigima ba” Shuru Maman Nafisa ta yi tana juya zancen a ranta ta san
muddin Nuriyya ta ce ta yi kewarta tabbas tana cike da damuwa mai tarin yawa ne. Yinin ranar
haka ta yi shi zuciyarta cike da tunanin ɗiyar tata, da a ce Fiddoh za ta amince da ta kaiwa Noor
ɗin ziyara amma ta san da kamar wuya. Aikuwa Fiddoh na dawowa ta tare ta da maganar buɗar
bakinta sai cewa ta yi “Ni in je gidanta? To in yi mata mene?” Da ga haka ba ta sake cewa uffan
ba, domin zancen ma ɓacin rai yake saka ta.
Amnoor kuwa shuru ta zauna a ɗakinta tana tunanin abin da ke haddasa rigima
tsakaninta da mijinta sai dai duk iya bincike da ta yi ba ta gano komai ba, ƙarshe haka ta kwana
da matsanancin ciwon kai, ko da ta farka da Asuba da ƙyar ta iyayin sallah ba ta samu damar
yin azkhar ɗin da take yi kullum ba haka ta kwanta tana riƙe da kanta. Rashin jin motsinta ba
ƙaramin damunsa yai ba, domin ta saba zuwa duba shi ko da ba su kwana wuri ɗaya ba. Ga shi
ko abincin kari bai ga alamar za ta kawo mishi ba, an ya ma ba fushi ta yi da shi ba? Tambayar
da ya yi wa kanshi wanda ba shi da mai ba shi amsar kenan. Haka ya yi wanka ya shirya ya fito
ɗakin Laraba ya leƙa nan ya ga ba ta nan, tun da ya doso ɗakin yake jin yadda take nishi tare
da sheshsheƙan kukanta, da sauri ya ƙarasa ganinta yai dafe da kai tana juyi ga hawaye da ke
zariya bisa kuncinta “Ya Subahanallah Amnoor!” Ya kira sunanta cikin rikicewa yana ɗagota
“Mene ne? Ina ke miki ciwo? Daman ba ki da lafiya shi ne ba ki kira ni ba?” Duk wannan
tambayar ya jero mata lokaci ɗaya. Da sauri ya ɗauki waya tare da kiran likita yana faɗin ta zo
cikin gaggawa. Babu ɓata lokaci kuwa likitar ta ƙaraso kafin zuwan likitar ya yi ƙoƙarin ba ta tea.
Nan ta yi mata allura domin jikinta har da zazzaɓi magunguna ta ajiye tare da faɗa mishi yadda
za ta sha su sannan ta ƙara da faɗin “Damuwa ya yi wa Madam yawa, ya kamata a kiyaye abin
da zai dinga haddasa mata wannan damuwar” Tana gama abin da za ta yi ta yi tafiyarta.
Yana zaune jikinta har ta farka “Sannu Amnoor yaya kike jin jikin yanzu?” Ɗan murmushi ta
sakar masa tare da daurewa ta ce “Ya yi sauƙi, ya naka jikin? Ka sha magani yau?” Ta yi
maganar tana ƙoƙarin ta shi zaune. “Na sha kuma na ji sauƙi sosai” Miƙewa ta yi ta gyara ɗakin
sannan ta nufi toilte ta wanke duk inda ta gifta yana binta da ido cikin zuciyarshi yana jinjina
ƙarfin hali irin nata har ɗakinsa sai da ta je ta gyara ko’ina sannan ta shiga kitchen ta yi musu
girki. Haka ta dinga daure ciwon kan da yanzu yake takura mata tana aikinta izuwa yanzu
rigimar tasu yai sauƙi batun kwana gado ɗaya ne dai har yanzu babu in ya fita aiki yana ƙoƙarin
dawowa da wuri kasancewar tana cikin kaɗaici yanzu ita ɗaya a gida a hakan ma wani lokaci
Amrah na kawo mata ziyara wacce ita ma yanzu karatu take gadan-gadan ba kama hannun
yaro shi ya sa ba ta samun zuwa wurin Amnoor ɗin.
Cikin barci ta fara jin warin hayaƙi buɗe idanunta ta yi tana kallon yadda tsakiyar ɗakin ya
turniƙe da hayaƙi babu jimawa ta fara jin sautin dariya na muryoyi daban-daban wani irin juyawa
ta ji kanta na yi dafe kunnuwanta ta yi da duka hannayenta tare da runtsa ido. Gabaɗaya ta
mance da addu'ar sai jujjuya kai take tana runtsa idanu. Kimanin mintuna talatin ana haka kafin
ta ji komai ya ɗauke zubewa ta yi a ƙasa tana mayar da numfashi daga haka barci yai awon
gaba da ita. Ko da gari ya waye ta kasa faɗa mishi abin da ya faru, shi kuwa kasa shuru ya yi
ganin yanayinta kamar a firgice take, ya yi mata tambaya sai dai ta ce babu komai, haka ya
ƙyaleta ba don ya yarda ba. Yana kammala shiryawa ya fita aiki. Tun bayan fitar shi al'amarin
jiya ya dawo, na yau ma ya fi na jiya tsananta domin wuni aka yi ana firgitata duk inda ta juya
sautin ihu da dariya ne ke kaiwa kunnuwanta farmaki ga shi ta kasa furta kalma ɗaya na addu'a
sai gab da magariba ta ji gidan ya yi ɗif tamkar ba shi ne ya ke juyawa ba juyowan da za ta yi
ne ta yi arba da shi yana tsaye, da gudu ta nufeshi ta rumgumeshi tana fashewa da wani irin
kuka, sosai ta yi kukan shi ma bai hanata ba domin ya lura tana cikin damuwa sai da ya ga
kukan ba mai ƙare wa ba ne ya shiga rarrashinta washegari ma yana fita gidan ya juye mata
zuwa wani sansanin daji na daban. Kwana biyar tana cikin firgici da tashin hankali wanda ta
rasa da wane yanayin za ta yi masa magana ya fahimce ta. Gabaɗaya ta rame ta susuce tare
da fita a hayyacinta. Bata iya taɓuka komai yanzu hatta abinci ba ta iya girka musu sai dai ya
sayo musu. Shi kanshi yanayin da take ciki na damunsa amma da zaran ya tambaye ta sai dai
ta ce bakomai so biyu yana kaita gidan Hajiya Umma a nashi tunanin ko zama ita ɗaya ne ke
sanyata cikin damuwa amma duk da hakan ba ta dawo yadda take da ba. Yana cikin shirin
tafiya aiki ta kalleshi tare da faɗin “Daddy ina so inga Maman mu” Jakar shi ya ɗauka tare da
faɗin “Bari in na dawo anjima sai mu je tare” Sunkuyar da kai kawai ta yi domin ta san muddin
suka tafi tare ba wani daɗewa zai barta ta yi ba.
Ya fito daga Ofishin sa kenan sakataren shi ya kira shi yana sanar da shi baƙin su sun iso dole
ya shi ne ya nufi filin jirgi domin tarban su, da ga nan ya je ya kama musu masauki a tsattsaye
ma suka gaisa domin gabaɗaya tunaninsa ya yi gida ganin har bakwai saura yau bai je gida ba,
ga shi ita ɗaya ce a gidan. Da hanzari ya fito yana kallon wayarshi da ke haske alamar shigowar
saƙo kasancewar ya saka wayar a silent nan ya ga miss call haɗe da saƙonninta tana tambayar
lafiyarshi da abin da ya hanashi dawowa gida. Mayar da wayar yai cikin aljuhunshi tare da buɗe
motar yana ƙoƙarin shiga. Da ga bayan shi ya ji an dafa kafaɗar shi da mamaki ya juyo yana
tunanin waye haka? Nan ya yi arba da ita wani dogon tsaki ya ja tare da sake tamke fuska cikin
ɓacin rai ya cire hannunta a jikinshi yana binta da ƙasƙantaccen kallo ganin irin shigar da ke
jikinta wanda gabaɗaya ya bayyana komai na jikinta kasancewar kayan ɗamammu da su.
“Alhaji na...” Wani irin zubewa ta yi a jikinshi gabaɗaya tare da fashewa da wani mugun dariya
da ga haka idanunta ya fara rufewa Emanuel ne ya ƙara so wurin da sauri tare da ɗaukar ta
yana faɗin “Yi haƙuri Alhaji ta yi sama sosai” Saboda tsananin takaicin kwanciyar da ta yi cikin
jikinsa kasa magana ya yi. Haka ya ja motar yana me jin ƙyanƙyamin jikin nasa har ya ƙara sa
gida.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa da sauri ta taho ta amshi jakar da ke hannunsa “Barka da
dawowa Amnoor” Lumshe mata ido ya yi tare da jinginuwa da ƙofar shi ma yana sauke
numfashi “Ki yi haƙuri yau ban dawo da wuri ba” Ɗan murmushi kawai ta yi tare da riƙo
hannunshi zuwa d'akinshi. Sai da ya yi wanka tare da yin sallah sannan ta kawo mishi abinci
tare da magani, kaɗan ya ci sannan ya sha maganin, kwashe kayan ta yi ta mayar da su kitchen
kana ta nufi ɗakinta, wanka ta yi ta fito ɗaure da zani ba ta san yana ɗakin ba sai da ta ji ya yi
gyaran murya sannan ta waigo tana mamakin zuwan nasa kasancewar yanzu bai fiya shigowa
da dare ba. Karɓan man da za ta shafa ya yi tare da jan zanin nata gefe kawa kawai ya ji yana
son rage ma kanshi zafi da ita bayan tsawon lokaci da suka ɗauka ba tare da wani abu ya shiga
tsakaninsu ba, duk wanan sheɗaniyar yarinyar ce ta saka shi cikin wannan halin (Fiddoh) haka
ya fara bin santala-santalan cinyoyinta yana shafa mata mai cikin wani irin yanayi kasa daurewa
ta yi da sauri ta riƙe hannunsa tare da girgiza mishi kai. Wani irin kallo yai mata sannan ya
kwance zanin gabaɗaya ya jawota cikin jikinshi sannan ya kashe hasken ɗakin, nan ya dinga
birkita mata lissafi wanda har kuka sai da ta yi mishi domin ya kunnota da ga ƙarshe sai ya kasa
yi mata komai takaicin wannan abin ya sa ta juya mishi baya, shi kuwa a rayuwa
07, December 2025
Habib Musa abdulkadir
We love ur book