Showing 42001 words to 45000 words out of 70225 words

Chapter 15 - Amnoor Complete Romantic Hausa Novels by Aysha JB.pdf

ya tsani irin
haka wai su kwana gado ɗaya kuma mace ta juya mishi baya.

Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya zaman lafiya ya yi ƙaranci a tsakaninsu tamkar masu
almatsutsai yanzu-yanzu za su yi magana cikin daɗin rai ba jimawa kuma za su fara faɗa.
Wannan abin shi ya sake ƙara mata damuwa sosai, yau yana fita ta haɗa kayan da za ta
buƙata ita ma ta nufo gida lokacin da ta zo Maman su na aikin turarenta ta yi sallama da ’yar
siririyar muryanta tare da zama jikin Maman Nafisa tana sauke ajiyan zuciya nan da nan ta ji
wani nutsuwa ya zo mata take ta fara barci shafa kanta Maman Nafisa ta yi tana ƙare mata kallo
ganin yadda ta sukurkuce ta lalace duk ta rame, gyara mata kwanciya ta yi sannan ita ma ta ci
gaba da aikinta sai zuwa ƙarfe biyun rana ta farka za ta yi magana Maman Nafisa ta ce “Yi
addu'a tukun na” Lumshe ido ta yi tare da karanto addu'a. Ruwan rubutun da ta sa Zaliha ta
amso mata wurin malamin makarantar su tun kwanaki ta ɗibo tare da miƙa mata. “Ki sha da
Bisimillah” Haka kuwa aka yi tana gama sha ta dire kofin tana sauke ajiyan zuciya.

“Me ke faruwa?” Maman su ta yi mata tambayar tare da ƙura mata ido, sunkuyar da kai Amnoor
ta yi domin ba za ta iya kallon maman tasu ba bare har ta faɗa mata abin da ke faruwa ba.
Ganin yadda take matse 'yan yatsun hannunta ya sa Maman fahimtar ba faɗa mata za ta yi ba,
daman ta san halin kayanta da ƙyar ta iya faɗar damuwarta. Cikin jin haushin halayyarta
Maman su ta ce “Ki tashi ko koma ɗakin ki...” A sukwane ta d'ago idanunta cike da hawaye tana

faɗin “Dan Allah..” Dakatar da ita Maman Nafisa ta yi da faɗin “Ba za ki zo ki tasa ni a ga ba
kina min hawaye bayan na tambaye ki damuwarki kin ƙi faɗa min ba, gwara tun wuri ki tattara ki
tafi, shin mijin naki ya san kin fito?” Girgiza mata kai ta yi alamar a'a shigowar Zaliha ya sa ta
yin shuru tare da miƙewa “Wayyo Aunty Noor ke ce a gidan mu yau? Dan Allah Aunty ba ni
wayarki in yi abu” Miƙa mata wayar ta yi tare da shegewa ƙuryar ɗaki tana kuka. Ita dai ba za ta
koma gidan Alhj Aminu ba, gwara ta zauna gidan su wurin Maman Nafisa kawai.

A gajiya ya fito daga motar domin yau gabaɗaya bai huta ba saboda ayyuka da suka mishi
yawa, da sallama ya turo ƙofar falon yana me kiran sunanta domin ya saba da in ya dawo tana
zuwa karɓan jakarshi ko kuma ta rumgumeshi tana mishi oyoyo yau kuma sai ya ji shuru
ɗakinta ya nufa yana tunanin ko dai sallah take nan ma bai ganta ba toilte ɗin ma shuru gaban
madubin ya ga takardan da ta rubuta mishi saƙo. “Ka yi haƙuri na fita ba tare da izinin ka ba,
Daddy na gaji ba zan iya ci gaba da zama da kai a haka ba. Rayuwa haka muna matsayin
ma'aurata sam babu armashi a lokacin da ban saba ba kai ka sabar min, tun ba na jin daɗi har
ka koya min jin daɗin, tun ina gajiyawa har na zama gwana. Ta yaya zan zauna bayan ina jin
mararin abun? Akwai cutarwa sosai, na yi iya haƙurin da zan yi dan Allah ka fahimta. Ina mai
roƙon ka da ka sawwaƙe min kawai dan ba zan iya zama kullum muna faɗa da junan mu ba”
Lumshe ido yai yana jin wani zafi a ranshi da ƙyar ya iya yin wanka tare da sallah sannan ya
nufo gidan na su.

“Kin wani kwaso jiki ke kin dawo gida to uwar me kika zo yi? Kin san dai halin baban mu wallahi
in ya fara miki tijara ko ƙala ban cewa, haka kawai kin bar gidan mijinki kin zo kin tasa mutane a
gaba kina cika mana kunne, an tambaye ki me ye matsar kin ƙyale mutane to me za a miki?”
Cikin faɗa Fiddoh take mata magana domin ta ɓata mata rai, dan tana kwance tana jin maganar
da Maman Nafisa ke mata. Kallon Fiddoh Amnoor ta yi hawaye na ci gaba da tsiyayo mata “Shi
kenan duk cikin ku babu me lallashi na...” Saukowa Firdausi ta yi daga saman gadon tana faɗin
“Lallashi? Ke yarinya ce da za a lallasheki?” Da ga haka ta ja dogon tsaki tare da shigewa bayi
tana mita ita ta hanata barci. Tana fitowa ta karɓi wayar Maman su ta kira Amrah dan ba zai
yuwu Amnoor ta zauna musu a gida bayan kuma da aurenta ba. “Ki zo ki tattara ƙawarki ta
koma ɗakin mijinta tun ɗazu ta zo ta hana mutane saƙat da kukan banza”

Ajiye wayar ta yi tana kallon Nuriyya duk da zuciyarta cike yake da tausayin 'yar'uwartata amma
ba ta ji za ta lallasheta bayan ba ta faɗa musu damuwarta ba. Suna zaune sai ga Amrah ta yi
sallama ta shigo gaisawa suka yi da Maman su sannan ta nufi wurin Amnoor “Aminiyar me ke
faruwa ne?” Ta faɗa tare da kwantar da kan Amnoor ɗin saman kafad'arta. “Amrah sun kasa
fahimtar halin da nake ciki..” Da sauri Amrah ta ce “Haba Noor, ta yaya za su fahimta bayan ba
ki musu bayani ba. Daddyn nawa ne ya miki wani abun bayan rashin jituwan da kika faɗa min
kwanaki?”
“Amrah ni na gaji ne wallahi ba zan iya zama..”
Zaro ido Amrah ta yi tana faɗin “Innalillahi Noor! Me ya yi zafi haka? Da bakin ki kike cewa kin
gaji da zama da Daddy me ya miki?” Kallon Amrah ta yi sosai a hankali cikin rawar murya ta
fara sanar da ita halin da take ciki tun da ga kan rashin lafiyarshi da faɗar da suke yi har
gane-ganen da take yi. Duk hirar da suke Maman Nafisa tana zaune tana jinsu, ita daman ta

san Hajiya Laraba ba za ta taɓa ƙyale Nuriyya da mijinta ba, ta yi shuru ne kawai lokacin da
Zaliha ta zo take yabon halayyarta ita ta san wace ce Laraba ta san baƙin kishinta ashe dai
zagon ƙasa take yi wa Nuriyya, aikuwa ba za ta ƙyale a kassara mata ɗiya ba.
Ɗakinta ta shige ta barsu suna ci gaba da tattaunawa, Amrah ta ce “Ikon Allah! Wannan lamari
da ɗaure kai yake na ma rasa abin da ma zance wallahi” Zaliha ce ta miƙo mata wayarta da ake
kira tun ɗazu. “Aunty Noor ana kira” Kallon Amrah ta yi tare da mata nuni da wayar “Ki ɗauka
mana” Girgiza mata kai kawai na yi domin ban san abin da zance mishi ba. Ƙarshe ma kashe
wayar na yi gabaɗaya ina ji kamar ban kyauta mishi ba, na san yana can cikin damuwa amma
haka za mu yi haƙuri da juna. “Ki yi haƙuri Noor, zai fi kyau ki koma ɗakin ki, kin ga azumi na
gabatowa bai kamata ki bar shi shi kaɗai a gida ba..”

“Ai ba ni kaɗai ba ce, Amrah zama na da Amnoor babu wani armashi, ko gado ɗaya ba mu
kwana bare a kai ga batun biyan buƙata, babu fa abin da yake tsinana min kullum sai dai ya yi
ta laguda ni yana ɗaga min hankali da ga ƙarshe ya barni da ciwon mara ina juyi ni ɗaya...”

Cike da kunyar zancen nata Amrah ta rufe bakinta tana faɗin “Tabɗi! Amnoor daman za ki iya
wannan maganar? Lallai an kai ki maƙura tun da har kika iya faɗar wannan maganar. Ni wallahi
har kunya ya kamani” Girgiza kai kawai Na yi domin ni ma sai da na yi maganar na dawo ina jin
kunyarta.
“Za mu canza Please a dai yi haƙuri kamar yadda aka fara a ƙarasa bai kamata Daddy ya yi
azumi shi ɗaya babu iyali ba, kin ga tun da Mommy ba ta nan ya kamata ke ki zauna dan ita
daman tun asali ba zama take ba, tana harkan business ɗinta”


Shi kuwa ganin ba ta ɗauki kiran ba ne ya sa shi juyawa ya nufi gidan Hajiya Umma yana sanar
da ita abin da ya faru. Shuru kawai ta yi masa domin ba ta san me za ta ce masa ba, saboda
takaici wai ya zo ya zauna yana faɗa mata matarsa ta yi yaji to uwar me za ta mishi?.

A ɓangaren Hajiya Laraba kuwa murmushi kawai ta yi tana sauraron maganar da Maman
Amrah take faɗa mata. “Wallahi ki ji tsoron Allah ki bar 'yar mutane ta yi zaman aure tun da ke
ba auren ba ne a gabanki na rantse ko kaffara ba zan yi ba da sa hannun ki a duk matsalolin da
Nuriyya take fuskanta tsakaninta da Alhaji Aminu dan na san halin baƙin kishin ki, duk wani
dariya da rashin damuwa da kike nunawa duk a fuska ne bai kai zuci ba! Koma dai mene ne
akwai Allah kuma gaskiya nake faɗa miki ki ajiye duk wani business ki dawo dan watan ibada
za mu shiga” Dariya kawai ta yi tare da faɗin “Allahu akbar! Sannu fa na gode” Da ga haka ta
kashe wayar tana jan tsaki.
“Ai ba ta ga komai ba ma, ba de ta ce mijina ba? Sai na haukata 'yar banza!” Da ga haka ta
ɗaga kiran Hisham wanda yake damunta da maganar dawowarsa nan ta sauke mishi kwando
bala'i kafin ta kira Suhaima tana tambayar lafiyarta.

Kwana biyu kenan da dawowata gidan mu Fiddoh kuwa ta saka ni a ga ba da bak'ar magana ita
dai haushin dawowata take ji takan ce min “Ki ba ki ji daɗi ba ma Allah ya ba ki miji me ƙaunar

ki yana ririta ki, ni ga shi neman Alhaji nake yana wulaƙantani sai ce min yake yana da matar da
ta fini komai” Ire-iren maganar da take faɗa kenan wanda sai dai in jita amma ban ce mata
komai, ina mata addu'ar idan shi alkairi ne a gareta Allah ya haɗa su domin ba na son rayuwar
da take yanzun abin nata ma ya daɗe lalacewa dan shigar nuna tsiraici take tamkar ba ɗiyar
musulma ba, in na yi magana ƙarshe sai dai faɗa ya biyo baya. Maman mu kuwa ƙala ba ta
cewa dan ta yi magana ta yi nasiha ta gaji sarautar Allah kawai zuba ma ido. Zaliha na kalla ina
tambayarta baban mu domin tun zuwa ta ban ji motsinsa sa.

“Tab! Ai tun da Daddy ya ba shi jari yanzu linƙafa ta ci gaba. Yana can yana harkan caca be ma
zaman gari sai dai ya kira mamar mu a waya kawai”

“Ya Subahanallah! Maimakon ya kama wani sana'ar da za ta amfane mu shi ne sai caca?” Na
faɗa ina kallon maman mu da take miƙo min ruwan rubutu. “Karɓi ki sha da Bisimillah in kin
gama ki shiga ba yi ki yi wanka na ajiye miki ruwan maganin” Da ga haka ta miƙe ta fita.

Haka Maman mu ta dinga cusa min wasu magunguna na tsarin jiki tare da na karya sihiri na
sha da wanka, da kuma hayaƙi, sannan ta shiga min gyara na musamman kwana na goma
muka ɗauki azumi ranar farko da aka fara azumi Daddy ya aiko mana da kayayyakin buƙata.
ranar da muka kai azumi biyar Abban Amrah ya zo gidan mu shi da Hajiya Umma, ban san abin
da suka tattauna shi da Maman mu ba kasancewar har yanzu baban mu bai dawo ba, na ga dai
ta shigo ta ce min in shirya in koma gidan Daddy. Wani irin fad'uwar na ji da sauri na kalleta zan
yi magana ta ce “Ki yi haƙuri watarana komai zai wuce ki riƙe ibadarki ki dinga zama da alaula
ko da ba ki da tsarki Allah yana tare da ke kuma shi zai kare min ke, ga wannan ruwan rubutun
ki yi ƙoƙari ya sha in Allah ya yarda magana rashin jituwa za ta kau, maganar rashin kwana wuri
ɗaya duk zai wuce, zai kasance tare da ke. Sannan ki kula da tsaftar jikinki, kwalliya, sanya
kayan da zai ja hankalin shi, ba wai kullum za ki dinga yawo cikin atamfa da leshi ba ne, akwai
kayayyaki na zamani wanda za ki dinga sakawa mijinki a gida ki lura inda ya fi so, nan wurin shi
za ki dinga gyarawa imma tafiyarki ne, ko magana, ko wani abin da ya danganci jikin ki ne, duk
ki san yadda za ki jawo hankalin shi” Duk wannan maganar da take idanunta na gefe ko kallon
inda nake ba ta yi. “Allahu akbar! Gaskiya mamar mu kin burge ni anan, sai yanzun kika samu
damar faɗa mata abubuwan da suka dace ta yi a matsayinta na matar aure, ina fatan ni ma
randa nawa ya tashi za a faɗa min fiye ma da haka...” Girgiza kai Maman Nafisa ta yi tare da
faɗin “Ubangiji Ya shiryar da ke”

Zaliha ce ta fito min da kayana a wurin mota na tadda Hajiya Umma durƙusawa na yi ina
gaisheta domin ba ƙaramin girmamata nake ba kasancewar tana sona ba ta taɓa nuna min
wani hali na daban ba. “Taso-taso ɗiyar kirki. Allah Ya shiga lamarin ki, ki ƙara haƙuri da
Aminulllah kuma zan ja mishi kunne kar ya yarda ya sake miki abin da zai sa ki dawo gida,
kodayake hakan ma ya yi min tun da ya ɗanɗana zaman gwauranci mata biyu duka babu ko
ɗaya. Yanzu dai na san za a kula da shi” Ɗan murmushi na yi ina sunkuyar da kaina na fahimci
tana son cewa na kular mata da shi ne duk da ba ta fito ta faɗa min ba. Gidanta muka fara zuwa
a can muka taho tare da shi ashe yana can yana jiran zuwan mu. Tana fita a motar ya shigo
tare da kama hannuwana yana sauke ajiyan zuciya, kissing hannuwana ya yi yana faɗin “Ki yi

haƙuri Amnoor...” Gyaran murya Abba ya yi tare da faɗin “Ai ka bari mu ƙarasa gida wannan
rawar jikin duk na mene ne?” Hararan shi Alh. Aminu ya yi yana faɗin “Amma fa kai ɗan iska ne
Sa’id , ban son sa ido fa”

“Au haba? Abin da za a saka min da shi kenan bayan na yo maka biko ko?” Haka suka dinga
hira har kuma ƙaraso gida. Ciki na shiga na barsu suna tattaunawa, gidan ya yi fes ga dukkan
alamu ya sa an gyara ne, haka ma ɗaki na shi ma a gyare yake har da ƙarin wasu abubuwan
ma. Ba yi na shiga na yi alaula tare da gabatar da sallar Asham. ina cikin sallah ya kwaso kayan
da na bari a mota ya shigo min da su, zama ya yi har na sallame tare muka shafa addu'ar tare
da faɗin “Allahumma Amin Allah Ya sa ni dai an haƙura” Ƙala ban ce mishi ba haka na tashi na
gyara kayayyakin sannan na ce “Wannan maganinka ne, maman mu ta ce a ba ka”

“To ina godiya”

Kwanciya na yi na barshi zaune. Shi kuwa kallonta kawai yake ganin yadda take wani basarwa
maganin ya sha sannan ya nufi ɗakin shi ya shirya ya zo ya kwanta kusa da ita. Kasa haƙuri ya
yi ya jawota jikinshi yana sauke ajiyan zuciya a haka suka yi barci ƙarfe uku ta farka tare da
zare jikinta a nashi ta haɗa musu abin da za su yi sahoor. Ba ta wani sake mishi haka suka ci
gaba da zama har aka kai azumi ashirin gabaɗaya ya yi wani yanayi ba ya jin daɗin sauyawan
da ta yi, ko 'yar hirar ba ta ba shi fuskar da za su yi.

Kasancewar yanzun bayan sallar la'asar yake dawowa gida ne ya sa wani lokaci sai dai ya
zauna yana kallon yanda take kai-komo daga kichin zuwa falo tana shirya musu abin buɗa baki.
Yau tun da ya tashi yake jin shi a takura domin ko da asuba ya so ya lallaɓata ko zai rage wani
abun amma ganin irin yadda take ɗauke mishi kai sai ya ƙyaleta kawai. Tana gama shirya komai
ta nufi toilte dan yin wanka ganin shida har ya yi yau ba ta kammala aiki da wuri ba.

Miƙewa ya yi tare da binta ɗakin dan yana jin in bai yi wani abun ba akwai matsala. Daidai ta fito
ɗaure da zani kanta ta yafa towel tana gogewa ba ta damu ba a tunaninta wani abun ya zo
ɗauka sai da ta ga ya ƙaraso gareta ya yatsa yana binta da wani kallo daidai ana kiran sallah
“Wani abu kake buƙata?” Ta faɗa tana ƙoƙarin jawo himar ɗinta da ke rataye gefen mirror sai jin
hannunshi ta yi saman nata da sauri ta juyo za ta yi magana ya yi saurin kai bakin shi saman
nata runtsa ido ta yi sosai jikinta na ɗaukar ƙyarma. Sake tallafo fuskarta ya yi sosai yana ci
gaba da tsotsar lips ɗinta cikin wani irin yanayi yana sauke numfashi. Jan zanin ya yi ƙasa tare
da rumgumota gabaɗaya yana jin tudun ƙirjinta kan nashi yanda take motsi nonuwanta na sake
gugun ƙirjinshi abun ba ƙaramin sake gigitashi yai ba. Gyarata ya yi tare da kai hannuwanshi
yana shafa nonuwnata yarrr taji tsigan jikinta ya miƙe cikin wani irin kasala ta kwace bakinta
tare da sauke numfashi tana faɗin “Daddy an kira sallah...” Jin kanshi tsakiyar nonuwanta ya sa
ta yin shuru tana sauke ajiyan zuciya dan wani irin tsotar nipples ɗinta ya shiga yi yana sauke
wani gwauron numfashi gabaɗaya notikan kanshi ya kwance miƙewa yai ya cire kayan jikinshi
tare da yi mata rumfa nan ya haɗe bakinsu a gefe guda yana ni man hanyar da zai juye ruwan
da ke tare a mararshi kuka ta fashe da shi tana faɗin. “Dan Allah mana! Wallahi ba zan iya
komai ba a yanzu...” Kanshi ya

07, December 2025
Habib Musa abdulkadir

We love ur book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login