Showing 1 words to 3000 words out of 35201 words
*THE WORLD MAN*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 0️⃣1️⃣➡️0️⃣2️⃣
Tafiya sukeyi cikin nutsuwa suna hira su biyu Hauwa'u ta kalli Inteesar tare da
cewa"Inteesar gaskiya ina ganin musamu wani gurin mu fake saboda naga hadari na niyyar
tasowa ke sarkin mura".
"toh yanzu a ina zamu fake anan gurin".
"kinga wata rumfa can muje muɗan fake in ruwan ya ɗauke semu wuce gida".
"toh".
nan suka ƙarasa rumfar wani me shayi suka zauna zamansu keda wuya ruwan sama ya kece
aka shiga ruwa kamar da bakin kwarya.
Andaɗe ana ruwan sannan ya ɗauke suka tashi suka cigaba da tafiya sunyi nisa sukaga wasu
motoci ƙirar Land cruser baƙaƙe se ta tsakiyar data ƙasance roice-roice fara tas me baƙin tintac
motar itace ta cikon ta bakwai wato dai ma'ana a tsakiya danno kai sukayi sunzo wuce daidai
su Inteesar bazato sukaji ruwan taɓo da kwatami ya watsomusu a jikinsu sakamakon motar
fallatsamusu da tayi cikin sauri da zafin zuciya Inteesar ta wawuri wani dutse dake kusa dasu
ta jefi ɗaya daga cikin motar dutsen be tsaya akan kowacce motaba se a glass ɗin farar motar
nan ta tsakiya tass kakejin ƙarar fashewar glass ɗin a razane Hauwah ta kalli Inteesar tare da
kallon motocin tace"nashiga uku Inteesar kinsanko motar wa kika fasawa glass kuwa?".
cikin masifa wadda ita kanta batasan tanada itaba tace"ko motar waye ina ruwana meyasa su
masu kuɗi basusan darajar ɗan Adam ko cemusu akayi muba mutane bane ke bakiga abinda
sukayimana ba ruwan kwatamifa suka fallatsamana kina kallo kuma ko niyyar tsayawa basu da
ita amma ke saboda rashin kishin kai yasa ki cemun wai nasan motarwa na fasawa glass ina
ruwana ko wayemana ai tare suke".
Jin ƙarar glass yasashi ɗagowa daga karatun daily thrust ɗin da yikeyi tare da zubawa gaban
motar da yike ido wow na furta sakamakon ganin haɗaɗen matashin guy ɗin yagaji da haɗuwa
komai nashi abun burgewane saurin fita drivern yayi bejimaba ya dawo cikin girmamawa
yace"Oga wasu yarane kan amfallatsamusu ruwan taɓo shine ɗaya daga cikinsu tayi jifan
amma gashi can su Muhd sun zagayeta".
cikin muryarsa da kamar ammasa dole yace"buɗemun mota".
"angama ranka shidaɗe".
nan drivern ya buɗemasa a hankali ya zura ƙafarsa waje yafita cikin takun zaratan maza masuji
da class yaƙarasa gurin wanda hakan yayi daidai da ɗaga hannun Muh'd ze wankawa Inteesar
mari.
a ɗan daƙile NAMIJIN DUNIYA yace" Dakata Muh'd".
yaƙarasa maganarsa tamkar wanda aka tilastawa
Wani ƙasƙantaccen kallo me cike da zallan ƙyama da wulaƙanci yake jifanta da shi Cikin lion
voice ɗinsa yace" ke Waye Ubanki da me kike gadara da har zaki fasamin glass ɗin motana
ubanki waye a ƙasarnan".
Lokaci ɗaya Idanunta suka rine saboda tsananin ɓacin rai saboda dukda suke talakawa
batason a wulaƙantamata iyaye a zuciye tace "Da Uban da kake gadara dashi nake gadara
mutumce kamarka".
Azuciye ya ɗaga hannunsa da niyyar yarfa Mata mari yaji an riƙe Murmushi ta saki me cike da
takaici da ƙunan rai tace" daka mareni tabbas da ka aikata kuskure mafi muni atarihin Rayuwar
ka idan har ka yadda wannan wulaƙantaccen hannunka ya taɓa tsaftacciyar fuskata ta".
ta faɗa tare da yin wurgi da hannunsa Bata jira Jin abinda zeceba ta finciki Hannun Hauwa da
jikinta keta rawa suka bar wajen.
Hannu yasa ya hargitsa tulin sumar dake kansa kana ya furzar da iska me zafi daga bakinsa
wani irin tsuma jikinsa keyi yayinda jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu-ruɗu dasu tabbas tunda yake
babu wani mahalukin daya taɓa muzantashi irin wannan bagidajiyar yarinyar tamkar ze tashi
sama ya juya yashi ɗaya daga cikin motocin guard ɗinsa kafin yaƙarasa sun buɗemasa ƙofa
shiga yayi tare da lumshe sexy eyes ɗinsa yayi da sukayi ja dasu tare da furta "senayi
maganinki ko ƴar waye harni NAMIJIN DUNIYA za'ah samu wata dirty girl zata gaggayamun
magana nayi alƙawari sekinyi regreting ɗin abunda kikayi ".
yana wannan zancen zucin har suka isa wani tanƙamemen building dogo kallo ɗaya zakayiwa
haɗaɗɗen building ɗin ka fuskanci ma'aikatace saboda mutane daketa hada-hada a gurin suna
gama parker motocin Muh'd yace"Oga mun iso".
buɗe lumsassun idanunsa yayi da sukayi ja ya kalli handle ɗin ƙofa alamar a buɗemasa
buɗemasa Muh'd cikin takun ƙasaita haɗe da jiji dakai ya fito ma'aikatan dake gurinne gabaki
ɗayansu suka shiga gaidashi ba tare daya amsaba yashiga tafiya saboda tsananin ɓacin ran
da yike ciki be zame ko inaba se gurin elavatorn da shikaɗai yike hawa ya danna yashiga ya rife
a hawa na goma elavatorn ya tsaya tare da wangale ƙofar fita yayi tare da nufar wata
haɗaɗɗiyar ƙofa yashiga nan take wani haɗaɗɗen guri ya bayyana se wata mata datasha atarch
akanta yare-yare fuska tasha mai ga heavy make up data cika fuskarta dashi tana danna waya
ta bayyana tana ganinshi ta ƙara gyarawa cikin ƙissa tace"Oga sannu da zuwa".
be amsamataba hakan yasa tagane yau yana cikin ɓacin rai dan haka takama kanta tare
buɗemasa ƙofa yashiga tanƙamemen office ɗinsa daya gaji da haɗuwa kallo ɗaya zakayiwa
office ɗin kasancewa kuɗi sun zauna domin komai na more rayuwa akwaishi zama yayi
sakatariyarsa daketa kwarkwasa tashiga zayyanemasa shadul ɗin ranar jingina yayi da
kujerarsa tare da lumshe ido fita sakatariya Zeezee tayi bata jimaba se gata da wani haɗaɗɗen
cup a hannunta taƙarasa gaban table ɗin da Namijin duniya ke zaune tace"sir your copee is
ready".
ba tare daya buɗe idoba yayimata da nuni data bashi miƙamasa tayi ta juya a hankali yashiga
shan copee lokaci ɗaya yaji wata nutsuwa tazomasa ya aje cup ɗin tare da danna wayarsa
yayi dialing wata number bugu ɗaya aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren wancan yace"Oga ɗiyar
massenger ɗin Sir Ahmad ce".
wani murmushin gefan baki Abdallah Namijin duniya yayi ba tare da yayi maganaba ya kashe
wayar tare da tura text ya jingina da kujerarsa yana tinano irin abubuwan daya tanazarwa
Inteesar.
Ɓangaren Inteesar ko suna barin gurin Hauwa'uh ta kalli Inteesar tace"nifa tsoro nikeji saboda
nasan NAMIJIN DUNIYA baze taɓa barinkiba Inteesar meye danya watsamana ruwa".
"gaskiya duniya ba gaskiya wato shi bakiga abinda yayimanaba saboda yanada kuɗi seni nawa
kika gani ba wani tsoronsa da zanji ai mutum ne shina kamar kowa kodon kina sonsa shiyasa
kike kareshi".
"ba haka bane ƙawata kawaidai……".
saurin dakatar da ita Inteesar tayi tare da cewa"dame kikeso naji da baƙincikin gidanmu koko
dana irin wa'innan watsatstsun mutanen da basusan darajar ɗan Adam ba".
"ya haƙuri ƙawata".
suna wannan zancen suka iso gidansu shiga gida tayi itama ta shige gidansu.
Kamar kullum Inteesar nashiga gida ta tadda su Uwar Gwarama da maƙarrabanta a tsakar gida
tanata zuzzubs tsumi a roba wanda ta zabga uban flavour a ciki seka ɗauka tsumin arziƙine
bakinta ɗauke da sallama tashiga ba wanda ya amsamata Inteesar tayi gurin Innah Uwar
Gwarama ta duƙa cikin ladabi tace"Innah sannu da hutawa". taɓe baki Uwar Gwarama tayi tare da cigaba da zuba tsuminta ba tare dataji haushiba ta miƙe
tafara tafiya bazato taji su Ruƙayya da Bilki sun tintsire da dariya Bilki tace"dolema mutum ya
rasa mashinshini tunda an riga angama badakai a waje".
"kema dai banda abinki waye zeje ya auri ragowar ƙarti yanaji yana gani da kuɗinsa".
"wallahi sede a ƙare abinsu waje ba'ah wannan hotel ba'ah wancan yawon karuwanci da sunan
makaranta".
wata matashiyar yarinya ce tafito me tsananin kama da Inteesar tace"badai yayata ke yawon
karuwanciba sede waccan".
ta nuna Uwar Gwarama dake zuzzuba tsumi nanfa Uwar Gwarama tashiga bala'i tana
cewa"ƙarya akemata ai gaskiya suka faɗa inbanda ta tsaya yawon barikinta aida tini tasamu miji
saboda kowa yasan metake aikatawa mijin aurema ya gagareta ba'ah taɓa zuwa nan gidan da
koda sau ɗayane gurin Inteesar ba". "hakane Iyah muma nan gida zamu barta danba mesonta".
suna cikin wannan maganar Abbansu ya shigo fashewa Uwar Gwarama tayi da kuka tashiga
zayyanemasa ƙarya da gaskiya aiko yashiga jibgar Inteesar da Khadija seda yayi me isarshi
sannan ya kyalesu.
AFTER ONE DAY
Sanye Abbah yike da Uniform ɗin masu shara sega wani me irin kayansa gaisawa sukayi
yace"a'ah Ahmadu se yanzu kazo".
"a'ah na daɗe da zuwa ina bayane yanzu gashi inji Oga tin ɗazu yabayar yace abaka inkazo".
ansa Abbah yayi yana dubawa yaga takardar sallamace daga aikice sosai hankalinshi ya tashi
yana ƙoƙarin tafiya office ɗin Ahmad Malam Ahmadu ya dakatar dashi tare da cewa"yace kar
abarka ka shiga gurinsa".
sosai hankalin Abbah yaƙara tashi a wannan ranar duk yadda yaso dayaga Ahmad abu ya
faskara dole haka ya tafi gida.
Jiki ba kwari haka Abbah yashiga gida tare da zama kusa da Uwar Gwarama jiki a sanyaye
kallonshi Uwar Gwarama tayi tare da cewa"lafiya kashigo hannu na dukan cinya Malam".
"Ladidi an koreni a aiki".
Khadijat dake zagayowa dake zagayowa daka backyard ɗin gidan ce wani farinciki duk ya
lulluɓeta da murnarta ta shiga ɗakinsu tana ƴan waƙe-waƙenta ɗago kai Inteesar tayi daga
karatun Alqur'anin da takeyi tare da cewa"meyafaru naga kina murna".
"Abbah aka kora a gurin aikinsu".
"shine kuma kike murna".
"eyi ai gwarama da aka koresa daga aikin koba komai a dena banbantamu da ƴaƴan so shima
yaji yadda mukeji a zuciyarmu na abinda yikemana kamar ba ƴaƴansa ba duk ya tsanemu ni
wani lokacin har tinani nike anyako Abbah ne babanmu".
"Khadija meyasa kike irin wannan ne koba komai ai mahaifinmune kidena irin wannan inkuma
ba hakaba zamu ɓata".
"yi haƙuri Aunty".!!!!!!
Votes and Comments
Plz share fisabilillah
*Dan Allah a tayani share*
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_
*THE WORLD MAN*
(NAMIJIN DUNIYA)
*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
*BOOK 1*
*PAGES* 0️⃣3️⃣➡️0️⃣4️⃣
Jiki ba kwari Abbah yamiƙe yaɗauki buta ya zagaya be wani jimaba segashi yafito yaƙara
zama kusa da Uwar Gwarama baki buɗe Uwar Gwarama ke kallon Abbah sannan tace"amma
dai gaskiya Malam se yanzu na yarda da zancen Uwani na cewa zuciyarka a mace take murus
yo inbanda haka meyasa bazaka nace gurin wannan yaro arziƙinba kaji ba'asin abinda yasa ya
korekaba se kawai ka yayo jiki ka tawo gida to wlh Malam ahir ɗinka dan tashi zakayi ka koma
bazan riƙa ci dakai da wata ƙatuwa da ƴaƴanta ba akan wanne dalilin kamar kai nikeyiwa
neman imma zaka tashi kaje kaji meke faruwa kaje danni bama zan iya cida me ƙashin tsiyaba
wallahi wani yahana uwarsu yin sana'ah tace se ƴaƴanta sunyi karatun boko yanzu aisaci boko
a wuta aikaga ko maga abinda bokon nasu ze tsinanamasu dukda bamma yadda bokon
akeyiba ba babban bokoba wanda harka mutu baza'ah dena yimaka gori ba danni bame ɓatani
ƴaƴana basu jawomun abun kunyaba na wata su jawomun haka kurum a'ah ba dani za'ayi
wannan sa lallen kazarba atoh".
har Uwar Gwarama ta gama zazzage Abbah becemata ƙalaba yashafa sumar kansa tare da
cewa"to a temakeni da abinci konaji sanyi a zuciyata".
wani banzan kallo da Uwar Gwarama ta makawa Abbah da sauri ya miƙe tare da washe baki
yace"ya haƙuri bara inje ɗin".
"yadaifimaka ".
nan Abbah yafara tafiya daidai nan Wata matashiyar mata tayi sallama wadda bazata wuce
shekaru42 ba jin Uwar Gwarama bata ansamata ba haka Abbah shima ta nufi ɗakinta.
Tana shiga Khadijana yiwa Inteesar kitso ta saki da sauri ta rungumeta tare da cewa"sannu da
dawowa Ummah".
murmushi Umma tayi itama Inteesar ta rungumeta rungumesu tayi gabaki ɗayansu sannan
tace"ko ni Aishatu zaku karyani ku sakeni inzauna".
murmushi sukayi gabaki ɗayansu suka zauna cikin farinciki Inteesar tace"ya aka baro su
Halima".
"suna gaidaku".
cikin zumuɗi Khadija tace"Ummah kinsan wani abun farin ciki ko daya samemu kuwa".
cikin farim ciki Ummah tace"Auta meya samemu haka naga kina farin ciki haka".
kallonta Inteesar take da mamaki dan ita batasan meya samesu na farinciki da Khadija keta
farin ciki hakaba tana wannan tinanin ta tsinkayi muryar Khadija na cewa"Ummah anfa kori
Abbah daka gurin aikinsa kinji daɗin danaji kuwa ".
haɗe rai Ummah tayi tare da cewa"Khadija meke damunki ne haka da har kike farinciki dan an
kori mahaifinki daga aiki ashe duk huɗubar danakemuku ke bata shiga kunnenki Khadija
mahaifinku nefa kome yike yimana bekamata kiyi farin cikiba Khadija ".
"ai Ummah……".
saurin katseta Ummah tayi ta hanyar cewa"ya isheki haka a rayuwa duk wanda bashi da haƙuri
baze kai labari ba kuma komai na duniya ɗan haƙurine watarana se labari komai kaga yasamu
bawa da sanin Allah kuma komai muƙaddarine daga Allah ba'ah taɓa dawwama a abu ɗaya
shiyasa kullum bani da abinda zancemuku sede kuyi haƙuri kunji shi haƙuri riba garesa".
Ummah na cikin yimusu magana Uwar Gwarama ta buɗe ƙofa cikin masifa tace"ga kayana
can kije ki wanken".
ta wuce fuu Ummah takalli Inteesar tare da cewa"tashi kije kiyimata".
"toh".
zumɓurar baki Khadija tayi tare da cewa"saboda Allah Ummah duk gasu Bilki da Ruƙayya
bazasuyiba se Aunty saboda itace karkatacciyar kukar gidannan me daɗin hawa haba".
"au bakiji nasihar dana gama yumuku ba kenan ko saboda kinada kunnen ƙashi ko".
Inteesar ta fita tsakar gida Khadija ma tabita tashiga tayata cikin kayan harda nasu Bilki da
Ruƙayya hattana pant ɗinsu da suka gama period seda suka haɗa nan Inteesar tashiga
wankemusu.
Kwance yike akan sofa ya lumshe idanunsa kamar me bacci a hankali ya buɗe idanunsa da
suka yimasa nauyi yayi kana ganin fuskarsa zaka gane yanada damuwa tashi yayi ya nufi
tanƙamemeb wardrobe ɗinsa ya buɗe ya zari wasu haɗaɗɗun ƴan kanti yasaka ya feshe jikinsa
da turarukansa masu daɗi kanshi sannan ya ɗauki phones ɗinsa ya fita.
A hankali yike sakkowa daga stairs yana ɗaura gucci watch a hannunsa tunda ta ɗaura
idanunta akansa ko ƙiftawa batayi harya ƙarasa sakkowa cikin takunsa kamar yana tausayin
ƙasa yaƙarasa sauka ya nufi falon Haneefa ce zaune ita kaɗai cikin wasu english wears riga da
wando rigar kusan rabin ƙirjinta a waje fuska tasha heavy make-up kamar ga atarch yare-yare
da murmushi tace"morning sweetheart".
Abdallah(Namijin duniya) kallo ɗaya yayimata ya ɗauke kansa gefe yaƙara haɗe rai kamar
wanda aka aikomasa da mutuwa yace"lfy what of you".
"lafiya ƙlau".
ya miƙe ya nufi ƙofa ɓangaren granny ɗinsa ya nufa yana shiga ya tadda Abbih ɗinsa da
Mummy zaune ƙarasawa yayi bakinsa ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa taɓe baki Innah tayi tare da
cewa"yaudai ban dafa abincina dakaiba dunkum dangin tsaka atoh inma zakaci abinci da
Mamanka tayi kaci dan bazan bakaba". dariya Mummy tayi tare da cewa"rabu da ita Son ai se inbaka nawa".
murmushin gefan baki yayi ya zauna tare da cewa"ina kwananku ".
"lafiya ƙlau Son yaka tashi".
"lafiya ƙlau Abbih".
"masha Allah".
miƙewa Abbih yayi tare da cewa"Ammi ni zan wuce inada wani meeting".
"to Allah ya tsare".
"Ameen ya Allah Son seka fito".
"toh Abbih".
nanya fita Mummy ta miƙe tace"Ammi se anjima Son seka dawo ".
"toh"
yafaɗa a daƙile Mummy washe baki Ammi tayi tare da cewa"toh Fatimah Allah yayimiki
albarka".
"Ameen".
nanta tafi murmushi Abdallah yayi ganin Ammi ta kauda kanta gefe yaƙarasa gurinta tare da
cewa"Ammi an tashi lafiya".
"da ban kwanaba ka ganni zaune kamar duniya ne".
murmushi yayi yace"Ammi tuba nike ayi haƙuri".
"aini tunda kaƙi jin maganata nabarka da halinka ace yaro kamar wanda akayiwa mugun abu
bakason yin aure anjuma nan zan shirya inje gidan aminiyata inma wani abun akayimaka naji
dan bazan bari a cuci jikana kwalli ɗaya ba a duniya atoh bara in zubomaka abinci inshirya ku
ajeni gidan Ta Annabi ina dalili ina ɗan mafari a sabautamun jikana ga abokinka har zeyi aure
nanda sati biyu amma kai shiru akeji ".
bece komaiba a ta wuce a zuciyarsa yace"hmm Ammi bazaki gane abinda ke damuna ba a
duniya ba macen da zata yarda ta aureni matsawar tasan meke damuna".
yana wannan zancen Ammi ta fito ta ajemasa plate ɗin irish kaɗan yaci ya miƙe tare da kallon
agogon hannunsa yace"Ammi sena dawo bara se su Muhd su kaiki ni kuma na wuce inada
meeting".
"toh seka dawo".
nanya fice ta taɓe baki tare da cewa"imma wanine yasamun hannu agun jikana zanji koma
meye".
nanta tafi ɗaki ta shirya ta fita suka tafi.
Yana fita ya shiga mota suka fara tafiya har sun ɗauki hanyar gurin aikinsu ba tare daya buɗe
idoba yace"Hospital zamu".
"toh Oga".
nan suka canza akalar motar suka nufi wani katafaren asibiti suna isa ya zagaya ya buɗemasa
nanya fita cikin takunsa na isa harya isa ciki ya nufi office ɗin doctor Muhseen murya can ƙasa
yayi sallama ya shiga murmushi ɗauke a fuskar doctor Muhseen yace"sannu da shigowa".
"yauwa".
Namijin duniya yafaɗa tare da zama kan kujerar dake kusa table ɗin Muhseen ya miƙamasa
hannu suka gaisa bayan sun gaisa Doctor Muhseen ya ɗakko wata farar leda tare da miƙawa
Namijin duniya ya ansa cikeda kulawa Doctor Muhseen yace"bara inɗakko maka water seka
sha". "ohk".
nanya ɗakko mishi ya buɗe drugs ya buɗe bottle yasha sannan ya miƙe yace"se anjuma".
nan ya fita be jira amsar doctor Muhseen ba wani irin tausayin Namijin duniya ne yakama doctor
Muhseen a hankali ya furta "Allah na sane dakai Abdallah insha Allahu Allah ze baka lafiya
kamar ko wanne mutum".
nanya nutsatsa yana tinanin Allah yabawa Namijin duniya komai amma Allah ya rageshi da
wata babbar ƙaddara megirma yace"insha Allahu Abdallah zaka cinye wannan jarabawar".
jiki a sanyaye ya cigaba da cike files ɗin dake gabansa.
5:00pm
Zaune Abdallah yike yana danna phone ɗinsa kallo ɗaya zakayimasa kasan tinani kawai yikeyi
a guest house ɗinsa Ahmad ya buɗe ƙofar falo