Showing 9001 words to 12000 words out of 46523 words

Chapter 4 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf


"Na gaji da jiran zuwanka na sako maka matarka Siddiqah a jirgi, ta taho, so nake ku rayu
tare rayuwar sunnah a gidanka da duk inda zaka shiga, daga nan har karewar numfashi.
Tunda naga alama baka san zuru ba, da irin sacrifice dinda iyayenta masu dattaku suka yi
mana, suka baka aurenta ba tareda sun ko gan ka ba".
Sai Prince ya tsaya sakatoto! Da waya a hannu, jin Dade ya kashe wayarsa ba tareda ya
bashi damar kara yi masa tambaya ko neman karin bayani ba.
Ya koma ya zauna a hankali bisa kujerar da ya mike daga kai lokacin da zai amsa kiran
mahaifinsa.
Prince bayan gama sauraron Dade sai ya kasa cigaba da aikin da yake yi, zufa sai yanko
masa take yi daga goshi, ya koma ya zauna yayi tagumi da hannu bibbiyu, yana ji kamar yayi
ihu. Domin wannan shine (hukunci mafi tsanani da tsauri da iyayensa suka taba yi masa).
To amma ya kamata yaga laifinsu? Sun bi duk ta hanyar data dace don ya kawo mata da
kansa, don yayi aure ya cika mutum a lokacin da ya dace, sun yi fadan sunyi lallashin, sunyi
barazanar aura masa guda hudu daga danginsa, Nenne har kuka tayi a gabansa, akan
zarge-zarge marassa dadi da ake masa, Emir ne kawai yake yi masa uzuri, har kauracewa
Baffanninsa yayi akan suna so yayi aure don radin kansa da zabin kansa, ya cika tarbiyyar
gidansu abu ya gagara, don haka kada yaga laifin kowa a kan zabin da suka yi masa yanzu
wanda shine hukunci na karshe da ya biyo baya, na biyo shi da yarinyar har inda yake finally.
Kamata yayi ya ga laifin kansa, bana yarinya ba, wadda aka katsewa rayuwar kuruciya itama
aka turo ta aure inda bata da kowa ba da son ranta ba.
Ko kusa bai kamata yaga laifin iyayensa ba. Sun bi duk hanyar daya kamata su bi donbashi
hakkinsa a addinance da al'adance.
Yarinya ita akafi cuta ma, kasancewar da kuruciyarta an hadata da tsohon tuzuru kamar sa.
Nenne ta gaya masa maganar auren tunda jimawa amma ya gudu ba tareda ya damu ba, in
zai iya tunawa daga lokacin bata kara yi masa zancen yarinyar ba, ta koma normal rayuwarta
ita da shi. Ashe ba hakura suka yi ba dungu suka yi masa.
Yau dai ga matar nan an biyo shi da ita hara Ajantina, ba kwabonsa babu darinsa, a wurinsu
karshen gata sun gama yi masa, a wurinsa karshen katsalandan da takurawa an yi masa, in ba
Dade din ba wa ya isa yayi masa wannan karan tsayen a rayuwa?
Ko Akannis tara bazasu fara ba. Kai ko Emir ba zai masa hakan ba.
Shi tunda ya koma Qatar bayan rashin lafiyar Nenne, lokaci-lokaci maganar yarinyar na fado
masa, yakan tuna wai yanzu an masa aure, sai kace wani a zamanin da.
Tabbas za'a gaji da ajiyar matar nan kuwa, a karshe a maidawa iyayenta don ba zai taba
dauka ba.
Sai kuma ya tuno kamannin yarinyar, wanda ko bai rike hakikanin kamannin ta a ransa ba,
hakika ya rike kalar idanunta masu kama dana kwan zabo, wadanda suka nuna tsantsar
damuwar rashin lafiyar Nenne cikinsu da wani irin innocence.
Ya dade a zaune kafin ya yanke shawarar takamaimai me ya kamata yayi? Gashi an ce ta
rigata taho.

Ya bi bayan kiran Dade ne yace ta koma sai ya shirya ko yace bai shirya iya zama da iyali ba
har yanzun a kara masa lokaci? Har zuwa sanda yake jin ya shirya?
Ya riga ya saba da rayuwarsa ta kadaici ayyukan cigabansa, and his horses always makes
him busy, baya maraba da duk wani abu da zai canza masa tsarin rayuwar nan da ya riga ya
saba da ita.
Kamar ya kira Taiwo, ya gaya mata abinda Dade ya kira shi yanzu ya gaya masa in yaso ya
nemi shawararta kan abinda ya kamata yayi, don gaskiya Dade ya shammaceshi, sai kuma ya
fasa kiran nata. Dalilin tunawa da yayi cewa Taiwo tun rana ta farko da tazo Lagos taga yarinyar
ta yi masa korafin yarinyar da Nenne ta aura masa bata yi mata ba, because they are so much
different from the grounds of age and social class. Bai taba tanka mata ba don shi bai dauki
zancen ma da muhimmanci ba.
So yanzu ya kirata yace an sako yarinyar a jirgi ta taho masa, bai san abinda Taiwo zata ce
ba, banda ta sa shi ya maida ita. Ita dama ta saba rikici da iyayensu in sun yi hukuncin da baiyi
mata daidai ba.
Wata zuciyar tace to ko Kiki zai dauko daga Ilorin su zauna tare?
Nan ma yaga hakan bazai yiwu ba musamman kasancewar Kiki na makaranta kuma
watarana itama aure zata yi. Shi kam! Yayi duk iyaka tunaninsa bai ga ta yadda zai iya zama
gida daya da mace da sunan partner ba.
Bayan tsanar su da yayi, har gobe duk kallo iri daya yake yi musu, koda da wace niyyar
alkhairi suka dumfaro shi. Uwarsa da ‘yan uwan sa na ciki daya kadai ya kebance daga cikisu.
Gidan nasa babban ‘Ranch House’ ne hade da gidan gona (farm house), tsarin ginin flat ne
aka gina a can tsakiyar ranch din. A cikin wannan flat din akayi babban (sitting room) dake
kunshe da dakunan gidan, falon gidan (is kitchennette) wato hade yake da budadden kitchen na
zamani da ake yayi yanzu da dining area. A cikin wannnan babban (sitting room) din ne masterbedroom din Prince Abdulrasheed yake.
Sai wasu (two extra two bedrooms) din, kowanne da bathroom a cikinsa, wanda asali ya
tanadi dakunan ne domin ‘ya uwansa mata da haularsa dake zuwa hutu wajensa akai-akai.
Daga harabar wajen flat din nan ne Ranch na Dawakansa, suna cikin stable dinsu a jere abin
gwanin ban sha’awa. Ko ka samesu sun watsu cikin korran ciyayi a ranch house din suna ci
daga garesu, suna kuma sha daga ruwan dake tsiri sama yana sauka kasa (katon swimming na
gidan gonar), inda anan ake kiwon fararen Agwagin ruwa, Dove, Babba da jaka, Kangaroos,
Jimina, da Gada Mai tsalle, a can karshen gidan kuma wajen kiwon Shanu ne irin na turai masu
yawan haihuwa akai-akai inda ake milking danyar Madara.
Prince har ila yau yana kiwon tsuntsayen gida irin su kajin gidan gona jajaye, farare da
bakaken tantabarun Ingila, Dawisu da Argentinian Parrots (Aku-kuturun Argentina)
manya-manya masu magana. Duk a cikin wannan kasaitaccen ranch din.
A can karshen gidan gonar ne sassan Pareto da sauran ma’aikatan gidan gonar yake, da
babban (store house) na ajiye abincin Horses dana sauran dabbobin.
Yana zaune still yanata tunani ya ankara lokaci na tafiya, ya dade a wannan halin na zama
shiruuu, ya rasa ta ina zai fara. Cika umarnin mahaifinsa ko bin hukuncin zuciyarsa?
Kararrawa ta gaya masa ana magana dashi a kofa, da kyar ya iya mikewa don kafafunsa
sun masa nauyi, zuciyar sa ko tayi nauyi sosai, da kyar Prince ya isa ga kofar ya bude.
Pareto ya gani tsaye rike da kayan sa da ya wanke ya goge, ya bashi hanya ya wuce ya

ajiyesu akan daya daga cikin (three seaters) din (sitting room) din, don a ka'ida Pareto baya
shiga (master bedroom) dinsa.
Kawai sai Prince ya samu kansa yana ce ma yaron gidan nasa.
“Bude daki daya cikin biyunnan ka gyara, ka karbo abincin da nayi order, ka ajiye a dakin,
zan kawo baki daga gida Lagos anjima”.
A gidan gonar Prince, Prince ruwan zafi kawai yake iya dafawa da kansa, duk abinda zai ci
daga ‘African Cuisine Restaurant’ dake kusa da gidansa yake saka order ake kawo masa,
kullum sau uku, in har yana Argentina kuma yana gida bai je tournaments ba, to 'El Buen Sabor
Africano' su suke bashi abinci na al’adarsa wato (traditional Yoruba food). Pareto ya bi umarnin ubangidansa ya je ya fara gyara dakin wanda dama a gyare yake, sai
abinda ba'a rasa ba don baya sati biyu bai gyarashi ba, ko su Fatima sun zo ko basu zo ba
yana yawan sharewa ya goge, dama dai Taiwo ce tafi sauka a cikinsa don yafi girma, ko ita ko
Nenne. Dayan twin Princesses da Kiki ne ke sauka cikinsa. Pareto Yana feshe dakin da room
freshener bayan ya gama mopping, yana yi yana tunain ko su wa Boss zai kawo? Ya san da ba
lokacin hutun kannensa bane ba, ko Twin Sis dinshi Mrs Taiwo.
Da ya kammala ya fito sai ya samu Prince har lokacin a zaune inda ya barshi da alama yana
cikin tunani. Ya kasa yankewa kansa shawarar zuwa Airport din ne don cika umarnin Dade ko
a’ah?
Saida ya rage bai fi mituna talatin jirgin ya sauka ba ya mike cikin zafin nama ya suri mukullin
mota ya fita.
Kuma yana isa wajen ya hango yarinyar tana tahowa kanta tsaye, duk da dai Dade ya kara
da turo masa hotonta ta waya da ko budewa bai yi ba, yana ganin ta jikin sa ya bashi, zuciyarsa
ta amsa, yayinda kwakwalwarsa da idanunsa kuma duk suka shaidata.
**** **** ****
Aisha nata tunanin shiga motar ne ko yaya zata yi? And the Prince is patiently waiting for her
to decide, kamar yasan shawara take yi da zuciyarta tsakanin binsa ko a’ah.
A ransa yace baida matsala kan duk abinda ta zaba.
Shiga motarsa ko kin shiga zabinta ne, shi dama dan cika umarni ne kawai.
Ya mika hannu ya bude mata kofa, wani privilege da bai taba yiwa wata mace ba bayan
Nennensa, a iyaka saninsa tun tasowarsa sai dai shi a bude masa.
Ya kunna injin motar wanda baya making any noise ko kadan, kasancewarta lafiyayyar motar
tsere (Sport Car) ta zamani, sa’annan mai lafiyayyen sabon inji, Siddiqah ta gayawa kanta
gaskiya idan Prince ya gaji ya tafi ya barta a wurin nan ina zata je a wurinnan da batasan kowa
ba? Inda ko kallo kowa bai ishi kowa ba, kada ma taje Police su kamata a wurin a bisa tuhumar
rashin yarda da ita, don gasunan birjik cikin fararen kayansu suna ta shawagin tsaro a filin
wurin.
Ko me ya bata tsoro? Prince sai gani yayi bakuwarsa tayi kundumbala ta shigo motar da
sauri. The way and manner da Siddiqah ta sako kai ta shigo motar ma kamar mai shiga daki ya
saka Prince yamutsa fuska, domin ba ta haka ake shiga motar ba. Ya dan kalleta kawai ta gefen
ido yana so yace ta rufo kofar, mulkinsa na gaya masa yayi mata banza, ita bata san ya kamata
ba? Komai sai an gaya mata zatayi? Shi baya son yawan magana a nature dinsa, don sai ya
wuni bai yiwa kowa magana ba in ba SAHEEB ba, ko zai baiwa Pareto da ma’aikatansa umarni
ba kullum bane. Amma wannna bakauyar yarinyar ya ga alama a komai tana jira a bata

command ne, in kuma an bata din ba kasafai take ganewa ba.
Sai kawai ya mika hannu ta gabanta ya rufo kofar da kansa, a hankali ya hau kwalta suka
soma tafiya, nanma ya ga bata da niyyar daura belt, haka kawai zata jawo masa attention din
road safety. Da wata murya kamar yayi kuka don tausayin kansa, na aikinda Dade ya hadashi
dashi Prince yace da ita. “Please, fasten your belt!”.
Siddiqah ta dago tana duban Hamma Prince da ‘yar rudewa, cikin alamu na son ya fassara
mata, don har ga Allah wannan karon ma bata gane me Hamma yace ba. Don haushin data
bashi Prince bai kara maimaitawa ba, sai kawai yasa hannu daya yayinda yake tuki da dayan
yana daura mata belt din a bayan kwibinta, saida Aisha ta janye numfashinta sama kadan,
sakamakon kakkarfan kamshin masculine turaren Prince “Boss Intense” daya bakunceta.
Don da farko bata fahimci me yake kokarin manna mataa kugu ba, wanda hakan ya sata ‘yar
karamar kidimewa, don haka har Prince ya gama zura mata, ya cigaba da tukinsa numfashin
Siddiqah ya ki komawa daidai yadda yake, sakamakon tsoro da kidimar data shiga kafin ta gane
belt ne Hamma ya saka mata. Ko irin kalle-kallennan na bakin hanya na bakunta da bako ke yi in ya zo bakon wuri, banda
Aisha-Siddiqah. Titi kawai ta kurawa ido ba abinda yake burgeta duk kyau da kyatuwar birnin.
Hankalinta da tsinkayenta duk basa jikinta a yanzu, suna ga irin rayuwar data tunkarota, a kasar
Polo ta Ajantina, amma ta san ko babu komai tana da Allah, tana kuma da albarkar iyayenta
tareda ita.
Kuma Umma da Malam suna sane suka kawo ta don ta rayu da dan Nenne, sabida darajar
iyayensa, amma ko me yasa ba ruwan kowa da feelings dinta akansa wane iri ne? Shima din
kuma yana sonta ko a'ah? All they care for shine dansu yayi aure da mace mai tarbiyyah yar
masu dattaku, ya samu ya cika martabarsa da tasu. Ummanta da Abbanta kuma damuwarsu akan ta samu iyayen miji na kwarai ne, Nenne da
Dade kuwa sun hada wannan, burin nata iyayen shine suyi mata aure cikin lokaci, sannan su
kaita inda za’a rike musu ita da daraja.
A ganin Aisha Siddiqa lamarin is far beyond this only, ya kamata ayi la'akari da zuciyarshi a
kanta, ita tata mai sauki ce tunda ta rasa Ishaq, to bata da sauran zabi akan mijin aure.
Ishaq kadai takeso. Don haka a rashinsa kowa aka zaba mata sunansa Umma ta gaida
Aisha, wato sammakal, don bata da ja akai.
Tun Daga kallon data yi masa suka hada ido a filin jirgi bata kara yarda ta dube shi ba balle ta
kalli cikin idanunsa masu tsananin kwarjini. Ta kan dai dan saci kallon gefensa yana tukin.
Tafiyar mintuna kusan talatin ce ta kawo su gidan Prince tsakiyar garin Buenos Aires (capital
of Argentina). Tausayin yarinyar ya dada kamashi ganin ta kifa kai a jikin allon motar tana sauke
ajiyar zuciya ita kadai bayan tayi kukan ta gaji.
Ya kashe motar yace da ita cikin sassauta sa “mun zo. Ko zaki iya shigowa ciki?” Da
sassaukan turanci ya fada. Wannan karon bata isa tace bata gane ba, domin kuwa Prince yayi
lowering accent dinsa da voice tone dinsa sosai.
Pareto ne ya iso da hanzari ya budewa ubangidansa kofa kafin ya zagayo ya budewa Aisha.
Ya umarceshi da ya shigar da jakunkunan ta ciki. Yana fatan kuma ya karbo mata abincin da
yace ya karbo mata.
"Master abincin tun kafin fitarka na karbo shi, na shirya shi a dakin".

Aisha ta fito tana zare kyawawan idanunta a gidan gonar Prince Abdulrasheed (Kehinde).
Wani babban ranch house ne wanda tun daga nesa zaka hango daidaikun Dawakai na alfarma
farare da jajaye da bakake, sun watsu jefi-jefi suna cin korran grass, wani abun sha'awa da ko a
talbijin bata taba gani ba sai yau a zahiri. Prince ya wuce gaba, Aisha ta hadiye kauyancin ta da tsoronta ta bishi a baya zuwa ainahin
(sitting room) din dake cikin ‘ranch house’ din.
Da suka shigo tsakiyar falon, Prince sai ya maida kofar ya rufe yayi gaba ya barta a wurin.
Siddiqah ta cira kai a hankali tana kallon wannan kayataccen muhalli wanda saidai taga
kwatankwacinsa a finafinan larabawa dana turawa, shigifa ce ta alfarma mai hade da karamin
madafi na zamani da akeyi a cikin falo (kitchennett). Girman falon da fadinsa yasa kujeru
kala-kala saiti uku kosassu na musamman yaci, batare da kowacce ta san da zaman ‘yar
uwarta ba. Dole tsarin komai na sitting room din Hamma Prince ya burge bako, har dai in wanda
ya san kimar muhalli mai daraja ne, ba kamar Aisha-Siddiqah ba, wadda iyakacinta Gombe da
Billiri.
Sai ko yanzu data dan samu 'yar gogewa a zaman ta na gidansu Prince a Lagos tareda
Nenne.
Ita kyawun falon da dukiyar da aka zuba a cikinsa firgitata yayi, maimakon ya bata sh’awa, ya
kara kidima 'yar nutsuwar da ta fara samu.
Tsayawa tayi a tsakiyar falon harde da hannuwa a kirji, tana jiran ya bata umarnin zama, ko
ya nuna mata kujerar data dace ta zauna. Ta kwaso gajiya ba ‘yar kadan ba kafafunta har
mintsininta suke, ba abinda take bukata a lokacin irin ruwa mai zafi a kwami ta shiga ta
wartsake wannan gajiyar zaman data kwaso, sannan ta samu ta sauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login