Showing 21001 words to 24000 words out of 46523 words
Chapter 8 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf
bangare tafi Haseenah da yayiwa hakikanin SO na
soyayya akan radin kansa cikar martaba, asali, da kyakkywar nasaba.
Ko babu komai ita duk sanda aka ga dama za'a je aga iyaye da danginta, koda basu da
komai ya tabbata sunada asali, tunda har Nenne da kanta ta ga dacewar auro masa ita saboda
kwadayin wata nagarta data gani a tareda mahaifiyarta.
A kwana shidda kadai da zuwan Aisha tsarin kitchen da sitting room din Prince ya canza,
komai ta maida shi yadda tafison ya kasance. Aisha ta canzawa kanta da kanta rayuwa a gidan
Prince Abdulrasheed Kehinde.
Kullum zaka sameta cikin tsafta da wanka da shiga mai kyau kuma ta mutunci. Taga cewa
zaman me zata yi in bata motsa jikinta? Koda take son cikowa bata son irin kibar Fatima. Ta
soma koyawa kanta gyaran sitting room din da kitchennette din, da kawar da duk abinda suka ci
abinci ta wanke ta goge ta kife. Sannan ta fara sanyawa gidan turaren wuta masu tsananin
dadin kamshi da Nenne ta hado mata.
Ba'a jima ba ta gane yadda ake amfani da daukacin electronic appliances na gidan su dish
washer, kunna dispenser, washing machine don wanke kayan ta data yi amfani dasu, ta hanyar
karanta manuals dinsu.
Cikin kwana na bakwai da zuwanta Aisha ta fahimci da yawan abubuwan amfanin gidan, ba
tareda an koya mata ba, ta fara goge kauyancin data zo dashi kaso hamsin cikin dari, sai dan
abinda ba’a rasa ba.
Idan Aisha tayi girki ta kan tambayeshi idan ya fito ko zai ci? Sai yace yayi order. Don Prince
ganin Aisha yake bazata iya wani girki da zai iya ci ba har guda nawa take? Siddiqah bata wai
damu ba, sai ta dafa iya na cikinta ta kwashe a warmer tayi shigewarta daki da abinta.
Prince ya zo Argentina ne domin ya huta, don haka zuwan Siddiqah na bagatatan dinnan
baya ciki abubuwan da ya tsara a hutunnan nasa, don haka satin siddiqah biyu kenan amma
abubuwa sunki yi masa normal, na farko ji yake tamkar a kansa take zaune tsabar ya kasa
sabawa da zaman matar aure da motsinta a cikin gidansa. Duk da ita Siddiqah ba abinda ya dameta da Prince a cikin gidan, harkar gabanta kawai take
yi tsakanin kitchen da falo da dakinta, sannan ta riga ta kirkirarwa kanta abubuwa na debe kewa
da zasu lallasheta cikin wayar da Prince ya bata, social media plarforms ta sauke iri iri ba
wanda bata shiga ta ga me duniya ke ciki, bayan girke girke da take yi wa kanta don ta burge
kanta da kanta kullum. Yo ta burge kanta mana, sanin da tayi Prince bazai ci ba, musamman
ganin komai na girkin available kuma a wadace yasa take dafa duk abinda ranta ya kwanta
dashi.
Daga baya idan ta girka ta kan ajiye bisa dining din da yake zama don cin abinci, ganin cewa
da kudinsa ake yo cefanen koda bazai ci ba hakkinta ne ta bashi, musamman lokutan data
ganshi a gida, ko in ta ganshi ya fito zai fita unguwa ko kuma ya dawo, sai kaji tana gaya masa
cikin ladabi da sasanyan fulatancinta. “Ga abinci Hamma Abdul, ban sani ba ko zaka daure ka ci?”
A irin wanna lokacin da Siddiqah ta kwantar da kai tana masa tayin abinci cikin kwantar da
murya, jin kansa yake on top, irin yanda maigida ke ji a gidansa, ya ji shi a ransa yanzu ya cika
mutum, amma sai yaji sarautar ta motsa ta hana shi amsa mata da dadin rai, sai kawai yace
mata “na gode, I am okay”.
Ya kan ki kallon inda abincin yake, ya wuce ga abinda ya fiddoshi daga dakinsa, don kiri-kiri
Siddiqah tasa Prince ya ragewa kansa zaman (sitting room) dinsa, bata takurawa kanta sam a
zaman gidansa wai saboda shi ko don sanin cewa yana cikin gidan, tuni ta roki Ubangiji ya cire
mata tsoro da shakkar Hamma, da kwarjininsa dake sata bare-baren jiki tuni Allah ya ji rokonta
ya yaye mata.
A halin yanzu shine ma za’ace Siddiqah ta takurawa, don saidai in bazai zauna a sitting
room din ba yayi ta zaman daki, ba abinda ke hanata bajewa a falon gidan ta kunna talbijin, bai
taba ganin yarinya mara tsoro da shakkar idanunsa wadda kwarjinin sa bai sawa ta bar wuri irin
Siddiqah ba. In kaga yadda take sakewa a kitchen din tana kai komo domin shirya abinda zata ci kamar ta
shekara a gidan. Sau da yawa sai ta ta gama abinda zata yi na ranar ta shige bedroom dinta ta
kwanta yake iya fitowa ya zauna a sitting room din don yayi kallon labaransu na (PoloLine TV),
yana kallon yana shan Chamomile Tea, wanda shine ke sashi yin barci na nutsuwa a yawancin
lokuta.
Prince baya so ya zauna daga shi sai ita a falon, don sau tari kallon Siddiqah kadai idan yayi
tausayi take bashi, (no any other strange feeling) bayan wannan, tausayinsa akan wannan aure
da aka yi mata ne jaririya da ita da tsohon bachelor kamar shi. An kuma rabota da kasar
haihuwarta da kowa nata, sannan shikuma gashi bai ko iya hira da bare ba, baren ma mace,
yawanci in kaji hirarsa na fita tar-tar da Kiki ne ko Aunty Taiwo.
Koyaushe Aisha na magana da iyayenta suna kara karfafata, da kuma mutanen gidansu
Abdulrasheed su kuma suna kyautata mata. Princess Firdausi ta taba turo mata lambar Aunty
Taiwo tace ya kamata ta kirata ta gaisheta don taji tana yiwa Nenne korafin Aisha bata taba
gaisheta ba, ko a waya, kamar bata san matsayinta ga Kehinde ba. Amma Aisha ji tayi ko da wasa ta kasa kiran Aunty Taiwo. Tana kiran kowa na gidan
musamman Dade, harda Princess Fatima kuwa mai amsa mata sama-sama. Amma har lokacin
bata kira Kiki ba saboda alkawarin da ta yiwa kanta na ba dai Kiki taji maganar aurenta da
Uncle dita daga bakinta ba in duk gidansu an rasa mai gaya mata to aje a hakan. Haduwarsu cikin gidan ma ita da Prince ba sosai bane tunda baya zaman falon, wani lokacin
da safe in ya fito karya kumallo in ‘yan saukin kan na kusa yakan je har kofar dakinta ya
kwankwasa yace ta fito su karya kumallo tare, ta kance daga cikin dakin ba taredata fito ba
Hamma ya ci, ita ba yanzu ba, don tasan na order ne in ita tayi ta bashi baya ci ai sabida ya
dauka bata iya ba ko yayane oho.
Daga nan basa kara haduwa sai ko da daddare in zai yi dinner tana zaune a sitting room din
tana latsa wayar hannunta ko kallon tv, nan ma su kan hadu, kan ba yadda Prince zai yi, saidai
yaci abincinsa tana zaune don baya iya cewa ta tashi.
Ta fahimci duk yammaci daga karfe hudu zuwa shidda na yamma wato bayan yayi sallar
la’asar, Hamman nasu Fatima, yana kasancewa a ranch dinsa ne ya karasa wunin ranar tare da
Dawakansa.
Mu’amalarsu shi da Dawakan mai ban sha’awa ce, don sau tari takan hango su idan ta daga
labule don samun danyar iska (fresh air). Musamman wani babban doki a cikin Dawakan da ta ji
Hamma yana kira da suna SAHEEB.
Sau da yawa ta kan jiyo basarakiyar muryar Prince idan yana magana da dokinsa Saheeb,
ko in Pareto ya tadda shi a wurin suna maganar da ta shafi lafiyar dabbobin.
Ana I gobe zai tafi France din da ya shirya tafiya suka wayi gari da bakuwa a gidan ba zato,
“Kiki”.
Tun kafin kamo hanyarta ta komawa makaranta, Kiki ta yanke shawarar bari ta tsaya gidan
Uncle dinta tayi kwana biyu yadda ta saba tare dashi, sannan ta wuce makaranta, tayi kewar
Kawun nata sosai.
Da niyyar kwana biyu kacal Kiki ta tsaya wato zatayi Asabar da Lahadi in yaso Litinin ta
karasa Los Angeles daga Argentina, tuni a hakan tayi booking flights dinta tun farko.
Ko da ta sauka ma bata kira shi domin ya daukota ba, taxi ta biyo zuwa gidan nasa duk don
tayi surprising dinsa.
Pareto ya tabbatar mata Master na nan, kasancewar ya san matsayin Kiki a gidan yasa ya
barta ta wuce kai tsaye zuwa kofar shiga sitting room.
Kiki (Ruqayyat Toufeeq) taci gayunta kamar koyaushe, ta fito a Kikinta tsaf, ‘yar gatan Prince
(Uncle AK) inji ta, tana tafe kwas-kwas-kwas akan tsinin takalminta, sanye cikin wata ruwan
zumar kampala Yoruba Traditional Attire mai ratsin baki data sha dinkin bubu don Kiki kam
masha Allah bul take, shiyasa da wuya kaga tayi dinki wanda zai kama jikinta, ko English wears
da take yawan sakawa zaka ga cewa sakakku ne, Kiki tayi kyau har ta gaji duk da bata
make-up, da ganin ta kaga ‘yar hutun budurwa mai cin lokacinta da zamaninta, bayarabiyar
asali gaba da baya.
Wani dan share-sharen gyale ne Kiki ta yafa iya kafadunta da ‘yammata ke yayi, (chantily)
kalar kayan jikinta ruwan zuma, a kafarta wani siririn (golden heel shoe) ne mai tsinin dunduniya
sosai a santala-santalan kafafunta.
Kiki ta danna kararrawa mai sanar da zuwan bako (door-bell) a kofar shiga sitting room, tana
cike da dokin ganin Uncle din nata.
Aisha na zaune a sitting room tana kallon bakaken larabawan Sudan na wakarsu ta
Sudanese, shi kuma Prince yana daga can cikin Master bedroom dinsa. Kiri-kiri shi da falonsa
Aisha ta gaje ta hanashi zama, ta maida shi zaman daki dole, don baya so su zauna tare na
lokaci mai tsaho a falo ko mai yasa? Shima ya rasa dalili. Ya dai danganta hakan da baya so su
saba, ta shiga jikinsa.
Dadin wakar larabawa da akeyi a TV dinne yasa bata yi saurin mikewa domin taje ta bude
ba, ai tasan zai ji yazo ya bude tunda gidansa ne, karewa ma bin wakar take yi tana kada ‘yan
yatsunta a hankali da juya dogon wuyanta don tana matukar son wakar da akeyi din. Mai kiran
bai hakura ba haka ya cigaba da danna door-bell din a nitse, sannan da zaquwar son azo a
bude.
Dole Aisha ta mike ganin Hamma bashi da niyyar fitowa da kansa ya karbi aiken, ta isa kofar
dakin nasa tana masa knocking, don tana zaton Pareto ne, taji sanda ya kira shi ta waya ya
aikeshi ya samo masa chamomile tea.
Daga ciki Hamma ya amsa da.
“Yes, I am coming”.
Kafin ya bude ya fito daga shi sai farar bodycon da dogon bakin wandon Jeans, Aisha ta
sunkuyar da kai don ta kasa kallon sa da suttura a jikinsa, ga (8 pack) dinsa duk ya bayyana ta
cikin (bodycon) din da ke jikinsa, kanta a kasa tace,
“Hamma anata sallama a kofa tun dazu”.
Prince yace “kuma ke baki iya bude kofar bane ko yaya?”
Ya fada yana binta da idanu daga sama har kasa, ita kenan kullum cikin dogayen riguna
abinta, kamar ita tasa aka kera jallabiyyas, bata yin wani abu (to make him attracted to her)
tsakanin ta da Allah ba kallon miji take masa ba, kallon babban Yaya ne. Ko kuma wani young
kanin Babanta haka. Prince a ’yan dakikannan saida ya gama karewa kyakkyawar surar jikinta
da fuskarta dake sunkuye kallo, sannan ya sauke wani boyayyen numfashi, ya ce,
“to naji, kije kisa kallabi mana, bana son ganin ki a gabansa kai a bude babu dankwali, ga
Pareto ba hankali ya isheshi ba, duk da yasan kina gidan amma kullum yana faman yi min
Pareti a gida”.
Kalmar tashi ta karshe “Pareto na faman yi min Pareti a gida” taso ta bata dariya. Daga haka
ya wuce Aisha a wurin, tana tambayar kanta ko meye gamin Hamma da daura kallabi a kanta?
Ita batama san lokacin da kallabin ya zame akan kujerar da take kwance a kai ba. Kodayake
ko ba komai daura kallabi abu ne mai kyau musamman ga matar aure a gaban wanda ba
muharraminta ba. Kenan Hamma bai fada don wata manufa ba.
Tana kallo ya isa ga kofar cikin takunsa na kasaita ya bude, don da gaske ya dauka Pareto
ne ya dawo daga aiken da yayi masa. Sai kawai ya ga Kiki ba zato tsammanin sa, kamar daga
sama.
Lallai kuwa Kiki tayi surprising Uncle din yadda tayi fata. Don can na ganeshi rike da bakin
mamaki, har fuskarshi hakan ya nuna, wato mamakin ganinta, at the same time, yaji dadin
ganinta.
Kiki ta yi tsalle zata rungumeshi yadda ta saba, ga mamakinsa yau sai ya kasa rungumar Kiki
gabadaya a jikinsa yadda ya saba, ko ba don Aisha dake bayansa ba, don ji yai girma ya karu
masa akan nasa, (girman aure da haibar dake cikinsa).
Itama kuma Kiki sai bata damu ba ko don ta san ta girma yanzu? Duk da cewa niece din shi
ce sannan al’adarsu ta Yoruba bata hana hakan ba, dan side hug ya dan yi mata a kafadunta
sannan ya kama hannunta yarike cikin nasa.
"Kiki? Kece da gaske? How comes kika zo ba sanarwa, meyasa baki gayamin kin taho ba,
inje in dauko ki bayan saukar ki?"
Kafin Kiki ta bashi amsa ya sake cewa "ki daina zuwa ba sanarwa, tunda kin san ba nikadai
bane a gidan yanzu".
Da mamaki Kiki ta ce "Kai da waye toh a gidan Uncle AK?".
Sai kawai ya matsa ya bata hanya ta shige cikin sitting room din. Zakin muryar Kiki mai amo
kamar na marokiya da taji kamar cikin mafarki yasa ta juyowa da sauri daga gaban talbijin, sai
idanunta suka sauka cikin na Kiki-Ruqayyat.
Kiki saura kadan ta koma baya da gudu, don kuwa ba karamin tsorata tayi da ganin Aisha a
gidan Uncle dinta Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni ba.
How dare she came here? Ta ina tabi tazo har Argentina kuma gidan Uncle dinta? To me
tazo yi? Me ye gaminsu? Kodai-kodai Aisha aljana ce bata sani ba, tukunnama meye hadinta
da Uncle AK da zata dawo gidansa da zama?
Iyakar tsorata da shiga rudani Kiki ta shigesu ta kuma firgita, mamaki ya kusan kasheta daga
tsaye, sai ta koma daga bayan Prince ta dan rike rigarshi ta baya, tana buya tana lekowa
kadan.
“Uncle AK boyeni, kawata Aisha-Siddiqah ce take yi min fatalwa a gidanka ba don ta mutu
ba”.
Watakila tun zuwan Aisha gidan Prince batayi dariyar data fiddo fararen hakoranta waje ba
sai yau. Da kyar Prince ya zaqulo Kiki daga bayan sa yana cewa “bana son shirme Kiki, kina
nufin baki santa ba ko yaya ne? Mutuwa tayi da zata yi miki fatalwan?”
Da gudu Aisha ta taho ta janyo Kiki ta karfi daga bayan Uncle ta rungumeta. Kiki na kokarin
zamewa tana dojewa tana cewa.
“Ba wani hugging dina da zakiyi. Ba wannan a tsakaninmu yanzu. Nayi fushi, nayi fushi sosai
Siddiqah.
Ki gayamin kawai saboda Allah me kike boye min haka tuntuni?”
Kiki ta juya ga Baban nata cikin rudewa tace “Uncle AK, ku fiddani duhu, I am perplexed, that
means Aisha-Siddiqah is your wife since?”
Prince rasa amsar da zai baiwa Kiki yayi, don sosai yaji nauyin ‘yar tasa ta yadda zai ce
mata kawar tata da basu fice shekaru daya ba matarshi ce ta sunnah, ba wani (age gap) ma
tsakaninta da Kiki. Duk da haka yayi mamaki da bata sani din ba.
Sai kawai ya zuba hannayenshi a aljihu yana kallon Kiki tana murje ido wai dai ta tabbatar ba
mafarki take yi ba, Hamma ya samu hannun kujera ya zauna, ya mika mata hannu yace.
“Come on my darling daughter, zo ki zauna kusa da ni, ki gayamin yaya hanya? Uncle
missed you for long!”.
Kiki taki zama, ta soma kukan dadi daga tsaye, tana bubbuga kafa a kasa na shagwaba don
zuwa yanzu duk da bai furta ba ta gama gane komai.
Cewa Kiki take daga inda take tsaye cikin kukan da ya wuce da dariya, “wayyo ni Kiki! Wayyo
ni Ruqayyat! Uncle AK kawai kace min kayi aure, ashe inada rabon ganin wannan ranar?
For how long akayi toh da har ni ban sani ba???
Auren ma kuma da Aishata! Itace na dade ina yi maka sha’awa fah!”
Ta koma Yarbanci ziryan tana fadin “God so kind, yau da wace kalma zan godewa
Ubangijina?
Uncle dina yau da matar aure a cikin gidansa a Ranch dinsa?”
Sai