Showing 45001 words to 46523 words out of 46523 words

Chapter 16 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf

daki? Kamar kinsan yana son Afang Soup, ki ta lallaba shi a haka
har ya ware ya koma sha’anoninsa kin ji ko Aisha-Siddiqah?”.
Sukayi sallama da Nenne tana ta saka mata albarka.
Sai taji Hamma daga bayanta yana cewa.
“toh ni baby ne da Nenne ke checking up on me haka, kuma through another baby din like
you za’ayi checking up din? Lallai!”
Maganarsa ta baiwa Aisha dariya sosai. Ta yi ‘yar dariya tace “saboda ta damu ne ai, nima
dazu ai ka bani tsoro da naga kana kukan” Prince yace “Oh! So you are genuinely worried
about me, not because of Nenne?” Aisha bata bashi amsar wannan ba, tayi murmushi ta karasa
tashi tace “muje kaci abinci toh Hamma”.
Ashe dankwalinta ya zame ta baya akan kujerar data tashi bata sani ba. Nan Prince yaga
wani zallar bakin gashi mai laushi da sheki yana zagin idonsa.
Wani abu Hamma ya hadiye a makogaronsa, kafin yayi ta maza ya zauna ya fara kwasar
daddadan girkin amaryarshi Aisha.
Koda suka gama cin abincin ma haka tayi ta lallabashi. Da taga ya zauna shiru zata fara yi
masa hira.
Har lokacin kwanciyar Prince yayi, ya mike ya na ce da Aisha.
“Ko zan samu ‘yar tayin kwana? Banason kadaici yana dawo da damuwata baya, please
Aisha”.
Sunkuyar da kai Aisha tayi, kamar mai tunanin taje ko a’ah?
Hamma ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye yana fadi cikin lallashi, “I only need your
presence, ba abunda zan miki Aysha. In baki son jina ma a kusa dake ba sai na kwana akan
gadon ba”.
Don haka da Prince ya saka hannun shi cikin nata suka soma tafiya, sai ta kasa resisting
offer dinsa.
Hamma ya cika alkawari, domin kuwa Pillow ya jefa akan kilishi ya bar mata ni’imtaccen
gadonsa, ba jimawa da kashe wutar da yayi barci ya daukeshi dama ga gajiya ya tara.
Saida Aisha taji numfashin Uncle na sauka a nitse ta tabbatar yayi barci sannan ta samu
sakuni a ranta, daga wata irin fargaba data shiga ranta a dalilin kwananta a yau master
bedroom tareda Prince.
Washegari tare sukayi sallar asubahi. Prince ya koma barci Aisha ta fita zuwa dakinta tayi
wanka ta shirya ta koma kitchen tana hada musu abin kari.
Da hantsi ya daga ma suna tare a parlor amma har zuwa lokacin fuskarsa da damuwa. Duk
dai don ya daina damuwar Aisha tace
“Hamma please, yau zaka fara koya min Polo”. Ya juyo with attention ya kalleta. Magana in
ta Polo ce dama Hamma na sonta, don haka gladly ya amince su fara. Amma yace ‘riding’ zai
fara koya mata kafin Polo. Dama kuma itada Saheeb sun riga sun saba sosai.
A haka Prince ya fara koyawa Aisha ‘horse riding’, yana ajiye damuwarsa a gefe.
Rana ta farko data biyu tare suka hau bayan Saheeb, don yanata koya mata amma ta kasa
ganewa, saida ya hau tareda ita ya saka ta a gabansa.
Rana ta biyu suna cikin yi Aisha ta kusa fadowa, Prince yayi saurin tarota da hannu daya,
inda unintentionally hannunsa akan dukiyar Fulani ya sauka. Da sauri ya saki, itama kuma haka

ta saki linzamin, duk suka daburce suka zamo tare daga bayan dokin.
To da yake ba gudu Saheeb din yake yi ba, ga uban tausasan grass carpet sai basu ji ciwo
ba. Saida suka fado ne Prince ya tuna abinda ya cafko, sai ya fashe da dariya, itama kuma
haka.
Ya fuske yace “to daga yau an gama, tunda fadowa zaki dinga samu muna yi”.
Ya dinga tsokanarta don yayi shaking off the awkwardness.
Sai bayan ya kwanta ne a daren, kafin shigowar Aisha, duk sanda ya tuno irin laushin da yaji
sai hankalinsa ya tashi.
Lokacin ne ya tabbatarwa kansa ashe dai lafiyarsa kalau, bai zama abinda shima yake
tababar ko ya zama ba. Something strange deep down inside him is working like ignition or
arousal.
Sha’awa tace salamu alaykum, shiyasa koda Aisha bata zo taya shi kwana yau ba itama
saboda kunyar abinda ya faru yau, shima bai je bikonta ba.
A rana ta uku ma da kyar suka yi one hour ana koyon Polon, gabadaya ya zama aware of her
body, da son taba ta da gangan, a wajen rike linzami da sukuwa da hawa da sauka daga doki
jikinsa a gugar nata yana kara birkita shi, kamshin jikinta da laushin fatar jikinta inda duk yayi
kuskuren kai hannunsa sai ya kidima shi, gabadaya Prince ya kasa gane kansa a wannan koya
Polon da Aisha ta saka shi. A haka a daddafe aka yi kwana biyar ana yi. Suna kuma kwana a
daki guda, amma Prince na kan pillow da kilishi rufe da duvet, ya sallama mata gadon, Aisha
bata san irin faman da yake da kansa ba kafin wayewar kowanne gari.
Sai ya zama Prince na Allah-Allah hantsi ya dubi ludayi wato lokacin Polo lesson din su yayi,
just to have that closeness da Aisha akan Doki. Sarai ya gane zata iya riding da kanta itama
kuma ta fada masa yanzu ta iya, amma yace sammm, bai yarda ba fadowa zatayi in ya barta ta
hau ita kadai. Duk dai don ya samu wannan kusancin da Aisha, da dan body contact dinnan mai
hargitsa duk wata nutsuwa da Prince din ya mallaka cikin dare da ido biyunsa.
A sati guda da akayi ana koyon Polo Prince ya samu duk wata sha’awarsa ta da namiji ta
dawo jikinsa.
Aisha bata san haka ba ta koma saka lingeries da nighties din da Kiki ta sai mata.
shakuwarsu kullum daduwa take yi, they have build a good bond of friendship, a satin da ya
biyo baya Prince ya soma kai Aisha yawo da shopping, ita kuma ta saki jiki da shi sosai ta sake
dashi kullum tana zuba masa hirar gidansu da nasu gidan, ta fito a real Aisha dinta ta Billiri mai
baki zauu. Unknown to her, komi tayi kashe shi take yi da soyayyarta cikin ransa.
A wadannan satittikan Prince Abdulrasheed ya gama sanin komai game da matarsa
Aisha-Siddiqah. Itama kuma ta kara sanin abubuwa da yawa game da shi da rayuwarsa da
zuri’arsu ta Akanni gabadaya.
Ya soma kiran iyayenta a waya akai-akai yana gaishesu. Ya kuma gayawa Aisha shi ya kaisu
airport ya saka su a jirgin da zai maidasu arewa lokacin da suka zo Ilorin yi musu ta’aziyyar
Emir kafin dawowarsa. Dade ya gabatar dashi ga Ummanta da malam Yunus. Ba karamin jin
dadin wannan labarin Aisha tayi ba. Suna cikin wannan yanayin da yafi gaban biro ya rubuta don dadinsa garesu, suka wayi gari
da bakuwa a gidansu. Aisha dai Pareto ya zo ya gaya mata sunada bakuwa. Tayi mamaki.
Amma tace kawai ya shigo da ita jin cewa mace ce.
Prince na dakinsa yana shiryawa zasu fita lokacin da Haseenah ta shigo falon. Aisha tayi

mata sannu da zuwa fuskarta ba yabo ba fallasa. Ita kuma Haseenah sai karewa Aisha kallo
take, small beautiful girl, wadda ganinta yafi jinta! Irin kallon da Haseenah ke mata, da irin
shigar dake jikinta duk basu yiwa Aisha ba. suka zauna shiru a falon, Haseenah bata ce mata
ga wanda tazo nema ba, ita kuma taga bai yi daidai tace mata wa take nema ba. sai suka
zauna zaman kurame a falon. Haseenah na kallonta da budadden ido Aisha na neman inda
zata boye kanta kada wannann bakuwa da bata san ko mayya bace ta cinyeta.
Sai ga Prince ya fito daga dakin sa cikin shirin fita, yana cewa “Aisha ina kika saka mukullin
Lamborghini?” sauran maganar makalewa tayi a makwallatonsa, da yayi arba da Haseenah
Ambursa zaune a falon gidansa.
Mu karasa a littafi na hudu (4)

(INA MAI TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a
wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements
ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control?
Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA
LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da
kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo
ku bani labari.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login