Showing 6001 words to 9000 words out of 46523 words
Chapter 3 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf
lumshe, tayi kukan har ta
gaji, sai ajiyar zuciya take yi yanzu kuma, zuciyarta ta cunkushe da tunaninninka marassa dadi;
muhimmi cikinsu shine ganewa data yi iyayen Abdulrasheed bakidaya sun dora hope din
daidaituwar rayuwar tilon Dan su a wuyanta, wato samuwar farin cikinsa da canzuwar
rayuwarsa ta hanyar aure.
Dade da Nenne, Sun bata dukkan ‘trust’ dinsu, da duk wani fatansu nagari na cewa ita din a
yadda take da kuruciyar nan (in her teens) zata ita iya canza Prince Abdulrasheed mai shekaru
sama da arba’in daga rayuwar data sameshi a ciki, ya kuma karbeta ya bata gurbi tare dashi ko
yanaso ko baya so. Gashi tasan bata taki komai ba, bata da idea bata da wata fasaha akan zama da Dan su
Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni, wanda alamu sun gama nuna ba ita Siddiqah
kadai ba, baya maraba da kowacce mace cikin rayuwarsa balle ita diyar Mallam Yunusa.
Ko abubuwan nan da Kiki tace su suke gigita maza su so mace, ita Siddiqah bata dasu bata
mallaki ko dayansu ba (frontward-backward) ta bakin Kiki. Taji da kunnenta sanda Murjanatu
(Taiwo) take kusheta, Ya Allah! Murjanatu ma kenan wadda tafi kowa kusanci dashi, tafi kowa
saninsa, ta san abinda zai iya so da wanda bazai taba so ba, balle ita Siddiqah da ba sidi ba
sadada!
Tsabar tunani irinna rashin self-confidence, lack of motivation da inferiority complex da suka
bi suka dabaibayeta yasa har aka ajiye mata abincin jirgi a gabanta bata sani ba. Abu daya take
da kwarin gwiwa akansa har gobe, idan ta tuna cewa ita bafullatana ce a kansa, tanada wannan
ego din na cewa kabilar data fito tafi tasa daraja (a tunaninta). Kabilarta wato (Hausa/Fulani)
babu ya ita a kabilun Najeriya wannan kadai idan ta tuna shi yake bata karfin gwiwa.
Kenan ethnocentrism dinta har yanzu yana nan, bazai taba barin zuciya da kwakwalwar
Siddiqah ba har abada wato perception dinta na (alfaharin kabila).
Tana cikin passengers masu tafiyar dare, da suka tashi zuwa babban birnin (Beunos Aires)
din Argentina, kai tsaye tun daga Lagos, tafiya ce suke yi mikakka ba tareda transit (dakatawa a
wata madakata ba).
Lokacin da jirgin su ya sauka a ‘Aeropuerto Ezeiza’, wato filin jirgin (Buenos Aires), saida
kowa ya gama ficewa amma still har lokacin Siddiqah tana zaune a mazauninta kamar an kafe
ta, ta rasa inda zata tsoma zuciyarta da rayuwarta taji daidai. Har saida ma’aikatan jirgin suka
ankarar da ita cewa kowa ya fita ya barta. Sannan ne ta mike ta saba Jakarta, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta dinga jan
kafa, jaye take da trollies dinta guda biyu da basu cika girma ba.
Aisha sanye take da ruwan makubar Abayat da mayafinta kirar Taiwan, mai adon manyan
stones da suka maida rigar mai dan nauyi, ba tareda Siddiqah ta san ina zata dosa ba kawai ta
tasa kai a gabas take tafiya.
Ita tasan ba wata shaida da take da ita da Hamma zai ganeta, kamar yadda Dade yake zaton
itama zata iya gane shi, bata tsammanin ko kamannin fuskarta Prince ya sani. Kodayake Dade
yace wai hotonta zai tura masa na jikin pasfo ko yaya dai?
Itama kuma bazata iya tuna kamanninsa ba, don kallon shifcin gizo tayi masa a asibitin
Lagoon lokacin da aka kwantar da Nenne, abunda zata iya tunawa game dashi guda daya ne
zuwa biyu; na farko turarren tabon sallahr dake saman goshinsa, wanda ya ciza sosai ya nuna
cewa Sajidi ne (mai yawan sujjadah). Na biyu kuma ingarman jikin sa murdadde da tsayayyun
kafadunsa, wadannan ko ya juya baya ne ta gansu zata ganeshi dasu, don ba duk maza Allah
yayiwa baiwar halittar da yayima Hamma ba.
Ta cigaba da wuce mutane tana tafiya a ba tare da ta san ina zata dosa ba. Don haka ba
jimawa Siddiqa taji wani marayan kuka ya zo mata, ba don ta rasa Uwa ko Uba ba, amma jin
kanta take yau a marainiyar karfi da yaji, mara gatan kowa. Tana ta kokarin hadiye kukan da
hawayen, tana gayawa kanta Allah na nan, kuma shi zai zama gatanta a nan inda bata da
kowa.
Hannayenta hagu da dama jaye da jakunkunanta ta wuce cikin terminal.
Tana tafe idanu a rufe duk hawaye ya jika fuskarta, ba tareda ta san ina take jefa kafa ba
saboda rudanin zuciya da kwakwalwa, Siddiqah tafiya kawai take kanta tsaye har ta kan kusa
bige jikin mutanen dake wucewa ba tare ta kula ba, sabida idanunta sun rufe ruf! Da hawaye,
sai ji tayi gab! Tayi wani uban karo da mutumin dake tahowa direct gabanta. Kawai sai ta samu kanta da dagowa a hankali, da bude ido jikakkun idanunta da suka
kankance don kuka ta dubi mutumin, bata san sanda ta saki marikin jakunkunan hannunta kasa
ba.
Don kafin taga komai ta hango tabon sujjadar dake saman goshinsa, kafin ta sauko da
rinannun idanunta akan faffadan kirjinsa wanda shine ya bashi suffar da za’a kira shi da
INGARMA…
A yawan hirar Kiki akan Kawunta, ta kan ce mata wai mazan duniya aji-aji ne su, a kamanni
na halitta da kasaita, amma cikinsu da wuya a samu irin Uncle dinta….
Kiki tace “Uncle dinta zatinsa da kyawun surarsa ya zarta yadda duk zata misalta mata su ta
gane baiwarsa mai yawa ce, ta dauka Kikin koda Ubannata kadai take yi a wancan lokacin, don
ita bata ga komai da zata iya noticing har ta karar a tare dashi ba, a dan ganin data yi masa.
Amma yau ta ga zahirin maganar Kiki-Ruqayyat, saboda ta yi masa kallo ne sak na rahma
da salama, bana cikin halin taraddadi ba (ba irin wanda tayi masa a ganinta na farko dashi a
asibiti ba). Ga cikar zati da kamala irin na jinin sarauta tsantsa da Allah ya yi masa, sannan
kwarjinin fuskarsa a bayyane yake duk da a hade ta ke tamkar hadarin da ya nausa yayi gabas,
sun nuna cikakken basarakensa, bayeraben usuli mai surki da ruwan jikin fulanin Gombe,
wanda shine ya hadu ya maida shi tamkar ruwa biyun kasar Habasha, wato kamar dan kasar
bakar fata ta Ethiopia, wannan kadai da kallon kyarr da ido da yake mata ne yasa ta gane cewa
ba kowa bane a gabanta; HAMMA PRINCE ne……
Bata bukatar sai wani ya fada mata cewa ya ganeta, ko sai ya gabatar da kansa cewa shi
dinne kafin ta yarda ta bishi. Shima kuma bai ce komai ba, sai kawai ya sunkuya yana daukar
jakunkunan da ta saki a kasa ….
Kafin Prince ya dago daga sunkuyon da yayi don daukar jakunkunanta, Aisha Siddiqah taji
mararta ta cika taf! Da wani fitsarin razana da ke shirin balle mata daga yanzu zuwa kowanne
lokaci, saboda tsabar kidima hade da rudewar da ta sameta lokacin da Prince ya dago manyan
maganansa ya dubeta suka hada ido. Hamma ya wara manyan idanunsa a kanta, kallon da yake mata kamar yana son karanto
dalilin wannan bewilderment din da ya gani a tare da ita.
Ga hawaye na babu gaira babu dalili dake ta tsere a fuskarta wani na korar wani, Aisha ko
damuwa bata yi data sharesu, ga jama’ar dake wucewa suna kallonta. Prince ya dan juya
hagunsa da damansa a sace, kamar yana son ganin kota jawo masa hankalin mutane da
wannan kukan nata, a dauka ko bata son binsa ne, ko batan hanya tayi. Sa’arsa daya sai yaga ba wanda ya basu hankalinsa wucewa kawai ake yi hagu da dama ba
tareda an kula da ita da koke-kokenta ba.
A cikin jikakkun idanunta kadai ya karanci cewa ta ganeshi, domin bayan rudewar ganinsa
daya mamaye idanunta har da kallon sani dana bakunta a gareshi, da kuma kallon rashin sanin
kalmar data dace ta furta masa mai nuna cewa ta gane shi din.
Don duk wata kalma data kama a kan halshenta don furta masa, sai taga bata yi daidai ta
furta masa itaba, har gara ma tayi shiru ta bishi da ido.
Sai kawai taga ya juya dauke da jakukunan nata a hannunsa yayi gaba abinsa, ya kasa furta
kalmar "biyoni" ko "follow me" don bai san yaren data ke ji sosai ba, tsakanin hausa da fillanci
ko ingilishi, ya san dai Nenne tace daga Gombe ta ke, balle yayi mata tsammanin yarbanci.
Kalarta da shigar jikinta da komai nata yafi nuna na ‘yan garinsu Nenne din, wato typical 'yan
matan arewacin Najeriya.
Aisha ta kasa cira kafa tabi bayan Hamma Prince tunda dai bai mata umarnin hakan ba, kada
ta bishi ya zama ta zaqe, ita kuma a rayuwarta ta tsani zaqewa, kawai taga ya dau
jakunkunanta ne yayi gaba. Ba tareda yace mata komai ba.
Har sai da ya dan yi nisa ne ya ankara da cewa ashe bata biyoshi ba. A sannu ya juyo don ya
tabbatar, sai ya ganta kuwa tsaye standstill a inda ya barta, bata ko cira kafa ba.
Prince ya dakata yana tambayar kansa wannan wace irin yarinya ce kamar ‘yar goye Nenne
ta kawo masa?
Domin koda ya juyo gani yayi tana ta share ido bata taho ba din, tana jiran sai ya gaya mata
me ya kamata tayi ita bata san facial expression ba?
To idan kuma bai iya yaren data ke ji bafa, don shi ba wai ya kware da Hausa bane. Bayan
dama cikin haushin an masa katsalandan da zuwanta gareshi ya wuni, alhalin yazo Argentina
ne yin dogon hutun karshen shekara don ya samu ya huta, ya rage stress, yanzu ga rainon 'yar
goye an kawo masa, yo raino mana! Don wannan a shekaru ai bata fice sa’ar Kikinsa ba.
Budewar ido kawai Kiki ta fi ta.
Ko Kiki fama yake da ita har gobe akan shirmen kuruciya, balle wannan mai ruwan ‘yan
fulanin cikin garin Gombe. Dawowa yayi inda take tsaye yana kokarin hadiye fushinsa, don yasa
a ransa cewa ba laifinta bane zuwan da tayi, umarnin iyayensa ta bi.
Prince ya dan hade giran saman idonsa ya cure su, yace.
“Are you waiting for my command? If yes, then follow me!”. (Kina jiran umarnina ne? In haka
ne ki biyo ni toh).
Aisha ba wai bata jin turanci bane ko yaya, tanada turancinta ba laifi tunda ‘yar makaranta ce,
amma wannan karon kwakwalwarta ta kasa fassara turancin nasa, domin sak yake furta shi
kamar na turawan yamma, wato accent din bata saba jin irinsa ba ko yaya ne dai ita dai bata
gane me yace ba. Shikuma Prince sai bai kara cewa komai ba ya juya ya cigaba da tafiya, jinin mulkin ya
motsa, yana cewa a ransa in bata biyoshi wannan karon ba baisan ya zaiyi da ita ba kuma. Don
kuwa ya tabbata ta ji shi saidai in shakiyanci ne kuma abin nata, tunda ya tabbata ba kurma
bace ai ya santa a zuwan da yayi Lagos tana gidansu. Tafiya yake a nitse akan marbles din wajen da jakunkunanta, bai kara waiwayota ba, ya barta
a wurin tana zare jikakken idanunta ta rasa me zata yi takamaimai, don rudewa tasa ta kasa
fassarawa kanta umarninsa ba rashin jin turanci ba.
Kafin ta baiwa kanta shawarar kawai ta bi shi, shi ya fiye mata alkhairi fiyeda cigaba da
tsayuwa a wajennan. Idan ya bace mata cikin mutanen da batasan kowa ba sai shi, tabbas zata
gayawa aya zakinta.
Sai kawai ta cira kafa da hanzari ta bi bayan Prince, harda hadawa da dan gudu-gudu, domin
ya fara yi mata nisa.
Prince sai jin motsin gudun-gudunta da sassarfarta yayi a bayansa, ya dan tsaya har ta
cimmasa, kafin su jera tare zuwa parking lot na filin jirgin, yana gaya mata ta tafi a sannu akan
santsin wurin, kada ya kada ita.
Motar da Prince yake budewa Siddiqah ta bi da kallo domin da fari ta dauka ba mota bace
wani abun ne daban, domin gani tayi murfin ya dage sama da kansa, wato kofar motar ta daga
sama automatically, sannan samanta a yaye yake. (Sport Car, Toyota Supra) duk iyaka dauriyar
Siddiqah da dakewarta na kada ta nuna kauyanci ta kasa karfafawa kanta gwiwar ta shiga
motar nan, ba don komai ba sai don tsoron ganin cewa samanta a bude yake gabadaya.
Idan iska ta daukota tayi wurgi da ita akan titi Ummanta kadai za'a yiwa asara. Shi a gatan
da yake dashi a gobe za'a auro masa gomanta. Goman Siddiqah harda kwarori.
Don haka shiga wannan motar ai tsautsayi ne da ganganci a ganin Siddiqah. Sai ta kara jin
tausayin kanta na wannan rayuwar bakon wuri, da kasaitaccen basaraken bayeraben mijinta
data samu kanta rana daya. Siddiqah ta kasa tsayar da hawayen ta sam.
Prince bai lura da halin da take ciki ba ya sanya jakunkunan nata a bayan motar, sannan ya
bude bangaren direba ya shiga ya zauna, har zuwa lokacin tana tsaye kikam. Shi tunda yake
bai taba sanya mace a gidan gaban mota ya tuka ta ba inka cire Fatima ko Firdausi ko Kiki.
Amma haka ya daure ya mika hannu ya budewa Aisha kofar barinta ta hanyar danna wani
madanni a jikin allon motar, yana lallashin kansa da kansa, yana gaya ma kansa yarinyar nan
taci albarkar DADE dinsa da NENNE. Iyayen da bai hada alfarmar su data kowa.
A komai ma zata cigaba da cin albarkacinsu, tunda sun zabeta gareshi sama da kowacce
mace, har gobe sun kasa gane uzurinsa na bashi da gurbin adana kowacce ‘ya mace a ransa
da cikin rayuwarsa.
Amma Siddiqa ta ki shiga don kauyanci da rashin sabo na shiga gaban mota daga ita sai
katon namiji, gani take motar babu sirri, kowa yana ganinsu, sannan yadda take babu nauyin
nan iska zata iya daukota ta jefota waje in aka fara tafiya.
Prince ya fara zama bored da kauyancin Aisha don kiri-kiri kana iya karantar tsoron motar
take ji a kwayar idonta, bayan kasancewarta cikin takurar zuciya har a kan fuskarta, har ila yau,
kana iya ganin kauyancinta baro-baro. Shi bai ga dalilin kukanta ba ko sau daya, tunda da
yardarta akayi komai, koda yake ya kamata yayi ma kukan nata uzuri, rabuwa da kasar
haihuwarka rana daya da iyayenka bakidaya da danginka zuwa inda baka san kowa ba baka
taba zuwa ba ba wasa bane.
Amma in banda haka ai ba’ayi wa bakunta kuka in ma bakunta ce.
A ganin Prince shi ya dace ya dora hannuwa aka yayi ta rafsa ihu yau ba ita ba, shi da aka
turo masa mace bagatatan, macen da ya riga ya rufe babinta aka sako yau cikin gidansa da
rayuwarsa.
Watakila kuma tana kuka ne kan an aura mata tsoho kamar shi, yarinyarta da ita danya
sharaf, gata nan santaleliya son kowa kin wanda bai samu ba.
Amma ya kamata ta duba cewa bai je inda take da kansa yace yana sonta ba, balle ta yi
kukan auren dole dashi.
Inda wanda zata tuhuma akan hakan to nata iyayen ne da suka yarjewa nasa iyayen, ba
tareda sun ko gan shi ko a hoto ba balle a zahiri.
Ya tuna abinda ya faru jiya. Yana zaman zaman sa Dade ya kira shi a waya. Inda cikin raha
Dade din yace.
“Kehinde, me kake yi daga yau zuwa gobe ne?”
“Dade it's month end ai ka sani (kuma ya kama Asabar din karshen wata), so nafi zama a
gida a duk rana irin wannan, Pareto yayimin lissafin abubuwan da suka kare a gidan, da abincin
dabbobi da sauran bukatunsu, muna checking lafiyarsu kuma, sannan in biya ma'aikata
albashinsu na wata, sannan muna yin lissafin abincin Horses da zamu ajiye na tsayin wata
guda. So I will be busy the whole day, daga yau zuwa goben har in samu in kammala da duk
wannan”.
Cikin tsokana Dade yace "kawai kace min “The Prince and his ranch activities dai, to Allah
ya taimaka, inaso yanzu ka ajiye komai ka sa a shiryawa Aisha-Siddiqah dakin da zaka
sauketa, jirginsu ya taso zuwa Argentina yanzu daga Lagos, zasu sauka a (Ezieza International
Airport Bueunos Aires) nan da awanni ashirin da biyu”. Saida ya baiwa kwakwalwarsa aiki na wucin gadi yana son gane me Dade ke magana akai,
kuma wacece Aisha Siddiqa din, har saida ya ga cewa ya gaza wajen ganewar ya tambaya
cikin girmamawa mai hade da mamaki.
“Dade wacece Siddiqah kuma wajen wa zata zo?”
Sai Dade ya juya harshe zuwa (native language) yana masa bayani don dai Prince ya yarda
cewa seriously yake magana dashi yanzu. Cikin harshen Yarbanci yace ma Prince din.