Showing 39001 words to 42000 words out of 46523 words

Chapter 14 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf

shanun Prince ta ke shiga inda ake tatsa (milking) mai kula da shanun yana mata
bayanin madarar sayarwa kamfanonin sarrafa madara suke yi. Pareto ya sha mamakin sabon
da ya ga ya shiga tsakanin Siddiqag da Saheeb cikin dan lokaci. Sosai abin ya burge shi. A
rashin abin yi Siddiqah ta mayar da Ranch din dawakan wajen shakatawarta da debe kewa da
shan iskarta.
Wani zubin kuma ta tsaya kallon dramarsu shi da Pareto. Daga irin dramar da ake bugawa
tsakanin Saheeb da Breeder din nasa Pareto Siddiqa ta ji doki Saheeb ya kara shiga ranta.
Koyaushe ta zo gun Saheeb sukan gaisa da Pareto ta zauna a kujera a gefe tana kallon yadda
al’amuransu ke gudana tsakanin Saheeb da mai kula da shi, tamkar saheeb wani dabba ne mai
tarin hikima da baiwa, duk mai kula da shi ya sanshi farin sani.
Kadan-kadan Saheeb ya fara gane fuskar Siddiqah, watarana cikin dari-dari ta kai hannu ta
fara shafa jikinsa da kyakkyawan gashin wuyansa, har Pareto ya tsorata ya zo da sauri zai
hanata, sanin halin Saheeb da yayi, na ba ya barin kowa ya zo inda yake bai yi harbi ba.
Amma abin mamaki sai ya ga Saheeb ya kwantar mata da kai kasa tana shafa shi yana dada
kwantar da kai.
A haka a haka har karambani ya sa rannan ta ce da Pareto tana so ta hau bayan dokin.
Pareto ya gaya mata cewa ba ya bari a hau bayanshi in ba mamallakinshi ba. zaiyi tutsu a ita.
Aisha ta dage cewa she wants to give it a try. Dole Pareto ya kyale ta ya saka mata sirdi ta
hau Saheeb, ya rike mata linzami suka shiga zagayawa cikin Ranch din. Sune har kofar fita
‘ranch’ da wajen BQ din Pareto, daga nan suka juyo suka dawo stable dinsa. Siddiqah ta sauko
lafiya. Sai hakan yasa ta kara sabawa da Saheeb sosai, kullum nan ne wajen wuninta. Kusan ba ta
da damuwa a yanzu, don Saheeb ya debe mata kewar kowa da komai.
Siddiqah na nan tana fama da Saheeb, Prince yana Ilorin jikin Kakansa Sarki Abdulrashed
Akanni ya rikice.
Likitoci har uku ne ke tsaye a kansa a gidansa na masarautar Ilorin, tare da ‘ya’yansa (Ten
Akannis). Ciwon cikin wuni uku daya firgita zuri’ar Sarki Abdurrasheed gabadaya. Prince kwana
yake tare da Kakansa a turakarsa don ko matansa na aure basa bari dashi.
Yau da dare jikin nasa da sauki sosai, don an masa allurar barci, amma cikin dare ya farka ya
ga Prince a zaune a gefen kansa yana gyangyadi, lokacin kowa ya je ya kwanta.
Sarki Abdurrasheed Dan Abdullateef Akanni, ya ce da jikan nasa Prince.
“Kehinde! Barci kake yi a zaune?”
Kamar cikin mafarki ya ji muryar Kakan na kiran sunansa, tuni ya wartsake ya matso daidai

kansa. Sarkin ya kamo hannunsa ya rike cikin nasa, ya ce cikin harshen yarbanci, “Kehinde
Jikan Sarkin Ilorin, jika mafi soyuwa a gareni, me yasa baka zo min tare da matarka na hada ku
na sa muku albarka ba? Ina fatan zuwa yanzu komai ya daidaita tsakaninku yadda muke fata?
Ka karbi zabin mahaifiyarka da hannu bibbiyu? Nan bada jimawa ba zaka ajiye min mai
sunana? Wanda zai gaji gidannan tunda ba kwa son gadona kai da Ubanka?”
Prince rasa amsar da zai baiwa Emir ya yi, sai cewa yayi cikin yarbanci “tana lafiya Allah ya
ja zamaninka, na baro ta lafiya cikin koshin lafiya, kuma maimartaba na dade da karbar matar
nan da kuka zaba min da godiya da yabawa. Tana da attributes na matan kwarai da ban san su
a tare da ‘yammatan wannan zamanin ba”. Sarki Abdulrasheed ya gyada kai cikin gamsuwa da jin dadi, sai kuma yace.
“A yadda nasan ka kullaci mata, da yadda giyar mulki ke hanaka sakewa, ina da yakinin har
zuwa yanzu ba ka dora mata idda ba. Ko Qur’ani zan dafa akan ba ka dabbaqa sunnarka ba
har yau, me yasa? Donni in za’a shekara ana cewa ba ka da lafiyar aure ba zan taba yarda ba,
na san lafiyarka kalau, baka samu wadda kake so bane, kuma bazaka iya hada jiki da matar da
baka so ba shine babban dalili, tunda na san yaya halittar sarakuna take a kan matan da suke
so. Kada ka manta na so Kakarku Murjanatu kamar raina. A lokacin da take raye ban taba
zaton zan tsufa ba, kullum sabuwar samartaka take kara min saboda soyayya, ina gaya maka
kayi gaggawar dabbaqa sunnarka kafin ranar da wankin hula zai kaika dare, wato ranar da zata
gane tana son ka tayi maka bore ta hana ka kanta”.
Prince ya hau zufa daga goshi, ga kunya da ta kama shi. Ya kasa cewa komai. Amma da zai
iya da yace da Kakansa sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba, amma ya fara jin
sauyi a zuciyarsa da gangar jikinsa sosai a kan Siddiqah.
Sun kwana suna hira shi da Kakansa abin gwanin sha’awa, inda ya sa shi yi masa alkawarin
zai kula da aurensa, zai kuma kula da Siddiqah kwatankwacin yadda Dade yake kula da Nenne.
Ya kuma tabbatarwa Kakan nashi cewa shi lafiyarsa kalau ba kamar yadda mutane ke kuskuren
fahimta ba. Yana jiran ya ga yadda Allah zai yi dasu ne shi da Siddiqah. Emir kuma ya ce masa “ka yi amfani da dama a lokacin da ta ke hannunka”.
Har aka kira asubahi idonsu biyu, Kawunsa Malami Ubandoma, da mai bi masa Mufti of Ilorin
suna daga shigifar farko a nan suka kwana, Prince ne kadai ya kwana tare dashi da asubah
yayi masa alwallah yayi sallar asubahi daga kwance, sai ya ce da Prince yasa masa bargo
sanyi yake ji. Kuma ya kunna masa Suratul Mulk a radiyonsa. Prince yayi duk yadda Kakan ya ce cike da kauna da kulawa, sannan shi kuma ya tada tashi
sallar.
A nan inda ya yi sallah kasancewar ya yi kwanan zaune barci mai nauyi ya yi awon gaba da
shi.
Har gari ya soma haske Abdurrasheed bai farka ba. Ashe sallamarshi kenan da Kakan nasa
Emir Abdurrasheed Akanni.
Abinda ya faru yana barci shine Kawunsa Mufti ya shigo kawo karin kumallon Sarki, a lokacin
da aka kawo daga cikin gida, shi ya gane cewa ran Emir ya yi kaura zuwa ga mahaliccinsa.
Sai ya tashi Prince daga barci ya yi masa nuni da abin dake faruwa. Prince ya isa ga Emir ya
tallafo kansa ya tabbatar wannan ruhin da ya rayu shekaru sama da shekaru arba’in da biyu
yana lelensa yana kula dashi yana kyautatawa rayuwarsa yau babu shi. He is more than
shocked. Don ko kusa bai kawo wa Emir mutuwa yanzu ba, don ya saba ciwo fiye da wannan

ma ya girgije ya tashi.
Shi ya san ya yi rashin da ko iyayensa ne suka fadi yau suka mutu suka barshi iyakar kukan
da zai yi kenan.
A wayewar garin ranar labarin mutuwar sarkin Ilorin, Sarki Abdulrasheed Akanni, ta riski
al’ummar kasar Najeriya, labarin yayi tambari ya riski duk wani jininsa, kafin kace meye wannan
kafatanin zuri’arsa na garuruwan Najeriya da wajenta sau bubbugowa suke yi Ilorin. Akannis
sun gigice sun dimauce baki daya, amma babu wanda ya kai Prince AbdulRasheed gigicewa,
su Nenne ma da su Princess Fatima, duk a ranar suka taho Ilorin, Taiwo da ke nan Ilorin kuma
akan idonta aka yi wa sarki suttura, duk a ranar suka taho masarautar, haka dukkan ‘ya’ya da
jikoki na nesa da na kusa suka hallara. Sun dade basu shiga halin dimauta da gigita irin na
wannan lokacin ba.
**** **** ****
Tun Siddiqah na zuba idon ganin Prince ya dawo a satinsa na biyu da tafiya har ya zamanto
ta fara damuwa da rashin dawowar tasa, duk da ba wai shiri suke yi ba, ba kuma shakuwa ce ta
sosai a tsakaninsu ba, amma mutum a cikin gida rahma ne. Kai ita yanzu ta fara jin tsoron
zaman gidan ma, daga ita sai Dawakai da dabbobi. Ta yi da na sanin rashin yin bore na sai ta
bishi kamar yadda Kiki ta ke so ta dinga yi, wato ko’ina Hamma za shi ya tafi tare da Aisha.
Amma cikin hudubobin Kiki na arzikin wanne ta dauka? Kusan a inda ta bata su, tun tafiyarta
a nan ta ajiye mata su saboda taurin kanta. Yanzu ga shi rashin Hamma a gidan ya dame ta,
musamman da ko sau daya bai kirata ba.
Sati biyu kenan da tafiyar Hamma Ilorin, ranar da aka yi rasuwar Nenne ta kirata, nan ta gaya
mata rasuwar Kakan nasu Fatima. Sai kuma Kiki ma ta kirata suna gama magana da Nenne.
Kiki tana cikin damuwa domin makarantarsu ba za ta bata excuse din zuwa gida ba kasancewar
ba ta jima da dawowa ba. Nenne again a washegarin ranar rasuwar ta sake kiranta, ta ce, ta kira Abdulrasheed ta yi
masa ta’aziyya. Domin kuwa shi aka yiwa mutuwa a kafatanin zuri’ar Akanni, ta gaya mata babu
wanda ya kaishi kusanci da shakuwa da Sarkin. Kuma babu wanda Emir yake girmama
sha’aninsa da kaunarsa cikin jikokinsa kamar Prince din, wadanda a kiyasce jikokin na Emir
Abdulrasheed Akanni sun tasar ma (82).
Nan fa ake yinta! Don Siddiqah da Prince ya kirata bayan saukarsa a Ilorin, ya gaya mata
saukarsa lafiya ya kuma tambayi yadda take coping tace masa batada matsala, ashe lokacin ko
lambar Prince din bata yi saving cikin wayarta ba, tsabar yadda bata daukeshi matsayin mijinta
ba face Yayanta/Babanta, wannan abun kunya da me yayi kama? Taji kunya sosai yau, sannan da kunya ta tambayi Nenne wai lambar mijin da suke kwana
gida daya. Har suka yi sallama da Nenne jikinta a salube yake, bayan ta sake yi mata tata
ta’aziyyar, Nenne kuma ta kuma hadata da Dade shima tayi masa, da Princess Firdausi da
Princess Fatima, ba ta iya ta tambaye ta lambar Hamma ba. Me Nenne za ta dauke ta? A yau sai ta ga cewa ma a gabadaya zamansu wanda ya ki samun daidaito da fahimtar juna
har lokacin ba laifin Hamma Prince bane, laifin ta ne. Saboda Hamma yayi iya kokarinsa da ya
karbeta a matsayinsa na wanda aka yiwa auren dole, ita da take mace ita ya kamata ta canza
shi zuwa yadda iyayensa sukayi fata, suka kuma dora burin hakan a wuyanta saboda
kyakkyawan zaton da suke dashi a kanta. Amma me ta tsinanawa Hamma na kyautatawa tun
zuwanta? Hasalima bata dauki auren nasu a matsayin aure ba sai zaman biyayya.

Bata shiga sha’aninsa yadda ya dace tayi, ba abinda Kiki bata ce mata ba wanda shi zai sa
ta kusance shi su shaku da juna, ba abinda bata koya mata ba cikin dabarun abinda Bayeraben
miji yake so daga matarsa, wanda zai sa ta kama zuciyar Hamma nan da nan, haka
mahaifiyarsa ta dade tana bata training akan zama da shi. Amma a ciki wanne ta aikata baka da
zuci?
A zahirin gaskiya bata cika expectations din iyayenshi a kanta ba, da yardar da suka bata
dari bisa dari na zata iya, zata kawo kyakkyawan canji a cikin bahaguwar rayuwarsa.
Cikin watannin data yi tare da Hamma Abdulrasheed wane abun ku zo ku gani ta kulla a
zaman nasu, wanda in aka tambayeta progress na zaman su zata iya adarwa da babbar
murya?
Idan da ta bi shawarwarin da Kiki ta bata, duk da ake cewa Kiki bata da nutsuwa, in aka
dauka a tsanake aka dubasu za’a ga cewa shawarwari ne masu kyau da za su taimaka a
rayuwar aurenta. Tunda auren nan ya riga ya zama rubutacce daga Allah! Wanda babu yadda
za ta yi ta guje wa kaddarar kasancewarta mata ga Prince Abdulrasheed jikan marigayin sarkin
na yarbawa.
​ **** **** ****
Daga wannan lokacin Siddiqah ta yi kyakkyawan kudiri a zuciyarta na in Prince ya dawo daga
ranar zata canza irin zaman da suke yi, zuwa zama mai armashi da ma’ana koda bazai bata
hadin kai ba. ta fannin ta zata yi kokarin sauke nauyin duk da iyayensa suka dora mata, sama
da komai Ubangiji ma ya dora mata. Zata koma kyautata aurenta dashi iyakar kyautatawa.
Kiki ta kira a lokacin da take tsaka da wannan juyayin, Kiki na cikin alhinin babban rashin da
suka yi don itama Emir yana sonta albarkacin son da Abdulrasheed ke mata.
Yau sai ta ji hatta Kiki din abin kunya ne babba ta tambaye ta lambar Hamma. Amma har
gara ta murje ido ta tambayi Kiki, a kan dai ta tambayi Nenne.
“Kiki am, nace ba, ko zaki ba ni lambar Hamma don Allah, ina cikin damuwa, tunda ya tafi ya
kirani sau daya bai kara kira na ba, ni ma kuma nayi wani kuskure da ban kira shi ba, na dauka
nayi saving no. din tun a lokacin, ai yanzu na duba ban ganta ba, a tsammanina zai kira again,
sai inyi saving to amma yanayin da yake ciki nasan shi ya hana bai kira din ba”. Kiki was shocked da wannan ganganci zata ce ko childishness na Aisha. Ta ce,
“Aisha me ki ke cewa? Sati biyu ba ki ji motsin mijinki ba, kuma ba ki kira shi ba ke? Sannan
ba ki da digits dinshi a wayarki?
To kenan ashe duk shawarwarin da na bata lokacina na baki ma babu wanda ki ka dauka
kika gudanar kenan?
Aisha me ke damunki har haka na tabbata ba kiyayya bace. To menene? Kin san girman
hakkin Uncle AK da ke wuyanki kuwa? Haba Aisha, kankantar shekaru da rashin soyayya ba
hauka ba ne, domin bayan dukkansu akwai abin da ya kamata mace ta yi la’akari da shi a
zaman aure, shine sanin yakamata da sanin girman hakkin mijin duk da Allah ya rubuta shi ne
mijinta”.
Jikin Aisha duk ya idasa macewa, dama kuma ko kafin ta kira Kiki Rukayyat, duk ta yi
wadannan hasashen itama, Kiki ta ce,
“Lallai ne yanzu Uncle ke bukatar kulawarki da soyayyarki Aisha. Ya yi rashin masoyin da bai
da kamarsa”.

Nan Kiki ta shiga bai wa Aisha labarin irin kaunar da ke tsakanin Sarki da Hamma. Ta gaya
mata hatta dokinsa Saheeb data gani yana matukar so, da daya matashin ‘Criollo Horse’ din,
duk kyauta ce ta musamman daga Emir zuwa gare shi. Abubuwa da yawa da bata sani ba a
kan rayuwar Prince, a ranar yau duk ta ji su a bakin Kiki. Aisha daga karshe kashe wayar tayi
tun kafin suyi sallama da Kiki, saboda zuciyarta tayi rauni, tausayin Hamma Abdulrasheed
Prince, hade da wani sabon ni’imtaccen feeling da ke sauka a kasan ranta a kansa.
Kiki ta turo mata lambobin ta hanyar text message, ta kara da turo mata sakon text.
“Text him. And call him tonight’.
A take ta rubuta sakon text ta tura wa Prince. Sakon ya kunshi ta’aziyyah zallah a kan rashin
da ya yi, da fatan Allah ya bashi hakuri da danganar musulunci, ya kuma jikan Maimartaba
Sarki.
A kasan sakonta ta rubuta sunanta;
“Aisha-Siddiqah Yunus”.
Prince bai bude wayarsa ba sai da ya zo kwanciya barci, bayan fitar Taiwo kenan daga
masaukinsa, yau ne aka yi sadakar bakwai, kuma har ya soma shirin komawa Argentina.
Yanzu Taiwo ta bar masaukinsa tana masa wasu maganganu da suka ba shi haushi da
mamaki, ko dai Taiwo ta manta irin rashin da yayi ne da ta zo tana masa wannan shirmen?
“Kehinde, yanzu saboda Allah don zubar da aji da barar da kima, yarinyar nan mai kama da
kazar mayu ka dau hoto da ita ka dora a status? Ka san iya mutanen da zasu bude? Me kake
nufi da kalaman daka rubuta a kanta? Abu daya ma yanzu ni nake son sani, tunda aka tura
maka ita ‘have you ever touched her?” Dan bude idanu ya yi a hankali wadanda duk sun kankance, yana kallon ‘yar uwar
tagwaitakarsa Taiwo Akanni, his very own twin sister Taiwo. Sai ya rasa amsar da zai bata,
domin tambayarta ta fi kama da crossing limit da shiga personal marital affair dinsa.
Taiwo ta ce, “Don in baka tabata ba in ba ka shawarar amfani da kwararon roba, tunda naga
alama ta fara samo kanka, na san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login