Showing 42001 words to 45000 words out of 46523 words
Chapter 15 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf
it will not be easy for you to be using condoms, yadda ka
dauki lokacin nan ba aure, ace ka daure ka iya hakan. Amma Kahinde ka sani ba ta isa mu
hada zuri’a da ita ba, make her your sex slave kawai, Allah ya gani ba zan taba son yaran da za
ta haifa ba”.
Abdulrasheed sai ya bude idanunsa gaba daya yana kallon ‘yar uwar tasa da mamaki da
tsoro. Da kyar ya iya motsa bakinsa da yayi masa nauyi, don magana ma wahala ta ke masa
tun bayan rashin Emir, yace,
“Maman Kiki, bana son yadda ki ke min maganarta. Alaqata da ke daban, wadda ke
tsakanina da ita daban”.
Ya hadiyi wani abu da kyar da ya tsaya masa a makoshi, a dalilin dacin da ke zuciyarsa na
rashin Kakansa, ya dubi Taiwo sosai ya kauda kunya yadda itama ta iya kauda kunya ta yi
masa wannan zancen. Yace.
“Shin Maman Kiki in tambayeki please. Zaman zina nake yi da ita da zan yi amfani da
kwararon roba a kanta? Ko Concubine (kwarkwara) aka kawo min itaba matar aure uwargida ba
I will never do this. Kamar na wofintar da umarnin Nenne da Dade ne.
Kin ce bazaki taba son ‘ya’yan dana haifa da ita ba don kawai diyar talakawa ce. Ni kuwa kin
ga ko da ‘Kare’ ki ka haifi su Kiki bama mutum dan Adam mai kima ba, banida kamar su, ba zan
taba kin son ‘ya’yan da na tabbatar daga jikinki suka fito ba”.
Da wannan Prince ya maida bakinshi ya dinke. Ya ki kara kallonta. Ya maida hankali ga
kunna wayarsa dake kashe tun safe.
Taiwo sai ta ji kamar bakar magana ce Kehinde yau ya gaya mata a kan mace. Macenma
wannan mara aji irin Siddiqah, wadda ba diyar kowa ba.
Wato Kehinde ya fara sanin dadin mace har ya dube ta yau ya gaya mata baqar magana irin
haka akan Siddiqah?
A take Taiwo taji ta kara tsanar matar dan uwanta. Kwafa ta yi ta mike tana cewa,
“Kehinde maida wukar I came in peace in dai akan ‘yar Malam Shehu ne. Abinda ya kawo ni
gareka ma ba zancenta bane rabon in samu rabon bakar magana ne.
Inata so in gaya maka tuntuni cewa I met Hasina coincidently. She explained to me all what
happened between she and Tukumbo. She made a mistake and she realized it. She is haunted.
How much she hurt you had been haunting her. Tana ta neman yadda za ta ba ka hakuri but to
no avail. Daga baya ta yi aure har sau biyu a UK ta fito, ta ce min ta tabbata alhakinka ne ya
hana ta zaman aure. Ina rokonka ka yafe mata, ta ci albarkacina”.
Prince ya ce a dan hassale,
“Maman Kiki ba ni da say a kan wannan batun da ki ka zo da shi, sai dai in ce, please!
Please!! Don’t mention that bitch again to me, idan kin yafe mata is okay ni ma na yafe, domin
kada ki manta abin da ya yi Kehinde shi ya yi Taiwo”.
Da sauri Taiwo ta ce, “A da ba… kafin ka samu abun hutawa, amma a yanzu kana neman
canzawa ne completely daga Kehinde dina”.
Kehinde din sai ya yi shiru har Taiwo ta yi tsaki ta wuce yana mamaki. Me ya shiga kan Taiwo
dinsa ne? Tunda aka yi masa auren nan ta ke acting kamar ta samu tabin hankali a kan
matarsa.
Ya yi nafila raka’a biyu ya sha zazzafan chamomile tea, ya kunna wayarsa kenan sai ga
sakon Siddiqah ya shigo.
Ya karanta ya maimaita, sai ya samu kansa da tura mata reply da kalmar, ‘thank you’, a fili
kuma ita ma haushi ta bashi. Ko da ya san ba auren so aka yi musu ba amma fisabilillah yana
iya kokarinsa wajen kyautata mata a gidansa.
Bai tsangwame ta ba, bai kuma rage ta da komai ba. Amma ace ya yi tafiya irin haka har
tsahon sati biyu Siddiqah ko sau daya ba ta kira shi ba, sai da ta ji ya rasa Emir?
Saboda shi Prince a mulki irin nasa matarsa ce ya kamata ta dinga kiransa don yana son
respect mai yawa daga matarsa.
Kusan wannan dabi’a ce ta mazan Yoruba, suna da tsananin son respect, musamman daga
matan su. Musamman a wannan lokacin da yake ganin jinyar Kakansa ya zo, ita ya kamata ta
dinga kiransa don jin ya jikin Maimartaba. Amma ba ta yi hakan ba sai yanzu?
Bai san cewa ita Siddiqah ko digits dinsa bata yi saving a wayarta ba, saboda bata dauki
auren nasu da wani alkibla a baya ba. Bayan zama na biyayya.
Amsar da Hamma ya bata nan take, duk da a gajarce ne, showing nothing, shi ya ba ta
kwarin gwiwar kiransa.
Kirjinta da zuciyarta baki daya suna harbawa a cikin kirjinta, don yau ji ta ke Hamma na
samun wani special reception a gunta, data dangata shi da tausayinsa.
Yana kallon lambobin Siddiqah suna shigowa da mamakin kiran kamar ta san me yake
sakawa a ransa, shi yana da lambobinta ai, kasancewar layin da wayar duka nashi ne a baya.
Kuma daya bata din, sai ya yi saving da sunanta, sunan da zuciyarsa ta ga damar bata a
lokacin, wato “Baby”, don a wurinsa Siddiqah jaririya ce kamar yadda Kiki take a idanunsa.
Sai da kiran ya yi dab da katsewa Prince ya amsa,
Aisha ta tausasa murya tace.
“Assalamu alaikum!”.
Sai kuma ta yi shiru tana shirya abin fadi, don duk wata hikima da ta ke da ita a lokacin
subucewa ta yi. Prince ya ciccibe ta, ta hanyar amsa sallamarta.
Sai ta samu kwarin gwiwa ta yi masa ta’aziyya ta fatar baki. Hamma ya yi godiya sannan ta
ce a raunane,
“Uncle yaushe za ka dawo?”
Shi kuma ya amsa, “Ranar dana tashi daga Uncle dinki!”.
Siddiqah sai ta yi wani murmushi mai kyau kamar Hamma yana ganinta. Yace “Ko ba haka
kika ce ba, kallon kamar Babanki kike min ko Aishah?” Girgiza kai kawai tayi kamar yana
kallonta amma ta kasa amsawa. Prince yace “To yaya gidan ince ko babu matsala?” “Babu
matsala Hamma, gidan kawai yayi tsit da baka nan babu dadi”. “To ko in aiko miki ticket ki taho
duk da gashi ina shirin komowa?” “Tunda zaka dawo soon ai bai kamata kuma in taho ba, zan yi
hakuri harka dawo”. “Yaushe har kika damu da presence dina ai ba wani banbanci da ina nan
da bana nan a gunki Aisha, ba kya sakin jiki dani tunda Kiki ta koma”. Aisha taji wani irin dadi a
ranta, (something more of excitement). Hamma ashe yana yinta, koda ita bata damu dashi ba.
Murmushi Aisha tayi ta sake rike kan wayarta sosai a kunnenta, tace “ina kara yi maka
ta’aziyya Hamma Abdul. A gaidasu Maman Kiki”.
Prince ya amsa da cewa, “Za ta ji, yanzu ta bar nan, ina fatan idan na dawo inga canji, kuma
duk abin da kike so Pareto was there to help, he is always at your service”.
A tare suka ajiye wayar, Prince na ajiyar zuciya ya ce a ransa, ita Aunty Murja din tana nan
tana binki da mummunan kulli, ke kina cewa a gaishe ta Aisha.
Tana fatan kada a hada zuri’a da ke, ‘yar mallam shehu. Tana neman kariya daga hada jini da
ni, don matata bata yi daidai da ra’ayinta ba.
In ya ce bai ji zafin abin da Taiwo ta fada ba ya yi karya, amma ya zai yi? Dole ya hadiye
tunda Taiwo ce. His very own twin, his one and only Taiwo.
Ranar lahadi Prince Abdulrasheed ya dawo gidansa, Siddiqah tana can wajen Doki Saheeb,
bata da masaniyar dawowarsa.
Ta kama sirdi ta haye, shi kuma ya soma tafiya da ita a hankali, tana tafe kan Saheeb tana
rangaji irin na tafiyar doki a hankali zuwa karshen ranch. Kawai sai Saheeb ya hango shi daga
nesa ya harde hannuwa a kirji yana kallonsu.
Saheeb ya fara kokarin gudu da haniniya har yana neman jefo Siddiqah, da karfi ta ce,
“Saheeb!” Dan saura kadan ya jefo ta kasa, amma tsawar nan da ta yi masa ya sa ya koma
cikin nutsuwarsa, ya fasa fudun ya kuma daina haniniyar.
Abun ya kashe Prince da mamaki daga tsaye, ta yaya Siddiqah ta yi ta samo kan Saheeb
cikin sati biyu haka, har da bashi umarni kuma ya bi? The Prince was dumb-founded. At the
same time, abin ya burge shi matuka gaya.
Sai lokacin Siddiqah ta ankara da Hamma, fuskarta ta haskaka da ganinsa, Hamma ya rame
sosai a idonta, ta jefa masa murmushi (full of innocence), a idonsa she looks pure and angelic,
ta kada linzamin Saheeb suna tahowa inda yake tsaye. Murmushinta na kara fadada, domin
harr anta taji dadin ganinsa, tace “Uncle shine baka gayamin yau zaka dawo ba? Sannu da
zuwa Hamma Abdul! Sannu da hanya Uncle!”
Cikin dan lokacin nan zuciyar Prince ta shiga wani yanayi na raguwar radadi, ya dan mance
da zugin da zuciyarsa keyi na gajeren lokaci, ganinta kawai kuma akan Saheeb ya zama tamkar
haske maganin duhun da zuciyarsa ke ciki, ya samu kansa da takowa domin ya cimmasu.
Suka game a tsakiyar filin wajen, hamma yace “ashe haka kike da karambani? Idan kika fado
fa?” Aisha tayi murmushi kawai tace “sannu da dawowa” tana kokarin saukowa daga bayan
Saheeb, Hamma ya shagala da kallonta ya mika mata hannu ta kama cikin jin nauyi ya kama
kugunta ta sauko, sai lokacin yaga takalmin sa na hawa Doki ne a kafarta (chukka boots) duk
da ya mata yawa.
Bayan ta sauko Hamma ya tsaya yana kallonta tana dan manne a jikinsa, Siddiqah ta
sunkuyar da kai duk ta rikice ta kasa kallon idon Prince, haka ta kasa gasgata abubuwanda ke
faruwa yau.
Ganin rikicewar data yi dinne yasa Hamma ya cikata, yana dan tsokanarta da cewa.
“Inye Siddiqah, yaushe na baki takalmin da kika dauka mun, haaa!” Siddiqah na murmushi
kamar ta nitse a haka suka jera a tare yana rike da hannunta suka shige cikin gidan.
A sitting room ya zauna yana nazarin yadda Siddiqah ta gyara shi, ta canza zaman kujerun
zuwa yadda ya fi yi mata daidai, ga kamshin turaren wuta na tashi mai dadin kamshi.
Siddiqah ta tsugunna tana masa barka da zuwa tare da sake yi masa ta’aziyya, ya tambaye
ta ko ina Pareto? Ta ce, ta aike shi cefane.
Daga haka ya shige dakinsa bai kara fitowa ba har la’asar. Siddiqa ita kadai a kitchen tana
girki duk ta bi ta damu da rashin jin motsinsa. Ganin Hamma yau ko abinci bai nema ba, sannan
ba ta kara jin motsinsa ba har yamma.
Don sai yanzu ne ma bayan ya dawo ya kadaice a dakinsa. Mutuwar Kakan ta soma taba
shi, rayuwarsa da Emir ta dinga dawo masa filla-filla tun lokacin da yake yaro, da moments
dinsu tare, da karfin soyayyar Emir a gare shi.
Ya tabbata ya yi rashi irin wanda ba zai taba mayar da shi ba. Prince sai yau yake kuka da
hawayensa tun bayan rasuwar Sarki Abdulrasheed.
Domin sai yau ne ya samu kadaici, a can gida Ilorin koyaushe yana tare da jama’a, ga Dade
da Uncles dinsa da basa bari ya bar kusa da su sai lokacin barci.
Idan ma ya shiga barci Taiwo na biyo shi ne ta taya shi hira, kasancewar tunda aka yi
rasuwar tana nan main house dinsu ba ta koma gidanta ba. Toufeeq ma ya zo ya musu gaisuwa
ya koma UK.
Da taji shirun nasa yayi yawa ta kasa daurewa ta isa ga kofar bedroom din nasa tana
knocking a hankali. Prince ya share hawayensa da hankacif yace “Yes!”
Sai Siddiqah ta bude kofar ta shiga a hankali, karonta na farko da shigowa masterbedroom
din na Prince, dakin ya tsaru iya tsaruwa, komai ya zauna a muhallinsa cikin tsari mai ban
sha’awa, ga kamshin turarukan Prince da suka hadu suka cakude dana room freshner. Aisha
taji wata irin nutsuwa na shigarta karo na farko da shigarta turakar mijinta, shima kuma Hamma
ganin Siddiqa yau a dakinsa sai wani bangare na zuciyarsa yaji contentment na cewa yau gashi
ga macen Sunnah a dakin barcinsa, lallai da gaske yanzu ya yarda yanzu an masa aure.
Kallo daya Aisha tayi masa ta gane kuka Hamma yake yi, taji wani irin damuwa ya tsirga a
ranta, da kyar ta daure tace dashi cike da kulawa.
“Uncle na ji ka shiru ne, are you okay?”
Ya sunkuyar da kai, jin wasu sabbin hawayen na kara fito masa bayan wadanda ya share
kafin shigowarta, amma yayi kokarin hadiyesu. Yace “No Aisha. But Alhamdulillah!”.
Aisha ta sake yiwa Hamma sabuwar ta’aziyya, ta bashi hakuri, Prince yana mai yabawa da
hankalin Aisha a ransa yace “ya gode”.
Aisha tace “don Allah ka dai na kuka haka Uncle, in babba na kuka abun yana tada mun
hankali sosai”, itama tayi narai-narai da ido nata hawayen na shirin zubowa.
Abin ma sai yasa shi dariya, yace “to na dena, jeki cigaba da abinda kikeyi”.
Tace “tau abinci ne nake maka dama, bansan yau zaka dawo ba, ai zaka ci don Allah ko?”
Aisha tayi maganar a shagwabe da zuciyarta daya, bata ma san tayi ba.
Hamma yace “tohh!”.
Sai ta fita ta saka karatun Al’qurani a falon Suratul Noor, tana girkinta tana sauraron karatun
har ta gama. Lokacin taji ana kiran Magriba, shiru har lokacin Hamma bai fito ba, ta sake isa ga
kofarsa ta sake yin knocking, sai taji shiru, ta bude a hankali ta shiga sai ta ganshi akan sallaya
yana barci. Aisha tayi tsaye a kansa yau tana karema Uncle kallo. “A beautiful man, with a
beautiful heart” ta fada a ranta.
Bata san lokacin da Hamma ya bude ido ba, sai muryarsa taji yana fadin “Aisha, yaya dai
kiketa kallona?” Taji kunya sosai ta juya masa baya, tace “anyi maghrib ne, na jika shiru nazo in
ga ko lafiya?” Yace “subhanallah!” sai yace mata “bari nayi wanka nayi sallah ina zuwa”. Aisha
tace “toh, na gama abinci ma, inyi setting table yanzu?” Hamma yace “no, jeki yi sallah ki gama,
nima wanka zanyi inyi sallah tukunna”.
To sai ta koma dakinta ta shiga wanka, ta fito ta saka ‘lounge wear pink and white’ wando da
riga sakakku da basu kama jikinta ba, wandon kamar pallazo amma mai taushi, samfurin ‘duvet
days collection’ sunbi jikinta sun kwanta, Aisha ta saka ‘plush slipper’ na cikin gida shima pink ta
zama tamkar angel don kyau, ta shafa turare mai sanyin kamshi, daman tayi jan lalle a yan
yatsunta, ga gashinnan bata dade da wanke shi da steaming dinsa ba, Aisha ta jima tana shan
SABAYA da Ummanta ta bata lokacin da taje gida Gombe sallama so Aisha ta kara cikowa
sosai. Saida tayi sallah magrib da isha da shaf’I da wutr sannan ta fito falon, taje ta shirya table
ta sake kunna oil burner na turare. Ga sanyin AC ya hade dana turaren, taje ta zauna akan 3
seater tana kallon PoloLine TV.
Nenne kamar ta san halin da Prince ke ciki a daidai wannan lokacin sai ta kira Siddiqa.
Siddiqah ta amsa kiran Nenne alhalin ta saka wayar a handsfree. Da damuwa a muryarta
Nenne ta ce,
“Aisha ya kuke? Ya Hamma din?” “Nenne yana kokari ba laifi” “yaci abinci?” “na dai gama
masa pounded yam (Iyan) da Afang Soup shinake jira ya idar da sallah ya fito” Nenne tasa
mata albarka, tace “ki kasance tare da Hammanku a wannan lokacin kin ji, yana bukatar mai
karfafa shi da ba shi kwarin gwiwa. Na san halinsa sai yanzu ne zai soma nashi ‘mourning’ din.
Ki tausashe shi, kin san yadda yake da Kakan nasa”.
Aisha cikin jin kunya ta amsawa Nenne da cewa “Insha Allah Nenne zan kula da Hamma”.
Bayan da idonta har lokacin bata ga Hamma din yanada alamar fitowa ba, yau dai Hamma
tunda ya sauka ko Ranch dinsa bai shiga ba, ko kula Dawakan nasa bai yi ba tunda ya kama
mata ta sauko daga Saheeb, komai ya fita kansa saboda rashin Sarki. Aisha bata kula da fitowarsa ba harma yana jinsu itada Nenne, daidai sanda Nenne ke fadin,
“to ko zaki bishi da abincin