Showing 27001 words to 30000 words out of 46523 words

Chapter 10 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf

karadinsu tun daga sitting room, kofarsu kuma a bude. Kawai ya samu kansa da tsayawa a bakin kofar yana kallon yarinta da kurucci zallahrsu,
sunata guje-guje, yana kuma sauraron su kalma bayan kalma. Duk maganganunsu ya gama ji
tsaf.
Ya sa hannu ya taro Siddiqah don saura kadan ta yi mugun faduwa a gabansa, Kiki kuma na
gab da kama ta.
Da matsananciyar faduwar gaba Siddiqa ta dago suka yi ido hudu da Hamma Prince, gata
kuma cikin hanunsa gabadayanta, ya samu kansa da kara riketa sosai saboda laushin jikinta,
wai yau shine da mace cikin hannunsa! Wani irin kallo ya yi mata mai wuyar fassarawa, ya ce a
hankali. “Old Uncle ko? Kuma Babanki dan 52 years kike aure ko Ayshah?”
Ya cikata, ya juya ya wuce ya barsu a wurin yayi hanyar fita, wajen Saheeb ya tafi domin ya
yi masa sai da safe.
Aisha komawa ta yi kamar jikakken tsumma saboda mutuwar jiki, tayi tsaye jingine jikin kofa
bayan wucewar Hamma. Kiki ko ta ce me zata yi ba dariyar Allah kasheni in huta ba?
Ta dinga sheka mata dariya ta ce, “Ai gara da ya ji da kunnensa irin tsufan da kike kallonsa
da shi”.
Aisha ta dawo gefen Kiki ta zauna. Jikinta ya mutu, bata yi zaton Uncle na jinsu ba, don data
ji shi shiru tun dazu ta dauka ya fita ko ya jima da yin barci, da ko kusa bazata fara wannan
tabargazar ba, ita tsokanar Kiki take yi, ta kama hannun Kiki cikin sanyin murya tace.
“Gaskiyar magana Kiki, auren nan namu fa babu wanda ya gaya miki me ya kunsa ne, don
ba auren na-gani-ina so bane.
Ba wata soyayya tsakanina da Babanki, sai ganin girmansa da nake yi saboda ya girmeni
sosai, da albarkacin Nenne ce ta haife shi nake zaune gidannan, shikuma yake mutuntani
saboda iyayensa sun karrama ni a idanunsa. Kin-ji kin-ji yadda komai ya wakana”.
Nan ta shiga labarta wa Kiki komai, tun haduwar Ummanta da Nenne a Saudiyya. Har zuwa
ranar da Dade ya sako ta a jirgi ta taho Argentina.
“To kin gani Kiki ni da Uncle dinki duk biyayya muka yi ma iyaye shi ya sa tunda na zo nan I
feel like Hamma kamar Yayana ne ko wani karamin Uncle dina nake tare da shi. No any other
strange feeling bayan wannan”.

Yanzu kam Kiki ta fahimta sosai, ta ce, “Amma Pretty, kin taba yin saurayin da ki ke so ko?
Kina mi kama da wadda tayi rashin masoyin dake matukar sonta”
Nan ma Aisha ta baiwa Kiki labarinta da Ishaq Hassan Nafada, daga A har Z, da irin rawar da
ya taka a rayuwarta, rabuwar da suka yi ba tareda ko sallama ba bayan tafiyarsa NYSC a
Ibadan, tace rabuwar kenan, har yau ba su kara ganin juna ba.

Duka wannan ma a rashin saninsu a kunnen Prince Abdulrasheed, domin ya kasa nisa da
dakin Aisha, bayan jin maganarta ta dazu, sai ya zama glued ga son jin me zata ce kuma,
bayan data fahimci ya ji kallon Babanta take masa, don haka a jikin tagar dakin Aisha wadda
kuma take a bude yake tsaye yana jiran isowar Pareto inda yake, domin su karasa su zaga cikin
‘Ranch’ don tabbatar da lafiyar Dawakan, don Pareto ya gaya masa a waya cewa Saheeb ba ya
jin dadi.
Shiyasa ma ya kasa kwanciya ba tare da ya zo ya duba lafiyarshi ba.
Hasken fitilun lantarki na alfarma manya da kanana sun taimaka sun maida daren kamar
tsakar rana a hamshakin ‘Ranch House’ din na Prince Abdurrasheed (Kehinde) Idris Akanni.
Ga dukkan mamakin Abdurrasheed, sai ya ji ransa ya sosu matuka, yana kuma cigaba da
sosuwa da wannan labarin da Aisha take baiwa Kiki a kan ‘Ex’ dinta Ishaq Nafada. A ransa ya
ce, ashe ma tana tsaka a kogin soyayya da wani banza can aka tsigota ni aka ba ni? Saboda
cewa nayi na rasa matar aure ko? Bayan an san bata da gurbin saka kowa a zuciyarta shine ni
aka bani? Irin wannan soyayyar ta kuruciya wuyar mantawa ne da ita a zuciyar mace.
Ga shi nan da aurensa ma kuma a gidansa take ci gaba da bada labarin tsohon saurayinta
cikin bege mai tsanani.
Abdurrasheed ya ji wani irin bacinrai na taso masa, kafin haushin kansa mai tsanani ya kama
shi, ina ruwansa da yarinyar nan nema? Balle Ex BF dinta ya dame shi? Ya girgiza kai yana ce
da kansa, to tun farkoma meye nasa na jin haushi don yayi musu laben da shi yasa kansa?
Allah ma ai ya hana labe. A take Prince ya baima kansa amsa da cewa, ai ko babu komai shine mijinta a yanzu, akwai
igiyar aurensa har ukku rus a kanta, wadda ko babu So, tabbas akwai ta. Aure kuma girman
matsayinsa da martabarsa ya wuce duk yadda za’a kwatantashi. Darajarsa dole a jita a rai ko
da So ko ba So. Ba wai don wani abu daban ba yaji haushin maganar saurayin Aisha sai don
cewa shine mijinta yanzu short and simple. Kwarai kalmar nan ta Aisha “Babanta/Babban
Yayanta/Uncle dinta” ta zafafe shi a rai.
Wato shi ga shi tsoho ko? Irin sa’an Babanta dinnan, don haka yaro sabon jini can shi ta ke
tunawa da bege da soyayya a matsayin daidai ita. To shi yanzu in ma ba ya fada da bakinsa ba
wa zai ce shekarunsa 42? Yau da babu Kiki a gidannan sai Aisha ta farraqe banbancin aya da
tsakuwa, don sai ta gaya masa da bakinta yaushe ya haifeta, don kawar da komai zaiyi a
tsakaninsu na rashin sabo da rashin soyayya ya nemi hakkinsa na aure, ta hakanne zai nuna
mata miji ko dogara sanda yake yi don tsufa sunansa miji ne ba “Uncle” ba a gun matarsa koda
kuwa ace ita matar jaririya ce don yarinta.
Isowar Pareto ne ya katse masa zazzafan tunanin, amma yaji dadin isowar tasa koba komai
ya ceceshi daga sauraron Kiki da Aisha, don baya son cigaba da jin muryar Aisha, kasancewar
ta jefashi a tunani da bacin rai, kuma tunaninta da Ex dinta zafi yake masa a rai, don bai saba
da irinsa ba. Karfi da yaji maganganun Aisha da sanyin muryar tannan so suke yi su jefa shi a
wani hali na jin radadin kishi wanda bai saba da shi ba.
Da Pareto ya iso inda yake sai Prince ya taka ya wuce gaba. Pareto na binsa a baya, suka
karasa stable din Saheeb, don abinda ya fito da shi cikin daren kenan, wato ya duba lafiyarsa
sosai don shima ya tabbatar Dokin ya rage walwala a satinnan.
Yace da Pareto dole da safe yayi gaggawar kiran Vetrenary Doctor din Saheeb ya bashi
allura da magani.

Daga nan ya rufe ko’ina na gidan ya kashe wutar falon ya sa kai zuwa dakin barcinsa, yana
shiga ya maida kofa ya rufe kansa. Lokacin kusan karfe goma na dare. A dakinma Prince kasa
barci yayi akan lokacin da ya saba, Aisha’s low tone voice mai nuna tayi rashin abinda bazata
iya mayarwa ba wato soyayyarta da Ishaq Nafada, ya tsaya masa a rai. Bai so aka hado shi da
wadda zuciyarta na tareda waninsa ba.
Amma yanata sharewa da baiwa kansa tabbacin ba kishi bane ke damunsa, it’s just normal
ai aure ne, tunda koma meye aurenta yake yi shiyasa yaji ba dadi, ya kuma ji tana zancen
waninsa a gidansa ko wanene dole zuciyarsa ta motsa.
Duk yadda Kiki ta yi kokarin wai Aisha ta tafi ‘master-bedroom’ din Hamma ta tayashi kwana,
har tana gaya mata cewa ta dinga kokarin yi masa tausa da kanta zata samu lada, don ta ga da
injin tausa yakewa kansa messege, dan Polo ne dole zai bukaci yawan tausa kullum, tace ta tafi
don Allah ta samu ladansa ta bar mata dakin ita kadai, Aisha tayi fumfurus ta ki amincewa, ta
ce,
“Kiki ki rage karambani, da kaini inda Allah bai kai ni ba, ki bar mu yadda ki ka same mu kin ji
ko malama, har gobe zamu cigaba da zamanmu ne irin wanda kika zo kika taras, a matsayin
‘Diya da Ubanta”.
Sai Kiki ta kule, dama tana da saurin shaka, ta jefa pillow a kan gado ta haye can karshen
gadon, ta ja duvet din bisa gadon ta rufe rabin jikinta ta juyawa Aisha baya, tana cewa.
“Zauna nan wayiya, ki ci gaba da maida shi Baba, in kinso ma kice masa Kaka, har ranar da
zai samo wadda za ta dauke shi Darling, duk girman nasa.
A gefe guda kuma mala’ikun rahma sunata kwashe miki albarka!”.
Aisha ta zaro ido tace,
“Kiki!”.
Kikin tace daga kwance, tana kara jan duvet ta rufe har saman kanta,
“Yess, gaskiyar maganar kenan. Mala’iku nata tsine miki. Kina kwarar Babana Aisha me yayi
miki? Baki duba shekarun da ya kwashe babu aure ba haba, yayi auren ma bada son ransa ba
amma kina raba daki da shi ba wata kulawa ba tarairaya. Ina gani fa ko magana ba kya son yi
masa shikuma duk ya damu da rashin kula shi da kike yi Am sure ba haka Nenne ta zata zaki yi ba”.
Daga haka Kiki bata kara magana ba ta soma jan rago (minshari) ta bar Aisha a zaune
dungurgur, tana tunani da jin ba dadin hakan a zuciyarta. Musamman data ambato Nenne. Ta
kuma tuna amanar da Nennen ta bata akansa na ta yi kokari ta canza shi daga yadda ta same
shi. Amma ba abinda zata iya a cikin abinda Kiki ke so tayi wato tafiya (master bedroom) da
sunan ta biyo miji turaka. Ko wanda Nenne ke so tayi, wato ta dinga shiga rayuwarsa tana
motsi, alhalin shi da yake namiji bai nemi faruwar hakan ba in one way or the other.
“Kiki kuma sai in tafi uninvited? Walk before you run Dear. Komai dan a hankali ne, kuma
komai da lokacinsa, amma ni bazan je ba tareda ya nemi zuwana ba”.
Kiki da farko ta yi mata shiru, don minsharin karya take yi, tasan ta hada mata zafi, amma
don Aisha ta san ta jita kulata ne bazata yi ba, sai ta kware bargon ta mike ta dauko wayarta a
caji, ta kunna ta zauna gefen ta soma kiran layin Tosin AbdulNaseer, ta murguda baki tana
cewa, “ni in ki ka kara kula ni Allah ya isa, tunda ba kya son Babana”.

Kiki sai ta koma bata dariya rigimarta da giringidishinta Allah yayi yawa dasu, kamar ‘yar fari
ba uata ba, ta kuma yarda kaunarta da Uncle dinnata mai girma ce don tsakaninta da Allah tayi
Allah ya isan.

Washegari da safe ma sun sha gardama ita da Kiki, don Kiki ta dage sai ta bi Uncle daki ta
gaishe shi da safiya.
Aisha ta ce, “Kiki ki bari sai ya fito (sitting room), ki fahimceni bana son wuce gona da iri,
tukunnama kan ki zo kin san ya muke zaune da yanzu za ki bi ki dame ni a kan abinda bazan
iya ba, ba kuma zai taba yiwuwa tsakaninmu ba?”
Kiki ta shaka, ta yi kwafa ta kyale ta, ko girkin safe da Aisha ta fara Kiki wanka ta shige ta ki
taya ta, ta ce tunda ba ta je ta gaida Babanta ba bazata kuma taya ta girki ba.

Da misalin karfe goma na safe Prince Abdulrasheed ya fito (sitting raoom) din. Yana sanye da
kayan barci farare sol. Daren yau ne zai tashi zuwa kasar France wasan tseren Doki na
Concacap Polo Championship.
Aisha ya hango a kitchennette ita kadai, tana kai da komowa, don kokarin hada musu karin
kumallo.
Motsin Uncle da kamshin turarensa ta ji a bayanta yana shigowa madafin. Da hanzari ta juyo
sai ta ga Uncle ne cikin kayan barcinsa, da alama ko wankan safe bai kai ga yi ba. Aisha sai ta
tsugunna ta gaishe shi, ya amsa a dake yana cewa,
“Ina bakuwar taki ta barki da aiki ke kadai?”
Aisha ta amsa da cewa, “Kiki ta shiga wanka”.
Ya ce, “Yau zan yi tafiya zuwa tournament, zan yi akalla sati guda kafin na juyo.
Kiki ta gaya min ta fasa tafiya gobe za ta zauna dake har sai na dawo.
Sai ki kula da gidan, da komai, kada ki manta ban da zuwa wajen Horses don suna harbi da
kafafunsu.
Musamman Saheeb, ba ya so kowa ya je inda yake in ba ni ko Pareto ba, he is very Anti
Social”.

Kafin Aishata bashi amsa Kiki ta fito ta sha gayunta kamar koyaushe, ta tadda su suna
maganar tafiyar tasa. Ta ce,
“Uncle sai ka bamu kudi, kudi sosai fa, muna da activities masu yawa nida Pretty. Kama daga
Shopping, zuwa su Hiking da Camel Riding. Tunda Aisha ta zo na tabbata ko sau daya ba ka
fita da ita ta ga kasar nan ba”.
“Ke ba sai ki fito da itan ba, uwar ‘yan kankanba da kilbibi, baki kamar na Aku-kuturu, halan
ba’a gasa bakinki yayin omogwu ba?”.
Kiki tasa dariya tace, “ka tambayi Maman Hakeem (Aunty Taiwo). Nidai kawai Uncle ka yi
mana izini muna da wuraren zuwa mu mike kafa tunda baka nan”.
Katin cirar kudinshi na daya daga cikin bankunan da yake ajiya ya ciro ya mika ma Kiki, ya
ce, su sayi ko me suke so har ya dawo.
Sannan zai bar masu mukullin mota daya Kiki ta kai su ‘tour round the city’.
“Banda kai wa dare Kiki, kin ji na gaya miki”.
Kiki ta amshi credit card din ta yi godiya, ta ce, “Insha Allahu Uncle ba za mu dinga yin dare

ba”.
Aisha dai tana gefe tana jera abincin da ta gama bisa tebir ba ta saka musu baki ba.
Kiki ta ce, “Aisha ki yi mana godiya mana, an bamu dama mu je shopping, kuma in kai ki tour
cikin gari”.
Dan murmushin gefen baki Aisha ta yi ta ce, “Kiki ni ba abinda zan saya, sannan kuma bana
son yawo, gajiya zan yi”.
Kiki ta ce, “Ai da ma ban tambaye ki ko za ki sai wani abu ba, ni na san duk abin da ki ke
bukata kuma ni zan dauko miki”.
Hamma bai saurare su ba, ya ja kujerar dining daya ya zauna, yau ma a tsakiya suka saka
shi, Aisha na dama Kiki na hagu, suka soma cin abincin.
Bayan Kiki ta yi serving dinsu kamar jiya. Jefi-jefi Kiki da Uncle dinta na magana cikin
yarbanci akan abin da ya shafe su.
Maganar Kiki kullum guda daya ce, ‘yasa baki Maman Hakeem ta yarda Tosin ya iso gida,
tunda dai shi da take kafa hujja da shi din yanzu ya kama Dahir”.
Aisha ta kudire a ranta zata kara zagewa wajen koyon harshen yarbanci da gaske daga
ranar yau, don ta lura Prince ba ya so ta ji ko me suke tattaunawa, shi ya sa ma ya koma
magana cikin kasaitaccen yarbancinsa.
Kiki ta ce,
“Uncle AK da ban zo ba kenan haka za ka tafi ka bar Aisha a gidan nan ita kadai?”
Prince ya harare ta, ya ce,
“Kiki ke ce uban ne ko ni ne?”
Dariya ta yi, Aishama saida ta murmusa, ta ce, “Amma dai Uncle amarya ba’a barinta ita
kadai a gida, son samu a ce tafiyar nan France tare ku ka yi ta, (as in honeymoon a tsakiyar
birnin masoya irin Paris) koh?”.
Kunya ta nuna a fuskar Uban Kiki. Yayi maza yace “na gaya miki amma tournament za ni je
ko? Kiki why are you disturbing me?”
Kiki ta bar zancen don bata son bata masa rai, ta ce,
“Shi ke nan Uncle, Allah ya kiyaye hanya. ‘yar ka zata kula maka da Aisharka har sai ka
dawo!”.
Prince ya tashi da daddare, Kiki ta tsara musu duk abubuwan da za su gudanar yadda za su
mori satin sosai, kafin ya dawo.
Tana so Aisha ta san gari, ta kuma daina bakunta da rashin sakewa a gidanta.
Washegari suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login