Showing 30001 words to 33000 words out of 46523 words

Chapter 11 - Aisha Saddiqa 3 Hausa Novels Complete by Takori Kabara .pdf

shirya ko break fast ba su yi a gida ba, suka tafi shopping. Kiki ita ce mai
diban kaya Aisha mai tarawa. Kiki ta daukar wa Aisha lingeries, English wears da nighties
kala-kala data lura bata dasu, ta ce,
“Daga yau bake ba kara saka atamfa a cikin gida, musamman in yana gidan, sai wadannan
da na zabar miki in dai kinason zaman lafiya da ni”. Aisha tayi dariya tace “wasa kike yi Kiki,
kema kinsan bazan iya ba”. Kiki tace “to ki ajiye ki boye, can gaba in kin yi kilin zasu yi miki
amfani”. Sosai Kiki ta bata dariya.

Suka koma bangaren kayan wanka ta daukar mata su feminine wash, deosprays da su body
scrub, daga nan suka je ‘sight seeing’.

Ba su dawo gida ba sai yamma lis.

Haka washegari suka sake ficewa zuwa ganin Penguins, waterfalls da wajen Camel Riding.

Ana saura kwana uku Prince zai dawo kiki ta kai ta aka yi mata SPA da Moroccan Hammam
(wajen gyaran jiki na mata na Moroccan Hammam).
Nan aka wanke Aisha tas, aka yi mata spa, body scrubing, pedicure da manicure, har da
gyaran gashi, aka wanke gashin Aisha aka yi steaming dinsa, sai ga fatar Aisha har sheki ta ke
yi abin gwanin ban sha’awa, dama ga ta fara tas, to sai ta koma pinkish, har wani jaja-jaja
fatarta ke yi. Kiki da aka kammala gyaran Aisha ta saita camera ta kashe ta da kyawawan hotuna, kuma
bada saninta ba kawai Kiki ta tura su wayar Uncle dinta, ta (whatsapp application) dinshi.
Saura kwana biyu Prince ya dawo da yammaci suka ga wani guri ana YOGA. Don haka
washegari tun da safe suka shirya suka tafi YOGA.
A can suka wuni sur! Aisha ta ji dadin session din nasu a can, waje ne na motsa jikin mata
zallah, sai yamma lis suka dawo gida.
A YOGA ma sun yi hotuna masu kyau, kawai Kiki ta hau turawa babanta hotunan da suka
dauka na charming lady dinsa AISHA-SIDDIQAH ba tare da Aisha ta sani ba.
**** **** ****

Prince yana reception na hotel din da ya sauka a kasar France yana hutawa kafin ya haura
sama zuwa dakinsa, kawai sakon Kiki ya cimmasa.
Yana budewa kyakkyawar surar ta bayyana kamar da an tabata jini zai yi tsartuwa. Gabadaya
fatar jikin Aisha ta canza daga yadda ya santa. ‘Moroccan Hammam’ din da ta sha da SPA sun
karbeta, gashin kanta ya sha steaming da gyara na musamman ya kwanta a dokin wuyanta,
gashi bakikkirin da shi, sai sheki yake yi. Wani bala’in murmushi da ta sakarwa Kiki a hoton, sai daya kusa kashe idon Prince
Abdulrasheed Kehinde.
Bai taba yi mata kallon da har zai ga natural features dinta a fili ba, sai yau a hoton nan.
He was dumb founded, domin bai taba ganin abu mai kyau irin Aisha-Siddiqah ba.
Ga naivity ga innocence appearance dinta wadanda sune attributes dinta da ya fi so. Prince
jinsa ya yi duk ya zama wani upset, a karshe ya kasa zaman reception din domin ji yake tamkar
bafaranshan da ke bayanshi yana taya shi kallon hotunan matar tasa, sai kawai ya rufe ya tashi
ya bar reception din, ya bi lift zuwa dakinsa. Kyawun wadannan hotunan ka kallesu daga
kwance kuma bada alwallah ba.
Kwanciya yayi rigingine a gadon hotel din ya dora kafa daya a kan daya, ya ci gaba da
bankado hotunan nan na Aisha da Kiki ta antayo masa, yayi ta kallo yana admiring kowacce
kankanuwar halittar da ke tare da matarsa “Aisha Siddiqah Yunus”.
Alama ya gani na cewa Kiki ta saka sabon status, a kan whatsapps dinta.
Yana budewa ya ci karo again da zafafan hotunan nasu da suka fi wadanda ta turo masa
haduwa da nuna natural beauty din Aisha. Prince har da zooming iya fuskar Aisha, yana kara
kare mata kallo, wani irin abu na motsawa a zuciyarsa da illahirin gangar jikinsa, kawai sai ya
samu kansa da kiran Kiki a waya ransa a mugun bace, da wani abu mai kama da allura da nan

take ya soki zuciyarsa, (KISHI).
Ko mintuna biyar Kiki ba ta yi da dora status din nan ba ta ga kiran Uncle AK yana shigowa
cikin wayarta kamar kiran kansa a fusace yake shiga wayarta.
Da murnarta ta daga zata soma yi masa karadinta da korafi da mita na rashin kiransu
akai-akai tun tafiyarsa, Hamma yace a fusace.
“Kiki wait, ina so ki cire hotunan Aisha da ki ka dora a status yanzu, idan abokanki da
samarinki maza suka gani fa? Ke ba ki san matar aure ba ce ne? Ko an ce miki daya kuke ke
da ita?”
Kiki ta hau danne dariya, don bata taba jin Uncle AK na fada haka har da tada jijiyar wuya ba
sai yau, fada sosai yake yi kamar ya ari baki ya kara akan nasa, bai ma dace dashi ba tunda
sparking irin wannan ba halinsa bane.
“Na baki minti daya maza-maza ki sauke su duka”.
Kiki ta ce cikin kokarin boye dariyar da ta taho mata.
“Uncle I’am sorry zan sauke su yanzu”.

Hamma ya koma da baya ya kwanta, ya kasa ajiye wayar ya ci gaba da kallon matarsa
Aisha-Siddiqah, wani kallo na kurillah da bai taba yi mata ba sai yau.
A zuciyarsa har tasbihi, yake domin Ubangiji ya yi halitta. Har gaya wa kansa yake wai
wannan beautiful sweet 16 din matarsa ce, wane kyakkyawan aiki ya yi wa Ubangiji haka, da ya
cancanci wannan kyautar da bai taba tsammanin samu ba?”.
Komawa ya yi kan status din Kiki yana saving kowanne cikin wayarsa. Sai kuma ya ga Kiki
na sauke wa din. Uncle ya kasa karashe sauran kwana biyunsa a France, a kwanansa na
shidda ya canza booking. Gara ya koma gida haka, kafin Kiki ta koyawa Aisha bariki. Don yaga
gabadaya ta canza masa mata, fatar jikinta da tsarin kwalliyarta duk ya canza.

Ranar da Uncle zai dawo Argentina bai gaya musu ba, kuma ranar Kiki ta tuna ba su je
‘Hiking’ ba. Don haka ta kwashe su a motar Prince suka tafi Hiking (long walks na hawa
duwatsu).
Ranar daga Kiki har Aisha ‘sport wears’ suka saka na mata, cikin wasu kayan Kiki ne, shaf
Kiki ta manta da gargadin Uncle na dawowa da wuri, kuma dai bata da masaniyar yau Uncle zai
shigo Argentina ta aza sai jibi.
Aisha da Kiki suka sha ‘sport wear’ abinsu riga da wando sakakku, suka zama tamkar
tagwaye don kayan iri daya ne sai kala da ta bambanta, gasu tsaho daya, saidai kasancewar
Kiki baka ce mai jiki, Aisha fara siririya maia mugun shape. Kodayake yanzu Aisha ba ta a layin
siraran mata, tunda bazamu kirata mai kiba ba, haka ba za mu kira ta siririya ba, saboda samun
diet na kabilar Yoruba mai kyau.
Suna can suna ‘hiking’ Uncle AK ya dawo gidan tun azahar. Bai taddasu ba. Har zuwa la’asar
shiru ba su dawo ba, kuma bai ga sun shirya masa wani abu da zai iya ci ba. gashi sun koya
masa kyankyamin takeaway. Ya kuma ki kiran Kiki a waya don ya ga iya gudun ruwansu.
Ashe dama dare suke kaiwa haka a gantalin nasu?
Aisha dama bai taba gwada kiranta ba, tun tafiyarsa, sai dai ya ce da Kiki ta gaishe ta.

Ya zauna a ‘sitting room’ ko kayan da ya dawo da su a jikinsa da ‘socks’ din kafarsa bai cire
ba, don ba ya son ya tashi su shigo, so yake su shigo a kan idanunsa ya kare musu tanadi tas.
Ashe lasisin gantali ya baiwa Kiki tayi da matarsa da ya bata mukullin mota shi bai sani ba?
Bai zaci ko fitar da suke yi din suna wuce azahar din da yace musu ba, amma ga shi har
magriba Kiki na waje da matar aure don rashin hankali da rashin mafadi.
Wayarsa ya kunna yana amsa sakonni da kiraye-kiraye, don dai ya rage bacin ransu, nan ya
jiyo dirin motar da ya tabbata su ne suka dawo gidan.
A tare suka shigo sitting room din suna hirar wata zamowa da Aisha ta kusan yi daga kan
dutse, ana dariya ana maida yadda aka yi, idon Aisha ne ya fara fadawa cikin na Uncle da ke
zaune a three sitter, ya dora kafa daya kan daya rike da waya, yana kallon shigowarsu rai a
matukar bace. Ransa ya kara baci da ganin kayan ‘sport wear’ din da ke jikin Aisha, duk da ta dora mini
hijab, kuma kayan ba masu kama jiki sosai bane, amma sun fiddo kirar jiki da kugun Aisha
sosai. Wani abu ya huda zuciyar Hamma Prince, wanda bana ko tantama kishi ne kamar yadda
Kiki tace, amma sai yayi fadan nasa a jumlace, ya ce. “Kiki am? Uban wa ya ce ku saka wannan kayan ku fita? Kwatakwata kin manta da matar
aure ki ke tare ko? Sannan kin san tun yaushe na dawo gidan nan ba ku dawo ba? alkawarin da
kuka yi min kenan?”
Fada sosai Hamma yake yi yau, fiyeda wanda yayi mata a waya kafin ya dawo. Yana fadan
yana kallon Aisha ta gefen idonsa, wadda ta yi tsumu-tsumu, ta kuma rikice duk a lokaci guda.
A nature dinta bata son fada ko daga waye, balle daga babban mutum irin Hamma. Kiki kuma
ko a jikinta, sai faman rike dariya a cikinta take don fadan ma Uncle bai iya ba, bai yi masa kyau
ba, musamman da bai saba ba, ta fahimci kawai dai kishin an fitar masa da mata titi da ‘sport
wear’ ne ya birkita mata Babanta.
Amma a zahiri shima a nasa idanun Prince yasan Aisha ba karamin kyau tayi ba, kamar a
sace ta a gudu (looking takeaway). Hamma ya kasa danne zuciyar sa da fushinsa ganin sun
masa shiru, ya sake kankance ido yana kallon Aisha. Wadda take jin idanun Hamma na zaneta
tamkar saukar bulala a jikinta, da wannan kallon kankance ido da yake mata. “A irin hankalinki yakamata ku rika saka irin wadannan kayan ku fita ko, in Kiki bata da
hankali sai ki biye mata? Kin manta matar aure ce ke Kuma Uwarta ce ba kawarta ba da zaki
maida kanki kamarta. Duba agogo ki gayamin karfe nawa kuna waje don rashin mafadi da
rashin sanin darajar aure ko Aisha?” Wannan karon kai tsaye da Aisha yake kuma ita ya jefawa tambayarsa.
Aisha ta sunkuyar da kai, tayi tsumu-tsumu, idonta fal kwallah, karo na farko da taji Hamma
ya ambaci sunanta kai tsaye. Kasa cigaba da tsayuwar ma tayi kada taje Baban Kiki ya hada da
duka.
Sum-sum-sum ta wuce dakinta, domin Uncle fada yake sosai, sai da ya surfe su tas.
Sai da y agama ya zauna a kujera yana maida fushi Kiki ta ce, “Uncle kai fa da hannunka ka
saya min wadannan kayan a wancan zuwan naka Ilorin, ka manta ne?”
Shi da kansa sai da ya ji kunya, tabbas shi ya sayawa Kiki kayan, bai san ba ya so a saka din
ba ya sayo mata sai da matarshi ta saka, Kiki da bai saba da yi mata fada akan sanya suttura
ba itama wannan karon ta shaka, don shi da kansa ya sayo mata kayan ya kai mata har
gidansu.

Aisha ta shiga daki ta zumbulo katon hijabin sallarta ta fito ta wuce su a falon har yanzu suna
wajen suna kaftawa ta wuce zuwa kitchenette don ta samar musu abin da za su ci, bata ga
alamar ya ci komai ba sai fada, gashi daga tafiya ya dawo. Jikinta har bari yake da fadan
Hamma. Kiki kuwa daga baya ganin da gaske yake ta daina boye dariyar ta koma sai hakuri ta ke
bashi, duk da ranta ya sosu. Sai ga Aisha ta fito Hijabi yana binta yana jan kasa ta wuce ta
gabansu zuwa kicin, Prince bai san sanda dariya ta kufce masa ba.
Wai hausawa suka ce ta baya ta rago. Ita dai fatanta ya kyalesu haka da fadan nasa don har
ga Allah ya kidimata.
Itama Kiki dariya ta saka da ganin hijabin da Aisha ta zumbudo, don Hamma ya daina fada.
Bayanta ya bi tana firar dankali tana share hawaye, because she hates to offend someone,
balle babban mutum kamar Uncle AK.
Daga bayanta ta ji motsin mutum da kamshin turaren Uncle AK, ba ta juyo ba ta ci gaba da
fere dankalinta jikinta da hannunta yana rawa, space din da ke tsakaninsu bai fi taku biyu ba. Ya
kuma fahimci hawaye Aisha ta ke yi kadan kadan saboda yadda fadansu ya rikitata.
"bar firar nan, baiwa Kiki tayi, kiyi a hankali kada ki yanke". Inji Hamma.
“Haba Aisha, am, ni ban ce ki je ki sako hijabi a cikin gidanki ba. Bayan kin gama nuna wa
mazan waje abubuwan da ni kadai addinin musulunci ya yarda in gansu.
Sai kuma ni a zo a zumbuda min hijabi me kenan akayi?
Fita ce nace bai dace a yi da wadannan kayan ga matar aure ba. Amma ba a cikin gida ba.
Ba ki ga yadda kayan suka yi miki kyau ba ne, looking ravishing!”.
Da sauri Aisha ta juyo don ta tabbatar wa kanta Uncle ne yake wannan maganar a kunnenta?
Kuma a tausashe? Shi ma kuma cikin borin kunya sai ya juya ya bar wurin don kamar subutar
bakin ba-zata ne ya same shi.
Ko da Prince ya koma dakinsa ya rasa me ya sa duk ya koma upset saboda Aisha, wani irin
emotional ya tsinci kansa. Sai da ya nutsu ne ya gane kukan da ya sa Aisha ne ba komai ba ya
birkita nutsuwarsa.
Kiki kuma a daren ta hau hada kayanta, da ma a gobe ne za ta wuce makaranta. Ga haushin
fadan da Uncle ya yi mata don kawai tana kokarin maida Aisha ‘yar gari, ta daina tsangwamar
zaman kadaicinta. Ai dai yasan ba za ta kai Aisha inda za ta cutu ba ko a cutar masa da ita.
Tana cikin hada kayan Aisha ta shigo dauke da tray din abinci da ta gama girka musu, bayan
ta ajiye na Uncle a kan dining, express ne tayi musu chips ne da agada (plantain). Ta ajiye tray
din a gaban Kiki, hankalinta duk ya tashi da ta fahimci Kiki tafiya za ta yi.
“Amma Kiki ya kamata ko sati daya ne ki kara, kin ga ni ban saba da Hamma ba har gobe,
zuwanki ne ya sa muka dan saba har muke cin abinci tare, ni in ki ka tafi ki ka bar ni daga ni sai
shi takura zan yi”.
Kiki ta harare ta tana cewa, “Aisha da sauranki, nikam ban iya zama daku alhalin kuna
wannan rayuwar mara ma'ana, sannan taurin kaine dake bakya jin shawara, alhalin kuna
matsayin ma'aurata amma kin kasa jan mijiki a jikinki. Sabida wauta da rashin wayo kin zauna
Uncle ya maida ke hoto a gidansa ba matar gida ba. Na farko kin barshi yana kwana shi kadai a dakinsa, ke ya ware ki a nan kamar kanwarsa
Fatima.
Yana tafiya wata tournaments yana barinki gadin gidan gona, halan maigadi aka kawo masa

daga Gomben?
Dan night dressing din nan na gayu da gyaran gashinki yadda za ki bada kala ki dimauta
uban nawa duk ba kya son yi, kullum sai uwar atamfa da leshi da jallabiyya a cikin gida, haba
Aisha shi ya sa fa ‘Yoruba Demons’ ke raina matan Hausawa.
Dazu kuma saboda Uncle na fada kika wani je kika sungumo hijabi kina asarar hawaye, in ni
ce ke wallahi shigar da tafi ta farkon fitsara zan yi in kara fitowa in yi juyi a gabansa, in kada
masa bombom, ke in makaleshi ma in masa kyakkyawar sumba, in yaso ya yi
gunduwa-gunduwa da ni karewar fada. Don abin haushi har da wani kuka-kukan ki ke ga ki mai Uba ko? Na ce Babanki ne shi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login