Showing 9001 words to 12000 words out of 44786 words

Chapter 4 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf

bata taba
gaishe shi ko yi masa magana ba, shi dai ko gaisuwa bata hada su tun da ya gane bata da
kwalli a idon ta, sannan Alhaji baya kwabar ta, ta raina duk wani maaikaci na gidan, aka ce
hanyar lafiya a bi ta da shekara, sosai ya kama kan sa, ko ya ganta zai bar wuri shima, don ya
san zuciyar sa ba irin ta sauran maaikatan Alhaji bace, da suke iya shanye duk wani rainin ta da
wulakancin ta saboda Alhaji.

A haka suka rayu tsayin lokaci a gidan Hon. Usman, ko in ce tsayin shekaru, har Amani ta
soma zama budurwa sosai, babu wata sanayya ko wani cordial relationship a tsakanin ta da
Mukhy.
Tana gama sakandire ba jimawa ta samu gurbi a Jamiar Bauchi, da taimakon Baban Hamida,
suka fara karatun su ita da Hamida Hashim Balewa a ATBU, sai rayuwar ta ta koma Bauchi
gabadaya, ko an yi musu hutun karshen zango ba koyaushe take zuwa Katsina ba saboda bata
shiri da Haj. Laura ko kadan, wato sabuwar amaryar gidan su matar da Alhaji ya auro a lokacin,
sai tayi zaman ta gidan su Hamidah sai dai shi Alhaji da kan sa yayi ta zaryar zuwa ganin ta,
don harr aba su dambe aka yi kwanaki tuni Alhaji ya yanke shawarar sallamar Haj. Laura don
itama kamrar sauran, ta kasa da Amani sabida rashin tarbiyyar ta. A haka Amani ta kammala
jamia ta yi hidimar kasa duk a Bauchi din.
Daga lokacin ne Alhaji ya maida Faskari Investment ya koma da suna Amani Faskari
Investment ya maida hakkin mallakar komai nasa da sunan ta.
**** **** ****
Ta haura sama inda dakin ta yake tana gaya wa kan ta in har Daddy ya dage lallai sai
Mukhtar ne zai taimaka mata wajen gudanar da tafiyar shagon ta, to kuwa zata hakura da
shagon.
Ita ta san kasuwanci ai ba sai mutum ya karanta shi ba ne zai iya tafiyar da abun sa, karatun
ta na International Relation and Diplomacy ya ishe ta komai, kawai Daddy ya bar ta ya ga
iyawar ta, ya daina underestimating din ta don tana mace, bata bukatar taimakon Mukhtar a
dukkan shaanonin ta. Shi kuma Daddy abun nasa kamar wanda aka camfa, ko aka sihirce, from all indications,
baya samun gamsuwa idan ba ya hada shaanin kasuwancin sa kowanne iri ne da Mukhtar din
ba. Idan Mukhtar yana tsaye akan abu, ji yake kamar shi da kan sa ne ya tsaya ya kula da abun
sa. Tsabar yarda da aminci. Don haka ta san ko me zata fada a yanzu ba zai yi tasiri ba,
kowanne irin bore zata yi Daddy ba zai saurare ta ba, in dai a kan kada Mukhtar ya saka mata
hannu ne a ragamar Boutique din ta.
Tunda shi Ya riga ya yi amanna cewa komai nasa sai Mukhtar ya saka hannu ne zai tafi
dai-dai.
To ita bata son taimakon nasa a kan komai nata, a bar ta tayi irin tata iyawar da kokarin, a
boko-akida irin nata what man can do, a woman can do better.
Ta shaki iska cikin fushi sannan ta furzar ta bakin ta. Ba wanda zata gaya wa damuwar ta a
kan mutumin nan ya fahimce ta sai Hamida Balewa. Aminiya daya kwal da bata da tamkar ta,
duk da nisan gari da ya raba su yanzu, kullum suna tare a waya, hakannan suna ziyartar juna
lokaci lokaci su yi kwanaki a gidajen juna, dama an ce garin masoyi ba shi da nisa. Zamantowar Hamida a Bauchi Amani a Katsina bai rage komai na karfin amincin dake
tsakanin su ba. Har abinda ba zata iya gaya wa Daddy ba tana iya gaya wa Hamida
kasancewar bata da yar uwa mace, musamman matsalar matar sa ta yanzu wato Hajiya Rabi
idan ta saka ta gaba. Ta san Hamida mai fadin gaskiya ce a kullum, kuma mai yi wa kowa adalci. Duk da raayin su
baya zuwa daya. Amma zata yi adalci tsakanin ta da Daddy a kan mutumin nan, ta kuma bata
shawara ta gaskiya na yadda zata yi da zaman sa a gidan su. Wani banbanci dake takanin ta
da Hamida shine an ce sai hali ya zo daya ake abota, amma ita Hamida kowa dake tare da su

ya san ba halin su daya ba, haduwar jini ce ta mikar da abotar su domin Hamida Hashim, bata
da girma kai, bata da dagawa sannan bata raina kowa duk da kasancewar ta diyar tsohon
gwamna.
Wayar ta ta dauka ta kira Hamida Balewa tana tsaye daga can saman balcony na sassan ta
dake saman gidan su. Daga inda take tsaye tana iya hango duk abinda ke faruwa a
yalwatacciyar harabar gidan nasu mai cike da korran shuke-shuke.
Yaya aka yi mutuniyas? Kwana biyu ban ji duriyar ki ba, halan kin fara shirin tafiya Sierra
Leone dinne? Hamida Balewa, ta fada bayan ta daga kiran aminiyar tata.
Amani ta yi tsaki tana fadin Hamdy, ba ta wannan nake ba tukunna. Don wanda ke min
binciken inda Maman nawa take ta karkashin kasa ya bukaci wasu kudade masu yawa a hannu
na, wadanda ban san yadda zan fidda su ba a yanzu haka, ina nufin, ba zan iya fidda su ba tare
da shaidanin nan ya ga alert ba, kuma tabbas zai gayawa Daddy a sanda ya gani din, idan
kuma ya tambaye ni me nayi dasu bani da amsa don ya sha ce min in na zabi bin Mama na ko
neman inda take, to tabbas in manta cewa ya haife ni, zai bar mata ni a kowanne hali na same
ta, zai yafe soyayyar da yake yi mun komai girmanta, tunda bai rage ni da komai ba na duka
soyayyar UWA da UBA.
Actually har gobe ban san me yayi zafi haka tsakanin Daddy da Mama na ba, kuma ina so in
sani, sama da komai ina so in ga uwata nima kamar kowa in ji dumin jikin ta tunda dai tana
raye.
Amani ta soma hawaye tana fadin Hamdy, I want to see my Mum, ko sau daya ne a rayuwa
ta, koda a bukka take rayuwa a Sierra Leone din zan je gare ta zan kuma iya zama da ita, ba
kuma don Daddy ya min komai ba, ko ya gaza da kulawa da ni ta wani bangaren, ba kuma don
bana son cigaba da zama da mahaifi na ba, aah, shaukin soyayyar uwa da ban taba samu ba
ke diba na, so nake kawai in gan ta a gefe na, nima in san cewa uwa da uba ne suka haife ni ba
Uba namiji shi kadai ba .
Hamida ta ce Da yardar Allah zamu je ga Mama bada jimawa ba duk inda take, amma bisa
yarda da amincewar Daddy. Amma kamar yaya kike nufi in kika fidda kudi masu yawa daga
account dinki Mukhtar din Daddyn ki zai ga alert?
Amani ta numfasa tana fadin ba zaki gane ba Hamdy, Daddy na wani irin SMART ne,
mutane ne ke ganin yana sangarta ni, yana min duk abinda nake so, baya hada kaunata data
kowa haka babu abunda ya kai ni muhimmmanci a gun sa. Eh, hakane da gaske amma kuma
bai yarda da sakin rayuwata sakaka in yi abunda na ga dama ba, musamman bayan haduwar
sa da shaidanin mataimakin nan nasa, kullum sai kin gan shi da sababbin dabaru na kiyaye
dukiyar sa.
Zancen dana ke miki yanzu ko me nake so Daddy zai min, amma dole yaron nan ya sani,
kuma yana saka ido sosai akai na da abinda nake kashewa kullum ranar Allah ta hanyar
wannan fitinannen yaron, mai kwakwalwar huda-huda da ya hada account dina da lambar
wayar sa (corporate account). Wallahi Hamdy na tsane shi bana ko son ganin shi, ba don komai ba sai don yadda Daddy ya
daukake shi yake girmama shi, yake fifita shi da daukaka shaanin sa a kan kowa a gidan nan
yanzu.
Karo na farko kenan dana kasa samun abinda nake so a gun Daddy; wato yaki yi min abunda
nake so kamar koyaushe na bukaci ya kori maaikacin da bai yi min ba, wannan karon ya nuna

min bai iya rayuwa sai da wannan mutumin, ya shiga gabana da yawa a gun Daddy Hamdy, ko
asiri yayi masa ni ban sani ba, Im extremely jealous of him!”
Hamida ta soma dariya, dariyar da ta kara kular da Amani don ita tsakanin ta da Allah take
fada mata damuwar ta, damuwar da tafi kowacce girma yanzu a gun Amani wato zaman
MUKHTAR DIFFA tare da mahaifin ta Hon. Usman, Hamida ta hadiye dariyar ta jin Amani na
kwafa, tana fadin Amani ki taka a sannu fa, ki bi abin a hankali, you are complaining too much
about this guy, Kaman kina exaggerating abun ma, in ban manta ba duk ranar da kika kira ni
complain din sa kike fara yi min, baki saka comma baki saka full stop, anya?
Baki fa san inda rana zata fadi ba, shaaah!
This dislike and hatered you have on him are beyond my understanding (kiyayyar ki a kan sa
ta yi yawa har ta wuce fahimta ta) kuma na rasa dalilin ta, ina laifin mai son Baban ka, da
taimaka masa kan dukiyar sa da shaanonin kasuwancin sa da zuciya daya irin wannan
mutumin, calm, cool and reserve da shi? Ni wallahi ta koina ya yi min, kin ga dai daga nesa kawai kika taba nuna min shi last zuwa na
KT, kuma ban ga fuskar sa sosai ba sai bayan sa yana shiga mota, amma ko daga tsayuwar sa
da zatin bayan sa kadai mutum ya gani ya san Allah ya ajiye namijin duniya a nan, haibar sa da
kamalar sa sun tafi da ni, da duk nutsuwa ta, kyawun sa ya tafi da Imani na na dade ban daina
tuna shi ba.
Ki ga min mutum kamar shi ya yi kan sa don kyau, ga iya daukar wanka, ga iya dressing, ga
jan aji nna karshe, da iya takun tafiya, yana tafiya gib-gib tamkar basarake, ga wani special
class (aji na musamman), na kasaitattun maza. Watakila saboda idon ki ya rufe da kishin sa da
kiyayyar sa saboda son da Daddy ke masa ne yasa baki hango abubuwan da ni na hango a
tare da shi ba..
Babu shiri Amani ta katse wayar ta, bayan ta lailayo ashar ta yarfawa Hamida. Haka kwana
ta yi tana tsinewa furucin Hamida da Hamidar kan ta a zuciyar ta.
Washegari tun da Amani tayi sallahr asubah bata koma barci ba, ta zauna bisa dardumar
sallahr ta tana tunanin yadda zata yi ta fidda wadannan kudade daga corporate account din,
wanda Daddy ya bude mata shi ne don ajiyar jarin kasuwancin ta kadai, ya kuma bude shi tare
da sunan Mukhtar ne a matsayin Director kuma sakataren ta, sannan kuma mai kaso daya bisa
uku na abinda ke cikin asusun, Hon. Usman yayi haka ne kawai ba don da gaske ya mallakawa
Mukhtar din wannan kason ba aa, komai na Amani ne, ya yi ne kawai don Mukhtar din ya zama
spy din sa a kan duk wani transaction na Amani da kuma sunan wanda ta turawa, ba don
komai ba sai don ya san ta da almubazzaranci da saurin mika wuya wa mutane, shikuma ga shi
da son abun hannun sa, bai yarda a ci da gumin sa ba.
Tun bayan zuwan Mukhtar wajen sa Hon. Usman ya fito da wannan idea din, ta joining
account din Amani da Mukhtar a matsayin corporate account na kasuwanci, yardar da ya yi
masa mai yawa ce, don ko dan sa na cikin sa ba zai sakarwa sirrikan sa irin yadda ya sakar wa
Mukhtar ba, yana jin takaicin almubazzarancin Amani don shi ko wane sisi da kowanne kobo
abu mai daraja ne a wurin sa, kashe kudin Amani ya yi yawa, musamman ga dangin sa na
Faskari, inda wani abu mai kyau guda daya tak cikin halayen Amani to kyauta ce.
Amani tana da hannun kyauta wa na kasa da ita kasancewar bata san zafin kudin ba, abun
duniya bai taba rufe mata ido ba kullum hannun ta a mike yake cikin yin kyauta ga wanda Alllah
ya tsaga da rabon sa. Wani zubin tana sanin an cuce ta ko an dafketa wajen sayen abu, amma

bata damuwa don Alhaji kullum kara tara mata yake.
Babbar damuwarta a yanzu tana so ne ta turawa dan sandan cikin dake mata bincike a kan
inda Mama Jalan take a kasar Sierra Leone. Dan sandan ya bukaci wadannan makudan
kudaden da suka wuce hankali ne ganin yarinyar ta zama desperate a kan neman mahaifiyar ta,
kuma ya ga alamar akwai kudin tare da ita sannan bata son shigar da kowa cikin maganar tasu. A karshe Amani ta ga cewa babu mafita fa dole sai Mukhtar ya ga debit alert dinnan, wanda
ke nufin sanin Daddy, domin tabbas ne Mukhtar sai ya gayawa Daddy a irin amanar da ke
tsakanin su cewa ta fidda miliyoyin kudi don ta san dalilin hadasu a account guda Kenan, don
ko sau daya Mukhtar bai taba daukar wani abu a ciki ba. Don haka ta kai azahar a daki tana qulubi, tana bacin rai, ga shi dan sandan cikin wato DSS
din da ke mata aikin ya tabbatar mata data tura masa kudin da ya bukatan a take zai turo mata
adireshin Maman ta da ke Freetown wato babban birnin Sierra Leone. Kai har ma da lambar
wayar ta ya ce duk ya samo. Amma sai ta fara biyan sa wadannan kudaden da ya kayyade mata tukunna.
**** **** ****
Abu daya da ta san bazata taba iyawa ba shine rokon Mukhtar alfarma, don tana ganin bai yi
wannan isar a idanun ta ba. Ba don haka ba da ta roke shi ya yi mata alfarma ya rufa mata asiri
sau daya a rayuwa, kada ya gawa Daddynta ta fidda 5 millions ta baiwa wani a boye domin ya
nemo mata Innar ta. Idan Daddy yasa ta gaba da tambaya da kwakkwafi (query) tabbas zai
gano shirin da ta ke yi ta karkashin kasa na son ziyartar mahaifiyar ta a boye.
Tana cikin wannan tunanin wayar ta ta hau ruri. Ganin sunan Daddy a daidai lokacin da take
tunanin sa sai da gaban ta ya fadi. Ta amsa a sanyaye.
My Daddy!
Daga can barin sa Hon. Usman ya ce Tafisu ki sauko falo na yanzun nan.
Iya abinda ya fada kenan ya kashe wayar sa.
Ta zura siraran kafafun ta cikin silifas din bakin gado sannan ta fita ba tare da ta canza kayan
barci farare samfurin Calvin Klien da ke jikin ta ba.

Falon Alhaji Hon. Usman Faskari, wani irin makeken falo ne wanda sai da ya ci saitin kujeru
uku iri daban-daban saboda girman sa. Ya kawatu da kayan alatu da air condition ta tsaitsaye a
kowacce kusurwa, komai na jin dadin rayuwa yaji a wannan falo mai kama da palace, din wani
gwamnan kai ka ce babu ranar mutuwa a zuciyar mamallakin sa. Amani ta shiga tako matattakala tana saukowa daga saman benen ta tana tafiyar nan tata
tamkar bata so.
Kallo daya Mukhtar da ke zaune gefen Alhaji ya iya yi mata a lokacin tana saukowa daga
stairs din, cikin takun nan nata tamkar na macen Dawisu mai ji da kasaita, ya yi maza ya
sunkuyar da kai cikin jin faduwar gaba don bai taba yi mata kyakkyawan kallo ba, yau din ma
kamar kullum, a sace ya kalle ta, amma ya ga surar jikin ta sosai a cikin kayan barcin, sai ya
samu kan sa cikin jin takaicin wadannan sharasharan kuma bingilallun kayan dake jikin ta a
matsayin ta na mace kuma Musulma a cikin mutane, domin kamar kanwar sa ya ke kallon ta.
Har ga Allah Amani bata san da shi a falon ba ta riga ta saba gaida mahaifin ta da kayan
barci in har tana son su gaisa kafin ya fita, kasancewar sa maabocin sammako. Tana cigaba da
saukowar bugun zuciyar Mukhtar na dada karuwa, ba tun yau ba hakan ce take kasancewa da

shi a duk a lokacin da ya hangi Amani ko daga nesa ne. Duk da dai wata kalmar fatar baki bata
taba hada su ba. Amma Tafisun tun dawowar ta daga ATBU take yi masa kwarjini sosai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login