Showing 30001 words to 33000 words out of 44786 words
Chapter 11 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf
shi da Haj. Rabi, ka roki Alhaji kada ya kara bawa mutumin nan damar gani na, tunda ya
zage shi ya ci mutuncin sa. Alhaji Sadi ya yi tsaki ya tashi ya fice daga gidan. A ran sa yana
cewa ba don albarkar abota ba sai yayi wa yarinyar nan asiri ta rasa mijin aure. Mukhtar ya zuba hannayen sa duka biyun a Aljihu, ya zuba ma Amani ido tana ta kuka, ta
cigaba da cewa ka fada ma Alhaji na bashi wuka da nama ya aura min duk wanda ya ga dama
amma ban da wannan mutumin kuma na yi masa lamuni ya saki Haj. Rabi. Ka rokar min shi ya
gaya min inda uwata take, na yi alkawarin maido masa ita gidannan ko tana so ko bata so.
Amma ban yarda ya kara auren kowa ba in dai don siyasa ne ya hakura tunda bashi da lafiya.
Tausayin ta ya tsirgawa Mukhtar har cikin ran sa, amma Mukhy da taurin rai irin nasa juyawa
ya yi zai bar dakin ba tare da ya ce mata komai ba. Amani ta tsanan ta kukan ta tana cewa ka
taimake ni!
Mukhtar saida ya dafa kofar ficewa ya juyo ya dube ta, da idanun sa da suka kada suka yi
jazir, ba abinda yake gani sai Amani zaune da Alhaji Sadi suna zance, in the first instance ta
san bata son shi me ye na saukowa kasa har ta kebe da shi? Sai don ya zage ta zata zo masa
da wasu zantuka da basu shafe shi ba? A fusace ya ce me yasa sai ni? Me yasa sai ni zaki aika
na gaya wa Alhaji sakon ki? Baki da baki? Baki fi ni kusa da shi ba? Ko ko ni dan aiken ki ne?
Mtsw!
Yasa kai ya fice daga falon, zuciyar sa da gangar jikin sa da Amani ta makalkale suna
vibrating. Kai tsaye mota ya dauka ya bar gidan zuwa nasa gidan da Alhaji ya bashi wanda
babu nisa zuwa na Alhajin.
Mukhtar yayi rigingine bisa makeken gadon dakin barcin sa ya na tuhumar kan sa akan me
ke faruwa da shi haka? Me ke addabar zuciyar sa? Me ke saka zuciyar shi cikin jin zafin Amani,
don kawai ya gan ta kebe da Alhaji Sadi? Shin abinda yayi mata anya ya kyauta tunda yau ta
zubar da makaman yakin ta ta nuna masa da gaske taimakon sa take bukata??? Why is he so harsh on her??? Duka baya da amsar ko daya, don haka ya ci gaba da tuhumar
kan sa yana nemo hujjar kare kan sa daga tuhumar da ya samu zuciyar sa na yi wa kana sa da
kan sa a kan Amani.
**** ***** **** ****
Amani da zazzabi mai zafi ta kwana, don bata iya ganin Daddyn ta ba sai a washegari. Shi
da Mukhtar suna balcony Mukhtar na bisa fararen kujerun roba da aka zuba a wurin suna
Magana, Alhaji na zaune cikin Wheelchair din sa. Da alama sensitive magana suke yi domin
Alhaji har share hawaye yake yi da hannun sa mai lafiya. Abubuwan da yake gaya wa Mukhtar
yau ko Amani bai taba gaya wa ba. Yana gaya masa tarihin sa ne da kauyen da ya fito wato
Faskari da yadda duniya da dukiya suka rude shi yayi abondoning dangin sa ko ziyara baya kai
musu balle ya taimake su, bayan dukkan su talakawa ne na gamu kashe mu masu tsananin
bukatar taimako.
Yace Mukhtar ban san halin da suke ciki ba yanzu, bani da masaniyar suna raye ko sun
mutu sun bar yayan su na garari cikin babu, ban tashi tuna cewa ban tafiyar da rayuwa ta dai
dai ba sai yau dana nakasa, ina kuma son su yi min wani amfani wato daura wa Amani aure.
Gaban Mukhtar ne ya yi bugawar dakikai masu yawa, kan sa ya wani irin sara. Ya dauka
Alhaji ya janye kudurin sa na aurar da Amani ga abokin sa? Ya tuna rokon da ta rika yi masa
jiya a kan ya taimake ta ya roki Alhaji ya fasa bata so, ko cikakken sauraro bai yi mata ba
sabida a wajen sa Amani ba mai cikakken hankali bace. Shi kan sa Alhaji, sai da yayi noticing canjawar da fuskar Mukhtar tayi. Mukhtar bai ce komai
ba a kan duka abubuwan da Alhaji ke fada masa, Alhaji ya cigaba da bashi labarin rayuwar sa
inda ya ce.
***** ***** ****
ASALIN HON. USMAN FASKARI
Na fito daga garin Faskari ta Jihar Katsina, mu uku ne a wajen mahaifin mu, mu biyu cikin mu
guda ni da Malam Idrisu. Dayar mace ce uwar ta daban wato kanwar mu Sahura.
Malam Idrisu yana da bataliyar Iyali domin kuwa matan sa uku kowacce tana da yaya maza
da mata sun haura goma. Sahura an yi mata aure a garin Funtua. Ban san adadin yaran da ta
haifa ba.
Asali na fito birni ne neman ilmin boko, sabanin yaya Idrisu da yafi maida hankali akan
sanaar mahaifin mu wato Dukanci.
A rayuwa ta ina da burin in tara kudi, in kuma auri kyawawan mata in cika gida dasu,duk da
ana yawan cewa ni mummuna ne Idrisu ya fini kyau.
Nayi makarantar koyon kanikanci a garin mu Faskari, da mahaifin mu ya rasu sai nayi wa
yaya na da kanwar mu Sahura sallama na ce na tafi karatu birni. Mahaifiyar mu a lokacin bata
tare da mahaifin mu tana aure ne a wani gari Kaita. Duk dai a cikin Katsina ne.
A wannan lokacin samun gurbin karatu a jamioin Najeriya ba abu ne mai wahala ba, saboda
gwamnati neman masu yin karatun take yi ruwa a jallo.
Na samu gurbi a Katsina state Polytechnic inda nayi HND dina a fannin Engineering, daga
nan na samu gurbi a Jamiar Bayero ta Kano, naje nayi digiri na na farko akan Architectural
Engineering. Na dawo Katsina na fada harkar siyasa.
Na shga siyasa da kafar dama, amma hakan bai hana ni shaawar kasuwacin kayan gine-gine
ba wanda akan sa nayi karatu na.
Alhaji Sadi Talle aminina ne tun na kuruciya a lokacin shi yana kasuwanci da kasashen
Africa. Shi ya sakani cikin harkar fitar da Aluminium Ore da Iron Ore daga Sierra Leone zuwa
kasar France. Kasuwanci ne wanda yayi mana sanadin samun arziki mai yawa, wanda idan
zamu dawo sai in saro kayan gine-gine daga can in taho dasu kasar Najeriya. Cikin dan lokaci Allah ya saka min albarka a cikin nema na. Na soma tunanin wasu hanyoyin
kasuwancin daban-daban har na samu na kafa kanfani na na farko wato Faskari Investment,
amma duk da haka ban bar siyasa ba.
Cikin irin tafiye-tafiyen da muke yi ni da Alhaji Sadi ne zuwa kasashen Africa muka shiga
Freetown wato babban birnin Saliyo, wannan karon mun zo ne musamman neman matar da
zamu aura, don mun jima muna shaawar auren kyawawan matan da ke wannan kasa.
Abokin kasuwancin mu da muka dade tare shi ya gaya ma na hanyoyin da ake bi a nemi aure
a wannan kasa, yace yayan attajiran kasar basa auruwa ga bako sai yayan talakawa, wadanda
iyayen su ke cikin yanayi. Shi ya hada mu da mahaifin Jalan wanda manomi ne a garin, kuma
talaka ne sosai, tun a hoto naga Jalan kuma tayi min dari bisa dari, na cika mahaifin ta da
dukiya mai yawa ba tare da yayi shawara da ita ba ya daura mana aure, ya kuma ce in dauke ta
in tafi da ita. Shi kuma Alhaji Sadi ya auri wata Jenaba wadda ita ta zame masa uwar yayan sa.
In takaice maka labari Mukhtar, ban sha ta dadi ba a hannun Jalan, domin bata sona ko
kankani, ni na san saboda muni na ne, don babu abin da ban mata a rayuwa ba ita da iyayen
ta, amma a cikin shekaru biyu da nayi tare da ita sau daya na taba morar sadaki na. A wancan
lokacin ni kuma son da nake wa Jaian mai yawa ne, don har gobe babu matar da zan so kamar
ta, duk matan da na aura bayan ta don na rufa wa siyasa ta asiri ne, amma ba don so ba ko
neman yaya.
Kullum gorin Jalan gare ni shi ne ba zata taba so na ba, domin tana da wanda tayi wa
alkawarin aure, na yaudari iyayen ta da abin duniya. Da tura ta kai bango na daina sakar mata
bakin aljihu na don na gaji da gorin da take yi min. Rana daya Allah ya bani saa a kanta kuma
ranar ne muka samu rabon Amani. Koda cikin ya isa haihuwa ta tubure lallai in maida ta kasar
su ta haihu a can, ni kuma da bazan iya barin ta ta koma kasarsu ba sai na dauko mata
mahaifan ta suka zo nan Katsina muka basu muhalli a cikin gidan nan, nace su zauna da ita har
sai ta haihu, domin kuwa Jalan tana ta min rantsuwa da barazanar ba zata haihu da
mammunan mutum kama na ba.
Ranar ne na fahimci Jalan saboda muni na take kina, in banda haka dame na rage ta da
iyayen ta? Har Hajji na kai su duka, in banda haka kiyayyar ta tayi yawa a kaina sai na soma
kankame aljihu na nima.
San da ta shiga watan haihuwa Jalan ta ci shinkafar bera don ta kashe kanta. Allah ya so
mahaifiyar ta da suke tare ta fahimta da wuri, muka kaita asibiti hankali tashe, likitoci suka yi
mata tiyatar gaggawa suka cire Amani, ita kuma suka bata duk wata kulawar da ta dace.
Tun da aka bani ya ta a hannu na, yar da aka ceto da kyar, naji na tsani Jalan, yau kuma na
tabbatar ba zata taba kauna ta ba. Sai kawai na rubuta mata saki na baiwa iyayen ta. Na kuma
basu kudin da zai ishe su koma wa kasar su da kula da lafiyar ta. Tun a aibiti da na rabu da su
ban kara bi ta kansu ba har gobe. Wanda sai yanzu nake tunanin ban kyauta ba, don ban ma
tabbatar da cewa Jalan ta rayu ba ko ta zarce, ban kuma san ya suka yi suka koma kasar su
ba.
Na dauki Amina wadda na sakawa sunan mahaifiyar mu na tafi Faskari da ita, garin da rabon
in shige shi har na manta sai a dalilin siyasa wato lokacin da nake neman kuriar kauyen namu,
Yaya na Malam Idrisu yana can da iyalin sa, har lokacin kuma da na fara karfi banyi kyan kan
taimaka masa ba ko yayan sa. Amma da yake aka ce naka sai naka, yau da bukatar taimakon
su ta kama ni haka na murje kunya na kai masa Amani nace ya baiwa daya daga cikin matan
sa ta shayar min da ita. Amma bawan Allahn nan bai dubi hali na ba ya karbi Amani ya baiwa
amaryar sa Maryama, ta hada da Kamilu dan da take goyo ta shayar da su. Maryama ba tayi
shekaru biyu cikakku tana shayar da Amani ba ta rasu. Sai Malam Idrisu ya dauke ta ya maida
rikon ta hannun kanwar mu Sahura dake aure a garin Funtua.
Amma zuwa na Funtua na farko naga bazan iya barin Amani ta cigaba da rayuwa a wannan
gidan ba saboda rashin tsafta da cikowa, gashi nifa bawai ina taimaka musu da komi bane kan
rikon da suke yi mata amma nazo na raina kokarin Sahura. Na karbo Amani tana da shekaru
uku na dawo da ita Katsina hannun matar da na sake aura, na daukar mata mai raino. Amma hankalin Hajara na kan yar kankanuwar yarinyar nan da yadda zata cutar da ita, shi
yasa da na gane na saketa babu bata lokaci.
Na sake aure, saina daina baiwa mata na hidimar Amani, na daukar mata mai raino daya
kwakkwara mai suna Rakiya, na sata a makaranta mai tsada, na ke kuma kirata AMANI don
boye sunan mahaifiya ta.
In takaice maka ko Mukhtar, kafin Amani tayi wadannan shekarun nata na yanzu aure na
goma, babu wadda na cika shekaru biyu da ita, don sun kasa kaunatar min yar nan, wadda
soyayyar da nake yiwa mahaifiyar ta ce bakidaya ta koma kanta.
Suma masu rainon kullum cikin canza mata su nake, Rakiya kawai na bari mai dafa mata
abinci har gobe, har Allah ya raya ta ta isa kula da kanta. Ita ta roke ni in daina aure-aure in
kuma daina korar masu aiki saboda ita, shi yasa muka dade da Haj.Rabi.
To ka ji Mukhy, wanan shine labari na da ya ta Amani, a yau ina cikin damuwar irin dabiun ta
da irin tarbiyyar da nayi mata, amma yaya zanyi? Ni da mahaifiyar ta Allah yayi ba masu rayuwa
tare bane na tsayin lokaci, kuma ban kyauta ba da ban kara bibiyar rayuwar Jalan ba, su kuwa
dangi na na Faskari wallahi sai dai Amani tayi masu kyauta amma ba dai ni ba, bana kai ta
wurin su, amma ita tana kai kanta lokaci-lokaci bama tare da na sani ba. Ba yabon nawa ba,
Amani ta fini kirki, ta fini son zumunci kai dai bar ta da sangartar ta wadda rashin tashi
karkashin kulawar uwa ko wata shaqiqiya mace ta jiki yayi mata sanadin sa.
Mukhtar ya jinjina kai ya shafe gumi daga goshin sa. A hankali yace Alhaji labarin ka akwai
darussa mai yawa a ciki Alhaji, sannan akwai tarin kurakurai a cikin sa.
Na farko Alhaji, ban yarda da abin da ka yarda da shi bana cewa Mama Jalan na kin ka ne
saboda baka da kyawun suffa wannan ba haka bane Alhaji. Hanyar da kabi wajen auren ta bata
dace ba, kamar ka sayo akuya a kasuwa ka kawo kasar ka ka ajiye ne, duk da mahaifin ta shi
ya aura maka ita, akwai bukatar ka nemi soyayyar ta da fahimtar juna tsakanin ku, kafin akai ga
maganar aure ba duka mata ake saye ba.
Amma irin wannan auren dama baya wata kima tunda da bakin ka kace min akwai wanda
take so da suka dade tare, har suka yi alkawarin aure.
Don haka ka cire maganar wai don munin kane bata son ka, kuma Alhaji da bakin ka kace
kana yi mata kankamo, mata da yawa musamman na kasashen Africa suna aure ne a inda
zasu samu wadata da kwanciyar hankali fiye da na kasar su ta asali.
Mu koma maganar dangin ka na Faskari, zan iya cewa kayi wa Yaya Idrisu da Sahura butulci
da rashin daukar zumunci da daraja. Dukiyar ka ta rude ka ka wulakanta zumunci domin sun
cancanci ace a irin wadatar da Allah yayi maka kamata yayi ace ka rungume su ka zama kaine
komai nasu tunda kace basu da karfi. Muhimmin abin da zaka yi a yanzu Alhaji shine gyara tsakanin ka da yan uwan ka, neman
yafiyar su, da janyo su a jiki, ka saka su a cikin niimar da Allah yayi maka.
Alhaji yana girgiza kai yace haka ne, haka ne Mukhtar, In sha Allah zan gyara, gobe-goben
nan ka shirya mana tafiya Faskari don Allah ni da kai da Amani da yardar Allah zan gyara
komai.
Mukhtar yace naji dadin jin hakan Alhaji, saura iyayen Mama Jalan da ita kanta ya kamata ka
neme su ka sada su da Amani.
Mahaifiyar ta na da hakki a kan ta fiye da wanda kake da shi. In ta mutu baka sada su ba sai
Allah ya tambaye ka Alhaji, Amani (is desperate) ga son ganin mahaifiyar ta, har taso ta bi ta
wata hanyar da baka sani ba don ta kai kan ta ga mahaifiyar ta ba don na hana ta ba, duk da
togaciyar da kayi mata akan zuwa gare ta. Kafin Alhaji yace komai suka hango Amani na tahowa inda suke da hanzari da sassarfa, suka
yi shiru suka maida hankalin su gare ta. Tana isowa ta nufi Alhaji ta zauna kasan kafafun sa ta
saka kuka.
Alhaji yace ni fa dadi na dake shagwaba da sakarci maras dalili, yaya zaki zo muna magana
ki saka mu gaba kina kuka? Mutuwa aka yi ko dukan ki aka yi? Amani ta dago jikakkun idanun
ta ta dubi Baban ta cikin ido ta ce Daddy sona ke ka saki Haj. Rabi, kuma kada ka kara auren
kowa, ba zasu taba