Showing 42001 words to 44786 words out of 44786 words

Chapter 15 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf

Yadda ya balbale shi da fada kamar kanin sa yana fadin ba ya son a zo a cika masa gida shi
bai iya jaye-jayen yayan dangi ba. Ya tuna cewa uwar Kamilun ita ta shayar masa da Amani, ba
don ita ba da bata rayu ba, ko sai da madarar gwangwani.
Yau ga shi ya dawo Faskari babu kafafu sai dai a tura shi a keken guragu, rabin jiki ba ya aiki,
kuma kai tsaye gidan Yayan nasa ya dosa, wato gidan su na gado, wannan abun kunya da
kayan nadama har ina?

Ita dai Amani da ke gefen sa tana danne-danne a waya, sai gani ta yi Daddyn ta yana
hawaye, ya kuma bar su suna ta zuba akan kundukukin sa ba ya ko sharewa wasu na korar
wasu. Idan ya kara tuna cewa uwar Kamilu ita ta shayar masa da Amani, amma shi ya kasa
daukar ko Kamilun ne ya yi yan watanni tare da shi na hidimar kasa duk irin arzikin da Allah ya
yi masa da girman gidajen sa a Katsina. Yailahi! Da wace fuska zai doshe su yanzu? Da wane
azancin harshe zai nemi gafarar su? Ba tare da sun yi tunanin sai da lafiya ta kare masa ba ne
ya neme su? Don in bai manta ba daga waccan wayar da suka yi da Baba Idrisu har gobe Baba
Idrisu bai kara neman sa ba, ya rike talaucin sa da mutuncin sa, ya rike yayan sa a kauye ko
birnin Katsina ya haramta musu shigowa don ma kada su nemi kanin uban nan nasu da bai san
muhimmancin zumunci da girman zumuncin Allah ba.
Alhaji shi ke nuna wa Mukhtar hanya har kofar gidan iyayen sa, soron gidan duk ya zube,
kana iya hango tsakar gidan da duk abin da ke ciki duk da an kare da zangarniyar dabino da
azara.
A nan ya umarci Mukhy ya yi fakin motar, daga can hanyar masallaci Alhaji ya hango Yayan
sa Malam Idrisu na tahowa, Mukhtar ya fito ya bude but ya fiddo kujerar Alhaji ya warware ta ya
dauko Alhajin daga mota ya sanya shi cikin kujerar. Amani ta fito tana ta cin magani da
yatsine-yatsine, har da zumbure-zumburen baki, ita ta tura Alhajin zuwa kofar gidan su, yayin
da Mukhtar ya tsaya kici-kicin fiddo kayan su.
Daga nesa Malam Idrisu ya hango su babu bata lokaci kuma ya gane Amani tare da wani
farin balaraben mutum da bai sani ba. Amma dattijon da ke cikin kujerar wheelchair ko kusa bai
kawo cewa kaninsa Usman ba ne.
Amani ta jira rike da hannun kujerar har ya iso, sai a lokacin ya gane dan uwansa.
Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Malam Idi, yana fadin, Me ya same shi? Me ya faru da shi
haka?
Zuciyar yan uwantaka! Tuni ya karbe shi daga hannun Amani, da kan sa ya tura shi zuwa
cikin gida.
Kai Isya je ka kasuwa ka kira Kamilu ya zo ya bude wa baki dakin sa su aje kayan su.
Yaron da aka kira Isya ya zura da gudu yana waiwayen Mukhtar don ya dauka bature ne ko
wani balarabe, fatar sa ta wanku da boko, ya karya hula damanga a saman kansa wadda ta
dace da launin shaddah getzner lemon green da ke jikinsa, kai ba za ka ce haihuwar Africa ba
ne shi ya fi kalar larabawa. Uwa, ku ne tafe? Sunan da yake kiran Amani, kasancewar sunan mahaifiyarsu ta ci, wato
Inna Amina mai rasuwa.
Amani ta zumburo baki, kafin ma ta furta wa Yayan uban nata gaisuwa ta alada sai da ta saki
korafi irin na rashin kunyar da ta saba yi wa Alhaji.
Za ka fara ko, daga zuwa na? Kira na da UWA? Shi ya ce min wani TAFISU kai ka ce min
wani UWA, bayan ga suna na mai dadi na yanka.
Dariya Malam Idrisu ya yi don shi a duniya yana son Amani, duk da halin ta kuwa, ya sa
matar sa uwargida Talatu ta yi musu shimfidar tabarma karkashin katuwar dalbejiya da ke tsakar
gidan.
Mukhtar ya gaishe shi cike da girmamawa, ya gaida Baba Talatu, Baba Idi na son tambayar
Amani inda suka samo kyakkyawan mutum haka, shi kuma ba balarabe ba, don ga hausa ras a
bakin shi, amma ya fi damuwa ya ji yadda aka yi dan uwan sa ya koma rayuwa a wheelchair.

Faduwa ya yi a bandaki, ka san yana da hawan jini, shine ya samu stroke. An fidda shi asibiti
har kaar Faransa Allah bai sa ya mike ba. Amma yanzu a hakan da sauki sosai, tunda yanzu
yana magana ras, yana kuma iya motsa duka hannayen sa.
Baba Idrisu da Baba Talatu suna ta sallallami da jajantawa, tuni suka manta da halin Alhaji.
Baba Idi ya ce sai a koma na Hausa, ya san inda ake maganin irin wannan lalurar ta hanyar
gargajiya a garin Kaita.
Wannan lalurar da suka samu Alhaji a ciki sai ta maida komai ba komai ba na laifukan Alhaji
a gun su, don dan uwan ya damu sosai, tunda shi da ma ba wai yana kwadayin abun hannun
shi ba ne, aah zumunci na Allah yake yi da shi, kuma kulawar sa garesu kadai yake bukata.
Kafin dan lokaci Kamilu da yayyen sa biyu Jibril da Usama sun iso gidan, Jibril da matar sa
da yayan sa hudu haka shi ma Usman da yaya biyu. Suna ta lale-marhabin da Baffan nasu, tare
da jajanta lalurar da ta same shi.
Alhaji sai ya fashe musu da kuka yana neman gafarar Baba Idrisu, yana kuma tambayar
Sahura.
Talatu ta ce, Gobe insha Allahu za ta aika mata ta zo daga Funtua.
Nan aka shiga mayar da zance tsakanin Alhaji da Yayan sa Malam Idrisu, ko ya rike dan
uwan nasa a baya, ganin halin da yake ciki da nadamar da ya zo da ita duk sai ya ji rikon na
narkewa a ran sa. Duk da haka ya fito fili ya gaya wa dan uwan sa yadda yayi wasarere da
zumunci bai kyauta ba, ba ya neman kobon sa amma dole ya kyautata zumuncin Allah muddin
yana son gamawa da duniya lafiya.
Alhaji har su Kamilu sai da ya bi daya bayan daya ya nemi gafarar su, ya tambayi kowannen
su abinda yake ciki, suka gaya masa, cewa wasu cikin su kasuwa suke zuwa wasu gona wasu
sun yi karatun NCE wasu har degree, sai Alhaji ce wadanda suka yi karatu a cikin su zai tafi da
su a duba ayyukan da suka dace da su a kamfanin Amani, wadanda ba su yi karatun ba ma duk
ba zai rasa irin aikin da ya dace da su ba.
Baba Idrisu ya ce, Ai kam ba ka kwashewa duka ka barmu mu kadai, sai kananan yara. Ka
dai dauki masu takardun bokon ka bar min sauran su ci gaba da kasuwa da gona.
Alhaji ya ce, Mukhy, sai a binciki irin sanaar da suke yi din a nan a bunkasa ta, a ba su
training a kai, sannan a ba su jari mai tsoka.
Consider it done Alhaji.
Abu dai ya yi dadi tsakanin Alhaji da dan uwan sa da yayan dan uwan sa.
Sai washegari Sahura ta iso don amsa kiran da Baba Idi yayi mata tun jiya, Alhaji sai ya ga
duk ta tsofe ta mokade saboda wahala, don mijinta ya rasu ya bar ta da yaya takwas. An yi
sulhu cikin tausayin juna sun yafe wa dan uwan su, suka ce ba su taba kullatar shi ba ko don
Amani da bata yada su ba ita, kullum addua suke masa koda kuwa sunan sa kadai suka ji an
fada a kafafen yada labarai.
Baba Idi ya ce, Ah toh ni ai ban damu ba, na sani ko ba-dade ko ba-jima za ka neme mu,
tunda ba ka da wadanda suka fi mu.
Kusan kwanan zaune suka yi ranar da Sahura ta zo ana ta maida zance da labarin juna.
Alhaji ya ce, tunda Sahura ba ta da karamin yaro duk ta aurar da su, na karshen ma yana
makarantar Alkalam a Katsina, to zai tafi da ita gidan sa ta zauna tare da Amani kafin wucewar
ta gidan mijinta. Sahura, Baba Talatu da Baba Idi har suna hada baki wajen tambayar Alhaji cikin mamaki,

Uwa ta samu miji ne?
Don su kam basu ga mijin da zai iya daukar Amani ba.
Alhaji ya gyara zama da filon da aka sa masa a bayan sa, ya soma warware musu tun ranar
farko na haduwar sa da Mukhtar a kasar Faransa, da irin gudunmawar da ya bayar ga habakar
dukiyar sa, amanar sa, halayensa, rikon addinin sa da irin gudun duniyar sa. Ya kare da ba su
labarin zuwan Alhaji Sadi neman auren Amani, da sanadin samun lalurar sa da jinyar sa da
Mukhtar ya yi a Paris, tare da Amani, halayen Amani da Mukhtar yake tolerating, har da ganewa
da ya yi cewa Mukhtar zai iya da halaye da dabiun Amani marasa kyau har ya samu ta gyaru ko
ba ta so, a dalilin ganewa da ya yi Mukhtar kadai ta ke shakka, kuma shi ke iya lankwasa ta ta
bi raayin sa ko ba ta so.
Wannan ne dalilin da ya sa ya yanke shawarar hada su aure duk da Amani ba ta so, domin
auren su ne kadai zai dorar da kyakkyawar dangantakar shi da Mukhtar din.
Yana so wannan ya zama wasiyya da ya bari ko da ta Allah za ta kasance a kan sa gabanin
ya daura musu aure da hannun sa.
Yan uwan nasa sun fahimta, sun kuma gamsu da hujjojin sa. Rashin kunyar Amani wa ta
bari? Tun tana karama yi ta ke har ya zame mata dabia a girman ta. Mukhtar din kamar yadda
Alhaji ya ce yana da dakakkiyar zuciya kuma ya san halin ta, sannan bai yi musu ba da Alhaji
ya ce ya ba shi aurenta. Suna da kyakkyawan hope na cewa zai rike Amani ko don kaunar da
ke tsakanin sa da mahaifin ta.
Amma sai Baba Idi ya ce, Ka binciki asalin sa? Ka gana da iyayen sa? Ka san daga inda ya
fito, kuma ina dangin sa?
Alhaji yayi danjim! Kafin ya ce, Ai ni ko daga sama Mukhtar ya fado, wato bai da iyaye, ko
tsintacce ne a kan bola na bashi auren Amani, shaidu ya rage su shaida.
Ni zan masa waliyyi, kai ka yi wa yar ka Amani walicci, goben nan nake so in mun sauko
sallahr jumaa lafiya a daura musu aure.
Jiki na na bani ko ma daga wane tsatso Mukhtar ya fito tsarkakken tsatso ne. Tsatso kuma
mai albarka. Zaka taya ni fahimtar hakan idan ka zauna dashi na kwana uku.
Baba Idrisu ya ce, Duk da haka, bayan daurin auren dole ya dauki matar sa ya kai ta ga
iyayen sa su sanya musu albarka, in basa raye to bazasu rasa dangi ba.
Alhaji ya ce, Na fahimta, amma a halin yanzu na fahimci Mukhtar yana da damuwar da ta fito
da shi daga gida wadda ta saka ko a yi masa zancen ya je gida ba ya so.
Bana so na takura masa (for now), da cewa lallai sai ya koma gida zan aura masa Amani,
zan ba shi lokaci har zuwa sanda shi da kan sa zai bukaci hakan a karan-kansa, ba abin da
lokaci ba ya iya canzawa a rayuwar dan Adam, amma zan roke shi kamar yadda ka ce kan su
je garin iyayen sa bayan auren ya gabatar musu da iyalin sa, don su san da auren sa, ba sai
sun tara yaya ba sannan su je musu, wajibi ne mu san mun damka Amani a hannun dangin sa
da kan mu, saboda gaba a ke hange da yayan da za a haifa.
Baba Idrisu ya gamsu da wannan shawarar ta Alhaji.
Sun tsayar cewa gobe Jumaah bayan saukowa masallaci za su daura auren Amani da
Mukhtar. Alhaji zai ma Mukhtar walicci Baba Idi zai wa Amani. Baba Idrisu ya dage Alhaji ya bar
Mukhtar ya biya sadakin sa da kan sa. Don da cewa ya yi sadakin ma shi zai biya masa.
Daga Amani har Mukhtar ba su san wainar da iyayen suke soyawa ba, don sun basu wuri ne
don su gana da junan su. Shi Mukhtar yana dakin Kamilu inda aka sauke shi, Alhaji dakin da

Jibril ya tashi ya bari aka share masa. Amani tana dakin budurwar gidan da ba a yi wa aure ba
mai suna Laure. Ta yi korafin cizon sauro, sai da Laure ta je ta sayo maganin sauro ta kunna
mata. Nan ma ta ce ba ta son warin sa, a nemo na fesawa. Laure ta fara gajiya da iskancin
Amani, ta ce sai ki koma dakin Baba Talatu, ni ba zan kara fita a daren nan ba. Amani ta ce, Aah, gara in yi maneji da nakin ya fi tsafta kada in je berayen ta da ke tsere a
gaban mutane su gwagwiye min kafa.
Washegari Baba Idi ya sa Baba Talatu ta yi karin kumallo mai kyau duk gidan, kunun tsamiya
aka yi da lafiyayyen kosai, aka kuma hada da shayi da biredi, saboda Amani da ta ce ba za ta
sha kunu ba. Baba Idi ya ce, Ki yi ta yi. Nan din dai shi ne asalin ki, sarkin iyayi da kidifiri, kuma
saboda ke tuwon gero za mu yi anjima miyar kuka da daddawa. Alhaji ya yi dariya ya ce, Tafisu ce, don Allah a dafa mata mai maiko.
Baba Idrisu ya ce, farin balaraben mijin ta ya ba mu na cefane ne? Tunda ya zo fuska ba
walwala, sai tamke fuska yake yana muzurai kamar yaci babu, a yi mutum kamar mai fuskar
shanu?
Amani ta tashi ta bar wurin, saboda bakin cikin Baba Idi ya alakanta aure tsakanin ta da
Mukhtar. A ran ta ta ce, Ah toh! Ashe ba ni kadai na ki jinin yadda yake da rashin walwala ba,
mai nuna zuciyar sa ba humanity ba compassion a cikin ta ko kadan. Balle a kai ga zancen
soyayya iri ta mata da miji. Amani ta kyabe baki, a fili ta ce Allah ya tsari gatari da saran shuka ba dai ni Amanin ba. ta
ce a ran ta muna komawa Katsina za su neme ni su rasa. Wallahi ba zan zauna a aura min
wanda zuciyata ba ta taba kauna ba, kuma har abada ba za ta taba so ba. Na bi jar fata da
gudu da bakin gashi na tattake ba takalmi a kafata. Ana saukowa masallaci a babban masallacin jumaa na garin Faskari Baba Idrisu ya gaya wa
Liman a dakatar da mutane, zai daura auren yar sa Amina diyar kanin sa. Tun wayewar gari ya
karbi sadakin Amani daga hannun Mukhtar Diffa, wanda ke ji da ganin komai na faruwa kamar
almara. Ya kasa gasgata cewa shi Mukhtar ne zai yi aure yau. Ya biya sadaki mafi albarka, wato
mafi kankanta daga aljihun sa, wanda ya kasance gumin sa ne. Bai gasgata duka abubuwan da
ke faruwa ba, wadanda yake gani kamar a mafarki, sai da ya ji an shafa fatiha, mutanen garin
Faskari da suka halarci sallar jumaa a yau duka suka shaida daurin auren Mukhtar da Amani.

***​***​***

Mu karasa a littafi na 2.
Sumayyah Abdulkadir
07030137870 (whtsp only)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login