Showing 3001 words to 6000 words out of 44786 words
Chapter 2 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf
Alhaji ya ce ba sunan da ya dace da ke irin Tafisu, saboda ai kin fi sun ne da gaske, ina nufin
kin fi tsararrakin ki gata, kin fi sauran yaya gatan Uba, kin fi su komai tunda kina da Uba iri na,
wanda ke tsaye a kan duk abinda kike so, da son tsaya miki kan duk mai son shiga hancin ki.
Ya fada babu wasa a maganar sa, ita ta san Daddy yana nufin abinda yake fadi, a shirye yake
ya tsaya mata a kan kowa da komai. Shi yasa itama bata hada kaunar sa da ta kowa a rayuwar
ta.
Hon. Usman Ya mika mata takardun yana fadin amshi ki duba Tafisu. Boutique din ki da na
dade da yi miki alkawarin bude miki a nan Katsina ya kammala, yana nan a jerin shagunan
Goruba Road, gobe sai kuje da MUKHY ki gani, idan da abinda bai yi ba, ko baa kawo ba, ko
zaa canza cikin kayan da kika bada list aka yi odar su, sai ki fada masa, in ya so sai a kara yin
sabuwar order, don yana da wata tafiyar dama nan da watanni biyu zuwa Mexico, ina saka ran
zai shigo min da wasu samfurin marbles, sai ya karo miki abunda babu din.
In yaso sai ku je tare ki gani, kina dubawa kina fada masa yana rubuta min komai a tsanake.
Ai kuwa nan da nan fuskar Amani ta yi kicin-kicin, ta zama kamar hadarin da ya nausa ya yi
gabas, ta yi mugun bata rai kamar bata taba fara a rayuwar ta ba, ta kirne kyakkyawar fuskar
nan tata ta wani irin yamutse ta, fuskar ta a wannan lokacin sai ta koma masa exactly ta Jalan,
wato mahaifiyar ta, idan kiyayyar ta ta motsa a kan sa; wata kwayar mace guda daya da ya taba
so a rayuwar sa, kuma daga kan ta bai kara son kowacce mace ba, yanzun da Amani tayi
hakan sai ya ga ta rikide ta koma masa Jalan har sai da gaban sa ya fadi sosai. Yanayin ta a irin
wannan lokacin yafi kama da na yayan nan da baa kwaba, baa hantara, wadanda saidai iyayen
su su bi abinda suke so ko basa so, fadi take cikin shagwaba, hassala da zumburo baki.
Allah ya tsare ni hada hanya da shi, Allah ya raba gatari da saran kuka, shin Daddy sau
nawa zan gaya maka ka manta ne? Magana ta gaskiya ka daina hada sabga ta da ta wannan
mai cunkusashshiyar fuskar da halin sumumu-kasau din.
Ina dalili mutum kullum yana faman kirnewa mutane fuska kamar malaikan daukan rai, alhalin
da bazar su yake rawa? Mutum dan siriri da shi sai kafirin girman kai da bakin hali kamar na
mutanen farko.
Daddy yayi kasa da murya duk da yana son yin dariya amma ya hadiye, saboda yadda ta
fitittike tana furzar da maganar zaka san an tabo fushin Tafisu, cikin lallashin yar tasa yake
cewa.
Uwa ta. Kullum ina gaya miki ki daina damuwa da yanayin fuskar Mukhtar cikin shaanin
kasuwancin mu ko muamalar mu ta yau da kullum da shi, kowa da kika gani a rayuwa, yana da
damuwa, mai yuwuwa damuwa ce a kasan ran sa take bayyana a kan fuskar sa, yanayin
walwalar sa ko rashin ta ni ba zai shafi alaqa ta da shi ba, o neman kobo na because its
obvious I cant do without him (a fili yake ban iya rayuwa sai tare da shi).
Duk yadda yanayin halittar sa yake zan iya going da shi a haka, haka kema nake so ki fara,
saboda babu mai iya yi min hidimar da yake yi min da jiki da kwakwalwa da lafiyar sa da zuciyar
sa gabadaya hidimtawa dukiyata yake, haka Allah ya yi shi da rashin walwala, ba ke kadai yake
yi mawa ba Tafisu. Kowa ma! Ki je office din mu ki gani, zan iya rantse miki ba wanda ya taba
ganin dariyar sa.
Kuma banda abin ki Tafisu, ina ruwan ki da faraar sa ko rashin ta? Amfanin da yake yi min,
da rikon amanar sa a kan dukiya ta zaki duba, kafin a samu mai amanar sa da gudun duniyar
sa da rashin zalama akan KUDI, zaa jima Amani.
Na sha gwada Mukhtar ta hanyoyi masu tarin yawa da tawa hikimar da Allah ya bani ta
testing mutane, amma ban taba kama shi da wani hali na son cuta min, ko yi min almundahana,
ko munafurci ba. Hasalima amanar sa ce ta hada ni da shi ta hada wannan bond din mai karfi
tsakani na da shi. Wanda ya wucde na ubangida da yaron sa nake masa kallon dan ciki na. A baya in kin tuna maaikata nawa nayi kafun shi, cikin su babu wanda bai cuce ni ba in one
way or the other.
Ban taba samun matashi nagartacce kamar sa ba, kuma kafin a samu yaro nagari irin
wannan a zamanin nan abu ne mai wuya Tafisu. Inada dalilai na a kan son yaron nan, da bazaki
fahimta ba.
Ai ba komai yasa kika ga na jure masa yana bata miki rai da halayen sa ba, sai don in muka
sallame shi kamar yadda kike so ba zamu taba maida asarar rashin sa ba, akwai maaikatan da
kai kake amfana da su, ba su suke amfana da kai ba, ko me zaka biya sub aka iya biyan su. Ki
saka Moukhtar Diffa a cikin jerin irin su. Saidai in ke zaki dinga yimin ayyukan da yake yi min din idan kika takura na sallame shi,
which is impossible. A matsayin ki na mace ba zaki iya abinda Mukhtar yake yi min ba, irin su
yawon kasashen ketare shigo da kaya da handling kamfani bakidaya, banda sauran wahalhalun
da yake yi min (personally) a cikin gida, a kan dan albashin da bai taka kara ya karya ba, kuma
cikin amana, girmamawa da tsantseni.
Ga ilmin kasuwancin Allah ya bashi, ga kwakwalwa kamar kwamfuta, duk wata hanya da kika
sani da zata maida min kobo ya koma dari cikin shekarun nan da suka gabata ina tabbatar miki
daga Mukhtar ne nake samun Theory, tun zuwan sa gare ni ban san faduwa ba sai dai riba.
Ya numfasa sannan ya dubi Amani wadda ke sauraron sa da kunne daya don kuwa hankalin
ta na kan wayar hannun ta, bai damu ba don ya san tana jin sa, ya cigaba da fada mata cewa.
Duk wata hanyar samun riba mai tsafta da kike gani yanzu a kamfanin nan shi ke kawo min ita.
One impressive thing about Mukhy, baya taba waiwaye da cewa ina kwarar sa da dan
albashin dana ke bashi kowanne wata, amma wallahi bai taba korafi ba, dan kuwa albashin
dana ke biyan sa ko kusa bai kai kimar yawan ayyukan da yake min ba, da abinda yake nemo
min, in aka yi laakari da cewa, ya mallakawa dukiya ta lokutan rayuwar sa baki daya, da kuma
tarin fasahar ilmin kasuwanci dake cikin kan sa. Ko iyayen sa bai taba ziyarta ba tun zuwan sa
hannu na.
Kullum na yi masa maganar zuwa gida cewa yake Alhaji in na tafi wahala zaka sha, don ba
lallai a bar ni in dawo ba.
Kin san akwai wasu jinsin mutane da sam-sam basu san wani abu wai shi jin dadin duniya da
da shagaltuwa da kyale-kyalen ta ba, irin wadannan mutanen su sai dai su taimakawa wani ya ji
dadin shi kadai, ko ya samu duniyar shi kadai ya ji dadin, ba tare da sun raina dan abinda zai
basu ba, to ina tabbatar miki Moukhtar na cikin su. Amani ta mike don zancen Mukhtar dinnan wanda ta laqabawa suna bare ka fi dan gida ya
fara isar ta, ya gundure ta. Ta kuma san in ba ta bar wajen ba Daddy ba gajiya zai yi da bata
labarin kirkin Mukhtar ba. Daddy ba zai sa comma ba bazai saka full stop ba kuma bazai gaji
ba. Sai idan baka yi zancen Muktar Diffa a gaban Hon. Usman Faskari ba. Yanzun nan zaka
soma jin nassi-nassi, maudhuI maudhui na kabakin alheri iri-iri daga bakin Alhajin a kan sa. Ta
ce,
Daddy, zancen ka ya shiga ta hagu, ya fita ta dama, ko me zaka ce a kan wannan yaron ni
kam bai yi min ba, na tsani mutum mai iko, mai fadin rai da jiji da kai, alhalin shi din ba kowan
kowa ba.
Ta soma taka stairs don komawa dakin ta kada Daddy ya cigaba da gaya mata abinda ba
shiga kan ta yake yi ba.
Alhaji Usman ya yi murmushi, ko yaushe Amani zata fahimci banbancin human personality?
kowa yadda Allah ya halicce shi ta fuskar personality, gashi har digiri ta yi a kan International
Relation amma har yau ta kasa gane personality na halittar dan adam baya taba zuwa daya,
wanda bai da alaqa da facial expression nasu, yace zo nan Tafisu, ya zaki tafi baki duba
takardun Boutique din ba? Amani ta ce ba tare da ta tsaya ba Daddy in komai yayi maka, nima
ya yi min, zan dauki maaikata da zasu kula da shagon mutum uku cikin yayan dan uwan ka na
Faskari, da wanda ka ce tare aka shayar damu Kamilu yake ko Kamalu? Ka bar su a kauye
suna noma da kiwo cikin wahala ka kama bare ka rike da daraja.
Ni bani da lokacin zuwa wani boutique, ni dai in ji alert na shigowa kullum a ka yi ciniki, in
sayi abubuwan da nake so shikenan.
Cikin sauri Alhaji ya katse ta.
Babu wasu yayan dangi da zaki dauka aiki a shagon nan kin ji na gaya miki, su zo su yi min
rubdugu a kan dukiya ta da basu taya ni tarawa ba, in da na biye musu da hidimdumun su, da
basa karewa, da yau ban tara abinda na tara miki ba.
Ki dauki inyamurai da suka karanci kasuwaci suka kware da kula da shago su kula miki da
shagon karkashin kulawar Mukhtar ba gayyar yan kauye ba, ko ki bar shi ya kawo maaikatan da
suka dace da kan sa, don na san ba zai kawo na banza ba, ko wadanda basu gogu da harkar
ba, ko marasa amana da zasu yi miki almundahana.
Haushi da takaici ya kara kama Amani, na yadda komai na mahaifin ta sai ya dangana shi da
wannan Mukhtar din yake samun aminci a zuciyar sa, wannan wane irin abu ne? Anya haka
farin baabzinen nan ya bar mata Uban ta? Shi kadai ne mai amana a duniya a wurin Daddy,
kamar wani dan sa na cikin sa, ga samari nan fal jinin sa yayan wan sa baya taimaka musu da
komai, suna kauye suna gararramba, wau sun yi karatu babu aikin yi, kai bata taba jin tana
kishin wani dake tare da mahaifin ta irin Mukhtar dinnan ba, wai har yafi yarda da shi a kan
yayan dan uwan sa?
Wadanda lomar abinci kullum sai sun fita sun nemo a kasuwannin kauye, wasu cikin su da
yawa sun yi karatu mai zurfi musamman Kamilu, amma babu aikin yi, alhalin suna da kanin Uba
mai wadata da gwamnati a hannu irin sa a kasar nan, amma gashi yana fadin a nemo inyamurai
wadanda ba lallai su kasance musulmai bane a basu aikin yi a karkashin sa, su yan uwan sa a
bar su cikin wahala, karkashin kulawar wani bare, wanda yafi jinin sa matsayi a wurin sa da ko
asalin sa bai sani ba.
Tana ganin tsayawa yi wa Daddy gyara a kan ire-iren kuskuren da yake tafkawa bata lokaci
ne don ba dauka zai yi ba, ba kuma denawa zai yi ba tunda rowa, mammako, rashin yarda da
wani ya amfana da shi, da rashin son nasa ya rabe shi halin sa ne zaunanne da ta dade da
fahimta tunda ta soma hankali. Ita kuma duk da halin ta na raina ajawalin kowa saboda iko da mukamin data rayu cikin sa,
da ganin kowa bai isa ba, Allah ya yi ta mutum ce mai yawan kyauta, da matukar son yan uwan
mahaifin ta na kauye duk da talaucin su, tunda bata san na mahaifiyar ta ba. Wani abu mai kyau
da zaa iya cirewa a halayen Amani shi ne abin hannun ta baya rufe mata ido sam, ke dai bar ta
da facaka da kudi wajen kwalliya mai tsada da gasar hawa motar yayi.
Ai kawai Daddy ka ce shi ka budewa boutique din ba ni ba, tunda shine mai ruwa da tsaki
wajen gudanarwar sa gabadaya, bayan shi ya je Mexico ya shigo da komai, sai kawai a
canzawa boutique din suna zuwa Mukhtar Collection.
Amani ta fada cikin bacin rai ko shagube zaa ce? Kamar ba da mahaifin ta take magana ba.
Tana mai tattaka matattakala don komawa dakin ta.
Murmushi Alhajin ya yi, maimakon ran sa ya baci ya kwabeta a kan rashin kunyar da ta yi
masa, amma sai ya buge da rubuta mata text message din lallashi da wayar hannun sa.
Zuwa shekaru kadan a gaba, idan Allah ya raya mu, Tafisu zaki zo ki gode min, for making
MUKHTAR DIFFA your Business Mentor, ranar da kika ga Mukhtar ya maida dan Boutique din
nan naki ya rubanya zuwa PLAZA guda.
Domin Allah SWA ya huwwace da ya halicce shi yayi masa hikimar maida taro ya koma sisi.
Trust him my daughter, work with him for a while, give him a try as your business mentor!.
**** **** ****
Sai da Amani ta zo kwanciya ta ga wannan sakon na Daddy, zumburo baki tayi tana tunanin
mutumin nan ba haka ya bar mahaifin ta ba. Yardar ta isa. Kaunar ta yi yawa. Ko shi ya haife shi
sai haka. Iya shaidar arziki da zai iya masa kenan.
Daddyn ta da duk wanda ta nuna bata raayi nan take zai yanke alaqa da shi ko waye kuwa,
ko da zai kasance jinin sa ne, amma banda MUKHTAR DIFFA. Farin baabzinen data taso ta
gani tare da mahaifin ta, yana rayuwa karkashin sa matsayin mataimakin sa, kuma yana tare da
shi kullum a gida ko ofis. Dan asalin garin Diffa, ta kasar Nijar, wanda ko asalin sa basu sani ba
har shi Daddyn kuwa, banda sunan garin sa da yake amfani da shi a gaban sunan sa DIFFA.
Daddy dai ya dauke shi aiki ne da farko a dalilin haduwar jini kawai, ta sanadin wani halin
amanar sa da ya bayyana gare shi, rashin zalama da rashin kwadayin abun duniya, in kana da
wadannan halayen, tabbas zaka zauna lafiya da Hon. Usman Faskari tunda shi bay a so wani
ya more shi ko yayi arziki da shi, sannan ga kyawawan kwalayen ilmi (educational
qualifications) din sa masu nagarta, domin Mukhtar Diffa, ya fitar da kwalayen boko biyu masu
darajar farko (B. Sc & M. Sc in Business Administration) daga jamiar Paris wato (Paris Saclay
University).
***** ***** ****
FARKON HADUWAR HON. USMAN DA MUKHTAR DIFFA
Asalin haduwar su da Alh. Usman Faskari a wata tafiya da ya yi birnin Paris ne, lokacin da ya je
shigo da wasu kayan assasa kamfanin sa na farko wasu shekaru kusan goma a baya.
Cikin tsautsayi Alhajin ya yarda wallet din sa a cikin jirgin kasa, wanda ke dauke da dukkan
katunan sa na banki daban-daban (credit cards), fasfo, ID cards, da duk wasu muhimman
abubuwa da ake sakawa a cikin wallet. Bayan ya sauka daga jirgin kasan, ya shiga motar da
zata maida shi masaukin sa ne ya lura babu wallet din sa a tare da shi, wadda ba katunan
bankin sa kadai ta kunsa ba, akwai kudade (Euros) masu yawan gaske a ciki.
Alhaji da kudi, ko sadakar dubu guda baya iya yi in ba ta hanyar siyasa ba. Yayi salati a
gigice yana kara laluba aljihun sa yana gayawa direban da dauko shi su koma, ya yar da
abubuwa masu muhimmanci su koma tashar jirgin kasa.
Komawar da bata haifar da komai ba sai bata lokaci, domin train din tuni ya dade da barin
Paris, ya nausa wata jihar dake gaba da Paris wai ita Bourdeaux. Ya dai bar report a ofishin
jirgin kasan da wajen yan sanda.
Hon. Ya shiga damuwa ba yar kadan ba a daren, domin a cikin wallet dinnan kusan duka
sirrin rayuwar sa ne gabadaya. Ga tsabar kudaden da ke ciki wadanda ya fitar dasu daga banki
ne da zummar zai yi amfani dasu wajen accommodation na tsayin zaman sa a kasar da
cuku-cukun clearance na kayan sa har zuwa komawar sa