Showing 6001 words to 9000 words out of 44786 words
Chapter 3 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf
gida. Damuwar sa tana karuwa in ya tuna identity cards din sa daban-daban na siyasa da na
kasuwanci duk a cikin wallet din sa.
Alhaji kamar ya zare. Amma ko minti goma bai yi da shiga masaukin sa ba ya samu kira a
wayar sa, a lokacin yana kokarin revoking katunan sa na banki don kada a samu damar yashe
shi. Duk da iya abinda ya mallaka ba wai a bankuna suka kare ba, yana da hannayen jari da
kadarori masu yawa da kamfanin sa na FASKARI INVESTMENT LTD. Yana dagawa ya ji an yi masa sallama da hausar da bata fita yadda ya kamata, ko dai
Francaise ya rinjayeta ko harshen Espanol, ko kuma abzinanci. Cikin ukun dai. Duk da haka a
kan gane hausar idan aka saurara, kasancewar cikin nutsuwa mai kiran yake yin ta.
Ina Magana da mai wannan layin ne? In sha Allahu kana tare da mai wannan layin Engnr.
Othman Fass. Ya kasa furta sauran da accent din sa. Amma Alhajin ya gane yana son cewa
Faskari ne.
Sai ya karasa masa da cewa Eh nine Engnr. Usman Faskari.
Alhmdulillah, ina zan sameka in baka wallet din ka yanzu? Na tsince ta a jirgin kasan da ya
taho daga Bordeaux zuwa Paris. Na samu wannan lambar a jikin daya daga cikin identity cards
din ka.
Alhaji a zaune yake amma bai san lokacin da ya mike tsaye ba yana hamdala, yana hailala,
ya gaya masa sunan Hotel din da yake, yace ya kira shi in ya zo reception.
Cikin daren baa kwana ba saurayin ya zo hotel din, suka hadu da Alhajin. Ya dauko wallet din
sa ya bashi. Ya tsaya har Alhajin ya bude ya duba sosai ya kuma kirga kudin sa ya ga suna nan
cif, a jere yadda ya jera su, ko kwarzane basu yi ba, ya tabbatar ba abinda aka cire.
Babban abun mamakin Alhajin, kudin sa na nan yadda ya bar su ko guda daya baa cire ba.
Har yaron ya juya ya tafi, Alhaji Usman ya kasa daure mamakin sa. Sai ya bi bayan sa. Ganin
cewa dan Afrika ne ga hausa kadan ya iya, duk da dai alamu sun nuna ba bahaushe bane
Baabzine ko dai dan kasar Nijar ne, wato irin matasan nan na Nijar wadanda ke tahowa karatun
boko kasar goyon su wato Faransa, daga Jamhuriyyar Nijar, kasancewar kasar Faransa ce ta
goya kasar Nijar.
Amanar yaron, exceptional personality, da kuma bravity din sa kai har ma da character da
attitude din sa sun yi matukar impressing din sa.
Alhaji Usman ya bi bayan sa da sauri yana fadin;
Ya ka Da na, dakata don Allah, yaya sunan ka?
Cikin halin sauri-sauri don kada ya rasa jirgin kasan komawainda ya fito, da koin kula irin
nasa, kuma ba tare da ya juyo ba, cikin rashin sakin fuska da rashin annuri ya ce da Alhaji
Usman,
suna na Mukhtar.
Daure ka tsaya ka ji Da na Mukhtar in maka godiya don Allah.
Amma bai tsaya din ba sai tafiya yake, Alhajin kuma bai fasa bin bayan sa ba, yana rokon sa
Allah Annabi ya tsaya ya bashi tukuici.
Ya dan tsaya har Alhajin ya cimmasa, juyin duniya Hon. Usman yayi a kan ya karbi kudin
dake cikin wallet din bakidaya don farin cikin taimakon da yayi masa, amma kyakkyawan
matashin baabzinen ya ki, duk kuwa da cewa a lokacin neman kudin jirgin da zai koma
Hong-Kong din China yake yi, saboda ya nemi wani aikin a can, kasancewar interview din da ya
yi ta neman aiki da wani kamfanin turaruka a nan Paris din bayan kammala karatun sa, bai yi
nasara ba.
To na ji bazaka karba ba, na kuma gode da karamcin ka, na kuma yabawa nagartar ka,
samun irin ka a cikin matasa is a blessing. Ka cigaba da wannan halin na taimako da amana zai
kai ka har inda baka taba zato ba.
Na sha gwada samari kamar ka, ban samu wanda ya san amana ba. Ni kuma mutum ne mai
son mutane masu amana. Don ta yi karanci a wannan zamanin.
Still fuska ba walwala ya ce na gode.
Sannan ya juya da sassarfa ya bar reception din. Tafiyar sa kadai abin a bi da kallo ne,
saboda taku yake da sassarfa, amma kamar na kasaita.
Yaron ya tsaya masa a rai har wayewar gari. Don haka washegari ya kira shi da layin da ya
kira shi jiya, suka gaisa.
Alhaji Othman ne ko?
Ya fada da kakkaurar muryar sa bayan sun gaisa. Ni ne Da na Mukhtar, ya ka je gida?
Alhamdulillah ya bashi amsa. In ba damuwa ina so in zo in gan ka kafin na wuce gida Nijeriya
gobe. Yace babu mishkilah, Allah ya kaimu, amma ka bari ni zan zo in same ka kasancewar
daga Clermont-Ferrand City zan taho, bana so ka sha wahala har nan Baba. Murmushi Alhajin
yayi yace na gode Da na sai ka zo, don Allah ina jiran ka.
Lokacin da yayi masa waya yace ya taso a train daga Clermont Ferrand, Alhajin yasa aka
shirya abinci na alfarma a dakin sa na hotel, dama kuma yayi sayayya ta sutturu masu tsada,
agogon maza na (Swatch) da takalma da turaruka ga Mukhtar din, da niyyar ya je ya kai masa
har gida a matsayin godiya, tunda ya ki karbar makudan kudin da ya barma shin. Wannan ya nuna ba karamar alfarma da haduwar jini Mukhtar ya samu a gun Hon. Usman
ba. Kasancewar shi mutum ne mai tsananin kankamo, bi maana, ba kowa ke cin arzikin sa ba
bayan tilon yar sa AMANI sai wanda rabon sa ya rantse, mutum ne mai rowa kwarai. Tsakanin
sa da duk wani maaikacin sa albashi kadai, babu ihsani. Amma shi wannan yaron ya nuna
masa akwai sauran masu amana da rashin kwadayi a duniya, sabanin daukar da yake yiwa
kowa, cewa mutanen yanzu duk kwadayayyu ne masu neman gasashshen tsuntsu daga sama,
shi yasa yake so ko yaya ya gode masa.
Don yana yawan gaya wa Amani yanzu duk mutanen duniya makwadaita ne, shi yasa suke
cewa ya fiya rowa, ya dauki kowa a irin dabiar da yake kai, wato son ci daga haram ko halak
kamar sa.
Sannan a ganin sa mutaen yanzu basa ganin kudi su kyale balle irin wadannan Euros dake
dankare cikin wallet din sa.
Ko a satin da wuce ya kori maaikata biyar daga kamfanin sa, da ya kama su da yi masa
sama da fadi da wasu yan kalilan kudade. Bayan kuma kudaden ma bata suka yi cikin lissafi
amma a hannun su.
Ya iso kofar dakin ya danna kararrawa, Alhajin ya bude masa yana lale marhabin da shi,
sanye yake da farar shirt an rubuta Fred Perry da bakin wandon CK Jeans. Dogon matashi,
kakkarfa, farin baabzinen usli, mai wani irin sassanyan kyau, hancin sa kamar an sa ruler an ja
masa shi an saka masa shi a tsakanin idanun sa, komai na halittar sa ya zauna a inda Allah
Subhana ya ajiye shi, kamar shi ya zaba wa kan sa zati da kamala, ga wata lallausar suma da
ta taru a saman goshin sa ta abzinawan usli, har ta dan kalmaso a kan goshin sa, ta maida shi
tamkar Baindiyen nan mai farin jini (Shahrukh Khan).
Alhaji ya bashi kujera ya zauna suka gaisa sannan ya nade hannun riga yace ya sauko kasa
su ci abinci tare. Ko kadan rashin walwalar yaron da shan kamshin sa baya damun sa.
Kamar ba zai ci ba, amma ganin Alhajin da an sa yayi serving din su a plate guda, sai ya
kasa tankwabe kulawar wannan dattijon, wanda ke ta haba-haba da shi cike da kauna, sai ya
sauko kasa ya kalmashe kafafun sa, suka fara cin abincin a plate daya.
Suna ci, Alhaji Usman na hilatar shi da hira cikin dabara irin ta manya, har yaji abinda yake
son ji, wato inda ya fito da kuma abinda ya kawo shi birnin Paris.
Nan yake gaya masa cewa daga wani yanki na jamhuriyyar Niger ya zo nan, ana kiran yankin
nasu Diffa Region, yau watan sa uku da kammala karatun digirin sa na biyu a nan kasar, daga
jamiar Paris Saclay University. Ya gayawa Alhajin tun baya kammala masters din sa ya nemi
ayyuka na wucin gadi har uku bai samu ba, kasancewar shi ba dan kasa ba, don haka zai koma
Hong-Kong yanzu ya nema a can. An ce suna bada ayyuka sosai ga yan Afrika, shi neman na
kan sa ya fito, ba yanzu zai koma gida ba.
Kasancewar a lokacin kasar Nijar na fama da matsalar durkushewar tattalin arziki babu
ayyukan yi ga matasa masu ilmi kamar sa a Nijar.
Alhaji Usman ya tambaye shi ko me ya karanta da level din karatun sa duk ya gaya masa,
cewa daga digirin sa har master first class ne. Alhaji Usman became highly impressed da jin
hakan, sai kawai Alhajin ya ce, ina ma za ka iya zaman kasar Najeriya, da mun tafi tare na baka
ragamar kamfani na, in ya so sai ka dinga zuwa gida kana ganin iyayen ka lokaci-lokaci, saboda
ni din bani da Da namiji, sai mace tilo, ina neman mataimaki a kan harkoki na wanda zan iya ja
a jiki na in sakar masa ragamar kamfani na. Na kuma yaba da halayen ka.
Mukhtar ya ce ban taba zuwa kasar Najeriya ba Baba, amma ina jin labarin ta, kuma ina son
aikin yi kwakkwara wand azan tsaya a kan sa da kafafu na, musamman wanda ya shafi
kasuwancin kamfani, a nan buga-buga kawai nake babu permanent job ga wadanda ba yan
kasa ba, ni kuma ba yanzu zan koma gida ba. Don haka zan bi ka in gwada in gani, idan naji dadin kasar, zan zauna, don bani da abun yi
ko na koma Diffa. Kuma babu wanda ke jira na a can.
Cikin mamaki Alhaji Usman ya ce ina iyayen ka?
Nan da nan fuskar Mukhtar din ta wani irin sauya, ta rine ta yi jajir abin ki da farin mutum.
Wani yanayi ya shiga na kokawa da numfashin sa da Alhaji Usman ya kasa karanta. Shi da kan
sa ya baiwa kan sa amsa da basa raye kawai. Sai ya shiga yi musu addua ba tare da shi
Mukhtar din ya ce masa komai a kan su ba. Amana ce ta hada mu, naji ina kaunar ka kamar dan da na haifa saboda halayen ka da suka
burge ni, ina fatan wannan amanar tayi ta yado da yabanya a tarayyar mu.
**** **** ****
Mafarin zuwan Mukhtar Diffa kenan gidan su Amani, tarayyar da ta zamewa Alhaji Usman
sanadin alkhairori masu yawa.
Bai sakar ma Mukhtar ayyukan sa na sirri ba sai da ya cigaba da gwada shi iyakar gwadawa
ta hanyar yawan aiken shi kai kudade banki, domin da farko kamfani ya kai shi, ya bashi ofis, a
matsayin Chief Operating Officer (COO) ya kuma bashi gidan zama a kusa da gidan sa wanda
babu nisa da kamfanin Faskari Investment cikin birnin Katsinan Dikko. Excellent Performance din da Mukhtar Diffa ya soma nunawa daga zuwan sa ya razana
kowa, domin yana zuwa ya canza akalar komai zuwa na zamani, ya kawo sababbin innovations
masu tafiya da zamani na yadda zaa bunkasa hanyoyin da kamfanin ke amfani da su wajen
shigo da kayayyakin da kamfanin ke shigo dasu Najeriya daga Faransa da sauran kasashen
Europe irin Mexico. Har ila yau, COO Mukhtar Diffa, ya kawo hanyoyin samun cigaba ga
maaikata ta hanyar karawa maaikata sani da dabarun kasuwanci a zamanance, ta hanyar
shirya (capacity building programs) iri-iri da yake shiryawa a kai-a kai ga kananan maaikatan
Faskari. Ya tsame masu lalaci daga ciki ya kai su kasa, ya maye gurbin su da masu hobbasar
cikin su.
Ya kuma takura wa Alhaji a kan kara albashi da welfare din maaikata da yake kankamewa.
Kan ka ce meye wannan hakan ya sayo ma Mukhtar farin jini gun kananan maaikata, ya kuma
kara musu himma da maida hankali, sannan ya kawo conducive working atmosphere ga dukkan
maaikatan Faskari Investment. Shi ba hausa ce ta ishe shi ba, amma da zuwan sa Katsina ba jimawa sabida cudanya da
hausawa da maaikata a company, da kuma shi kan sa Alhajin da ke masa magana kullum da
hausa don ya kware, a sannu bakin sa ya fara iyawa sosai, a hankali a hankali kuma accent
dinsa na Francaise da abzinanci ya fara barin bakin sa sabida rashin abokin yi.
Mukhtar Diffa, ya soma rikidewa yana koma wa zallan Ba-katsine, in ka cire nannadaddiyar
sumar kansa da launin jar fatar sa da ke fallasa shi, matsayin kyakkyawan Baabzinen mutum
dan hutu kuma dan zamani, hatta hausar bakin sa kafin shekara guda ta koma ta Katsinawa.
****** ****** ******
Sanda Alhaji Usman ya kawo shi gidan tana makarantar kwana aji daya a Ulul Albaab, ya
dade a gidan ma bata san da shi ba, a lokacin Alhaji bai mayar da kamfanin da sunan ta ba, so
ko ta zo hutu ba wani haduwa suke ba ko a ce bata san shi ba ko da ta hange shi, don bai cika
zuwa gidan ba a Kamfani yake rayuwar sa, daga gida sai ofis, Mukhtar ko aboki bai da shi, sai
Malam Tajuddeen mai gadin gidan Alhajin.
Ranar da ya fara ganin ta wata asabar ce, direba ya dauko ta daga makaranta yana cikin
motar Alhaji a harabar gidan yana jiran fitowar Alhajin zasu wuce duba wata gona da Alhajin ya
saya a garin Bindawa, ji yayi yarinyar wadda fitowar ta Kenan daga mota tana zagin direban ta
cikin daga murya wai yayi parking ba a kofar shifa falo ba, yana nufin da kafar ta zata taka har
kofar falon ko yaya? Ga zakin murya cau ga zare ido kamar tana yi wa dan ta fada, shi kuma
Malam Sirajo yah au rawar jiki yana bata hakuri tare da cewa Mukhy ne yayi parking a kofar
falon yana jiran fitowar Alhaji, amma duk da yadda ya kwantar da kai ya bata hakuri data fito sai
da ta tsarta masa miyau a fuska ta ce donkey, monkey, idiot!
Mukhtar na shirin fitowa ya dauke yarinyar nan da mari sai ga Alhaji ya fito hanzari yan cewa
yi hakuri Mukhy, ina jiran isowar TAFISU ne kada ta dawo bana nan an tafi dauko ta yana daga
ido kuma ya gan ta cikin uiform din ta ta doso shi da gudu, Alhaji ya bude hannu yana Oyoyo!
Da Tafisu na. Ta rungume Alhaji duk da ta fara kirgen dangi ma a lokacin suka yi ta murnar su
kafin Alhaji ya ce mata ta shiga ciki, ya sa an shirya mata komai, gobe sabuwar matar da auro
zata tare bazatayi kadaici ba wannan hutun. Direban data tsartawa miyau shi ya dauko jakar ta
ya shigar mata da ita bayan yasa hankici ya goge fuskar sa, a ranar kuma ya ajiye aiki a gidan
su Amani.
Mukhy da Alhaji suka kama hanyar Bindawa, Mukhtar ke tukin Alhaji na gefen sa yana bashi
labarin itace tilon yar sa Amani da yake bashi labarin tana makarantar kwana, ya ce ka gan ta
Tafisu akwai rigima ga kyuya, nikadai nake iya mata. Ai komai nata na uwarta ta debo, yadda
Jalan haka Tafisu take, kullum ina godewa Allah da bata debo kannina ba Mukhy dai tuki yake bai ce komai ba, amma a ran sa ya ce ai gara da kamannin naka ta
debo, da wannan halin nata na rashin kunya, yar karama da ita da raina na sama da ita. Shi bai
taba ganin rashin tarbiyya irin na yau ba. Imagine in shi ta yi wa abinda ta yiwa Malam Sirajo,
wallahi sai ya mare ta, kuma daga ranar ko nawa ake biyan shi bai kara aiki a gidan su. Basu kuma kara haduwa ba har ta koma hutu, don shi ba wani zuwa gidan yake ba sosai,
idan ba Alhaji ya neme shi a gida ba, duk harkokin su a kamfani suke yin su.
Ya zama cewa in tazo hutu sau tari ya kan gan ta ko daga nesa ne, a harabar gidan ko a
falon Alhaji, itama ta kan hango shi daga can saman balcony na saman benen ta, ko a falon
Alhaji in suna ganawa ta sirri, wani lokacin ta kan shigo, in ta gan shi sai ta koma,