Showing 36001 words to 39000 words out of 44786 words

Chapter 13 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf

ta saba yanzu in
Amani ta kira ta, to ta san Mukhtar ya kunso mata. Ita kuma ko kadan ba ta ganin laifin sa, ina
laifin mai son Baban ka? Mai taimaka masa?
Amani ta gyada kai kamar Hamida na kallon ta, ta ce, Shi ne Hamida, karewa ma yau komai
ya kare, tunda Daddy ya ba shi sadakar aure na.
Wata muguwar dariya ta kutsowa Hamida, ita da ma wannan so da Alhaji ke wa Mukhtar ta
san karshen tika-tika tik! Ko dai Mukhtar da kan sa ya ce yana son kyakkyawar diyar ubangidan
nasa, ko Alhaji ya hada da kan sa, don cikar kaunar da yake yi wa Mukhtar da kara janyo shi
jikin sa har abada. Hamida ta yi dariya iya dariya, amma bayan ta kashe wayar ta. Sannan ta sake kiran Amani
ta ce,
Afuwan Habibty, network ne, na ji abin da ya faru, amma abu bai yi dadi ba, shi ko Alhaji mai
yasa zai yi haka? Bayan ya san ba kwa jituwa? To amma ke yanzu a tunani da hankalin ki me ki
ka yanke?

Za ki yi wa mahaifin ki mai son ki, mai kaunar ki, mai tattalin farin cikin ki, mai hidimta miki iya
rayuwar sa biyayya ne ko kuwa kasa za ki bada masa a ido? Maganar Alh. Sadi fa? Ina ta
kwana?
Amani ta yi maza ta ce, kada ki daure ni da jijiyoyin jiki na. Ai hakkin sa ne ya so ni ya kula da
ni, amma banda auren dole. Da ne Daddy yake so na Hamida, yake kauna ta, yake tattalin farin
ciki na da gudun bacin rai na amma banda yanzu.
Idan har zaki lura da kyau zaki gane Mukhtar kadai yake so yanzu, tunda har yana fadin bai
iya hada jinin jikokin sa da na kowa sai nashi.
Ta sake rushewa da kuka, ta ce, Hamdy, ina cikin tashin hankalin da Allah kadai zai iya fidda
ni. Tunda har Daddy ya yi wannan tunanin. Kin sani na ki jinin mutumin nan da duk abin da ya
shafe shi, tun yanzu sai abin da ya ce ma Daddy, ina ga ya zama son inlaw din sa ko ya haifa
masa jikokin da baya da su? Ai shikenan kuma Daddy cewa zai yi ba ni ya haifa ba shi ya haifa. Hamida na ta guntse dariya, ta ce, Fisabilillahi Habeebty me ye abun tashin hankali a
wannan abun arziki? Cewa nake da tsoho zai aura miki saan sa? Da ki ka yi hakuri kika
fawwalawa Allah kika kuma bashi zabi, nima kuma nayi ta taya ki da addua ba gashi Allah ya
amsa ya dube mu ba? Shi da kan sa Daddyn ya fasa ba tareda rayuka sun baci ba, ya zabo
yaro santalele ya baki, son kowa, yaro sabon jini mai ilmi da nagarta, kuma mafi soyuwa a
zuciyar sa?
Ai kawai Amani ki manta da wata kiyayyar ki maras hujja, maras madafa maras dalili face
envy dake damun ki a kan sa, ki bawa Mukhtar dama ki san ko shi waye a wannan fannin, ta
hanyar yi wa mahaifin ki biyayya.
This man is a treasure!.
Hamida ta karasa fadi kasa-kasa ba tare da ta san lokacin da kalaman suka fito ba, tana jin
dan wani kishi-kishi a ran ta. Domin tun ganin ta da Mukhtar na farko ya tsaya mata a rai, ya
kuma shiga zuciyar ta. Har Allah-Allah ta ke Amani ta kira ta ta bata complain din sa don ita
haka nan abun yana saka ta nishadi. Wato tana son hirar Mukhy da Amani ke yawan yi mata
duk da cewa bata arziki bace.
Amma daga ranar yau insha Allahu ba za ta kara saka komai a ran ta a kan Mukhtar ba, sai
fatan daidaita tsakanin sa da sahibar ta.
A tata fahimtar sun yi balain dacewa da juna, kuma ita ma kamar Alhajin tana ganin ba
wanda ya dace da Amani sai shi, ba kowa ne zai iya auren Amani ya kuma jure zama da ita ba.
Sai mai jan wuya.
Gara shi Mukhtar din, tunda ya san mutuncin mahaifin ta, mai yiwuwa kuma ya san duka
halayen ta tunda ba yau suke tare ba. Don haka zai iya hakuri da jure zama da ita.
Ban gane me ki ke kokarin fada min ba Hamida?.
Hamida ta ce, Eh, ina nufin Mukhtar is a treasure ga duk macen da tayi saar samun sa a
matsayin miji kuma abokin rayuwa, hes a rare gem, sannan gashi mutum na musamman a
halayya da dabia mai dauke da dukkan attributes na cikar mazantaka. Ina nufin. mutum ne daya
cikin dubu, wanda kafin ki samu kamar sa a wannan zamanin sai an tona. Kamata ya yi ki gode wa Baban ki for giving you this treasure. Amani ta yi maza ta katse ta
da cewa, Ai sai ki zo ke a ba shi ke sadakar. Na yi rantsuwa duk yadda zan yi in fidda kudin nan
daga yau zuwa gobe zan yi in komawa mai binciken nan ya ba ni adireshi da lambar wayar
Mama na. Na rantse guduwa zan yi Hamida, da in auri yaron Baba na kuma wanda ban san

asalin sa ba, sannan mai mugun hali irin na Mukhtar gara na gudu gun uwa ta ko a bukka take
mu rayu tare.
Dama can na ki tafiya ne sabida Daddy da tunanin kaunar sa gareni, amma yanzu na tabbata
wallahi ya fi son bare a kaina.
Hamida ta kama kai, cikin cewa, Ki daina rantsewa Amani, Uban da ya haife ka baya hada
kaunar ka data kowa sai dai kawaici. Ba zan gaji da ce miki a kowanne alamari da ya tunkaro ki,
ki dinga neman zabin Allah ba, hakan shine daidai, kullum ina gaya miki haka. Yanke hukunci
cikin fushi kuskure ne babba, ki yi sallah rakaa biyu ki nemi zabin Allah ta hanyar istikhara da
Annabi SAW ya koyar, idan Mukhtar alheri ne a gare ki da addinin ki, Allah ya sanyaya zuciyar
ki ki karbi zabin mahaifin ki da hannu bibbiyu. Idan babu alkhairi Allah ya sa Daddy ya janye da
kan sa, ba tare da kin bata da mahaifin ki ba.
Amani ta ce cikin hargagi. Daman na san ba za ki taba bin bayana ba a nan, ke kadai ki ka
rage min da zan ji sanyi daga gare ta. Ba irin bayanin da ban miki a kan waye Mukhtar din nan
ba, da rashin mutuncin da yake yi min, kamar ba a karkashi na yake ci ba.
Amma kin ki ganewa da gangan, kullum sai dai ki yabe shi, saboda farar fata da bakin gashin
kan sa na rudar ki. Insha Allahu daga yau ba zan sake kiran ki in kawo miki kuka na ba, don na
san ba za ki share min hawaye ba in dai a kan Mukhtar ne.
Zan nemo mahaifiya ta da kaina in koma inda ta ke duk yanayin da zan same ta, na san ita
ba za ta taba yarda a yi min auren dole da wanda ba na so kuma ba zan taba so ba, har duniya
ta nade.
Ta kashe wayar ta tana kuka ta bar Hamida da mutuwar jiki. Ta fara yarda da gaske Amani ba
ta kaunar Mukhtar, ba yin kanta bane, tunda yau ta zabi ta koma gun mahaifiyar ta bayan duk
gatan da Daddyn ta ya yi mata a rayuwa. Yau ta zabi ta bar shi. Ba ta san ya za ta yi ta ceto
kawar ta daga fadawa fushin iyaye ba. Ko kadan Hon. Usman ba irin uban da yaya za su
bijirewa umarnin su ba ne domin bai ragi Amani da komai ba, sai ma dai a ce soyayyar sa gare
ta tayi yawa, har babu kawaici a cikin ta. Ta yanke shawarar tahowa Katsina don ta taimaki
kawar ta, don da gaske tana kan dokin fushi wanda zai iya saka ta aikata da na sani ko ya raba
ta da mahaifin ta dungurungum.
A daren Hamida ta hau shirin tafiya Katsina a washegari.
Amani ta manta shaf da maganar tafiyar su Faskari, kuma ba ta san Daddyn ta ya saki Haj.
Rabi ba, ta bar gidan tun daren jiya. Ta kwana cikin mawuyacin hali da tunanin Daddy ya daina
son ta. A daren ta cire wadannan kudade naira miliyan biyar, ba tare da tunanin komai ba, sai
na son ganin mahaifiyar ta, ta tura wa mai binciken kwakkwafin ta. Ta tura masa shaidar receipt
ta layin wayar sa, tana yi tana tuna alkawarin bogi da Mukhy ya taba yi mata na cewa shi da
kan sa zai nemo mata mahaifiyar ta on koboless. Amma ya nemo din? Tun daga lokacin har
zuwa inda yau ke motsi bai kara tada zancen ba, saboda ashe sun hada baki da Daddy za su
nakasta farin cikinta ta hanyar aura masa ita.
Allah Sarki rashin sani, domin kuwa ko a daren bayan ya koma gida, duk da halin da yake
ciki ya rubuta cikin schedules din sa na gobe cewa daga Faskari zai saka Daddy a gaba da
magiya da lallashi da ban baki irin nasa, ya yarda su wuce su kai Amani ga mahaifiyar ta. Ba zai
yarda Daddy ya yi mata aure ba da sani da sanya albarkar Innar ta ba, in har tana raye. Wannan wani alkawari ne da ya yi wa Amani, da yake da kyakyawar niyyar cika shi, duk da
rashin jituwar da ke tsakanin su. Ba ya daukar alamarin mahaifiya da sauki, ko don irin son da

yake yi wa tasa Ummamin, wadda bai samu tata soyayyar ba shima, so he can feel for Amani, a
kan rashin soyayyar uwa, wannan wani abu ne da ba ya son tunawa a yanzu. Cikin kurakuran
da yake so ya taimaka wa Alhaji ya gyara ko hakki ya ragu a kan sa, har da kai Amani ga
mahaifiyar ta. Kuma alhamdulillahi tunda ya yi saa Alhaji ya amince, a lokacin da nadamar abubuwan da
yake aikatawa na kuskure ta zo masa.
To amma me? A washegarin ranar da asubahi yana kunna wayar sa da alert din banki ya fara
cin karo, mai nuna an cire kudi miliyan biyar, zuwa akawun din wani Balogun Sunday. A take ya
gane me Amani ke shirin yi, da ya tuna maganar su ta rannan a mota.
Mukhtar ya kama kai cikin mamakin taurin kan ta. Wato ta yanke hukuncin data ke ganin ya fi
mata. Tafiya Sierra Leone ko ta halin kaka, da dai ta amince Alhaji ya hada ta rayuwa da shi,
don su kula da shi tare a kan lalurar sa har muddin ran sa. A fili ya ce.
“Why Amani?
Gaggawa daga shaidan ne!.

Ya kuma tabbata don ta guje wa auren sa ne da mahaifin ta ya furta ta yanke shawarar
guduwa any how, ba ta kuma da inda za ta je da nisa in ba can din ba.
A take ya kira Alhaji, wanda a lokacin yana sallar asubahi a kan gadon sa daga zaune kamar
yadda yake yi. Ganin kiran Mukhy a daidai wannan lokacin ya san ba lafiya ba, sai da wayar ta
tsinke ya kuma idar da sallah, sannan ya kira shi da kan sa.
Alhaji ka kula da takun Amani, kada a bar ta ta fita, ka sa ta a gaba mu tafi Faskari tare da
taki da ta so.
Ta fidda kudin nan da na gaya maka tana son fiddawa don a nemo mata Maman ta. She is
desperate Alhaji. A taimaka mata. Bayan ni da kai na na yi mata alkawarin ni zan kai ta da
kaina, zan nemo adireshin daga gare ka.
Na tsara in mun gama da Faskari, in roke ka mu bi jirgi zuwa Sierra Leone din mu dangana ta
da mahaifiyar ta. Ta yanke wannan hukunci cikin fushi, don haka ka bi ta a hankali ka rarrashe
ta mu tafi Faskari tare, sauran ka bar komai a hannu na.
Alhaji ya nisa, ba ya son kai yar sa ga Jalan da iyayen ta, don ya san Jalan bata son sa,
kuma bazata taba son sa ba, don haka bazata so jinin sa ba, amma ya ya zai yi da Mukhtar
tunda ya dage ya tsaya wa Amani a kan hakan? Jalan ta taya shi rainon diyar sa ne ko ko ta
taba tunanin ta tako ta zo ta gan ta ko sau daya? Ai ta san inda ta bar yar in dai ba kiyayyar da ta ke masa ce ta shafe ta ba, ya ci a ce ko sau
daya ta waiwaye ta ta ga cewa ta rayu ko ta mutu?
Alhaji ya manta cewa shi ya raba tsakanin uwar da yar tun ranar da ta kawo ta duniya, shi y
araba wannan kaunar da hannun sa, ya bar Jalan a halin da ita ma ba shi da tabbacin ta wuce
ko ta rayu, Hausawa suka ce, laifi tudu.
Alhaji ya ce, Kada ka damu, I will take care of her kafar mu kafar ta zuwa Faskari, in ka ga ta
je wani waje bayan Faskari, to sai tana a matsayin matar ka, bisa yardar ka da amincewar ka.
Biyayyar da ka yi min da kyautatawar ka gare ni Allah ya ba ka masu yi maka kai ma. Allah
ya sa Amani ta zamo alkhairi gare ka da addinin ka. Allah ya ba ku zuria masu irin halin ka, ba
masu irin nata halin ba.
Dan murmushin mamaki Mukhtar ya yi, yana so ya ce, Alhaji na furta maka na amince ne?

Amma kunya ta hana shi cewa komai, don karamcin Alhaji gare shi ya zama abin kwatance,
tunda har ya amince ya ba shi auren tilon yar sa ba tare da ya san asalin sa ba, ba tare da ya
san iyayen sa ko wani nasa ba, ba kuma tare da ya ga mahaifar sa ba. Sannan ba tare da
amincewar yar tasa ba, wadda kowa ya san ba ya son bacin ran ta amma a kan sa ya yarda ya
bata wa Amani karshen batawa da kan sa.
Ko don wadannan dalilan, da wasu da dama, sai ya ji ba zai iya badawa Alhaji Usman kasa a
ido ba. Zai rike masa amanar yar sa da dukkan halayen ta ababen ki, da dukkan tijarar ta da
rashin kaunar ta gare shi.
Zai iya rantsewa cewa zuciyar sa ta dade tana son AMANI, ita kuma ba ta son sa da alaqar
aminci dake tsakanin sa da mahaifin ta, wanda ya san shi ya fi komai sayo masa bakin jini, kishi
da tsana a idanun ta.
Alhaji ya soma kokarin kiran Amani bayan sun rabu da Mukhtar a waya.
Tana kallon kiran Daddy nata shigo mata amma ta kai zuciya nesa ta ki dagawa har ta katse,
ya sake kira. Amani sai hada kaya ta ke tana kuka, amma ba ta amsa ba.
Alhaji ya kira Malam Tajuddeen ya ce masa a rufe gate kada a bar Amani ta je ko ina in ba
tare da su ba.
Daidai lokacin Mukhtar ya shigo gidan, misalin karfe bakwai na safe, suka gaisa da Malam
Tajuddeen da sauran maaikatan gidan, ya wuce maadanar motoci ya fiddo wadda za su tafi a
cikin ta ya zuba mata mai da kan sa, sannan ya ce da Ali ya wanke motar amma wajen ta ba
cikin ta ba, sannan ya karasa sassan Alhajin. Da sallama ya shiga falon, Alhaji ya amsa ya ce, Yanzu nake so in kira ka ka je ka turo min
AMANI, tana can side dinta a saman bene. Na kira na kira ta ki dagawa.
Mukhtar ya ce, Alhaji ka fara yin wanka tukunna, ka karya kumallo, ka kwantar da hankalin
ka, everything will be alright, in sha Allahu.
Ya taimaka wa Alhaji ya yi wanka, ya fiddo masa manyan kaya ya saka, ya tambayi Alhaji ina
Hajiya Rabi don bai ga ta kawo breakfast ba har yanzu.
Alhaji ya ce, Na ba ta tikitin ta daren jiya ta tafi, tana barazanar danne ni da filo in ban sake ta
ba, daga kan ta na rufe aure in sha Allahu, zan zauna cikin kujerar nakasa in nemi lahira ta, har
zuwa ranar da waadi zai cika, kai dai ka rike min Amani da gaskiya, ka bunkasa mata dukiyar ta
har Allah ya baku zurria. Dan ku ya girma ya gaje ka kan shaanin kasuwancin mu. Idan na samu wannan na gama
samun duk wani farin cikin rayuwa.
A wannan lokacin Mukhtar ya jona kettle ya hada wa Alhaji coffee mai zafi ya bashi yana sha,
ya yi waya kitchen ya ce Rakiya ta shiryo karin kumallo ta kawo wa Alhaji, kuma ta kai wa
Amani. Ta lallashe ta ta tabbatar ta ci ko kadan ne,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login