Showing 39001 words to 42000 words out of 44786 words
Chapter 14 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf
don fita za su yi.
Alhaji na kurbar coffee dinsa yana jin abin da Mukhtar ke ce wa Rakiya, sai ya ji wani irin dadi
ya lullube ran sa. At least Mukhtar bai ba shi matsalar da Amani ta ba shi a kan hukuncin sa ba.
Ya tabbatar wa kan sa ko Mukhtar ba ya son Amani, to fa ba zai wulakanta masa ita ba duk irin
halin fitsarar ta, wanda a yau ya yarda rashin tashi da uwa ne ya janyo mata, ko wata
kwakkwarar uwar riko a gare ta. Kuma duk hakan ya faru ne bisa kuskuren sa da munanan
halayen sa.
Tun farko me yasa ya rabo ta da Sahura? Don kada ta sha wahala da rayuwar kauye. Me
yasa bai barta ta rayu a Funtuwa ta samu tarbiyyar data dace a hannun kanwar sa ba da
cikakken ilmin addini wanda zai sa ta san muhimmancin iyaye da girman da Allah ya yi musu?
Rakiya ta shigo ta kawo musu karin kumallo mai rai da motsi, sinasir ne da miyar ganye da ta
ji naman talo-talo, sai kunun gyada fari sal mai gardi. Mukhtar ya cikawa Alhaji plate ya tura
masa gaban sa yana ta yi masa hirar abubuwan da ke faruwa a company kwana biyunnan don
dai ya samu ya dauke damuwar da ke kwance kan fuskar Alhajin. Amma sai ya ji Alhaji ya ce, Na yi maka izinin hawa sama, har dakin TAFISU. Ka je ka zo min da ita nan cikin lallashi mu
ci abincin nan tare da ita.
Mukhtar ya rasa yadda zai yi da wannan umarni mai nauyi a gare shi na ubangidan sa,
amma ganin irin damuwar da ke kwance a fuskar Alhajin sai ya ce.
To Alhaji, amma idan ta ki fa? Zan dauko ta a ka ne? Ka san fa babu shiri irin wannan
tsakanina da ita.
Alhaji ya ce, Da irin haka ne za ku saba da juna. Har watarana ku kaunaci juna. Yanzu Amani
matsayin matar ka ta ke, shaidu kawai ya rage su shaida.
Mukhtar duk sai ya ji maganar ta Alhaji wani irin banbarakwai wai namiji da suna Hajara.
Alhaji ya kira Rakiya a waya ya ce ta zo ta raka Mukhtar sassan Amani.
Rakiya na gaba, Mukhtar na bayanta har dakin Amani. Ta kwankwasa kamar yadda ta saba
yi wa Amani.
Amani na can abu goma da ashirin ya ishe ta don har zuwa lokacin da ta tura wa Mr. Balogun
kudi da awanni biyu babu adireshi babu lambar waya na Maman ta da ya turo mata.
Ta yi ta gwada kiran wayar sa tun tana shiga yana kin dagawa har ta daina shiga
kwata-kwata. Ko dai an daina amfani da layin, ko an kashe wayar gabadaya. Sai ta dora
hannuwa bibbiyu a kanta tana son rusa ihu ko ta samu saidah.
Sai ga Rakiya ta murda kofar ta shigo, jin ta yi ta kwankwasawar Amani ba ta ba ta izinin
shiga kamar yadda ta saba ba, sai kawai ta shigo kan ta tsaye don ta ga ko lafiya.
Amani ta zuba wa Rakiya idanun ta da suka yi jazir da bacin rai, tana kallon ta tamkar ita ce
Balogun.
Rakiya ta karyar da kai gefe ta ce, Afuwan uwardaki na, Alhaji Mukhtar aka ce na rako wurin
ki. Alhaji da kan sa ya ce in rako shi.
Kafin Rakiya ra rufe baki, Amani ta samu zarafin ci mata mutunci, ko kunduma mata ashar,
Mukhtar din ya shigo dakin kan sa tsaye. Daga jikin kofa ya tsaya hannuwan sa harde da kirjin
sa yana kallon Amani da yadda a cikin dare guda duk ta zabure ta fice a hayyacin ta.
Rakiya ta juya ta fita har da rufo kofar dakin, tana fadin a fito lafiya Alhaji.
Mukhtar kallon ta kawai yake daga sama har kasa, wani irin kallo da bai taba yi mata ba. Duk
da cewa kayan barci ne a jikin ta gashin kan ta babu rufi, gashin duk ya tarwatse duk ya yi
buyaya da shi kamar sabon kamun hauka, shi a idon sa gani ya yi kamar an kara mata kyau da
kwarjini, duk da idanun ta sun jeme sun yi zuru-zuru din. Kallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin
Mukhy da Amani, kallon da su duka suka kasa fassara yanayin sa yayin da Mukhtar ya ji wani
abu mai kama da tausayi ya darsu a ran sa game da ita, ganin yadda duk ta sauya kamanni da
appearance a kwana daya.
Amma ya riga ya san Amani zuma ce sai da wuta ake iya sarrafa ta. Kamar ba zai yi magana
ba don ya san kiris ta ke jira ta saki tantrum, amma sai ya tuna damuwar da mahaifin ta ke ciki a
kan ta.
Ya tuna rokon da ya yi masa a kan ya lallaso ta ta zo ta karya kumallo tare da shi sannan su
wuce Faskari.
Alhaji yana da hope na cewa, shi kadai zai iya hakuri da tilon yar sa, mai tarin nakasu a
halayya da dabia, shi ya sa ya damka masa ragamar rayuwar ta ta hanyar da ta fi kowacce
muhimmanci ga dan adam, wato aure. Kuma a istikharar da ya yi daren jiya shi kam bai ji yana
kin alamarin nan ba, ya dai san zai sha wahala iyakar sha a hannun Amani, tunda Allah bai
halicci zuciyar ta da kaunar sa ba.
Mukhtar ya nisa, ya kira sunan Amani, ba cikin yanayin da yake mata magana da shi a baya
ba, na nuna halin ko in kula da alamarin ta. Wannan karon akwai kulawa da dan lallashi acikin
sautin sa.
Ya ce, Ki sani cewa komai ya yi zafi ga bawa bai fi karfin Ubangiji ba. Iyaye suna gaba da
komai a rayuwar dan Adam. Mahaifin ki ba yaron ki ba ne, ba kuma dan ki ba ne da za ki dinga
yi masa duk abin da ki ka ga dama ba.
Ya kira ki kin ki amsa kiran sa, kin bar shi a damuwa, anya Amani kina son gamawa da
duniya lafiya?
A hakan kuma ki ke so Allah ya ji tausayin ki ya hada ki da mahaifiyar taki? Alhalin shi din da
ya maye miki gurbin ta ba ki tsaya kin kyautata masa yadda yake kyautata miki ba?
Me ki ka dauki kan ki Amani da ki ka zabi yin fito-na-fito da mahaifin ki? Ni da bai haifa ba na
zabi in masa biyayya a kan umarnin sa, don na san ba zai ba ni matar da za ta cutar da ni ba.
Sannan yana cikin hali na rashin lafiya yanzu, wanda kyautatawa da tausasawa kadai yake
bukata daga gare mu. Yau in aka ce babu Alhaji sai kin fi kowa zama abun tausayi, ba ki ga tsuntsu ba ki ga tarko,
baki rabauta daga biyayyar uba ba, sannan uwar ma ba za ki san inda za ki gan ta ba.
Na zaunar da ke na ce ki bi shi a hankali, ki bar komai a hannu na, amma ki ka yi kan gaban
kan ki saboda ke ba ki da mafadi kuma ba ki yarda kina da na gaba da ke ba.
Zan iya rantsuwa da Allah kan cewa yan damfara ki ka tura wa kudi, bayan na gaya miki
kada ki tura, gaggawar ta mece ce tunda na ce ni da kaina na yi alkawarin kai ki ga mahaifiyar
ki amma karkashin umarni da amincewar mahaifin ki?
Yanzu ina adireshin da ki ka sayo miliyan biyar sai ki ba ni in gani.
Kuka ya kubucewa Amani, ba kukan shagwaba ta ke yi ba yau, kuka ne na kubucewar azanci
da tausayin kai. In ta ce maganganun Mukhtar ba su yi tasiri a zuciyar ta ba ta san ta yi karya.
Da gaske Daddy ya wuce komai a gare ta, kuma bai cancanci reactions din da ta ke yi mishi ba,
amma zabin da ya yi mata ne ba za ta taba karba ba, domin ya kaskantata, ya sayar da ajin ta
ya zubar mata da ego din ta, muddin Mukhtar zai bai wa auren ta.
Daga nan har kotun koli za ta je don neman hakkin ta a kan hakan, bazata taba yarda tayi
auren kaskanci ba, auren yaron Alhaji mara asali, mai halayen da ta ki jini, wato musamman
girman kai, da kin yarda a taka shi, ita kuma ta saba taka kowa da ke kasan ta, tunda ta yi
kokarin riskar mahaifiyar ta don ta samu mafaka a gun ta abun ya ci tura. Tana ta kuka tana fyace hanci da share ido da gyalen ta, Mukhtar ya ce, Taso ki biyo ni,
mahaifin ki na son ganin ki, in kuma kin ki tashi ko a ka ne zan dauke ki in kai masa ke, na
rantse.
A yadda ta ga idanun sa sun rikide cikin bacin rai ta san sarai zai iya aikata abin da ya furta,
sai kawai ta mike, ta na so ta ce ya ba ta wuri ta canza kaya, amma ya kasa ya tsare a kofar
dakin yana muzurai na ko ta wuce ko ya ciccibe ta.
To ka je zan canza kaya. Ta fada a turbune, fuskar kamar wani kauye wai shi Durbunde
saboda turbunewa. Mukhtar sai ya ga akwai bukatar ta canza kayan, bai kamata ta tafi har
Faskari da kayan barci ba, sai ya juya yana fadin, Na ba ki five minutes, in ban gan ki a falon
Alhaji ba da jakar fita unguwa da trolley din matafiya da kayan ki da zasu yi miki a kalla kwana
bakwai a ciki zan dawo.
Don tafiyar tamu ba mu san har yaushe za ta kai mu ba, tunda neman sulhu da gyara
zumunci ne zai kai mu.
Ya fice a dakin ya bar mata daddaddan turaren sa na sirnanawa a kofofin hancin ta.
Tana kuka tana komai ta canza kayan jikin ta, ta sanya doguwar riga sannan ta yi maza ta
yayibo mayafi ta jefa kaya kala uku da man shafawa da deo spray a trolley da yan sauran
abubuwan bukatar ta. A gurguje ta rufo dakin ta fito kada ya kara dawo mata daki, don ko
turaren sa ba ta son ji, balle ganin cunkusasshiyar fuskar sa mara annuri da rashin walwala. Sai da ya taimaka wa Alhaji ya gama kintsawa ya debar masa duk abin da zai iya bukata har
nan da kwanaki bakwai kama daga magungunan sa da kayan sanyawa ya kai komai mota. Ya
dawo kenan ya tadda ita a falon na Alhaji, da jakar tafiya a gaban ta. Alhaji na ta faman lallashin
ta kamar shi ne yar ita uban, yana gaya mata duk abin da ta ga ya yi mata soyayya ce, idan
kuma har ta zabi ta bijirewa umarnin sa ta hanyar tozarta shi a idon Mukhtar, to kuwa zai yi
hakuri da duk son da yake mata ya sallama ta, zai kwace komai da ya mallaka mata ya kai ta
wajen mahaifiyar tata su karata.
Mukhtar ya yi kamar bai ji me Alhaji ke fada ba a karshe, ya ce, Alhaji komai ya kammala,
mota an mata full tank an kuma wanke ta sai tafiya ya rage.
Allah ya yi maka albarka Mukhtar, dauki kayan ta ka sa mata a mota, jakar hannun ma karba
mata.
Yar murmusawa ya yi, a ran sa yana fadin, Alhaji ke kara lalata yarinyar nan, ya karba mata
jakar hannunta wato ga mijin Hajiyar Faskari ko? Ko Alhaji ba ya karba wa briefcase in za su fita
balle wannan fitsararriyar.
Tana jira ya daukar mata har jakar hannu kamar yadda Alhaji ya yi masa umarni, sai kawai ta
ga ya dauki trolley dinta da hannu daya ya bar falon. Ita ta kai zuciya nesa ta dauki jakar ta
rataya sannan ta turo Alhaji a kan keken sa.
Ita da Mukhtar din suka yi kici-kicin saka Alhaji a mota, ya nade keken nasa ya saka a boot
din motar. Gidan baya ta shiga ta zauna gefen Alhaji don tana ganin ta fi karfin ta jera kafada da
Mukhtar a gaban mota, alhalin yana matsayin yaron Alhaji ko kuwa ta ce direban ta. Zuciyar ta
ba za ta taba ba shi wani matsayi bayan wadannan ba. Alhaji zai yi korafin muhallin da ta zaba don zama sai gani ya yi Mukhtar ya tada motar, ko a
jikin sa, shima baya so ya hada kafada da ita, ko ba komai ta kula da Alhaji a bayan motar
wanda suka yi masa kujera ta musamman suka sanya mishi belt sosai.
Kamar ya san a karkashin zuciyar ta ta so ya yi magana ta gaya masa mara dadi, ta gaya
masa har abada shi yaron gidan su ne, kada wani zancen aure da Alhaji ya furta ya rude shi.
Sai aka yi saa bai tanka mata ba, ya ja mota cikin tukin sa na nutsuwa, na kwarewa da kamala
suka yi reverse, wanda ba haka ta so ba. Mukhtar ya sa a ran sa ba zai dinga biye mata ba yanzu kamar da, saboda jiya da ya yi wa
Alhaji b.p ya ga ya hau sosai. In ta rasa wanda za ta yi wa rashin kunyar dole za ta yi shiru ta
bar su su ji da abin da suka fuskanta yanzu, wato gyara tsakanin Alhaji da yan uwan sa.
Malam Tajuddeen ya bude musu kofa tare da daga musu hannu yana fadin, a sauka lafiya.
Mukhtar ya dan daga masa hannu shima, sannan suka fita gate din gidan. Sannu a hankali ya
hau bisa kwalta, sannan ya soma shimfida gudu da su kamar zai tashi sama dasu, abin da ya
san Amani ba ta so, wato gudu da mota musamman a babban titi irin wannan, baa cikin gari ba. **** ***** ****
Suna tafe kan titin da zai shiga garin Faskari Mukhtar ya kunna karatun Alqurani mai tsarki ya
kure a radiyon motar cikin Suratul Baqarah, duk yadda ta ke so ta yi masa korafin gudun da
mota da yake yi da su albarkar wannan karatun da ya kure sai ta kasa, ta samu kan ta da
nutsuwa tana sauraron ayoyin na karshe na suratul Baqarah da taji sun mata dadi, kasancewar
ita bata saba sauraren karatu ba sai music.
Mukhtar na tafe yana tambayar kan sa shin ko Amani ta taba yin islamiyya? Balle a je ga
batun sauke Alqurani? Ya nisa, umh. A lokaci guda Alhaji na tuhumar kan sa da ka sa a ran sa
da sakaci mai yawa da ya yi a kan tarbiyya da kuma upbringing din Amani in general. Ya tuna
ko hizfi biyar ba ta da shi a kan ta, don tun tana karama da ya dauki wani bayerabe yake zuwa
gida yana koya mata karatun Alqurani, da ta yi wayo ta kai munzali sai ta nuna ba ta raayin
koyarwar malamin. Dole Alhaji ya sallame shi. Daga wancan lokacin kuma Amani ba ta kara
shaawar tahfiz ba, dan wanda ta samu a gun bayeraben nan da shi ta ke karatun sallah har
yau.
Alhaji ya nisa yana fadi cikin ran sa,
na yi kuskure mai yawa a rayuwa ta. Allah ka bani ikon gyarawa kafin ka dauki rai na. Allah
ya sa Mukhtar ya rike min Amani da dukkan nakasun ta, ba tare da ya goranta mata tarbiyya,
ilmin addini da goyon gatan da na yi mata ba.
Yau ga shi ga dukkan alamu Amani na so na kasa lankwasa ta. Wa ya janyo komai?
Alhaji ya kara kudirewa a ran sa sai dai Amani ta mutu, amma sai ya cika kudirin sa, in yaso
ya wanke gawar ta ya fara kaiwa gidan Mukhtar kafin ya danganata da kushewar ta, amma ba
ta da miji insha Allahu sai Mukhtar din sa. Idan ta bijire masa wannan karon zai ba ta mamaki.
(Alhaji ya manta icce tun yana danye ake tankwara shi). Daidai lokacin da Mukhtar ya karya kan motar suka hau burjin da zai shigar da su garin
Faskari, Alhaji na ta kallon garin iyayen sa da kakannin sa with nostalgia, yana kokarin tuna ko
yaushe ne last shigowar sa Faskari? In zai iya tunawa daidai tun lokacin da yake nema kujerar
sanatan Katsina ta Tsakiya yana neman kuriar karamar hukumar tasa. Da ya zo ya dan yarfa
musu. Ya tuna lokaci na karshe da Yaya Idrisu ya kira shi a waya yana gaya masa Kamilu dan
sa ya kammala karatu an turo shi hidimar kasa cikin jihar Katsina ko zai ba shi muhalli ya zauna
a gidan sa yayi hidimar kasan?