Showing 1 words to 3000 words out of 25520 words

Chapter 1 - INDA RAI B 3 end Book True Wallafar A'isha Aliyu Garkuwa .pdf

01/01/2024

*INDA RAI*
*Part 3. Page 1*
NA
*Aysha Aliyu Garkuwa*


Gyara zamansa yayi tare da fesar da sassayan numfashi murya cike kamala da daraja ya fara
motsa lips inshi cikin nusar wa yake maganar.
"Ita ƙaddara haka take juya fari ya koma baƙi, ko ta juya baƙi ya koma fari, haka Allah ke tsara
abubuwa bi bayan bi, komai na faruwa tamkar yadda yake a ru babuce a lauhul Mahfouz, babu
abin da ke sauya baƙar ƙaddara ta koma fara kamar kusantar Allah da addu'a mai cike da yaƙini
da kuma tsananta wa wajan kiyaye dokokin Allah, haka babu rayuwa mai daɗi sama da bin
Allah da manzon sa, kiyaye dukkan dokar Allah na saka hasken zuciya da kwarjini da arziƙi da
ɗaukaka, ka bi Allah ka huta da masifar duniya, domin shi Allah ne ya ce kiyaye sallah na hana
mutum aikata alfasha.
Ubangiji Allah ya ba mu ikon bin Allah sau da ƙafa."
Tajj ya ƙara sa yana rufe alƙur'anin da ya biya wa Laylah.
Cikin nutsuwa Laylah ta ta ce.
"Amin Amin."
Ta ƙare tana rufe nata Alkur'anin tana turawa Afisha abin wasanta.

Ishmah ce ta shigo da tirtsetsan cikinta tana wata iriyar tafiya kamar mai shirin faɗuwa ƙasa.

A hankali ta zauna muryarta na ɗan rawa ta ce.

"Ina zaton naƙuda ce....."

Da sauri ya miƙe ya tunkarota ya taimaka mata ta miƙe suka koma ɗaki.
Yana dubawa ya ga tabbas haihuwar ce, yana ƙoƙarin taimaka mata wajan saka kaya Addawa
ta shigo a ƙagauce.

"Laylah ta ce min ta ji Ishmah na faɗin naƙuda ce..."

Cikin tashin hankali ya ce.

"Ita ce, asibitin za mu tafi yanzun nan."

Da sauri Addawa ta yo wajan Ishmah cikin kulawa.

"Sannu Ishmah, sannu kin ji daure, Ubangiji Allah ya raba lafiya, in Sha Allah cikin sauƙi za ki
haihu kamar yadda kika haifi Afisha."

Da Addawa da Tajj ne suka taimaka mata dan ilahirin jikinta rawa yake haka ciwon murɗa mata
yake sosai cikin jin azaba bayan sun shiga mota ta kasa daure ta na nishi ta ce.

"Wayyo Allah na Yah Afif wannan ciwo! Ya yi min yawa ya ilahil alamina ka sassauta min, dan
Allah Sheykh ka yi min addu'a."
Sai kuma ta sauke Ajiyan zuciya tana fitar da wani irin nunfashi.

Idan ciwon ya lafa kuma sai gumi, da ya dawo sai ta ƙanƙame hannunta akan mararta tana
nishin azaba jikinta na karkarwa ta ce.

"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan wa anta taj'alul hazna iza shi'ita sahlan."

Sai ta fara nishin azabtar jin zafi.

Da wannan ciwon suka isa asibitin, Dr Farida da Sister Nuraini, ce suka amshe ta.

Shi kuwa Tajj yana can neman zam-zam ɗin sa daya tanada dan ya yi mata addu'a.

Sai da ya gama ya kawo mata har a lokacin tana nuƙurƙusar azaba dan har ƙwalla sai da ta yi,
duk jikinsa ya mutu murus hak hankalinsa ya tashi dan bai taɓa ganinta cikin wahala irin yau ba.


Sai kusan bayan minti goma kana ta fara nishin da ke tabbatar da fitowar ɗa.

Da sauri ya sha mur ya ce Dr Farida da Nuraini su fita ya yi supporting ɗin matarsa.

Ala dole suka fice dan dama sun san a rina sun saba,

Cikin hukuncin Allah ta haihu ɗan yaron na fitowa wani ya ƙara fitowa mahaifarsu kuma ta zama
ɗaya, sun tabbata Identical twins kenan.

Tuni kukansu ya karaɗe asibitin, nan da nan Tajj ya yanke musu cibi ya shinfiɗe su kan ƙirjin
Ishmah yana murna da farin cikin baiwar Allah a kansa na ba shi duk abin da ya nema, da fari
ya nemi Afisha Allah ya ba shi yanzu ya nemi ƴan biyu ga shi ya samu duk maza.


Ita kuwa Ishmah duk da a gajiye take sai da ta ji tsananin farin cikin godiya ga Allah.


A lokacin da Tajj ya kuma yin sujudush shukur, a lokacin Dr Farida ta shigo tana cewa wallahi
sai ta taimakawa Dr Ishmah ko me za a yi ayi, tana zuwa ya ɗebo yace ta gayawa dukkan
ma'aikatan cikin asibitin tun daga kan Doctors har Nurses cewa zai ninka musu albashinsu na

wannan watar. patients ɗin dake cikin Hospital ɗin kuma yau duk kyauta za'ayi musu komai.


Kowa cikin asibitin cike yake da murnan abin alherin da ya samu, kana bakunansu ɗauke da
addu'ar Allah ya raya ya ƙara lafiya.

Ko da Laylah da Hamisu da Zulaihat da suka zo, dukkansu sun yi murna matuƙa.

Cikin jin daɗi Laylah ta ce.

"Ni ƴar gata, lokaci ɗaya na samu ƙanne maza har biyu ga Afisha ta kuma, alhamdulillah."

Hamisu kam matsowa yayi kusa da yayarta yana cewa.
"Ku dai rayuwa na yi muku kyau, Allah ya ƙara kyawun rayuwa a gaba, duk sanda kika tashi
haihuwa anty Ishmah sai ki haifa mana kyawawan yaran da za su zama abun kallo da ta'ujibi a
wajan kowa, gaskiya ƴan biyu suna da kyau, ga kama nan sak da Afisha." Murmushi tana tana
kallonshi cikin son ɗan uwan nata da takeji duk Qatar bata da kamarsa.
Sai dare ta koma gida domin ƙalau take daga ita har yaran, Afisha da ta fara iya magana duk da
ba sosai ake ganewa ba saboda tsamin baki irin na yara ganin kowa na murna itama ta fara
murna tana ta nuna yaran tana magana.

"Amty lelah ce ta she kannena ne ko?"

Haka take ta faɗa tana nuna yaran tana murna.

Ko ta sunkuyar da kanta ta rinkayi karatun Qur'ani tana tofa musu.

Tun a daren Tajj ya raɗa musu sunan da tun kafin a samu cikinsu suka yanke shawarar sa.
Ayeed da Ayaan. Rahma da Dr Amdaz ma a cikin daren ya kawo ta dan ta yi tsalle ta dire akan
ita fa dole ta zo ta yi wa anty Ishmah zaman wanka, daƙyar ya lallasheta akan kwana ɗaya za ta
yi ta dawo dan ya ce sai dai shi da ita su je gidan su tare dan ƙafarsa ƙafar matarsa.
Ethiopia kuwa sosai yan uwa suka rinƙa farin ciki da samun yan tagwayen Tajj More especially
team Arfah da Imran.

Hakama su Abba a Nigeria.

Ranar suna kam sun sha shagali duk lecture aka yi kamar wancan sai dai wannan an yi sa ne
akan falalar aure da tara zuri'a.

Ma sha Allah walima ta yi walima an raba kyautuka yara sun sha addu'a da fatan tsawon rai da
Kyakkyawar rayuwa.

Tun da akayi suna Hamisu ya ɗauki hoton Ayeed da Ayaan ya tura wa Arfah da Imran suke
tsananin murna dan sai da Arfah ya tura group ɗin su na dangi ya ce Uncle ɗin su na can Allah
na azurta shi da zuri'a masu albarka, haka kuma ya turawa Ya Abana yana faɗa masa idan ya
kore shi, to Allah ya raya shi da zuri'a cikin ƙanƙanin lokaci haka dai rayuwa taci gaba da
tafiya....


BAYAN SHEKARA BAKWAI.

Hall ne faffaɗan gaske, da ya haɗa manyan malaman musabaƙa na duniya.
Ko wacce ƙasa da wakilanta da kuma ɗalibanta wajan.
Kan mutane kowa ka gani cikin shiga ta kamala, dukkan wakilan gasar larabawa ne, gefe guda
kuma manyan malamai ne da suke zaune Alqur'ani a gabansu suna kallo, can gefe kuma
mutane tsagi-tsagi ke zaune ɓangaren maza dabam da na mata, haka gefen dama yara ne
matasa masu kalolin uniform kala-kala.
Dukkansu sun yi shiru suna sauraran Ayeed da yake karatun musabaƙa, yana gamawa wajan
ya ɗauki kabbara, kana aka fara kiran sunayen ƴan hizfi talatin, sunan makarantar su Afisha ne
a farko kuma makarantar ce zata waƙilci musabaƙar Duniya baki ɗaya da za'ayu a ƙasar tasu
na Qatar. Dalilin da ya sa aka fara kiranta dan ita ta wakilci makarantar ta su.


Cikin nutsuwa Kyakkyawar yarinyar yar matashiyar mai kimanin shekaru 8 da yan watanni a
duniya ta tashi sanye cikin Kyakkyawar shiga mai kamala uwa uba haiba da ƙwarjinta, a nutse
ta hau kan mimbari kana ta zauna bisa kujerar da aka tanadar musu, cikin ɗan taradadi ta
zubawa malamin da ke jan aya ido dan ta fara gabatar da nata karatun.
Cikin ƙwarewa malamin ya fara da Bismillah kana ya karanto tsakiyar suratul shu'ara'i.

Yana ajiye wa ta buɗe zazzaƙar muryarta da A'uziyya da bissimillah ta fara karatun cikin wata
ƙira'a mai fusgar hankalin da saka nutsuwar mai sauraronta da kuma kamanceceniya data
mahaifinta saidai banbancin muryarta na mace kuma da yarinta.


Tajj da ke zaune a cikin masu sauraro, tun da aka ambaci sunanta gabansa ya faɗi duk da yana
da confidence akanta, lokacin da ta fara ƙira'ar ya ji sautin muryarta na yarinta da kuma zaƙi sai
ya kwantar da kansa jikin kujerar ya lumshe ido yana jin sanyin daɗi da annushuwa kana
zuciyarsa na bin karatun cikin tabbatarwa kansa tana yin karatun dai-dai. Yanayin shirun wajan
da yadda duk al'ummar wajan suka bada ƙaimi wajan sauraron Afisha ya sanyaya masa rai da
ƙara masa daɗi ainun a cikin ransa.

Ita kuwa Ishmah, da hannunta ke riƙe yake da ƙaramar yarinyar ta da ta haifa Fatima suke ce
mata Daddey hankalinta ne ya kwanta tare da ƙurawa alƙalan ido tana kallon yadda suke gyaɗa
kai cike da nutsuwa da kuma kwanciyar hankalin yadda karatun nata ke fita harafi bayan harafi.
Hawayen farin ciki ya yi kwance saman idanuwanta, zuciyarta na harbawa ranta ya yi mata fari
ƙal, haka jefi-jefi tana kallon alƙalan cikin annushuwa da yadda jikinsu ya bayyana gamsuwa da
karatun Afisha dan sai jinjina kai suke cike da fuskar nuna gamsuwa.

Malamin ne ya sake janyo aya a cikin suratul Namli, nam ma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta ɗauki
karatun tamkar a cikin ƙwaƙwalwarta ta zana, harafin na fita dai-dai, haka babu algus a wajan
fitar da gunna da jan harka, da bayar da lamunin dai-dai-ta kowanne Ikfa'i Idgami, Iƙlabi, tamkir
da tafkeer, cikin lokaci ƙalilan ta saye duk mutanen wajan da dadɗan karatunta na shigar zuciya
da sa sanyi a zukatan masu sauraro mafiya yawa hawaye ke cika mazauna wurin ido.

Wani daga cikin malaman ne ya sake katse ta ya ɗauko suratul Ƙamar, har da Fathi da Gafir,
dama wasu surorin dukkan surorin nan babu wata sura da harafinta ko tajweedin ta ya ɓace
mata, ta biya su daidai.

A haka aka sallame ta.

Nan hankalin Tajj ya kwanta yadda ya ji kabbarar manyan malamai, nutsuwa da wani tsantsan
farin ciki na ratsa shi bisa baiwa da ni'imar Allah a gare sa, haƙiƙa samun ta a matsayin ƴa
babbar ni'ima ce, wannan kaɗai ya ishe sa wannan kaɗai ya gama masa jin daɗin duniya har da
na lahira. Shi kam yana jinsa tamkar ɗan gata a wajan Allah ga shi ya azurta shi ta
mar'atussaliha ga kuma ƴaƴa nagari wanda su Allah ya kira ƙawar duniya, sai ya sauke
numfashi yana hamdala da hailala bisa babbar ni'imar da ya samu.

A haka ka yi ta yi har aka zo kan su Laylah ƴan hizfi hamsin, itama ta yi namijin ƙoƙari domin ta
saka shi cikin nishaɗin da Afisha ta tsunduma shi duk da dai su team ɗin Chaina sun basu wuta
da wuya in basu dokesu ba.

Sanarwar da ake yi tasa ya ɗaga kai yana sauraro.
"A yau muka kawo ƙarshen wannan musabaƙar, in Sha Allah zuwa anjima za a ji sakamakon
idan mun tattara makin muna yi wa kowa fatan alkairi. Sannan bisa sabon doka iyaye za su
koma gida, za a raka ƴaƴan su har gida da sakamon da suka samu, muna yi wa kowa fatan
alkairi."
Bayan angama sun ta so a hanya ya yi ta saka musu albarka har yana ƙwallar farin ciki Ishmah
kam sai waya takeyi da yan uwanta da tuni Hamisu ya tura musu.
Shi kuwa Tajj tuni yayi gayyatar masu decorations houses, domin yana da tsammanin ƴaƴansa
na da nasara.

Kafin su je har masu decorations ɗin sun hallara sun fara aikinsu tuƙuru, cikin ƙanƙanin lokaci
suka gama kana ya yi ordern special cake na taya ƴaƴan sa murna da kuma sauran kyautukan

da ya saya dan ya ƙarfafa musu gwiwa musamman su Ayid da yaune suke cika shekaru bakwai
cib cib.


A nutse suke a falo sun zubawa tv ido duk jikinsu na azarɓaɓin jin sakamakon gasar. Jefi-jefi
yana duba media, dan gaba ɗaya media ta cika da vedios ɗin Afisha na karatu mutane nata
faɗin amazing voice, dan murya ce gare ta ta yara mai ratsa zuciya da salon karatu mai fusgar
hankalin mai sauraro, wasu da yawa na faɗin karatun ya tsuma su ta yadda har suka kasa riƙe
hawayensu, suna kuma addu'ar Allah ya sa ita za ta cinye tuni ake ta haɗa video'nta dana
babanta.

Yabon su da ƙarfafawar su ta kwantar masa da hankali dan yana zaune sai murmushi yake
yana girgiza kai, yana da tabbacin nan gaba Afisha za ta yi ɗaukaka ta ban mamaki akan ƙira'a.


Ya rasa me ya sa ba a sanar da sakamakon ba da wuri, duk sun bi sun ruɗar shi, kwatsam ya
jiyo muryarsu cikin sautin murna da zaƙuwa cikin rakaɗi ya jiyo muryar Afisha.

"Alhamdulillah bini'imatahi ta tummussalihun! Abeyna! I'm the winner!!!""

Ta faɗa tun daga farfajiyar gidan cikin ɗaga murya, a guje ta shigo falon Ayeed na binta a baya
shi ma yana cewa.

"Ni ma na cinye."

Da sauri Tajj ya ɗan miƙe daga kishingiɗen da ya yi akan kujera.
Idonsa ya lumshe kana cikin sanyi da sauƙaƙawa ya ce. "Alhamdulillah."

Ya kuma buɗe ido, zuciyarsa na luguden farin ciki, kana ya ce.

"Ma sha Allah, congratulation yarana masu tsananin albarka."
Ya ƙare mgnar yana buɗa musu hannunsa.

Faɗa wa jikinsa suka yi cikin murnar.
Rungume su tayi tsam kamar zai maidasu cikinsa.

Laylah ta shigo hannunta riƙe da Ayaan da fuskarsa take a turɓune, ita kuma tana ta lallashinsa.


Afisha ta kalle shi ta ce.

"Abeyna albishirinka, na zo ta ɗaya!"

Ayeed ya tare ta da cewar.

"Ni kuma a hizfi goma, shi kuma Ayaan yana ɓata rai ne dan ya zo a na biyu."

Cikin tsananin ɓacin rai Ayaan ya ce.

"Ka ji wannan Ayeed ɗin abin da da rabin maki ka wuce ni, kuma ai ma, son kai aka yi."

Sai ya yi shiru yana ajiyar zuciya.

Ishmah ce ta janyo sa jikinta ta fara lallashinsa, zuciyarta tamkar wacca aka yi wa babban
albishir

"Ka yi haƙuri, ai kaga kaine ka cinye a na hadis, kuma yanzu aka fara, sannan kace da rabin
maki ya wuce ka ko?"

Ɗaga kai ya yi cikin sanyin jiki kana ya ce.

"Kuma ma, komai rabo ne da ƙaddara haka Allah ya tsara Ayeed ne na ɗaya ni ma ina yi wa
kaina fatan alkairi Allah ya sa ina da rabo a gaba idan Allah ya rayar da mu."

Dukansu tsura masa ido suka yi saboda Ayaan a nutse yake magana kamar ba yaro ba, idan ya
yi wani furucin sai ka rantse koya masa shi aka yi.

Murmushi Tajj ya yi ya ce.

"In Sha Allah ɗan albarka, ai kai mai nasara ne, kuma dukkanku za ku ci gaba da nasara a
rayuwarku in Sha Allah."
Ya ƙare mgnar yana haɗasu duka a jikinsa yana kallon Laylah data
zauna tana sakin ajiyar zuciya.

"Ni ma fa nina nazo mana ta biyu a hizfi hamsin."

Kallonta Tajj ya yi ya ce.

"Ai dole na cike miki 60 ɗin nan Laylah kada ki gajiyar da ni akan sauke shi, har yanzu ba ki
haɗa sittin ba, haba ta gaban goshina zan dage kafin ki cika shekaru ashirin dai ki cike settin
cib."

Na rai na rai ta yi da ido sai kuma ta ce.

"Allah Abeyna ina iya bakin ƙoƙarina a kan hakan ai an kusa in Sha Allah Amman fa dudu wata
shida ne ya rage in cika shekaru ashirin ɗin fa."

Cikin yaƙini Tajj yace.
“In sha Allah kafin nan kin cikace settin”.
Ayeed ne ya miƙe ya fara tsalle yana karatun Alqur'ani cikin ƙwarewa.


"Abeyna, Allah anty Laylah ta ci ka wasa, sai ka haɗa mata da bulala.."

Hamisu ne ya shigo yana kabbara.

"Congratulation to me, duka kyawawan yarana ne suka yi nasara a gasar karatun Alkur'ani na
Qatar duk media da gari sun ɗauka ga matar ma anyi ƙoƙarin ai Yah Afif da cike settin da cike
shekaru ashirin da haɗe digree da ɗaura aurenmu duk a rana ɗaya za'ayi su ko."

Da sauri Laylah ta rufe ido.
Tajj kuwa cikin farin ciki yace.
“In sha Allah kuwa haka za'ayi."
Ishmah kuwa ruggume Laylah tayi cike da farin cikin haɗin ta sa Hamisu.
Shi kuwa Hamisu wani irin murmushi mai cike da farin ciki yakeyi.

Da gudu Ayeed ya tafi ya rungume sa yana dariya.

"Sosai ma duk mu muka yi nasara Uncle Hamisu. Anty Afisha na ɗaya a hizfi talatin da tafsir,
anty Laylah na biyu a hizfi hamsin Ayaan na biyu..."

Sai ya kalli Ayaan da ya ke kwance jikin Ishmah yana kallonsa shi ma.

Shafa kansa Ishmah ta yi ta ce.

"Ai shi ya fara ci a na hadisi kai kuma ka zo na biyu, yanzu kuma ka zo na ɗaya ya zo na biyu
shi kenan anyi balance equetion."
Shi kuwa Tajj wayoyinsu dana Ishmah ke ta ƙarar shigowar message ɗin abokan arziƙi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login