Showing 18001 words to 21000 words out of 34694 words

Chapter 7 - Tsutsar Nama Book 2 Complete Hausa Novels By billyn Abdull.pdf


Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu
guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru

Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika
zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah

Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975

____________

.......Su Alaja na ficewa a gidan dasu Samraah Madam tai wani ƙasaitaccen murmushi da cije
lips ɗinta. Wayarta ta shiga daddanawa tana tafiya har ta shige ciki. Dai-dai tana kai wayar
kunnenta takai cikin kujera. Cikin wani salon gogaggun matan bariki ta shiga jera kirari ma
wadda tai kira a maimakon gaisuwa. Bamu ji abinda aka faɗa mata daga can ba. Sai dai yanda
ta saki siririyar dariya zai baka tabbacin mai daɗi ne. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗaura da
faɗin, “Ina godiya da wannan ƙyauta hajjaju masu Lagos da wajenta. Kai Africa ɗin ma duka
taku ce. Na kiraki ne domin wani babban albishir da nai imanin zai faranta miki ranki matuƙa”.
Ta ɗan yi jimm alamar saurare. Wani murmushin mai faɗi ta sake saki da cigaba da faɗin,
“Godiya nake hajjaju. Dama akwai babbar haja da a yanzu akai cinikinta zuwa gidanku. Na

tabbatar irin kalarki ce shiyyasa ma na sayar babu ja'inja bayan na gane daga ina masu sayen
suka fito. Na tabbata idan kikaga wannan hajar sai kin sake min sabon biya dan ni kaina
buƙatar kuɗi kawai ta sakani sallanawa amma raina ya biya sosai.”
      Amsar da Hajiyar ta bata daga can ya sata sake sakin dariya. “Ayyah! Hajjaju Ayya. Ai ku
manyanmu ne. Kodan girmamawa ma kauda kai ga abinda ya dace daku. Sai dai kinga kayan
dan na tabbatar yanzu suna gab da zuwa gidan naku. Duk da dai tace zata bada as gift ne.
Kuna wani shagali ne a gidan naku babu gayyata Hajjaju?”.      Shiru alamar saurare, sai kuma ta tashi zaune da ƙyau tana furta, “Woow fantastic Hajjaju. Ai
dolene muzo wannan birthday party kuwa kodan ke. Dan haka sai kin gammu”.
    Daga haka sukayi sallama ta yanke wayar tare da ajiyeta gefe tana wata kalar shaƙiyyar
dariya. A ranta tana ayyana (lallai yarinyar nan tazo da arziƙi. Ai tun da na ganta nasan
mabuɗin arziƙina ce ita, dan zoben da babalawo ya bani yay wani irin haske da bai taɓa yi akan
sauran yaran da nasarata ke samowa ba. Sai dai fa nima yawuna ya biya, dan komai yaji a jikin
yarinyar nan, ga wani shegen fata kamar na dorinar ruwa. Dan haka sai na ɗanɗana koba
yanzu ba) ta saki wata dariya a zahiri. Hakan yay dai-dai da shigowar Janny. Ko kaɗan batai
mamakin gani da jin dariyar da Madam ɗin tata keyi ba. Sai ma takowa da tai cike da yauƙi jiki
na girgiza ta faɗa mata a jiki......

(Hummm)

        ����

      *_MAASH MANSION_* Shine rubuce da manyan baƙi da akai da kalar ruwan gold a jikin
babban makeken baƙin gate ɗin gidan da ya mamaye kaso mai yawa na street ɗin. Ƙirjina yay
wata irin masifar harbawa, ba sai an min bayani ba, hakan na nufin wannan katafaren gini shine
gidan su Maash ko gidan Maash. (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un) to yaya hakan ta faru? Maash
ɗin dana sani ne a Lagos ko kuwa wani ne mai irin sunansa?. Bani da mai bani amsa sai jikina
dake rawa sosai amma babu wani yinƙuri da zan iya yi. Dan tuni wasu garɗa-garɗan securitys
dake tsaren ƙofar sun miƙe, sai da suka gama kallemu ɗaya bayan ɗaya da gaida Alaja cikin
girmamawa sannan ɗaya daga cikinsu ya danna remote da ke hannunsa, a hankali gate ɗin ya
shiga zuge kansa. A jere motocin uku duk suka shiga makeken compaund ɗin da sam baida
iyaka ga mai kallo, kowacce ta tsaya a muhalin da ake son ganinta. Dolene ka shigo wannan
gida ka tsarkake sunan UBANGIJI mai rahama mai jinƙai, dan shike samarwa ga wanda ya so a
lokacin da yaso. Gini ne daya ginu karkashin mahaukatan maƙudan kuɗaɗe da sam zaka iya
rantsuwa da ALLAH ba'a Nigeria kake ba idan kana a cikinsa. Dan a iya compaund kawai da
abinda ke zagaye da gidan, da kallon ginin a tsaye ya isa tabbatar maka da naira tayi kuka.
Wani irin ɗunƙulallen gini ne mai matuƙar armashi da ƙayatarwa. Ga wasu irin korayen ciyayi da
furanni masu azabar ƙamshi da sanyaya gida da ƙawatashi da sukaima ko'ina ado. Ga
jibga-jibgan motoci jere a cikin rumfuna kusan biyar a tsare acan nesa sosai, wasu ma rufe suke
da tempol. Sosai ma'aikata ne ke kai-kawo, dan dole irin wannan gidan yana da masu kulawa ta
kowanne fanni. Driver ne ya fara fita a motar ya buɗema Alaja. Kafin ita kuma tai min nunin na
fito. Jikina a matuƙar sanyaye na fito ina mai bin katafaren harabar gidan da kallo. Brain ɗina
gaba ɗaya ta gama kwancewa, dan tunanina ya rabu biyu ne tsakanin haɗuwar gidan da sunan

dana gani rubuce ɓaro-ɓaro matsayin mamallakin gidan.
      “Oya muje”.
   Furicin Alaja ya katse min tunani. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki na fara takawa a
hankali ina bin bayansu. Drivern ta ne yay saurin buɗe dankareriyar ƙofar mai wani irin zubin
ƙyau da ɗaukar hankali da duk mai kallo zai iya tabbatar da an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi.
Alaja ce ta fara shiga da sallama, yayinda ni kuma ke biye da ita kamar bindi. Sai sauran
abokan tafiyarmu biye damu. Sai dai babu sauran yaran da aka ɗakkomu tare da alama an
barsu a mota. A haɗaɗɗen falo dake matsayin main perlor muka fara ratsawa. Komai na cikinsa
a tsaftace yake ga ƙamshi da sanyin ac kamar ka ɓingire barci. Sai dai babu kowa a cikinsa ko
television ma a kashe yake. Bamu tsaya anan ba, mun shiga falo na biyu daya kasance
katafaren gaske. Haɗuwar falon ba'a magana. Dan ya ƙawatu da ƙawatuwa ta musamman.
Komai sai ƙyalli da ɗaukar ido yake tamkar ba'a talauci a duniya. Shima dai ƙamshin ke tashi
mai nutsuwa, sai ƙafar bene da suka zama mahaɗar sassan gidan guda uku. Gashi ƙaton
gaske bana wasa ba, dan duk da set na kujeru kusan biyar da ke cikinsa group-group zama a
iya kawo wasu set goma sha biyar duk ya ɗauka batare da wasu sun matsi wasu ba.
      Anan kam akwai mutane. A hankali dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 1sitter da
laptop a gabanta tana sarrafawa a group na set ɗin kujerun dake farkon shigowa ta ɗago
fuskarta ƙawace da murmushi, laptop ɗin da tun shigowarmu ta dakata da sarrafawa ta ture
gefe, cikin ƙasaitacciyar muryarta ta furta, “Idanu na ne kemin gizo ko kuwa mafarki nakeyi? Da
ganin Auta”.
      Dariya Alajah tayi tare da nufarta ta rungumeta. Dai-dai nan wasu ƙyawawan ƴammata uku
dake can ɗayan rukunin kujerun suka taso suma a guje suna faɗin, “Oyoyo Aunty Mamah.
Juyowa tai ta rungumesu suma cike da kulawa da farin ciki. Sai da suka gama murnarsu suka
nutsu kafin su maida hankalinsu garemu. Ni suka fara zubama idanu, kafin su maida ga sauran
hajiyoyin fuskokinsu a washe da murmushi suna musu barka da zuwa cikin nuna girmamawa.
Ni dai ina daga tsaye gefe dan haka kawai naji shakkar ƙarasawa garesu har sai da Alajah tai
kirana tare da nuna min na zauna. Inda ta nuna min ɗin nakai zaune ƙasan carpet. Kaina a ƙasa
batare dana kallesu ba na shiga gaishesu. Hajiyarce kawai ta amsa, amma ƴammatan nan ko
kallo ban ishesu ba. Musamman ma babbar ciki wani kallon tsana data wurgamin tun farko sai
da najisa har a ƙasan raina. Dan haka nima sai banbi takansu ba...

       Munyi zama na kusan mintuna talatin a wajen kafin hajiyoyin nan biyu da muke tare da su
su miƙe alamar zasu wuce. Hajiya da Alajah ne sukai musu rakkiya. Yayinda ni kuma aka barni
nan maƙure waje guda ƴammatan nan na bina da kallon banza. Kusan mintuna biyar sai gasu
sun dawo. Basu zauna anan ba, sai umarni da suka bama ƴammatan cewar ai kiran Mama Bilki
shugabar masu aikin gidan taje dani sashensu zasu nemeta. Hakan kuwa akayi, dan atake
babbar cikin ƴammatan ta ɗaga telephone tai kira, cikin gadara da izza ta isar da saƙon Alajah
da tuni sun haye upstairs ta ɗaya daga cikin ƙafar bene ukun data ƙawata makeken falon na
alfarma. Ba'a ɗauki wani lokaci mai tsaho ba sai ga wadda nake ƙyautata zaton Mama Bilki
tazo. Babbar mace ce sai dai baza'a kirata tsohuwa ba. Abin mamaki kuma jikinta fes kamar
bamai aiki ba, amma tabbas zata iya haihuwar kamata. Cikin fara'a da kulawa ta bani umarnin
tasowa na bita. Nima sai na miƙe jiki a sanyaye nabi bayanta ina mai sakin ajiyar zuciya. Dan
dama zama a tsakiyar shegun yammatan duk ya gundireni. Ina jin wata a cikinsu na sakin tsaki

amma sai nan juyoba balle naga wacece.

         Tafiya mukai mai tsaho sosai data bani mamaki dan kamar bama a cikin gidan muke ba.
Kasancewar bata hanyar da muka shigo dasu Alaja bane yasa ban iya na fahimci komai ba. Sai
ma sake zama wata baƙauya nayi dan kalle-kalle nakeyi iya iyawata. Sosai nake sake girmama
girma da ƙudira ta UBANGIJI. Dan wannan gida sai ka rantse ba hannu ne ya gina shi ba
saboda ƙawatuwa da ɓannar dukiya da akai wajen saka masa kayan alatu. Ban sake tabbatar
da gidan ƙaton gaske bane sai da muka ɓullo wata hanya data fiddomu wajen ginin tanan ma.
Ashe ta gaban girmansa ba komai bane. Ta can baya da ginin apartment na masu aiki yake
ɓangaren maza daban na mata daban shine ainahin ƙaton gaske. Dan shi ta can gefe akwai
ƙaton garden da ko ba'a faɗa maka ba kasan shi ɗin ne. Sannan daga hannun dama akwai
wani ƙaton wajen wasanni na yara da manya. Akwai wajen ƙwallo, wajen..... Kai dama wasu
daban da ban gama tantancewa ba dan iya abinda idona ya hango kawai nake sanar miki Bily.
Shi kansa sashen masu aikin da muka shiga sai da notikan kaina suka nema kwancewa. Dan
tamkar ba na masu aiki ba. Komai fes akwai kuma kayan ƙawar suma duk da basu kai na
sashen masu gidan ba ko kusa ko kaɗan. Amma dai duk mai hankali ya kalla yasan an
girmamasu an mutuntasu. A tare ƴammata kusan takwas da muka samu a falon zaune suna
kallo suka zuba min ido fuskokin wasunsu da fara'a, wasu ko kallo ɗaya sukai min suka ɗauke
kawunansu. Sannu wanda suka nuna kulawar su suka shiga yi min, hakan yasa nima na amsa
musu da kulawa tare da gaishesu duk da sukansu bazasu wuce sa'anni na ba har ma da waɗan
da zan iya girma..........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*








*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_




_����� ������ ��_



_���� ���_
_��� ������_

__________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku
ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar
ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE
SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff

domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa,
lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai.
Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu
eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a
*BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba
mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha
ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka
kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen
ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge
masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*_


https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

___________


......Wajen zama Mama Bilki da naji sun ambata da Mama ta nuna min, babu musu na zauna. Ta
nuna wata dake gab da inda nake tana faɗin, “Sayyada kawo ma baƙuwarmu ruwa da abinci
ko”. Cike da fara'a wadda aka kira Sayyada ta amsa tana miƙewa. Wata ƙofa dake a falon can
inda ƙaton dining table yake na katako ta nufa, mintina ƙalilan kuwa sai gata da tire madaidaici
a hannunta. A gabana ta dire tana murmushi da faɗin, “Sister ga abinci ko.”
         “Nagode”.
       Na faɗa a hankali nima ina murmushin yaƙe. Wajen zamanta ta koma ta zauna. Yayinda ni
kuma na zuba ma abincin ido nai shiru har sai da Mama Balki ta zungureni sannan na kawo
numfashi. Abincin ta nuna min alamar naci, na ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin tausasa
murya nace, “Mama dan ALLAH zan fara salla tukunna”.      Cike da fara'a tace min, “Lah ai babu komai ɗiyata. Kinga A'i tashi ki rakata ɗakinku sai tayi a
can kunga kun samu abokiya kuma kun zama ku uku kamar kowa. Ɗan tsuke fuska wadda aka
kira da A'i tayi, sai dai kuma batace komai ba ta miƙe. Nima miƙewar nayi nabi bayanta ɗan
lungun da naga ta nufa. Dogon corridor ne mai ɗauke da ƙofifin ɗakuna kusan goma. Hannun
dama biyar haggu ma biyar. Babu yabo babu fallasa bayan mun shiga ɗaki na biyu a hannun
dama ta nuna min ƙofar bayi. “Ki shiga nan”. Daga haka ta juya ta fita. Komai bance da ita ba
nima, face cikowa da idona yayi da ƙwalla. Ji nake komai ya ƙwace min, gaba ɗaya nama
gagara hasashe balle tunanin komai akan wannan rayuwa dana jefa kaina. Dan a yanzu kaina
nake zargi ba kowa ba. Ina ma kaina kaico akan bin hajiyar nan da nayi, sai naji inama tashar
na nufa koda roƙo na samu kuɗin motar zuwa Kano. To amma bakin alƙalami ya riga ya bushe.
Ni bama wannan ne tashin hankalina ba. Son sanin wanene mai wannan gidan shine tashin
hankalina. Karfa ya zamto ANYI GUDUN GARA ne AN FAƊA GIDAN ZAGO. Kai amma da
nayima kaina kaico. In sha ALLAHU ma bazai kasance hakan ba.

      Bayan na idar da salla na jima zaune a wajen shiru, dan har sai da A'i ya biyo bayana
sannan na miƙe na bita. Kamar yanda na barsu haka na samesu. Sai dai an sake samun ƙarin
mutum uku suma duk manyan mata dan da kaɗan Mama Balki zata iya girmarsu. Gaishesu nayi
a ladabce, duk suka amsa min babu yabo babu fallasa. Na ɗan ji jikina yay sanyi, sai dai ban
bari al'amarin nasu yayi tasiri a raina ba na fara cin abincina. Ka ɗan na tsakura nace na ƙoshi,
Mama Balki tai murmushi da faɗin, “Ƴar nan baƙunta zakiyi mana?”.
      Murmushi kawai nayi kaina a ƙasa batare da nace komai ba. Itama sai tayi ƴar dariya da
cigaba da faɗin, “To ai shikenan. Bara nayi wani karanbani duk da Aunty Mama bata sanar min
ke wacece ba ko matsayinki. Amma dai duk wanda aka kawo nan mun san namu ne ai. Minene
sunanki?“.        Shiru nayi jimmm kamar bazance komai ba. Sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali na
furta Kandala”.
    Su dukansu sai da naga alamar shock a fuskokinsu game da jin sunan nawa. Amma ganin
yanda na fiske abuna ya sasu basarwa. Wasu a cikinsu suka furta Masha ALLAH. Yayinda
wasu suke taɓe bakuna a yamutse. Mama Balki ce ta katse yanayin da nuna kanta. “Ni sunana
Balkisu, amma suna kirana da Mama Balki kamar yanda kika ji. Ni ce shugabar duk wani
ma'aikacin wannan gida musamman mata. Mijina kuma shugaban ma'aikata maza. Wannan
kuma ta kusa dake Sayyada, sai Afrah, sai Sumayya, sai A'i, sai Asiya, sai Bintu, sai Mansura,
sai Kairat, sai Bahijja, sai Sadiya suna kiranta Aunty Sadiy, itama tana da miji. Ta nuna ɗaya
daga cikin manyan matan nan uku da suka shigo daga baya. Sai Aunty Kubrah itama tana da
miji, sai aunty Falilah. Dukanmu muna aiki ne a wannan gida. Kowa kuma da fannin sa. Wasu
gyara, wasu wanke-wanke. Kowa kuma da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login