Showing 21001 words to 24000 words out of 34694 words

Chapter 8 - Tsutsar Nama Book 2 Complete Hausa Novels By billyn Abdull.pdf

sashen da yakema aiki dan komai a ƙa'idarsa yake.
Idan har kema tamuce zamuji fannin da aka kawoki ki kasance”.
       Sosai ƙirjina ke wani kalar luguden daka tunda ta fara. Sai dai inata dauriyar danne yanayin
nawa. A rain kuwa komai ya dagule min, babu abinda nake ambato sai kalmar (Na shiga uku.
Yanzu kuma boyi-boyi na koma kenan? Mike shirin faruwa dani ne haka?). Bani da mai bani
amsa, dan haka na maida hankalina ga Mama Balki dake cigaba da min bayani. Sai dai sam
bana fahimta har tayi ta gama. Mun cigaba da zama har akai kiran sallar la'asar. Sai a sannan
dukanmu muka miƙe. Ɗakin dai ɗazun naje tare da wadda ta rakani A'i sai abokiyar kwananta
Bahijja. Bahijjar akwai fara'a, dan sai jana take jikinta cike da kulawa. Muna idar da salla ta
kwashe tarkacen kaya da suka jibge a ɗayan gadon ɗakin dan uku ne ta ce, “Nan shine gadonki
Kandala”. Yanda tayi maganar da murmushi ya sani nima mayar mata da murtani ina jinjina kai,
kafin na ɗora da mata godiya. A'i dai na jinmu amma tai kamar bata ɗakin. Bahijja dake ƙoƙarin
saka uniform ta sake kallona da faɗin, “Kiyi kwanciyarki ki huta mu zamu je can sashen yin aikin
yamma. Idan kuma zakiyi kallone to muje falo”.
      Da sauri na girgiza mata kaina. Sai kuma na murmusa da faɗin, “A'a bari na kwanta ɗin, ai
bazaku jimaba ko?”.
     Tsaki akaja kafin ta bamu amsa, atare muka kalla A'i dake ƙoƙarin ficewa alamar itace tayi
tsakin. Murmushi Bahijja tayi da maido idonta gareni. “Karki damu da ita haka take kamar mai
aljanu. Nima farkon zuwana haka ta dinga min kamar mai jin haushin mutane. Amma bari kiga
nan da kwana biyu zata fara kulaki. A'in ce kamar mai aljanu wlhy”.          Murmushi nayi yayinda ita kuma ta ƙare maganar da sakin ƙaramar dariya. Daga haka ta
cigaba da faɗin, “Ya danganta da yanayin aikin da zamu tarar. Musamman ma ni, dan iyayen

gidan nawa mutuncinsu ragaggene bare ma idan akace miki Aunty Azizat. Tana abu kamar mai
jin warin mutane. Bari naje dan in nayi latti zan sha maruka gashi ƙa'idarta ne iyanzu take
wankan yamma”.
       Kasa cewa komai nayi, sai kaina dana ɗaga mata kawai sunan wadda ta kira na min
kai-kawo a rai batare dana san dalili ba. Bayan ficewarta na saki nannauyar ajiyar zuciya. Sai
kuma na miƙe cikin kasalar jiki zuwa gadon da tace nawa dake a farkon shigowa. Na can
ƙarshen bango na A'i, na tsakkiya nata. Sai ni a bangon ƙarshe na farkon shigowa.....
      ❤️★★★❤️

   Tsakanin Halime da Dady dai tun wannan ranar ba'a sake haɗawa ba. Dan washe gari uban
aiki taci kamar kurar wasa. Dan kaf girke-girken da aka tanadama Alhaji Rufa'i itace tayi su. Tayi
kuma gyaran gidan musamman falon tarar baƙi da Mom ta sakata ƙalƙalewa kamar za'a canja
bangonsa. Ita dai bata san dalilin uban aikin da taci ba sai da yammaci take ji a bakin auta wai
Baby ce tayi baƙo. An kuma ce ta saka hijjab da niƙab takai masa abinci falon baƙi. Bata da
yanda zatai dole tabi umarnin Mom tayi shigar da akace taje takai komai. Da ɗunbin mamaki ta
fito mara misali. Yayinda taketa jarumtar danne dariyar dake cinta har sai da ta shiga ɗakinta.
Bata tsaya a tsakar ɗakin ba ta shiga toilet ta rufe kanta duk dan kar a jita sannan ta fara
kwasar dariya harda hawaye. “Kambu taƙashin nan. Yanzu ni Halime ina Baby ta samo wannan
tulun giyar, wlhy cikinsa kamar an kifa masakin Baba Lauren gidanmu na Daudawa. Gashi
sanƙameme kamar samudawan da suka zo mana a labari. Tab ɗi jan, daga dai ganin wannan
kasan sai dai a so shi dan kuɗi duk da dai ƙyaƙyƙyawa ne a fuska.” kiran da Mom ke ƙwala
mata ya sata fita a guje dan tasan idan tai na uku sai ta sha maruka a wajenta.

      Gab da magrib taji ihun Bibaa da Abbas ya cika gidan. Ta kitchen ta kasa kunne sai ta jiyo
ihun nasu wai duk murna ne akan Alhajin nan ya bama Baby makulin mota, tare da alƙawarin
kujerar maka gareta da Mom da Dad da kuma Abbas, su kuma  su Bibaa da Auta da Nabil yay
musu ƙyautar wayoyi iphones. Hakan dai na nufin su duka banda Yaya Musaddiq bawan
ALLAH kowa ya samu alkairi daga Alhaji Rufa'i. Baki ta yaɓe ta cigaba da aikinta. Daga haka
bata sake bi takansu ba sai washe gari da kakarsu tazo take jin har ƙyautar kuɗi yay ma yaran
gidanta itama wai naira miliyan ɗaya. Itama kuma kakar tasu harda ita a zuwa saudia, da yaje
gidanta kuma ya bata waya mai ƙyau ƴar dubu ɗari biyu harma ta sayar da ita yau. Sosai
Halime ta jinjina kwaɗayin wannan mutane da mamakin maganganun da taji suna tattaunawa.
Dan sai da Mom ta farga da ita sannan tasha maruka aka korata waje, daga haka bata san mi
suka ƙarasa tattaunawa ba.

WASHE GARI kuwa bata ma san lokacin da Mom ta fita a gidan ba tare da Baby. Sai
Bibaa da Auta da suka wuce makaranta. Shi dama Abbas ba'a sakashi a lissafin gidan. Yaya
Musaddiq kuma ta lura jiya kamar bai kwana a gida ba. Tana a falo tana shara da raira waƙarta
cikin zazzaƙar muryar nan tata taji kamar ana kallonta. Ɗan jim tayi cikin nuna tsarguwa. Sai
kuma ta cigaba da shararta amma ta daina waƙar da take rerawar ta (kwanana ya kusa ƙarewa
a gidanmu zan tafi ɗakina. A gidan mijina zan rayu zaman kaɗaici ya kusa yankewa).
      Cikin sauke ajiyar zuciya da rashin jin daɗin daina raira waƙar tata Abba ya ƙarasa fitowa

daga jikin ƙofar ɗakin barcinsa da yake maƙale.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*

*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_




_����� ������ ��_



_���� ���_
_��� ��������_


_____________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku
ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar
ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE
SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff
domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa,
lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai.
Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu
eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a
*BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba
mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha
ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka
kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen
ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge
masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*_

https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG



https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

_____________

......Daga ni har Mama Balki ƙasa muka zube gaban Alaja dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya
kan ɗaya tana daƙilar tab. Gaisheta na shiga yi, batare data ɗago ba ta amsa min. Kusan
mintuna biyu muna zaune kamar masu neman gafara sannan ta ɗago tana cire eyeglasses ɗin
idonta da bana raba ɗayan biyu na ƙara gani ne. A kaina ta zube idanun nata, sai kuma ta ɗan
saki murmushi. “Ƴammata sorry fa. Tunda mukazo ban sake waiwayarki ba ko? Nayi busy ne
da yawa.”
        “Ba komai Mama”.
    Na faɗa kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna ta cikin hijjab.
    “Ohkay, yanzun ma bani da isashen lokaci. Maman Nana kije da ita wajen Sunusy ya
gwadata a ɗinka mata uniform itama. Sauran kayan da zata iya buƙata kuma sai ki shirya zuwa
anjima kuje shopping. Zata cigaba da zama a hannunki kafin tasan aikin da zatayi”.
         “To Hajiya in sha ALLAHU yanda kikace haka za'ayi. ALLAH ya ƙara nisan kwana da
rayuwa mai albarka”.
    A hankali ta amsa da amin. Jin godiyar da Mama tayi nima sai nayi godiyar. Duk da kuwa
wani irin abune mai masifar nauyi ke neman riƙe min ƙirji. Ban san a wace kalar rayuwa kuma
na jeho kaina ba. Lallai na tafka kuskure. Inama Kano na nufa abina. Kai anya kuwa kuskuren
nawa ba daga baro asibiti bane da nayi. (Tun daga baro gidan mijinki dai a Kano) wani gefe na
zuciyata ya ayyana min. Jinai tsigar jikina yay wani irin tashi sama. A saman lips na maimaita
kalmar “Miji”. (Kai ina ai bazan taɓa zama matar kowa ba sai Mansoor in ALLAH ya yarda)..

        “K! waye wannan kika hayo mana har sama da shi?!”. Muryar dana tabbata naji irinta a jiya
ta faɗa cikin daka mana tsawa dai-dai muna sauka steps na biyun ƙarshe. Ganin yanda Mama
Balki ta dakata da sauri cikin nuna shakka ya sani mamaki. Cike da girmamawa da sauke kai ta
furta “ALLAH ya huci zuciyarki Aunty Azizat. Dama mun cika umarnin Aunty Mama ne. Dan
itace ta buƙaci ganinmu”.
       Fuska ta wani yamutse tana balla mana harara. Da alama dai bata da abincewa. “K kuma
uwar miye kike wani kallona? Shegiya mai kama da mayu!!”. Ta sake faɗa a fusace tana wani
ware idanu a kaina sosai cike da nuna tsagwaran tsanar da ban san laifin dana mata ba. Duk
yanda naso jin na bata girma a matsayin wadda na shigo gidansu da kuma girmata da tayi  a
shekaru dan zata iya kaiwa sa'ar Yaya Musaddiq amma sai naji hakan ya gagareni. Sai ma
tsareta nai da idanu ina ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa....
      Tauuuu!!! Naji saukar wani shegen azabebben mari asaman fuskata babu zato babu
tsammani. A take ta rashin jin ya yunƙuro, bamma san lokacin dana ɗaga nawa hannun ba na
sauke mata nawa yatsun biyar nima a saman fuskarta dake fara sosai a dama da haggu kuma.
Daga gani kasan akwai ƙarin farin kanti dan har wani yellow-yellow takeyi. Tamkar mutuwa ta
ratsa gidan haka yay wani irin tsittt na wuccin gadi. Kafin tai wani irin zuba min ido like wadda
tai suman tsaye. Bama ita ba hatta da Mama Balki wani irin waro idanu tayi da ɗaura hannuwa
duka a saman kai bakinta buɗe. Cike da dakiyar nan tawa da taurin kai na watsar da su tamkar
banga komai ba na raɓa zan wuce. Dai-dai nan ta wani saki kururuwa da girgiza tamkar
tsohuwar dodanniya ta damƙo min hijjab ta baya. Sai kawai ji nai an shaƙureni tare da jawoni
baya. Tabbas da banyi azamar damƙe hijjab ɗin ta gaba ba da zamesa da sauri babu abinda zai
hanata kaini ƙasa a wajen. Idan kuwa na faɗi zan iya buguwa, idan ma da tsautsayi zan iya rasa
rayuwata. Gaba nayi gaba ɗaya, dan yanda ta fisga ni kuma na fisge sai yay kamar an

hankaɗoni ne. Na gama sallamawa babu makawa a wannan gaɓar sai na kai ƙasan mayen
marbles ɗin nan mai tsananin sheƙi da ɗaukar idanu tamkar zakaga fuskarka a cikinsa. Dan
haka na runtse idanuna gaba ɗaya ina mai ambaton sunan ALLAH da sallamawa baki
ɗayana......
         
      ★★★★

    Cikin mintuna ƙalilan Halime ta dawo ɗauke da tray. Haka kawai take ji bazata iya tsallake
umarnin Abba ba. Duk da tana jin shakkar uwar ɗakinta tasan ta ƙetare umarninta. A hankali ta
dire tray ɗin a gaban Abba dake zaune a dining. Tun fitowarta kuma yake famar binta da kallo ta
gefen ido tamkar zai cinyeta. Ƙoƙari barin wajen take yi tamkar mai raɗa ya furta, “Baza'a zuba
min ba?”.
      Duk shirmen Halime sai da taji zuciyarta ta tsarga. Hannunta na rawa ta shiga zubama
Abba abincin. Ta kammala tana ƙoƙarin barin wajen ya katseta da faɗin, “Uhhm Kinga zo
mana”. Nan ma ƙiri tai tana kallonsa, kafin cikin sanyin jiki tai ƙoƙarin durƙusawa a ƙasa. Amma
sai yay saurin girgiza mata kansa da mata nuni da kujera. Gabantane ya sake faɗuwa. Tai
masifar waro idanu waje tana jijjiga masa kanta alamar dai bazata iya ba. Ƙyaleta yay, cikin
gyara yanayinsa ya ce, “Minene sunanki?”. Ganin yanda yaci serious ya sata nutsuwa itama.
Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa masa da, “Halime”.
     “Halimatussa'adiyya kenan?”.
   “Eh ta faɗa a hankali”.
“Ina ne garinku?”.
“Ƴan tumaki”. Ta bashi amsa kai tsaye.
      “Ƴan tumaki?”. Ya maimaita da ɗan waro idanu a kanta a tunaninsa shaƙiyanci ne. Amma
sai a mamakinsa yaga ta jinjina masa kai na tabbatarwa. Kasa haƙuri yayi sai da ya furta “A
wane state ne?”. Girgiza masa kai tayi da faɗin, “Katsina ne. Amma dai muna kusa da
Musawa”. Jin sunan Musawa ya sashi fahimta Katsina state kenan ɗin dai da gaske. Humm
mutanenmu da ganganci, ka turo yarinya mai cikar halitta jiki kamar wannan aikatau har wata
jiha. Cigaba yay da faɗin, “Miyasa kike aikatau?”.
      Idanunta ne suka ciko da ƙwalla. cikin rawar murya ta ce, “Inna ce tace Baba ya turani na
samo kuɗin kayan ɗakin aurena”.
       “Ita Innar mamanki ce?”.
  “A'a gwaggona ta rasu tun ina ƙarama. Matar Babana ce, amma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da
Gwaggona. Bayan ta rasu aka aurama Babana ita dan ta riƙemu ni da ƙanina. Sai dai kuma ta
tsanemu, kullum cikin mana mugunta take, gadonmu ma da Gwagginmu ta barin mana duk ta
cinye. Gashi Baba baya iya cemata komai, shima tsoron masifarta yake ma”.    Haka kawai yaji wani abu mai nauyi ya tsikarar masa zuciya. Tamkar walƙiya hoton Maman su
Samraah yazo masa a cikin idanu. Da sauri ya ture zancen zucin gefe ya cigaba da faɗin,
“ALLAH ya gafarta mata. Toke kina da saurayi ne da aka turoki samun kuɗin kayan ɗaki?”.
       Ƙasa ta ƙara yi da kanta sosai alamar jin kunya. Wasa ta farayi da yatsunta sannan cikin in
ina ta ce, “Duk wanda yazo wajena Inna korarsa take yi. Tace saina haihu a gida ɗan shege ko
zata bari nayi aure. A hakan ma sai su Lami sun gama yin nasu auren”.

      Sosai zuciyar Abba ta sake raunana da tsinkewa. Da ƙyar ya iya furta, ”Wacece ita Lami
ɗin?”.
    “Ƙanwata ce ita ta haifeta da su Lailah”.
Kasa sake magana Abba yayi tsahon lokaci. Sannan yace ta tashi taje ta cigaba da aikinta.
Shima sai ya miƙe dan ya gagara cin abincin kuma ya koma ɗaki. Shirin fita yayi zuciyarsa na
masa kaikawo. Bai wani jimaba ya kammala ya bar gidan batare da ya sake neman Halime
ba....
Duk yanda Abba ke son yaƙar zuciyarsa game da abinda take ƙwaɗaita masa hakan ya
gagara. Tun yana iya danne al'amarin har yana son fin ƙarfinsa. Yakan rasa sukuni a duk ranar
da baiga Halime cikin idanunsa ba. Al'amarin tun yana bashi mamaki har ya koma bashi tsoro.
Dan haka kawai yanzu rana tsaka zai baro kasuwa yayo gida dan kawai yaga Halime. Tun Mom
na masa uziri idan yace mantuwa yayi harta fara tsarguwa da tunanin ya saka mata ido ne akan
yawan yawon da take kwana biyun nan. Hakan ya sakata ɗan nutsuwa a waje guda. Yayinda
shi kuma Abba zaman nata a gida ya zame masa takura. Dan idan tana nan ko giccin Halime
baya gani saboda yanda take jin tsoron saɓa umarninta. A haka da ƙyar akai kwana huɗu. A
daren cikar na biyar ya gagara haƙuri ya nufi gidan abokinsa Alhaji Sadisu mai-agogo. Tsaff ya
kwashe komai ya sanarma Alhaji Sadisun. Shiko ya dinga dariya yana tsokanar Abba har sai da
yaga ya ƙulu sannan ya bashi haƙuri tare da bashi shawarar yanda ya kamata suyi dan ganin
komai ya tafi dai-dai. Sosai shawarar tayima Abba kuwa. Ya tafi gida cike da farin ciki....
      
      ★★★

      Wata irin ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin na faɗa kan abu mai taushi saɓanin inda na
gama sadaƙarwa zan faɗi. Rawar tsorata dana riga nayi jikina keyi, dan haka na sake ƙanƙame
abinda na faɗawar ina mai sake matse idanuna dake a kulle. Sai dai me, wani kalar wakitawa
ƙitjina da zuciyata sukayi a lokaci guda, a take tsigar jikina ta fara mimmiƙewa. Gabana ya sake
faɗuwa jin yanda wajen ya koma tsitt tamkar babu wani rai mai numfashi. Gaba ɗayan
numfashina ne ya ɗauke daga illahirin gangar jikina nima, tare da wata irin girgizawar zuciya
taban mamaki. Sake ƙanƙame abinda na faɗawar dai na sake yi. Wani irin jifff!! Ƙirjina ya sake
bugawa a karo na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login