Showing 12001 words to 15000 words out of 34694 words

Chapter 5 - Tsutsar Nama Book 2 Complete Hausa Novels By billyn Abdull.pdf

da Hajiya tai tsaff ta gane kasancewar taji
hausa sosai. Hajiya ma murmushin taketa faman yi, dan ita kanta tasan zata ƙaru da yarinyar
sosai...

      ★Washe gari kamar yanda Hajiya ta faɗa suka tashi da shirin wucewa Lagos, harda
Samraah nan dako sunanta basu sani ba har yanzu. Tunda suka tambayeta sau ɗaya tayi shiru
basu sake tambayar ba. Tun jiyan kuma tana ɗaki kwance sai dai akai mata abinci a ɗakko
kwano.. Janny ce mai ƙoƙarin kai-kawon, Hajiya dai nata bada umarni kawai, bakuma ta sake
neman ganin Samraah ba tun shigowarsu gidan sai a yanzu da suka kwana suka yini dan
tafiyar yamma zasuyi.
     Ita dai Samraah bata san ina zasu je ba. Koda ta tambayi Hajiya kuma sai cewa tai ta jira
zata gani. Badai tace ita ƴar Kano bace, zata bata mamaki ne. Al'amarin kamar asiri Samraah ta
gagara cewa da Hajiya komai. Hasalima jinta take jikinta duk ya gama mutuwa ga bakinta ya
mata nauyi. Sannan bata jin zata iya tsallake umarnin Hajiya sam koda cewa tai ta shiga wuta
ta ƙone ko ruwan teku.

       Tunda suka fito Janny taga Samraah na faman laɓe-laɓe a bayanta, Idanu Hajiya ta zuba
musu kawai. Sosai ƙyawun yarinyar ya ɗauki hankalinta, sai taga tama ɗara yanda Jannyn keta
kurantawa tun jiya. Baki ta buɗe zatai magana Samraah tai saurin faɗin, “Ina yini” cikin risinawa.
Murmushi Hajiya ta ɗan yi tare da ɗauke kai, sai kuma ta sake maidawa ga Janny. “Wai nikam
ashe amarya na kawo gidan nan ban sani ba. Irin wannan ɓoyo haka”.
      Dariya Janny takeyi sosai itama idonta akan Samraah dake ta faman sinne kanta, da alama
dai itama taji kunya, tunda koba komai ya kamata ta fito ta gaida Hajiyar da safe amma taƙi yin
hakan. Duk sun fahimci taji kunyar ne suma, dan haka Hajiya ta kamo hanunta tana murmushi.
“Daughter ai ko gaisuwa a fito muyi tunda dai naga baki son musan sunanki. Da alama dai yana
da tsadar gaske, ko sai mun saya ne?”.
         Karan farko na ɗago dara-daran idanuna masu shegen haske na sauke akan Hajiyar ina
mai girgiza kaina da sauri, idanuna cike da ƙwalla alamar ina gab da shirin sakin kuka, dan
haka kawai naji wani irin tsoro da shakkar matar ya shigeni mai tsananin gaske..
   “A'a da alama dai ɗiyar tawa shagwaɓaɓɓiya ce, to mun haƙura tunda dai ba'a son mu sani.
Mu sai mu saka miki namu sunan ai kawai kinga an huta canki canka ko”. Hajiya ta sake faɗa
cike da salo tana murza hannuna a hankali.
    Janny dai dariya take, yayinda ni kuma na duƙar da kai kawai, sai dai abinda Hajiyar ke min a
hannu sam bana so, amma tsoron janye hannuna nakeyi..
“Baby zata shiga gaba koni Hajiya?”. Janny ta faɗa dai-dai muna isowa gaban

hamshaƙiyar motar Hajiya data sha wanki take ta ƙyalli. Kallon Janny Hajiya tayi, yayinda ni
kuma na ɗan ɓata fuska, a raina ina ayyana (baby kamar wata ƴar tsanar wasan yara) a fili kam
sai na girgiza kaina a hankali na ce, “Sunana *_Samraah_*”. 
      A kusan tare Hajiya da Janny suka kalleni, Hajiya ta saki murmushi, Janny ta ce, “Woow
nice name dear. Dole ki mana yanga irin wannan golden name haka”. Ta ƙare maganar tana
ɗan rungumoni. Jikina na ɗan jaye daga nata batare dana sake cewa komai ba. Hakan yasa
Hajiya ɗan harararta akaikaice alamar ta sakeni. Jayewa Janny tai tana faɗin, “I'm sorry maa”.
Bata tanka mata ba ta kama hannuna muka shiga baya, dan tuni driver ya buɗe mana. Gaba
Janny ta shiga, daga haka driver ya harba mota zuwa gate. Mun ɗan tsaya a bakin gate Hajiya
tai magana da maigadinta, tare da bashi kuɗi masu yawa da suka bani mamaki. Shiko sai
faman godiya yake bakinsa a washe har motar tai nisa da gate ɗin bai bar ɗaga mana hannu
ba....

      ★ A cikin tafiyar ƙanƙanin lokaci muka iso airport, hakan sai yay matuƙar bani mamaki. Dan
na fahimci airport ne muka zo, sai dai na gagara iya cewa komai dan ji nake tamkar an ɗaureni
ne da sarƙa, bakina kamar an saka masa padlock. Wani irin sarawa naji kaina namin da tunani
barkatai akan inda zasu kaini, a wane rami kuma na sake jefa rayuwata ni Samraah, kamar fa
batun Lagos naji mutanen nan nayi, sai kuma zancen Hajiya ya sake tabbatar min da hakan.
Dan bayan fitarmu a motar take sanarma drivern ta yay ƙoƙarin wucewa Lagos da sassafe
gobe, bata son ya kwana a hanya bai iso ba. Shiko yana tabbatar mata da in sha ALLAHU cikin
girmamawa. Daga haka Janny ta gungura akwatinansu ita kuma Hajiya taja hannuna muka
shige ciki. Mun ɗan yi zaman mintuna goma a wasu kujeru kafin mu miƙe lokacin da ake sanar
da parssinges ɗin Lagos suyi himma. Cikin kasa haƙuri da suɓutar baki saboda sunayen ALLAH
da naketa ambato a ƙasan zuciyata na ce, “Muma wai jirgin zamu hau Hajiya?”. Kusan lokaci
guda Janny da Hajiya suka saki ƙaramar dariya, kafin Hajiya ta kamo hannuna cike da kulawa.
“Eh Samraah muma jirgin zamu hau zuwa Lagos, dan yafi sauƙin tafiya sai kiga nanda wani
ƙanƙanin lokaci mun isa. Idan kuma baƙya son zuwa ne bazamu takuraki ba, tunkan driver yay
nisa sai na dakatar da shi ya koma da ke, amma fa ba can gidan zaki koma ba, dole garinku
zaki faɗa ya maidaki gidanku”.
        A take batare da nasan dalili ba na ruɗe, na shiga girgiza kai idanuna na cika da ƙwalla.
Cikin rawar murya na ce, “Hajiya kiyimun rai. Wlhy dana koma gida gara ma ki kasheni kawai.
Sannan kuma shima ya tabbatar min zai iya salwantar da dangi.....” sai kuma nai shiru tamkar
wadda aka tsawatarwa har ina kai hannu saman bakina na dafe. Ganin kallon tuhumar da
Hajiya ke bina da shi da Janny ya sani sakin hawayen suka zubo. “Na yarda Hajiya ki kaini
koma inane, amma banda maidani gida, zaki sameni a mai yi miki biyayya ɗari bisa ɗari...”
        “Miya samu dangin naki?”.
    Hajiya ta katseni tana mai tsatstsareni da idanu. Ruɗewa nayi jikina ya fara rawa da lips ɗina.
Saina fara ƙoƙarin jan jikinna baya daga kusa da su. Dai-dai nan aka sake shelanta neman
passinges na flight Lagos. Hajiya ta ɗan ja numfashi ta fesar, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da
kamo hannuna. “Ok ok kiyi haƙuri ba sai naji ba. Muje kawai kar jirgin ya wuce ya barmu”.
Ƙoƙarin tirjewa nayi Hajiya ta sake damƙoni da ƙyau tana min magana a hankali mai nuna
alamar lallashi, sai dai nauyinta ya wuce duk yanda mai karatu ke hasashe....
        Sosai jikina ke maƙyarƙyata a cikin jirgi saboda zantukan Hajiya. Sai faman maƙurewa

nake a waje ɗaya alamar dai a firgice nake. Hajiya kam na riƙe da hannuna katamau tamkar
zan tsere mata ne. Janny dake daga can ɗayan gefenmu kam kallonmu kawai take tana danne
dariya. Dan duk wanda ya kalleni zai ɗauka ƙauyanci ne cike taf a kaina ba wai tsoro ba. A haka
dai jirgi ya lula sama  harda yunƙurin amai na amma na danne, bayan ya gama dai-daita dole
sai da Hajiya ta rakani restroom nayi sa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga zazzaɓi ya rufeni ruff
abinka da wadda bata gama murmurewa ba dama. Koda muka sauka a Lagos kaina a juye
yake ma gaba ɗaya. Dan bana iya gane komai yanda ya kamata har muka shiga mota zuwa
anguwar da Hajiya take....
          Babbar anguwace mara yawan cinkoson jama'a kamar ba'a cikin Lagos da nake jin ana
faɗa ba. Duk da kuwa kafin mu iso cikinta mun shiga cinkoson matuƙa wani gurin ma da ƙyar
muka fita, dan tafiyarmu daga filin jirgi zuwa gida yafi tafiyarmu daga Kano  zuwa Katsina nisa,
duk da dai shi wancan gari da gari ne, wannan kuma cikin gari dole akwai banbanci. Iya ƙagara
na ƙagu a zo gida, dan a yanzu ma amai ne keta faman taso min tunda muka shiga motar. Da
alama Hajiya ta fahimci halin da nake ciki ne ya sata siya min lemon zaƙi a hanya tace na dinga
shanshana ɓawon, sai goro da shi kuma na dinga ɗan ci kaɗan-kaɗan. Wannan ne ya riƙeni
zuwa gidan Hajiya.
       Anan ɗin ma dai maigadi ya buɗe mana gate, sai faman washe baki yake da jerama Hajiya
sannu da zuwa. Da taimakonsa mai taxi ɗin daya ɗakkomu ya fidda mana akwatinansu biyu
madaidaita. Janny ta tsaya biyan mai taxi ɗin, yayinda ita kuma Hajiya ta kama hannuna muka
nufi wata ƙyaƙyƙywar ƙofa fara da adon golden. Wannan gidan yafi gidan Abuja girma, lokacin
da muke shiga falon kuma ya sake tabbatar min da yafi wancan ɗin kayan alatun more rayuwa
ma. Dan falon ƙato ne na gaske, ga wasu manya-manyan hotunan Hajiya da wani mutum a jiki
tamkar zasuyi magana dan girma. Sai ƴammata biyu masu tsananin kama da juna sannan suna
kama da mutumin. Fitowar wasu ƴammata biyu da dattijuwa ya katse min kalle-kallen hotunan
da nakeyi. Nai tsai ina kallon dattijuwar da ƴammatan da suka zube gwiwa bibbiyu suna gaida
Hajiya da jera mata sannu da zuwa. Itako amsawa take cike da nuna isa da gadara tamkar ba
Hajiyar dana sani daga jiya zuwa yau ba. Dan bayan ta gama amsa su a taƙaice tai musu nuni
da ni. “Kuje da ita sashenku kafin na nemeta, duk kuma wanda ya mata wata any magana sai
na wulaƙantasa ta yanda sai yayi dana sanin sani na a gidan nan. Ina sauran suke?”.
        Da sauri dattijuwar ta amsa mata da “Madam Oyinka ta ɗauki Surayya da Umayyah, dan
tare sukazo da wata baƙuwa tun jiya da yamma kamar yanda na sanar miki a waya”.
     Kaɗan Hajiya ta yamutse fuska tana kallon agogo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa,
dai-dai nan Janny ta shigo maigadi biye da ita jaye da akwatuna. Hannu kawai Hajiya ta
ɗagama Dattijuwar alamar suje. Miƙewa duk sukayi suna min nuni da ƙofa.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_

_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*








*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_

_����� ������ ��_



_���� ���_
_��� �����_

_______________

Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu
guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika
zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su

Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah

Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975

____________

......Wani irin yamutsawa kaina ya shiga yi, dan gaba ɗaya suffar ƴammatan nan da dattijuwar
batai kama data mutanen kirki ba, sai irin gogaggun matan barikin nan da idanunsu ya gama
gogewa. Juyowa nai a karan farko na dubi Hajiya, itako ta ɗauke kanta gefe fuskarta babu
alamar wasa a yanzu. Kamar ba itace keta faman min murmushi ba a Abuja da lallaɓani.
Kallona na maida ga Janny da itama take kallon Hajiyar, a karo na farko na ce, “Dan ALLAH
Hajiya ku barni a wajenku”.
        Wata irin tsawar data gigitani Hajiya ta daka min. “Ka jimin shegiyar yarinya, su ɗin sama
suka ce miki suna da gida bayan wannan da suke ciki?!! Zaki wuce ko sai na banbance miki
tsakanin aya da tsakkuwa ku gammin yarinya da tsurku. Kin fini sanin abinda ya dace ne!”.
            Rawa jikina ya cigaba dayi har ina neman kifewa ƙasa. Bamma san sanda nabi wanda
akace nabin ba. Da harara Hajiya ta raka bayansu, sai dai suna ficewa taja tsaki da fincike
gyalen abayar data naɗe kanta da shi. Tuni gashin dokin kanta ya bayyana, ta jefar da ɗan vail
ɗin tana magana cikin yare, sai kuma ta miƙe ta fincike abayar ma. Anan ɗin ma wani wandon
bomshot ne na jeans ya bayyana a jikinta da riga best....
        “Hajiya ya haka?”.
    Cewar Janny tana dariyar shaƙiyanci. Da sauri ta harari Jannyn da zagaya hannunta saman
kai ta ce, “God for bed yoo, sunana Jannifer Can hajiyansu su ƙarata da shi bani ba Mtsowww!!.
Yanzu ma zanyi shirin Church pastor yay min addu'a akan hakan. I beg, give me wine na ɗan
sha ma ko zandawo hankalina da ƙyau”. Tai maganar tana komawa saman kujerar ta zube.
Wucewa Janny tai hanyar kitchen, babu jimawa ta dawo da kwalban giya mai tsadar gaske da
cups guda biyu. Ita ta ɓalle ta zuba musu tare da miƙamata itama ta ɗauki ɗaya, sai da suka
ɗan haɗa kofunan alamar chess sannan kowa ya kai bakinsa yana murmushin samun nasara.
Dan kuwa dai sun samo nasarar da suke buƙata a wannan tafiyar.

      (Tofa abin mamaki, idan na fahimta dai wannan Hajiya ta bogi ce, hasalima ba musulma
bace, ba kuma bahaushiya ba. Ko kuma dai bahaushiyar ce musulma ada tayi ridda? Tirƙashi,
muje zuwa wai maƙwafcin mai akuya ya sai kura)..

_______★

        “Duk yanda na lissafa miki kayan nan haka zatai amfani da su Jalilah. Sannan wannan da
za'a dafa abincin da shi ki tashi da kanki kiyi girkin bawai kiba wannan shegiyar mai aikin da
kika kwaso ba. Ni wlhy haka kawai yarinyar sai bata min ba, dan kawai kinƙi jin shawara ne”.
      “Wai Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Mai aikin nan fa dolece. Sanin kanki ne da ga Baby
har Bibaa babu abinda suka iya na aikin gida, ni kuma wlhy yanzu na riga na sangarce tunda
shegiyar yarinyar can ke komai tun tana ƙanƙanuwarta. Da nasan haka abin zai ƙwaɓe min
ALLAH da auren zan hanata gaba ɗaya a rayuwarta”.       Dariya Umman tata tayi da faɗin, “Daga baya kenan. Ni dai muyi abinda ke gabanmu nata
kuma ya zama labari ai tunda kin ɗebi rabonki. Yanzu babban burina Bibalo da takwarata su
auri mazan kere sa'a. Dan haka bana son wasa. Awakina na sayar har Niger naje amso kayan
nan kema kin sani, dan haka kiyi yanda nace ni zan wuce bana son mijinki yazo ya sameni
anan. Magana ta gaba kiyi duk yanda zakiyi waɗan nan samarin biyu ƴan uwan yarinyar nan
suma su bar miki gida dan nafi son na cigaba da ganin daga ke sai ƴan ƴaƴanki a cikinsa.”
      “Banƙi na naki ba Umma, sai dai fa yaron nan yanzu shine komai na gidan nan, ina mora a
jikinsa wlhy bazan so yabar gidan ba. Shiko ƙaramin dama yana makaranta sai lokaci-lokaci
yake zuwa. Mudai sake shawara yanzu ne lokacin cin amfaninsu su dama macen ce nauyi ai”.
         “Eh to da kuma wannan dan wannan. To wai tsaya ma, idan yaron nan kinga yana samun
wasu manyan kuɗi ne mizai hana mu haɗa shi aure da Bibaa”.
     “Bibaa kuma Umma?”.
  “Ƙwarai da gaske. Ga gida bai ƙoshi ba sai a kaima dawa. Ke dai ki nutsu ki sake tabbatar da
nauyin aljihunsa. Dan ni dama hidimar da yay a bikin ƙanwar nan tasa da wadda yake a baya
tana firgitani”.
         “Amma Umma iyakar yaron nan fa Sakandire”.
    “Ina ruwanmu da wani Sankandire ɗinsa ko digiri. Shi namiji ai aljihunsa adonsa. Yo ko besan
(A) ba indai akwai babbar (N) a aljihunsa miya damemu. Kidai yi nazari nima zan sake tunani”.
     Cikin jimamami Mom ta ce, “To shikenan Umma ALLAH yasa mu dace, sai na jiki ko kin jini.”
      “To mu huta gajiya. Amma ki tabbatar sunzo sun gaisheni fa ita da shi idan ya iso”.
     “Zasu zo Umma kar ki damu”.

Tofa ban ganeba wai anyi gabas da kare


★★★★

Gaba ɗaya a firgice nake da komai, dan wani irin juyewa ƙwaƙwalwar kaina ke neman yi.
Musamman ma da naga inda ƴammatan nan suka nufa da ni. Tacan bayan gidanne alamar Bq.
Sai dai an raba tsakaninsu da inda su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login