Showing 30001 words to 33000 words out of 34694 words

Chapter 11 - Tsutsar Nama Book 2 Complete Hausa Novels By billyn Abdull.pdf

sai ga ogansa yazo masa da wani

batu. Wai Companyn Maash na ƙera motoci da aka buɗe kwanaki sunzo garesa suna buƙatar
matasan kanikawa masu kwalin secondary. Shi kuma ya bada sunansa dan yasan yana da su.
A yanzu haka kuma sunce zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suna buƙatar ganinsa interview.
Rasama abin faɗa yay, sai hawaye da suka cika masa ido yana kallon ogan nasa kawai. Bai
san mizai sakankama bawan nan da shi ba a rayuwa saboda ɗunbin ƙaunar da yake nuna
masa da alkairan da yay masa...
      “Wai namiji da kuka Musaddiq?”.
   Ogan nasa ya katse masa tunani cikin nuna damuwa. Hannu yasa ya share hawayen da shi
kansa bai ma san sun zubo ba. Sai kuma yay murmushi tare da buɗe baki zaiyi magana. Da
sauri ogan nasa ya dakatar da shi da faɗin, “Basai kace komai ba Musaddiq. Ka cancanci fiye
da haka a wajen nan domin kai ɗin ɗan hakal ne wlhy. Da ace inada abinda yafi hakan zan
maka a rayuwa. Fatana dai ALLAH yasa wannan canjin da zaka samu ya zama sanadin alkairin
ka a rayuwa kai da zuri'ata. Kuma ina mai farin cikin sanar maka nima basu barni haka ba.
Akwai aikin dazan dinga musu, dan haka zasuzo su gyara wannan wajen ya koma na zamani
kamar yanda suka faɗa”.
      A take farin ciki ya sake mamaye Musaddiq. Sujidar shikur ya farayi kafin yaje ya rungume
ogan nasa. Dariya ya shiga yimasa, dan har ga ALLAH yana matuƙar ƙaunar Musaddiq saboda
gaskiyarsa da riƙon amana. Ga biyayya da kwazon aiki, da wahala kaga fushi a fuskarsa koda
kuwa faɗa yay masa. Mutum ne mai juriya da shanye komai koda bai masa daɗi ba....
    Rasa inda Musaddiq zai kai wannan farin ciki yayi, har ya danna Number Abba sai kuma ya
fasa sakamakon tsoratar da shi da zuciyarsa tayi kodan halin Mom. Haƙura yayi, sai da yamma
ana tashi daga aiki ya wuce Dawanau wajen Gwaggo Gudidi. Ita ya kaima wannan labarin farin
cikin, ai ko baiwar ALLAH harda kukanta tana ƙara godema ALLAH. Daga ƙarshe ta gargaɗesa
akan kada ya sanarma Abba yanzu kodan mugun halin matarsa zata iya shiga ta fita ta jefesa
da wani sharrin. Yana dai ganin halin da aka shiga game da auren Samraah abu kamar a film
ko a labaran hikayiyin marubuta. Ya yarda da shawarar Gwaggo ɗari bisa ɗari. Daga haka suka
koma hirar Samraah. Itama Gwaggo ta shiga damuwa sosai hankalinta kuma ya fara tashi,
anya kuwa basuyi gangancin aurama Samraah mutumin nan ba? Duk da dai a fuska yazo musu
da suffar mutanen kirki. Amma dai zatai magana da Kawu Musa domin a tuntuɓi magabatansa
da sukai masa waliccin auren.........✍️
    
       


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*








*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_




_����� ������ ��_

_���� ���_
_��� ������_

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku
ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar
ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE
SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff
domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa,
lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai.
Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu
eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a
*BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba
mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha
ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka
kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen
ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge
masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*_


https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG



https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

______________

......Sosai hirarmu da Bahijja ya tsaya min ƙyam a rai da zuciya. Duk yanda nake yaƙin son
turesa hakan ya gagara. Gashi tun ranar ban sake ganin makirin ba. Hakama cikin gidan ban
sake shiga ba. Bahijja dai ta sanar min Babansa da matar babansa sun dawo daga tafiya,
hakama ƙanin baban nasa da iyalinsa sun dawo suma dai. Sannan yau gaba ɗaya sunyi busy
wai ana aiki ne acan sashin saboda bikin birthday da za'ayi wai na mahaifiyar tasa. Ni al'amarin
ma sai na ɗaukesa hauka. Yo inba hauka ba, koma nace sunfi ita mai ciwon haukan zama
mahaukata mara lafiya dake buƙatar addu'a ce wai za'ama wani shegen birthday party. Kai
yawudanci ma baiyi ba. Ko kuwa dukiyar tasu ce ke neman zauta musu ƙwaƙwale ma oho
musu. Sosai takaici ya kumeni, ji nake kamar na buɗe ido na gansa a gabana. Wlhy da ko zai
tsireni sai na faɗa masa gaskiya sai dai ya mutu shiya sani. Ina nan kwance ina ƙullawa da
kwancewa wajen ƙarfe biyu su Mama balki suka fara dawowa. Hayaniyarsu tasa na fito falo
nima. Sannu na shiga musu, wasu su amsa wasu su shareni batare dana san mina musu ba.
Mama Balki ce ta dubeni da murmushi, cikin kulawa ta ce, “Ai kema daga gobe za'a fara miki
sannun. Dan Aunty Mama tace zaki fara aikinki. Kinga sai ki shirya idan mun gama zamu wuce

dake tare wajenta kamar yanda ta bada umarni”.
       Sosai naji wani irin abu mai nauyi ya soki zuciyata. Na dai danne da ƙyar ina murmushin
yaƙe. Da girmamawa na amsa mata da “To mama nagode”. Daga haka ban sake cewa komai
ba saboda baƙin ciki. Ni kuma haka rayuwata zata ƙare. Wahalar gidan Abba. Rabani da
masoyina, auramin azzalumin mutum irin wannan mutumin da bai san komai ba a rayuwa sai
kansa. Daga ƙarshe ma maimakon na shigo gidansu matsayin matar aure a ƴar aiki nazo.
Nasan shine ya tsara hakan, kuma zan tabbatar masa ya tsara ramin muguntar da shine zai
afka ciki daga ƙarshe. Dani yake magana Samraah Abdul-wahab gwarzo.....

       _Hummm Sam-G tamu. Koda yake aunty kike tunda matar Yayanmu ta_

      ❤️ Kamar yanda Mama Balki ta umarceni wanka nayi nima. A'i da yanzu ta ɗan fara kulani
itama ta kawo min doguwar riga ta farin Material da suma naga sun saka a jikinsu inji Mama
Balki. Nayi mamakin kayan, dan sababbine ƙal kuma daga gani ba ƙanana bane ba. Haka dai
na shirya ina zancen zuci. Ganin yanda Bahijja ta tsaya tana kallona ya sani mata alamar
lafiya? Da idanu. Murmushi tayi da sauke ajiyar zuciya. “Wlhy Kandala baki ganki ba. Sam
bakiyi kala da masu aiki ba. Kayan nan sun sake fiddo da ainahinki na ƙyaƙyƙyawar mace
wayayya. Dan ALLAH idan bazaki damu ba ki sanar min labarinki. ALLAH sai nake ji a raina ko
sunanki ba gaskiya kika sanar mana ba”.
      Idanu na ɗan waro mata kamar zanyi magana sai kuma na fasa nayi murmushi kawai. Dan
babu abinda na ɗauki zancen nata sai shirme. A girme zan iya girmar Bahijja, amma yanayin
inda take rayuwa da kuma halitta ta na mutum mai jiki yasa a ido zaka iya cewa sa'anni ne mu.
Riƙoni tayi zata sake yin magana Afrah ta shigo. A wulaƙance tace, “Malamai ku Mama ke jira
kuka wani zo nan kuka haɗe kawuna dan munafunc....”
      Ta gagara ƙarasawa saboda saukar idanunta a kaina. Ɗauke kaina nayi tamkar banga
kallon da take min ba. naja ƙaramin mayafin Bahijja na yafa nai ficewata na barsu..
         “Kan uba Bahijja kinga kuwa abinda na gani tattare da yarinyar nan?”. Afrah ta faɗa cikin
jimami da shiga ruɗani. Ƴar dariyar shaƙiyanci Bahijja tayi. “Yo mi kika gani?”.
      “Bahijja anya ba ƴar leƙen asiri bace ba. Sam yarinyar nan batai kama da wadda ta fito a
cikin wahala ba. Musamman kwana biyun nan da tayi a gidan nan jikinta ya sake murjewa sai
ainahinta ya fito. Duk da muma yawancinmu badaga ƙauye aka kawomu ba rashin gata ne da
neman rufin asiri amma yarinyar nan fa ta fita daban a cikinmu wlhy.”       Cikin son basar da zancen Bahijja ta ce, “Babu wani leƙen asiri. Itama dai neman rufin asirin
ne ya kawota. Acikin ƴaƴan talakawan ma ai akwai ƙyawawa da yawa irinta har ma da wanda
suka fita. Kin san dama irinsu gatan ne kawai babu, amma da sun samu kulawa sai ki gansu
tarr da su”.      Badan Afrah ta gamsu da bayanin Bahijja ba tai shiru. Dan Bahijjar na gama bata amsa ta
nufi hanyar fita itama. Kai kawai Afrah ke jinjinawa da sake tabbatar ma kanta dole ne ta
sakama yarinyar nan ido a gidan nan, dan sai ta san ko ita wacece....

      Koda na fito falon ma gaba ɗayansu suka zubomin ido. Hatta da Mama Balki naga alamar
shock a tattare da ita. Tuni na ƙara gyara yanayina, dan na fahimci fa nima sai na yarda na ari
wata rayuwa kafin na cimma burina akan mutumin nan dama zaman gidan nan. Sam bana fatan

zama a cikinsa na dogon lokaci. Amma ina da burin son sanin sirrin cikinsa da mutumin nan
keta faman ɓoyema duniya. Hakan kuma bazai taɓa ya kasance ba sai na zauna a matsayin da
kowa ke kallona a yanzu na ƴar aiki. Ta wani gefen kuma begen ganin mahaifiyarsa da
tausayinta na tsungulin min rai da zuciya. Sai dai ban san ta ina zan kama ba har yanzu.
Gaishesu nayi kawai na koma gefe kaina a ƙasa...
      “Tab ɗi lallai akwai rigima a gidan nan. A banga laifin Hajiya Azizat ba. Anya kuwa babu
alamar tambaya anan gurin?”. Aunty Falilah ce tai maganar cikin nuna baƙin cikinta muraran a
kaina. Dama na fahimci ita da sauran ƙawayenta su Aunty Kubrah basa ƙaunata sam. Kafin
wani ya sake magana Mama Balki tace muje. Dole kowa ya haɗiye abinda ke a ransa muka
fice. Cikin raɗa Bahijja dake ta gefena ta ce, “Kiyi haƙuri karki damu da su. Su dama su Aunty
ƴan neman fitina ne, sam basa riƙe girmansu a cikinmu saboda suna gadarar yaran Mammah
ne a gidan. Itace mai juya akalar kowa a gidan kuma hatta da mai gidan kansa da matarsa”.
      Murmushi kawai nayi batare da nace komai ba. Dan ta gefena su Afrah ne idan har nayi
magana zasu jini. Sosai an sake ƙawata gidan. Tako ina ka kalla kasan za'ayi shagali ne. A
maimakon cikin gidan yau garden muka nufa. Bamma san sanda na furta “Masha ALLAH” ba a
zahiri. Dan tsayawa muku misalin haɗuwa da tsaruwar da garden ɗin nan yayi ma ɓata lokaci
ne. Sai dai abin mamaki bamu tsaya anan ba. Ta wata ƙofa da ganyen flower ya baibaye muka
sake ratsawa sai gamu a wani killataccen waje da yafi wancan ƙatoton da muka ratso, wani irin
shiryayyen adon furanni da koriyar ciyawa akai masa tako ina masu ƙamshi. Ga ƙaton
swimming pool da ruwansa ke wani kalar ƙyalli da walwali tamkar ba normal ruwa ba.
Ƙasa-ƙasa Bahijja dake kusa da ni ta furta, “Wannan sashen garden ɗin babu mai shigowa
cikinsa sai a irin wannan ranar. Sau ɗaya a shekara kenan kawai”.
      Da mamaki nace mata, “Saboda mi?”.
      “Saboda bana kowa da kowa bane. Bakiga an zagayesa da waya ba. Uncle boss kaɗai ke
shigowa cikinsa, dan tanan shine jikin part ɗinsa”. Ta ƙare maganar da ɗan nuna min wata
hanya da aka ƙawata da koriyar ciyawa tamkar a irin lambun mafarkin gaibu ɗin nan. Na jima
ina kallon ƙofar abubuwa masu yawa namin kai-kawo. Sai dai bance komai ba face ɗan
kalle-kallen garden ɗin da nake yi. Komai a tsare a tsaftace. ga Docorretion ɗin da akai masa ya
bala'in sake ƙawatashi. Hannuna da mama tazo ta kama ya sani kallonta firgigit, murmushi
tamun da faɗin, “Zo muje ke anan zaki zauna har sai an buƙaci ganinki”.
       “Mama saboda mi?.
    “Saboda Aunty Mama bata bada umarni na shigo da ke har nan ba”.
Komai ban sake iya cewa ba har taja hannuna muka fito a wajen. A ƙaton garden ɗin na farko
muka dawo. Ta kaini can wani ɗan lungu ta ce, “Zauna anan. Kar kije ko ina dan ALLAH dan
akoda yaushe zan iya zuwa kiranki”.
    Kaina kawai na jinjina mata. Dan koda bata roƙeni ba ma bazan tashin ba. Nakai zaman
mintuna talatin a wajen dukan tunanina naga Yaya Musaddiq. Yau wani irin kwaɗayin son jin
muryarsa nake shi da Hafizzullah. Tamkar wadda hankalinta ke dawowa jikinta a wajen nake jin
ƙarfin zuciyata da komaina dake neman ƙwacemin a kwanakin nan na fara dawowa. Sai kawai
naji harshena ya ɗauki ambaton sunayen ALLAH. A jere na ringa sauke ajiyar zuciya kai kace a
barci na farka. Ratsa kunnenna da sautin muryar malam tayi yana karanto addu'a ya sani
lumshe idanuna a hankali. Ji nake hatta da jinin jikina yamutsawa yake yi har a cikin farautana
har malam ya kammala. Ajiyar zuciya na sake saukewa a karo na babu adadi, dai-dai nan sai

ga Mama Balki ta dawo kirana.
       Nasha mamakin ganin wajen yanzu dan cike. Dan komai da alama an tsarashi ne hatta da
mutanen dake a wajen. Ɗan bin kowa da kallo nake ƙasa-ƙasa nima har muka isa inda su
Bahijja ke tsaye jere. Dai-dai nan mc ke shelanta fitowar mai gayya mai aiki tare da tabbatar da
shi a madadin  mai birthday ɗin. Tsitt wajen yayi kowa ya sake maida hankalinsa ga hanyar da
Bahijja ta nunamin ta sashensa. Duk da yanda zuciyata ke tafasa na kasa ɗauke idanuna daga
kallon wajen nima. Ƙanjamammiyar baturiyar nan mai shegen iyayi da yaje da ita wajen taron
buɗe companynsa ce ta fara fitowa sanye cikin doguwar riga milk da wasu shegun dogayen
takalmanta. Siririn tsaki na saki tare da ɗauke kaina a wajen gaba ɗaya.
       “Woow masha ALLAHU”. Da Bahijja dake a gefena ta faɗa ya sakani ɗagowa na kalleta.
Ganin yanda ta saki baki da hanci da idanu tana kallo ya bani mamaki, kaina kawai na girgiza
zan ɗauke caraf ta kamo hannuna. ”Dan ALLAH ki kalla ado ya namijin ɗawusu Aunty Kandala.
Wlhy Uncle Boss na kasheni da salonsa, komai ya saka a jikinsa sai kiga kamar danshi dama
akayi kayan, wani lokacin sai nakeji kamar na ciza uwawuna”.
      Takaicin shirmenta ya sakani dalla mata harara. Nai ƙoƙarin fisge hannuna amma ta sake
damƙeshi. Haushi ya sakani kallonta, amma sai naga ma ita hankalinta sam baya a kaina.
Takaici ya sani girgiza kai kawai nakai dubana ga abinda take zuzutawar batare da nasan dalili
ba nima..........✍️
      _Bayin ALLAH kuyi haƙuri dani Please. Wlhy biki gareni na ƙanwata asabar ɗin nan. Jiya
kuma rasuwa akai mana data bugeni sosai. Amma in sha ALLAHU komai ya kusa dai-dai da
amarya taje ɗakinta zaku cigaba da ganina yanda ya kamata. Kuyi hakuri da asha ruwan
tsuntsayen nan nawa na yanzu_

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*








*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_




_����� ������ ��_



_���� ���_
_��� ���������_

......Akan takalman ƙafarsa na fara sauke idanuna, yanda suke sheƙi da ɗaukar idon mai kallo
ya isa tabbatar maka almubazzaracin da akai da kuɗi wajen sayensu. Coffee brown suit ne a
jikinsa, sai rigar ciki milk color. Kamar kullum botiran farko a buɗe har ana iya hango jikinsa
kaɗan. Luf-luff gashin kumatunsa ke kwance a saman fuskarsa tamkar masu barci, sai wani irin
sheƙi suke suma. Hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa ɗayan riƙe da wayar dake manne a

kunnensa yana wani motsa ƙananun pinkish lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima tilas.
Kamar kullum kunnensa ɗaya manne da ɗan kunne, daga tacan saman kansa zane da kitso
ƙwara biyu zane ata gefe da gefe, tsakkiya wiving kusan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login