Showing 15001 words to 18000 words out of 34694 words
Chapter 6 - Tsutsar Nama Book 2 Complete Hausa Novels By billyn Abdull.pdf
Hajiyan suke da katanga harda ƙofa. Akwai ɗan filin
tsakar gida, wanda ke da ƴan kayayyakin ajiya kamar su drum na ruwa guda uku, sai botikai da
yan tarkace na aiki. Sai murhun gawayi guda biyu da wasu tukunya masu girma guda biyu. Duk
da gidan a share yake tsaff ko kusa bai kama ƙafar ƙyawun inda muka baro ba. Lokacin da
muke ƙoƙarin shiga ƙofar da nake ƙyautata zaton ɗaki ne na kusa cin tuntuɓe da tarin takalman
dake a wajen, sai da ɗaya daga cikin ƴammatan ta taroni. Sannu tai min cike da nuna alamar
tausayawa, na gyaɗa mata kai kawai ina mai haɗiye abinda ke min kaikawo a maƙoshi. Ƙaton
falone sosai, sai dai babu komai a cikinsa sai carpet blue da aka malale ƙasa da shi. Sai ƙofofin
ɗakuna a jajjere a kowanne bango akwai biyar. Shima falon dai babu datti, sai dai carpet ɗin yay
masifar tsufa har a wasu wajajen ya yage wani gurin kuma ya gurje alamar yawan takawa, duk
naga hakane saboda hasken wutar lantarki dake haske dako ina. A hankali nakai zaune kamar
yanda suka umarceni, na takure jikina waje guda ina ɗan kalle-kalle. Kusan minti uku dattijuwar
nan ta kawo min abinci a plate ɗin roba. Shinkafa ce da wake da mai da yaji. Sai ruwan ƙwara
ɗaya.
“Bissmillah kici abinci ƴar nan. Sai kije kiyi wanka kizo ki kwanta”.
Kasa cema tsohuwar komai nai, sai binta da kallo kawai nake. Babu alamar ta damu da
hakan itako tai gaba abinta ta sake fita. So nake na danne komai a raina karna sakama kaina
wata damuwa ko tsoron inda na tsinta kaina. Dan haka na shiga turereniyar ture komai na fara
cin abincin. Kaɗan naci abincin dan bakina sam babu daɗi har yanzu, hakama jikina babu ƙarfi
sosai. Ruwanne na shanye gaba ɗaya, cikin sauke numfashi nai hamdala ga UBANGIJI.
Ƙoƙarin miƙewa nake dattijuwar nan ta shigo, kallonna tai ni da plate ɗin abincin, da yanayin
mamaki da gurɓatacciyar hausarta da zaman Lagos ya ɓata ta ce, “Ƴar nan badai har kin ƙoshi
ba?”.
A hankali na gyaɗa mata kai alamar hakane. Mama tai ɗan jimm kamar mai tunani, sai
kuma ta amshi plate ɗin ta ajiye tana faɗin, “Shikenan muje kiyi wankan sai ki kwanta ko?”.
Kai na girgiza mata, cikin yanayin dana tsinta kaina na sanyi da rashin ƙarfin zuciya kamar
wadda aka jefa na ce, “Mama zan kwanta kawai basai nayi wankan ba, dan in har nayi zan iya
samun matsala koda da ruwan zafi ne”.
Jimm mama tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Cikin sauke ajiyar zuciya tai min
nuni da hanyar ɗaya daga cikin ƙofofin dana gani. “Ba damuwa muje ciki to”. Ɗaki ne ƙarami
sosai. Amma duk da haka akwai katifu ƙanana irin na ƴan makaranta har guda biyar jere reras.
Kowace katifa akwai filo da bargo. “Nan shine zai zama ɗakin ki. Ba kuma ke ɗaya bace za'a iya
sake kawo wasu kuna kwana a tare. Sai dai a yanzu babu kowa sai ke kaɗai dan ankwashe
wanda suke ɗakin gaba ɗaya”.
“Mama saboda mi to?”.
Na faɗa cikin suɓucewar baki da jin wani irin ƙarfin zuciya a lokaci ɗaya. Komai mama batace
da ni ba. Sai ma juyawa da tai abinta ta fita kawai tana faɗin “Sai da safe”. Sosai mamaki ya
saka ni ƙurama ƙofar ido na tsawon lokaci. Sai kuma zuwa can na taɓe baki da ɗage kafaɗa
alamar oho muku nai kwanciyarta. Amma a can ƙasan raina aikin jaridancin ne ke faman
yinƙuromin, dan haka kawai nake ji a raina a wannan gidan akwai abinda ake ƙullawa. Abin
mamaki na farko canjawar Hajiyar nan da mai aikinta a lokaci ɗaya, ita da suketa tattalinna tun
daga jiya kamar wata ƙwai amma muna shigowa gidannan kamar basu ba. Na biyu wannan
ƴammatan dana gani anan da kuma shi kansa wannan part ɗin da alamu suka nuna mutanene
da yawa ke mu'amala da shi. Na uku ganin kusan ƴammatan duk hausawa ne musulmai
haihuwar arewa. Lallai ina buƙatar nasan wani abu kam. Sai dai ta yaya? A wajen wa?. Wannan
shine babban tsallen baɗaken....
Washe gari kiran sallar farko Maman nan ta tadamu, salla muka farayi, muna idarwa ta
tattaramu zuwa ainhin cikin gidan. Babu motsin kowa alamar mutanen gidan basu tashi a barci
ba. Aiki Mama ta rarraba mana, ta kuma tsaya a kanmu sai da kowa ya kama nashi yanda ya
kamata. Kafin kace mi cikin abinda baifi awa ɗaya da rabi ba mun kammala ko ina ƙal, sai
ƙamshin fresheners ke tashi da girkin da Mama keyi a kitchen. Can sashen nasu muka koma,
yayinda muka bar mama na ƙarasa girkin, a can ɗin ma ba zaman mukai ba, gyara ko'ina muka
shigayi, wasu kuma na haɗa wutar gawayi domin ɗora abincin kari. Ni dai duk abinda akace
nayi yinsa nake yi, yayinda nake faman bin kowa da komai da idanu cike da nazari. Babu
wanda ya tambayi sunana nima kuma ban tambayi sunan kowa ba, sannan ko'a junansu bana
jin suna hira balle ambatar sunayen juna, kowa aikin gabansa kawai yake baki ruff. Kafin goma
na safe mun kammala komai, masu shiga wanka nata ƙoƙarin yi duk da banɗaki biyune kacal a
sashen na toilet dana wanka, amma haka suke bin layi kamar wasu ƴan makaranta.
Kasancewar basu da yawa sosai basuja wani dogon lokaci ba suka kammala wanka. Zuwa
sannan mama ta dawo, ita ta rarraba mana abincin kowa yazo ya ɗauki nasa yaja gefe yana ci,
sai a sannan wasu ke ƴar hira ƙasa-ƙasa. Ni dai nama gagara cin abincin sai kallonsa kawai
nake har sai da Mama tai min magana akan na maida hankali naci dan Madam na buƙatar
ganinmu.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*
*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_
_ _
_ _
_ _
.......Wanke-wankenta take hankali kwance, yayinda bakinta ke faman raira waƙar Ado gwanja
ta Chass. Sosai zazzaƙar muryarta siririya ke faman ratsa zuciyar Abba dake falo zaune yana
waya. Shi kaɗai ne a gidan sai ita. Dan tun ɗazun Mom da Baby da Bibaa suka fita kasuwa wai
yi cefane Baby zata yi baƙo. Sai Auta dake ɗaki yana barci saboda zazzaɓi da yake yi kwana
biyu. Abbas kam ma yanzu sai ya gadama yake kwana a gidan. Shiko Nabeel yana hostel ne.
Ya Musaddiq ma ganinsa yayi wuya a gidan yanzu.
Halime kenan sabuwar mai aikin Mom da ta saka wata ƙawarta ta nemo mata tun bayan
wucewar baƙi ƴan biki da kwana biyu. Dan kuwa daga ita har su Baby sun gagara gyaran gidan
ga hargitsewar da yayi na hidimar biki. Da gaggawa ta buƙaci samun mai aikin dan haka ƙawar
tata ta kawo mata Halime da itama ta samo wajen wata mata mai kawo ƴan aiki daga ƙauye. Da
farko Mom taso ƙin amsar Halime, saboda ƙyaƙyƙyawar yarinya ce ga ƙirar jiki irin ta manyan
mata ALLAH ya bata. Rashin gyara ne kawai da rashin suturar kirki ya ɓoye baiwar da ALLAH
ya matan. Sai kuma ɗan shirme na rashin ilimi. Har tace ƙawar tata ta koma da ita a samo mata
wata su Baby suka shiga roƙonta dan su kam aikin suke gudu, dole ta haƙura ta amshi Halime
akan nan da wani lokaci za'a sake samo mata wata sai ta sallameta. Sai dai duk da haka ta
kafama Halime dokoki sosai a gidan musamman akan Abba. Dan tunda tazo gidan ma kusan
sati uku da wasu kwanaki kenan bai taɓa ganinta ba, itama bata taɓa ganinsa ba. Yau ma
Abban har ya fita kasuwa mantuwa tasa ya dawo gidan, kiran wayarsa da akayi ya sakashi
zama a falon yana amsawa. Gaba ɗaya wayar ta gundiri Abba, dan sosai muryar take sake
tasiri a zuciyarsa. Sallama yay ya miƙe zuwa ɗakin barcinsa yana ƙwala ma Mom kira dan bai
san basa gidan ba tunda ba gaya masa tayi zata fita ba. Cak Halime ta tsaya daga raira waƙar
da take yi, tai ɗan jimmm alamar saurare. Jin da gaske dai muryar namiji take ji na kiran
hajiyarta yasata ɗauraye hannunta a fanfo ta fito a kitchen ɗin. Dai-dai lokacin Abba na ƙoƙarin
shigewa bedroom ɗin da cigaba da ƙwala kiran sunan Mom. Cike da rashin wayo da gaɓanci
Halime ta ce, “Ikon ALLAH kai kuma waye haka kake kiran mafarauta sanƙamemen ƙato har
ɗakin kwanan mutane?”.
A bazata furucin nata ya shiga kunnen Abba, dan shaf yama manta da wata batun mai aiki
da Mom tace masa zata kawo, tunda shi dai bai taɓa ganinta na tunda tazo gidan, dan haka ya
juyo gaba ɗayansa. Idanu sosai ya tsira mata, ganin yanda ta riƙe ƙugu tana hura siririn dogon
hancinta da tura madaidaicin bakinta ya bashi dariya. Amma sai baiyi ba cikin suɓutar baki ya
furta, “Aljani ne”.
“Na higa uku ni Halime aljani kuma? Ita dama Hajiya tasan da aljanu a gidanta ta kawoni nai
mata aikatau”.
Murmushi Abba ya saki a karo na farko, yayinda a kaikaice yake sake ƙarema yarinyar kallo.
A fuska dai bazata wuce sha bakwai zuwa kaɗan ba. Amma a jiki akwai ƙira ta manyan mata,
dan tako ina a cike take. Ganin tana neman zurawa da gudu yay gyaran murya. “Kinga kwantar
da hankalinki ba aljani bane. Mai gidan ne. Ina hajiyar taki?”. Da mamaki Halime ta waro idanu waje sosai, sai kuma ta dafe baki tana juyawa ta kalla
makeken hoton dake falon, wanda tunda tazo gidan Ita dai bata gajiya da kallonsa saboda
ƙyawun da sukayi a jiki shi da Mom da su Baby. Su Samraah dai babu su daga ita har su Yaya
Musaddiq. Tabbas mutumin dake zaune kusa da Hajiya ne. Amma duk da haka sai da ta sake
juyowa ta kalla Abba. Kamar wadda aka tsikara ta zube ƙasa tana faɗin, “Na shiga uku wlhy
kuwa kaine ɗin. Alhaji dan ALLAH ai min aikin gafara”.
Murmushi Abba ya sake yi, sai kuma a hankali ya furta, “Ba damuwa tashi abinki. Ina
hajiyar taki?”.
Miƙewa Halime tayi, sai dai yanzu kanta a ƙasa alamar jin kunya. Cikin ƙanƙan da kai ta
furta, “Sun fita da Aunty Baby da aunty Bibaa”.
Ɗan jimm yay yana kallonta. Sai kuma bai ce komai ba ya kaɗa kansa zai shige bedroom ɗin.
Sai da ya juyo zai rufe ƙofar suka sake haɗa ido da Halime dake kallonsa itama. Da sauri ta
juya masa baya har jikinta na kaɗawa. Numfashi ya ɗan furzar da cewa, “Je ki cigaba da aikin
ki”. Bai ma kai ƙarshe ba ta zura da gudu hanyar kitchen. Kansa kawai ya girgiza yana
murmushi shima ya ƙarasa shigewa ciki....
★★★
Washe garin da nake cika kwana biyu a gidan bayan kammala aikin dana fahimci wajibine a
garemu a gidan muna dawowa wanka nayi na shige inda ke matsayin ɗakina batare dana shiga
aikin namu sashen ba. Kwanciya nayi wasu hawaye masu zafi na sauka min batare dana sani
ba. Gaba ɗaya na rasa mike damuna. Koda tunani nai ƙoƙarin yi akan kaina da zaman wannan
gidan sai kaina ya fara ciwo. A yanzu haka har ya fara saramin. Dole na tattara komai na watsar
na cigaba da kwanciya shiru a wajen har suka kammala aikinsu Mama tazo tai kirana dan a
zatonta banda lafiya ne. Da ƙyar na iya faɗa mata na ƙoshi. Jimm tai tana kallona, kamar zatayi
magana sai kuma ta fasa ta juya ma ta fita. Kusan mintun talatin da fitar tata sai gata ta dawo.
Wai na taso Hajiya na kiranmu. Babu musu na miƙe dan bama zan iya musun ba. Hasalima sai
wani irin tsoron Hajiyar ne naji ya sake shigata har zuciyata na rawa. Haka dai muka fito duk a
ɗarare.
Mun kai tsahon mintuna goma a tsaye bayan shigar Mama cikin falon kafin a bamu izinin
shiga ciki. Hamshaƙan mata muka samu har guda uku zaune cikin shiga ta alfarma. Basai an
faɗa ba, a kallo ɗaya da zakai musu zai baka tabbacin daloli sun zauna musu bama naira kawai
ba. Hajiya na zaune itama cikin tata shigar alfarmar tamkar mai shirin fita ma. Gefenta Janny ce
ke tausa mata ƙafafu a hankali. Gaishesu mukai a tare, duk suka bimu da kallon ƙurulla batare
da sun amsa ba.
“K fita anan banda ke”.
Furucin Hajiya ya samu ɗagowa gaba ɗaya dan bamu san dawa ake ba a cikinmu. Sai dai
ganin kai tsaye ni ta nuna yasa sauran maida kawunansu ƙasa. Cikin dokawar ƙirji na yunƙura
zan fita a cikinsu kamar yanda ta umarceni. Amma sai ɗaya a cikin matan ta katseni da faɗin,
“Kamar ya banda ita? Ai ni gaba ɗaya ma hankalina a kanta yake Madam”. Kai Hajiya ta girgiza mata. “No Alajah ita wannan sabuwa ce. Babu abinda ma ta koya balle
nai cinikinta. Sannan ba aikatau ne aikinta ba”.
“Babu wani damuwa a hakan ni tamun. Dan dama irinsu nake so sunfi daɗin sha'ani ya
zama komai kaine ka koya musu. Nima zayi gift da itane kar ki damu”.
“Amma Alaja.....”
“Basai kince komai ba zan ninka kuɗinta sau uku. Domin zanyi ƙyauyar girma ne”.
“Uku?”. Madam ta faɗa cikin waro idanuwa da sakin murmushi. Amsa Alaja ta bata da,
“Yes nan gaba ma idan aikinta yay ƙyau har ƙyauta ta musamman zaki iya samu. Dan gidan
girma za'a kaita dake kanki sai kin san kin zama mai sa'a a wannan gaɓar”.
A take kuwa Madam ta sallama. Babu ɓata lokaci matar tai kiran waya driver ɗinta ya shigo
da jakkar da bamu san minene a cikinta ba. Daga ganin yanda yayma Hajiya gaisuwa kasan
shima ɗan gida ne. Suma sauran duk sun zaɓi ƴammatan ɗaɗɗaya. Bayan suma an kawo tasu
jakar da bata kai ta Alaja girma ba Mama ta umarcemu da mu fito. Ni gaba ɗaya ma sai naji
kamar an ƙara ɗaureni da sarƙa. Sannan yanda nake jina ko wuta Hajiya tace na faɗa zan iya
hakan. Sabbin kaya Mama ta bamu mu ukun nan wai mu saka. Bayan mun kammala tace muyi
sallama da sauran ƴan uwanmu dan zata iya yiwuwa rabuwar kenan, idan iyayen gidanmu sunji
daɗin zama damu ba lallai mu sake waiwayen nan ɗin ba. Mu dukanmu tamkar waɗanda ake
sarrafawa da remote mukai sallama da su. Sai dai ƙasan zukatanmu mu kaɗai muka san halin
da muke a ciki sai UBANGIJINMU. Haka muna ji muna gani aka fiddomu harabar gidan inda
hamshaƙan motoci suke har guda uku. A ta farko da tafi kowacce ƙyau da tsaruwa akace na
shiga gaba. Yayinda aka buɗema Alaja baya ita kuma ta shiga. Sauran ma duk shiga sukai
motocin suka fice.
Haka kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga sakkomin. Duƙar da kaina kawai nayi na
cigaba da kukana batare da na bar sautin ya fita ba. Haka kawai nake jin takaicin kaina da
sauyawata. Jina nake tamkar bani Samraah Abdul-wahab Gwarzo ba. Gaba ɗaya tamkar an
kashemin zuciya da kuzari. Abinda kawai nake ganewa shine bin umarni. Munyi tafiya mai nisa
kafin na share hawayena na ɗago. Bansan lokacin dana furta (Masha ALLAH) ba a zuciyata
ganin wata irin ginanniyar anguwa da muka shigo. Sam tsarin anguwar baiyi kama da a cikin
ƙasata Nigeria ba. Victoria island na gani rubuce a babban symbol. Hakan na nufin sunan
anguwar kenan. Tun a farkon shiga street da shima aka rubuta a symbol sai dai banga farkon
sunan ba securitys suka tsaidamu. Sai dai ganin Alaja yasa suka bamu damar shigewa alamar
dai sun riga sun santa.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*
*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_
_ _
_ _
_ _
_______________
Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE