Showing 9001 words to 12000 words out of 34694 words

Chapter 4 - Tsutsar Nama Book 2 Complete Hausa Novels By billyn Abdull.pdf

Maash ya sanar
masa amma sai yaƙi ce masa komai. Ya kuma san minene ma'anar shirun ogan nasa, dan haka
ya sake birkicewa ya birkita likita da Nurses har ma da matar nan da tazo ɗaukar Samraah ɗin.
Kai dama kowa na asibitin dan har securitys basu tsira ba da sauran ma'aikatan...

        ���

   Ƙuuuuu!! Razanannen taka birkin ya karaɗe illahirin titin tare da sautin ihu mai firgitarwa. Ba
hamshaƙiyar matar dake cikin danƙarereiyar motar kawai ba, hatta da mutane dake kai kawo a
street ɗin tuni sunyo caa. Sosai Samraah da aka kusa kaɗewar ta matuƙar razana, dan
durƙushe tai ta cusa kanta a cikin ƙafafunta nuna alamar sadaƙarwa kawai. Haushi da takaici ya
saka mutane yimata caa da faɗa, dan duk wanda al'amarin ya faru akan idanunsu sun tabbatar
da laifin ta ne ba mai motar ba. Ganin yanda wasu ke ƙoƙarin kai mata duka ma adalilin yanda
har yanzu taƙi motsi daga durkuson razanar da tai yasa matar dakatar da su da sauri ta hanyar
riƙota ta miƙar. Rawa jikin Samraah ya cigaba da yi har hakan na rinjayarta tamkar zata faɗi.
Duk wanda ya kalleta yasan a gigice take har yanzu, dan haka matar ta shiga bama mutanen
daketa faman hargowar zagin Samraahn haƙuri tare da jan hannunta ta buɗe motar a gefen mai
zaman banza ta sakata. Sai da ta rufe sannan ta sake fuskantar mutanen da har yanzu sun
kasa barin wajen..
       “Kowa yayi haƙuri dan ALLAH kuma mu mata uziri. A yanayin halin rayuwar da ake ciki
yanzu muma zamu iya tsintar kammu a fiye da yanda yarinyar nan take ciki yanzu. Tun dai ma
komai bai sameta ba ai Alhamdullahi ko, sai muyi fatan ALLAH ya kiyaye gaba”.
     Da kalmar (Amin) suka shiga amsa mata cikin nuna gamsuwa da yabama ƙyaƙyƙyawar
zuciyarta, dan ba kowa bane zai iya yin abinda tai ɗin. Daga haka kowa ya fara watsewa itama
ta shiga motar dan ta tsarema mutane hanya har wajen ya fara tara mutane musamman masu
gadi na cikin gidaje nata fitowa. Bayan rufe motar ta ɗan kalli Samraah ta sauke numfashi mai
kauri, batare da tace komai ba taima motar key cike da ƙwarewa ta harbawa saman titi da ƙyau.
Tafiyar da bata gaza mintuna uku ba ta samu waje ta gangare gefen titin, dan bata son tai nisa
da anguwar ta zamto kuma anan yarinyar take duk da ta ganta da niƙaff a fuska. A yanzu ma
dai yarinyar kanta ƙudundune yake a cikin ƙafafunta, yayinda sautin shashshekar kukanta ke
fita kaɗan-kaɗan.
      “Ɗiyata a ganina godema ALLAH ya kamata muyi, dan da abinda yaso faruwa ya faru da ga
ni har ke da ba wannan matsayin muke ba ai. Kiyi haƙuri ga ruwan nan kisha ki samu nutsuwa
ko”. Shiru kamar bazata motsa ba, kusan cikar minti ɗaya kuma sai ta ɗago, Samraah
ƙyaƙyƙyawace sosai ta yanda hawayen da suka ma fuskarta kaca-kaca bai hana bayyanar
hakan ba.
      Idanu na tsira mata mai haɗe da sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci, sai kuma na kauda
kai na, a hankali na furta, “Ba kukan tsorata nake ba Hajiya, kukan baƙin cikin rashin
tabbatuwar abinda nai fata ne ya sakani kukan nan. Inama ace kin kaɗeni na huta da wannan
rayuwar da babu komai a cikinta face kayan ƙunci da baƙin ciki da ruɗani. Inama ace kin kaɗeni
na mutu banko shuraba na tafi tafiya ta har abada da babu dawowa na iske su Abbana. Hajiya

dan ALLAH ki fitar dani a motar nan na sake tarar gabanki ki bi takain.....”
         Cikin sauri ta katseni da faɗin, “Haba haba ɗiyata wace magana kenan! Miyay zafi haka
da irin waɗannan furuci masu tsauri. Ai duk da mun san zamu mutu bama fatan mutuwar a
kayinmu sai dai dan babu makawa sai ta zo ne. Amma muna addu'ar a koda yaushe ALLAH ya
jinkirta mana kodan tara ayyukan alkairi da neman gafarar UBANGIJI da ga na sharri da muka
aikata. Minene matsalarki? Miyasa kike ma kanki fatan mutuwa a wannan ƙarancin shekarun
naki da zamu iya kallo a matsayin yanzu ma kika fara rayuwar, ko kika fara buƙatar ta? Idan ban
shiga abinda ba hurumina ba ki daure ki sanar min ko zan iya fahimtarki da taimakonki da wani
abu....”
            “Ba taimako nake buƙata ba Hajiya, sannan babu wani abin sha'awa ko birgewa da
ƙawatarwa a labarina ko bayana. Ganni ki barni a yanda kika ganni yanzu kawai.” na ƙare
maganar da yunƙurin ɓalle murfin motar zan fice. Da sauri Hajiyar ta riƙoni tana girgiza kai. “A'a
ɗiyata yi haƙuri ki saurareni”. Juyowa nai na ɗan kalleta, sai dai bance komai ba........✍️

_Kuyi haƙuri da wannan Please. Zuwa anjima idan na samu damar yin wani zan ƙaro muku.
Wlhy abubuwane suka min yawa amma ina fatan kammalawa na dawo muku da ƙarfina_


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*








*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_




_����� ������ ��_



_���� ���_
_��� ���_


........A hankali ta ɗan sakar min murmushi da faɗin, “Ko zaki iya mun alfarma”.
      Cikin ƙosawa nace, “Tami?”.
   “Ta sanin inda zakije yanzu?”.
“Ban san inda na nufa ba, sai dai ina fata da addu'ar koma ina ne ya kasance hanyar cimma
ajalina”.
      Ɗan jimm Hajiyar tai kamar mai nazari, sai kuma ta saki murmushi mai ban mamaki tana
wani juya idanu cike da salo, “Bazan hanaki tafiya ba, amma zan so ki bani dama ta ƙarshe
muje gidana, maybe zan iya nuna miki hanyar cimma nasararki ta barin duniyar kamar yanda
kike fata”.       Idanu sosai na tsira mata tamkar mai son tankaɗe gaskiya da rairayeta akan fuskarta, kusan

minti ɗaya na ɗan kauce zuciyata na ayyana min na bita na samu mafaka koda na wasu
kwanaki ne, dan na tabbatar a yanzu na koma Kano makirin nan zai iya bina. Kuma Abba da su
Kawu bashi ni zasuyi, amma yanzu idan na laɓe a bayanta zan iya kiran Yaya Musaddiq muyi
shawara dan shiga Kano kai tsaye yanzu haɗari ne. Sai dai kuma ita kanta bawai ina jin na
yarda da ita bane ba ma ai. Amma bari na gwada sa'ata mugani. fuskata na ɗago na ɗan kalleta
da faɗin, “Kina so kiyi wasa da hankalina ne kawai Hajiya”.
    Da sauri ta dakatar da in da faɗin, “Ko ɗaya ba haka bane ba. Mizaisa nai wasa da hankalinki
ni kuwa, dama kawai nake buƙata daga gareki zaki tabbatar da abinda na faɗa ɗin in sha
ALLAHU”.
        Nan ma dai shiru nayi ina kallonta kawai, tai saurin faɗin, “Ki yarda dani koda na sati guda
ne, idan kinga ba hakaba zaki iya ɗaukar mataki kowane iri”.
     Shiru na sake yi na wasu ƴan sakanni kamar mai nazari, sai kuma batare da nace komai ba
na dawo da jikinna cikin motar sosai tare da jawo ƙofar na rufe kamar yanda take. Sosai Hajiya
ta sauke ajiyar numfashi da har ya bani mamaki, sannan ta ɗan kalleni, sai dai batace komai ba.
Nima ban sake cewa komai ba ina dai addu'a a zuciyata ALLAH ya hanata nasarar cutamin,
ALLAH kuma yasa ba daga ƙarƙashin makircin makirin nan Maash tazo gareni ba.

          ★(✷✷✷‿✷✷✷)★

     Tunda Hayatu yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba musanman a yanzu da yake
waya da Maash yana mai sanar masa guduwar Samraah daga asibiti. Dan Maash ɗin yayi wata
ƴar tafiya ne ta gaggawa, tunda ya fara harkar business duk inda zai je yana tare da Hayatu,
amma a wannan gaɓar ya barsa saboda al'amarin Samraah da ya kasance da ga shi sai shi
suka sani.
       Har tsawon mintuna biyu babu alamar Maash zai amsa. Kuma yana online. Hankalin
Hayatu ne ya sake tashi, muryarsa har harɗewa takeyi wajen sake faɗin. “Wlhy nayi duk yanda
kace Sir, zaman jiran isowarsu gidan kawai nake ma amma tai kirana wai basuganta ba. Ba
laifina bane, ba daga ɓangarena bane aka samu kurkure ka yarda dani. Ka kuma bani izinin
sanarma ƴan sanda na tabbatar tana cikin garin Abuja bata isa fita ba”. Shiru nan ma Maash
yaƙi ya tanka. Wayar Hayatu ya cire daga kunnensa ya duba, har yanzu yana online ɗin dai
tankawar ce bazai yi ba. Yafi kowa sanin halin Maash yanzu, dan ko iyayensa bazasu faɗa
masa hakan ba. Ko motsi da idanu ogan nasa yayi yakan fahimci yaren balle. Ya tabbatar
shirunsa a yanzu na ɓacin rai ne, kuma bazai tanka masa ɗin ba har sai idan shine yaso hakan.
Hakan kuwa akayi, bai tanka masan ba shi kuma ya kasa yanke kiran saboda shakka, haka ya
haƙura akaita ɗibar masa kuɗi har tsahon fin awa sai da shi uban gayyar ya gaji dan kansa ya
yanke kiran sannan hayatu ya kai zaune cikin kujera jagwab dan tun ɗazun ko zaman ya kasa
yi. Kansa kawai ya dafe yay shiru zuciyarsa na gudu. Dole ma duk yanda zai yi yayi dan gano
yarinyar nan kafin cikar awanni ashirin da huɗu. Idan ba hakaba yasan akwai matsala.....

        

   Wata shegiyar dariya Alhaji Sadisu mai agogo babban aminin Abba ya saki harda
ƙyaƙyƙyewa. Cikin ƙuluwa da nuna jin haushi kuwa Abban ya zuba masa idanu. Sai kuma ya

yunƙura zai tashi amma Alhaji Sadisun ya riƙosa yana faɗin. “Afuwan afuwan Imamu. Wlhy abin
naka ne zabban dariya. In kana abu sai naga kamar wani ɗan yaro bai mai garjejen saurayin ɗa
kamar Abbas ba. Yo banda abinka Gwaggo ai gata tamaka wlhy. Ka buɗe bakin aljihu kawai
malam musha biki ai ba wuce auren kai ba. Dama dai kaine kaso maida kanka pastor zama da
mace ɗaya shekara fin ashirin bayan ALLAH ya baka dukan rufin asiri. Yo ALLAH na tuba da
ana yin fin huɗu da ba tuni nayi ba”.
        “Amma dai ai na sanar maka matsalata ko Alhaji Sadisu. Kuma kaina shaida ne akan halin
Jalilah tunda na gwada son ƙara auren a shekarun baya har sau biyu amma aka nema nakasa
yaran mutane.”
    “Yo dan ta samu nasara a baya sai akace yanzu ma ka karaya zata samu. Alhaji Imam zama
namiji kaji, tun farko kai ne kake ɓata shirin dama da kake sanar mata da wuri. Kayi shirunka
yanzu har sai ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa sannan ka bada filin fara wasan jifa tunda
tsoronta kake ji”.            “Humm bazaka gane ba kawai, amma zan iya yarda da shawararka akan ɓoye matan. In
kuma hakan zata faru fa sai dai na nema auren a wajen kano.”
    “Wannan duk mai sauƙine, kabar komai a hannuna kawai. Kai dai jeka ka fara shirin gyara
inda amarya zata zauna nan da sati ɗaya zan maka jagora kai da kaina sai ka gode min saboda
inda zan kaika wlhy”.
    Murmushi Abba yay a karo na farko, dan haka kawai yake jin kuma batun ƙara auren na sake
masa tasiri a zuciya....

       Hummm Abba cin amana ko.

_________★

       Gida ne mai ƙyawun gaske madaidaici muka isa a anguwar mai tama kamar yanda na gani
a symbol, dan komai najin daɗin rayuwar gani da ido a kwaishi. Ƙamshi da tsarin gidan yafi
komai ɗaukar hankalina, dan haka nake ta ɗan kalle-kalle a kaikaice. A karo na babu adadi
Hajiya da tuni takai zaune cikin ɗaya daga kujerun falon ta dubeni ganin yanda nai tsaye a
farkon shigowa. Cike da kulawa ta ce, “Ƙaraso ciki mana ɗiyata. Kar kiji wani shakku ko tsoro,
wannan shine gidana anan Abuja, sai dai bana zaman daya wuce sati biyu a cikinsa a duk
ƙarshen shekara. Sai kuwa idan wani uziri ne ya kawoni nakanzo nai kwana ɗaya biyu har ma
zuwa uku wasu lokutan na koma. A yanzu haka ma kwana biyu ya rage na wuce”. A hankali na
haɗiye yawu alamar son cewa wani abu, sai dai kafin nace ɗin Hajiya ta katseni ta hanyar ƙwala
kiran sunan “Janny!”.
      “Yes Ma'am”.
  Wata murya ta amsa daga can gefen wata ƙofa da hanyarta aka shirya kujeru da tebiri. Kafin
na gama nazarin tsarin da kujerun dining ɗin sukayi da zamansu a wajen wadda Hajiya ta kira
da Janny ta fito. Budurwa ce itama sai dai zata girmeni sosai, da gani shigarta da uban gashin
attachment dake saman kanta ya isa baka amsar ba musulma bace. Cike da girmamawa Janny
ta sake gaida Hajiya tana ɗan satar kallonna. Nuna ni Hajiya tai da faɗin, “Kije da ita ciki, tai
wanka a bata abinci”.
    Murmushi Janny tayi a karo na farko, cike da girmamawa ta amsawa Hajiya tana nufoni.

“Sannunka”. Abinda Janny ta faɗa kenan tana mai riƙo hannuna. Ban amsa mata ba, sai ma
ƙoƙarin turjewa da nayi alamar bazanje ba. Hajiya dake kallonmu ta sake sakin murmushi.
“Kinga ɗiyata nasan mike a ranki, karki damu shi komai na rayuwa mataki-mataki ne tamkar ajin
makaranta. Ki kwantar da hankalinki zamuje gaɓar da kike buƙata. Bani nai miki alƙawari ba”.       “Amma Hajiya.....”
  “Shiiii!! Kar kice komai bita kawai”. Hajiya ta faɗa cikin katseni tana tsuke fuska a karo na
farko. Canjawar fuskar Hajiyar ya ɗan firgitani, dan haka nabi Janny kamar yanda aka bata
umarni tun farko....
     Cikin dauriya da danne duk abinda ke mun kai-kawo a cikin rai nayi wanka na fito fes dani
cikin doguwar riga mara nauyi ƴar kanti da Hajiya ta bani na saka. Ga wani ƙamshi mai daɗi na
tashi a jikina. Hatta da dunƙulallen gashina da zaman asibiti yasa baya samun gyara sai da na
wanke na busar da hair dryer dana gani a toilet ɗin. Yanda na fito da shi ne a buɗe yasa Janny
sakin baki tana kallona. Fuska na ɗan tsuke amma sai hakan bai sata yin shiru ba sai da tayi
magana. Da ga ƙarshe ta laƙemin wai zata tayani gyarawa. Mai sosai Janny ta saka min masu
daɗin ƙamshi da ma wasu abubuwan da suka sake miƙar da tsahon gashin nawa daya fara
dankwafewa tsaff, sannan ta fake min shi a ribbons. Ni a karan kaina sai da naji daɗin kan nawa
dama a kwanakin nan ya isheni da ƙaiƙayi. Shiru nayi kawai zaune ina ƙarema kaina kallo, a
take naji tausayin kaina ya kamani. Wasu hawaye masu zafi da ɗaci suka shiga sakko min.
Hannu nakai na sharesu da sauri, saboda tuna nayi alƙawarin bazan sake kuka ba akan halin
da nake ciki. Plate ɗin da aka kawo min na abinci na ɗan tsurama ido, sai kuma na tureshi gefe
dan bana buƙatarsa a yanzu duk da uban ƙamshin dake tashi mai tabbatar da abincin zaiyi daɗi
koda banga minene ba. Zamewa nai kwance a saman lallausan carpet ɗin da shima ke ta
tashin wani irin ƙamshi mai daɗi, gashi tsaf babu datti. Gajiya da wahalar dana sha ya sa barci
yin awon gaba da ni cikin ƙanƙanin lokaci..........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
[03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing_*








*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_




_����� ������ ��_



_���� ���_
_��� �����_


......“Madam bafa taci abincin nan ba, ko buɗe plate ɗin ma batai ba kuma tayi barci.” Janny ta

faɗa cikin nuna damuwa.
     Ƙaramar dariya Hajiya ta sauke tana wani lumshe idanu, sai kuma ta buɗesu akan Janny
cike da salon irin na wayayyun mata da suka gogu da sanin duniya. “Barta yunwar ai ba ƴar 
gidansu bace, dan kanta ma zata ɗauka taci”.
      Dariya tayi itama Jannyn da jinjina kanta. “Hakane Madam. Amma yarinyar yana da ƙyau fa
sosai, ina ka samo shi haka? Ko dashi zamuje Lagos ne?”.
         “Tsintacciyar mage ce, dan haka ma na dawo da tafiyarmu gobe kafin ta canja shawara.
Saboda na kula babbar kaddarace wannan, kwalliya da sutura kawai take buƙata”.
      Sosai Janny ta washe haƙwara, dan duk hausar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login