Showing 18001 words to 21000 words out of 26395 words

Chapter 7 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_


*______________________________________*

*_BOOK ONE_*
_Shafi na bakwai_
*______________________________________*


*_JAWAAD_*

............Cikin ƙunar zuciya da ɗacin da ya keji akan halayyar Shahudah yay shirin fita a
gaggauce domin komawa Office. Bai bawani ɓata lokaci ba ya fito cikin shigar ƙananun kaya sai
zabga ƙamshi yakeyi.

Shahudah na a falon kwance cikin kujera, ga kiÉ—a mai taushi ya na tashi ta cikin sifikun da
aka ƙawata falon dasu, sanye take cikin wando da riga masu azabar ƙyau kalar ruwan hoda,
kasancewar kayan robane sunyi mugun bin jikinta tamkar da fatarta aka haliccesu, wandon
iyakarsa gwiwa, sai rigar da bata rufe mata ko cibiya ba, dan ƙyau tayi ƙyau sosai, dolene ka
kalleta ka sake kallo.
Gaban ɗayan imaninta nakan waya ɗinta da take cheating, gefe ɗaya tana sauraren waƙa.
Har Jawaad ya gama sakkowa bata sani ba, sai da mayen ƙamshin turarensa ya bugi
hancinta ne ta ɗan lumshe ido tana zuƙarsa kafin ta buɗe ta yunƙura ta tashi zaune, ƙyawawan
fararen idanunta a kansa.
Shima idanun nasa na kanta, dan kwalliyar tata ta masa ƙyau, sai ya ji kaso mafi yawa na
haushinta ya ragu a zuciyarsa, sauran cake É—in da taci ta rage da kofin da ta sha tea ya kalla ya
kauda kansa, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yana sake haÉ—e fuska.
Murmushi Shahudah da ke kallonsa tayi, dan sam ita bata da riƙo, dama ko faɗa sukai zai
ta shareta, itako mintuna kaÉ—an ta manta sai kuma an sake wani.
Yanzu ma dai hakan ita harta huce, hakanne ya sata tasowa ta shige jikinsa tana magana
cikin shagwaɓa.
“Oh My BB kayi Æ™yau sosaiâ€.
Shiru yay mata, bai kuma rungumetanba shi.
hakan yasa ta É—ago tana kallon fuskarsa, ta kai lallausan hannunta tana shafa fuskar tana
murmushi, “BB kamin murmushi manaâ€. ‘Ta Æ™are maganar da sumbatar laɓɓansa’.
Duk da saƙonta ya shigesa hakan bai hanashi ture hannunta ba daga fuskarsa yana
ƙoƙarin janyeta a jikinsa, amma sai ta ƙankamesa tana bubbuga ƙafa cikin shagwaɓa.
Iska ya ɗan huro da ga bakinsa, a daƙile yace, “Wai mikikeyi haka kamar wata tata
Hudah? Ki bari karkimin Squeezing kayaâ€.
“Sai ka sake fuskanka to†‘ta sake faɗa a raunane’.
Kansa ya girgiza kaɗan yana riƙota sosai jikinsa, hakan ya saka Shahudah ɗago fuskarta
cike da annuri ta kallesa, shima kallonta yake cikin ido yana kuma narke idanunsa dake ƙara
tsundumata a ƙaunarsa.
“Idan kinaso ki sameni yanda kike buÆ™ata Hudah ki canja kamar yanda nima nake buÆ™ataâ€.
Yay maganar a hankali tare da sauke laɓɓansa akan nata da keta walƙiyar janbaki, ya
sumbata.
Kafin ta samu zarrar magana ya cireta a jikinsa ya nufi hanyar fita yana saka baƙin

Eyeglasess É—insa a ido ba tare da ya sake koda kallonta ba.
Murmushi Shahudah tayi tana wani juya idanu, tabbas tana ƙaunar Jawaad fiye da
hasashen mai tunani, dan shine namiji da ta fara so a rayuwarta, so kuma na haƙiƙa mai cike
da tsagwaran sadaukarwa, kuma tana fatan ƙare rayuwarta da ƙaunarsa. Matsala ɗaya da ke
tsakaninsu shine banbancin ra'ayi, Jawaad É—an gayune mai aji da cikar haiba, duk yanda kake
tunanin haÉ—uwarsa ya zarta nan, amma tana mamakin yanda kansa yake a tukunya game da
rayuwa irinta manyan yara, ta ɗan taɓe bakinta tana komawa cikin kujera ta zauna, tasan
canjawarta ta koma ra'ayinsa abune mai matuƙar wahala da iyawarsa a gareta zaiyi wuya, su
dai tafi a hakan kowa da ra'ayinsa zaifi basu zaman lafiya, kan ya matsa sai ta canja É—in dai-dai
da buƙatarsa.


★★★★★★

Ya isa Office ɗinsa da ya ƙawatu da kayan more rayuwa, sai ƙamshi mai daɗine ke tashi a
ciki, ya zauna cikin kujera yana mai miƙa hannunsa domin karɓar takardun hannun wanda suka
shigo tare. Shafin farko da ya buɗe ya maida ya rufe yana ɗago razanannun idanunsa, “Ina na
farkon?†Ya faɗa cikin karsashi.
Cikin ɗan ruɗewa da tambayar bazata Aminu ya shiga kame-kame, “S...o...so...sorry sir!,
dama Sir Qaseem ne ya karÉ“a, sai yace na kawo maka waÉ—annanâ€.
Gira É—aya Jawaad ya É—age sama, ya janye idanunsa da ke neman fara canja launi ba tare
da ya tankama Aminu ba, cikin nuna halin ko in kula ya mai da hankalinsa ga Computer É—in da
ke saman desk É—in gabansa.
Tsawon wasu mintuna da basu gaza biyar ba Aminu na tsaye, babu abinda jikinsa keyi sai
tsuma, zufa ta hudo dukkan ƙofar gashin da ke jikinsa.
Jawaad dake aikinsa ya kallesa ta wutsiyar ido yana faɗin, “Tsayuwar ka zaɓa ko komawa
dasu, idan ka karÉ“o waÉ—ancan ka haÉ—a ka kawo min?â€.
Sosai tsantsar firgici ya kuma bayyana a fuskar Aminu, ya sharce gumin da ya tsatstsafo
masa a goshi tare da gyara tsaiwa zaiyi magana.......
Wani mugun kallo Jawaad dake ƙoƙarin miƙewa ya watsa masa, ba tare da yace uffanba ya
zagayeshi ya fice da ga ma office É—in gaba É—aya.
Da tsantsar sassarfa ya biyo bayan Jawaad da ko kallonsa baima sake yiba.

Mutanensa biyar na amana suka take masa baya zuwa Office É—in boss É—insu, yayinda
Aminu ya bi hanyar da zata sadashi ga ubangidansa Qaseem Ali.
Yardar dake gareshi ga manyansa sam ta hana masa shamaki da neman izinin shiga
ofisoshinsu, kansa tsaye yake shiga ba tare da jiran iso ba. Sai da yay masa sarawar
girmamawa tamkar yanda al'adar jami'an tsaro take, kafin ya zauna a É—aya da ga kujerun gaban
ƙaton tabirin.
“Jay!â€.
“yes sirâ€.

“Ko kasan maganar sace Alhaji kokino tana neman shigo da shugaba Æ™asa a cikiâ€.
Cikin rashin fahimta Jawaad yace, “Sir! Kamar ya kenan?â€.
Shiru ogan yayi na wasu sakwanni, kafin ya É—ago kansa daga wayar da yake dannawa ya
maida kallonsa ga Jawaad, wayar ya miƙa masa yana faɗin, “Ɗazun nai magana da shugaban
Æ™asa kai tsaye babu shamaki kowa a tsakaninmuâ€.
Idanu sosai Jawaad ya zaro waje, “Sir, miya ce?â€. ‘Jawaad yay maganar a hankali, mai nuna
alamar tsorata’.
Kaɗan Sir Ahamad barewa ya buga tebirin gabansu yana huro iskar bakinsa, ya miƙe
tsaye tare da maida dukkanin hannayensa baya ya goya, sai da yay taku biyu zuwa uku kafin
ya juyo ga Jawaad, “Jay! Adadin lokaci, lokaci shugaban ƙasa ya bamu na gaggauta samo
Alhaji Sadi kokino, abinda ya bani mamaki annan yanda ya tsaurara, mika fahimta?â€. Jawaad dake bin ogansa da kallo kamar ya samu magiji ya sauke numfashi, tare da taÉ“e
bakinsa yana murza yatsun hannunsa da ke bada ƙarar ɗas-ɗas a hankali, zuwa kusan sakon
goma sha biyar sai kuma yaɗan zabura, cikin ƙanƙance idanu mai nuni da na tuno, yace, “Sir
sai naga kamar yana tunanin ana zarginsa da hannu a ciki....†“Exactly my dear!, nima wannan shine tunanina, Jay kana da ƙwaƙwalwa, shiyyasa a
komaina nake sonka a gaba†‘Sir Ahmad ya ƙare maganar yana komawa a kujerarsa ya zauna’.
Jawaad dake murmushin jin daÉ—in yabon da ogan nasu yay masa, ya sauke numfashi yana
gyara zama, “Sir inada shawaraâ€
Sir Ahmad dake kallonsa yace, “ita mukafi buÆ™ata ai ayanzu Jayâ€.
Jawaad ya lumshe idanunsa tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana jinjina kansa, “Zan turo
maka a rubuce Sirâ€.
“Okey babu damuwa Jay, yaya maganar zaÉ“in haÉ—a runduna?â€.
“Sir zanje na zauna dasu Asim yanzu insha ALLAH, zuwa yamma zamu aiko da jadawalin
sunayensuâ€.
“Okey, amm......â€
Maganar Sir Ahmad ta kakare dalilin Knocking ƙofa da akayi, haɗiye maganarsa yayi ya bada
izinin shigowa........


*______________________________________*
*BILKEESU*
*______________________________________*


Sakamakon tashi da hayaniyar yaran gidanmu a kowacce safiya, sai yau muka tashi
da hayaƙin sigari a gidanmu.
Gashi rashin samun isashen barci ya saka mafi yawancinmu makara sallar asubahi.
Hakanne ya kawo go slow É—in shiga banÉ—aki. A É—arare kowa ke komai saboda dokar rashin
yawan motsi da yaran Jazuuuga suka kafa mana, a cewarsu yana barcin safe, duk wanda yay
ƙwaƙwƙwaran motsin da ya tashi to lallai sai yaji a jikinsa, kuma komai tsufarsa basu ɗaga
masa ƙafa.
Hakanne yasa mafi yawan mazan gidanmu ficewa da ga gidan da wuri ba tare da ko

wanka sunyi ba, wasu kuma suka É—auki kayan wankan zuwa gidan wanka.
Mukan dama maman firdausi ta mana dabara, wani tsohon bokitin ƙarfenta da hannun ya
ɓalle tuni ta koma saka kayan tarkace a ciki ta ɗakko mana, a ciki mukai alwalarmu, bayan mun
kammala muka fita muka zubda ruwan. Hakama da zamuyi wanka saita yi dabarar saka labule
jikin murfin ƙofa da bango tace muyi cikin ƙatuwar bahonta. Muna kammalawa shirin makaranta
nayi, babu zancen zaman karin kumallo, baba ya bani naira É—ari akan idan naje makaranta sai
na karya, dan ita firdausi ta gama secondary tuni. Godiya nai masa na amsa na fito cikin
fargabar waÉ—anan shaiÉ—anu da suka wargaza mana farin cikin gida a cikin kwana É—aya kacal.
Sosai gabana ya faÉ—i, dan kuwa ina fitowa da Jazuuga na fara tozali, yana gaban fanfo
tsaye, daga shi sai gajeren wando, hannunsa riƙe da brush alamar baki zai wanke, sai yaronsa
ɗaya a gefensa riƙe da kofin ruwa.
Nai ƙasa da kaina, yayinda nakeji har lokacin shi nasa idanun na yawo a jikina. Tamkar
munafuka naÉ—an risina kaÉ—an ina faÉ—in “ina kwanaâ€.
Ban jira amsarsa ba nai ƙoƙarin wucesu.
“K zonan!â€
Naji an faɗa cikin wata sautin murya mai ban tsoro, sosai ƙirjina ya shiga sama da ƙasa, na
rimtse idanu ina karanto *Hasbinallahu wa ni'imal wakil.*
“K dan ubanki kurma ce?!!â€
Aka kuma faÉ—a cikin sautin da yafi na farko razanarwa.
Juyowa nai garesu, nazo gabansu na tsaya kaina a duƙe, dan bazan iya kallonsa haka babu
rigaba, duk da kasancewar gidanmu gidan haya ne bamu saba ganin haka da ga mazan
gidanba.
Shareni yay tsawon lokaci yana cigaba da brush ɗinsa, yayinda idonsa ke kaina ko ƙyaftawa
bayayi, sai da ya gama tsaf ya raÉ“a ta gefena ya wuce yana faÉ—in, “biyoniâ€.
Ba ƙaramin firgici na tsinci kaina a ciki ba, dan marata wani ƙugi tayi kafin ta ɗaure tamau
tamkar zata fashe. A cikin zuciyata kuwa ina tunanin na bisa nai masa mi? To. Ban gama samo
amsar data dace da tambaya taba naji an fisgi hannuna, duk iya ƙoƙarin tirjewata da magiyar
roƙonsa ya sakeni da nakeyi bai saurareni ba, sai da ya kaini har cikin ɗakin nasa sannan ya
wurgar dani saman lallausan kafet É—in da aka shinfiÉ—a yana huci.
“K kin sanni kuwa? Kinsan wanene ni? Dahar zaki ringa sakani maimaita miki magana!!â€.
Jikina na rawa naja da baya dajan É—uwawu ina girgiza masa kai, ga hawaye na gudu a
fuskata tamkar fanfo, ya kuma zaromin manyan idanunsa jajaye, cikin nunani da É—anyatsa
tamkar zai tsokale idona yake faɗin, “Karki bari na tsaneki a gidannan, inba hakaba wlhy saina
fatattaka rayuwarki, tashi maza ki gyaramin É—akinnanâ€. Cikin rawar jiki nake amsa masa da “to†na ajiye jakkar makarantana na fara gyara É—akin,
duk abinda nake yana tsaye a kaina tamkar wani dogari, niko sai hawaye nake zubarwa ba tare
da samun zarrar gogewa ba.
Cikin mintuna ƙalilan na kammala gyaran ɗakin, dama ba wani datti yayba. Ba tare da na
kallesa ba nake Æ™oÆ™arin magana, duk da nasan shi ni yake kallo, “N...na..gamaâ€.
“Saura shara†ya faɗa yana juyawa ya fita.
Tsintsiya na É—auka nai sharar ina cigaba da kuka, ina gamawa na fito daga É—akin, ALLAH ya
soni ya shiga wanka, yaransa kuma wasu sun fita sai mutum uku kawai.
A gudu-gudu na fice da ga gidan, duk da naga mafi yawancin matan gidanmu na laɓe ta

jikin labule suna kallona, wasu kuma ta Windown É—akinsu.

A yau kam inhar nace na fahimci wani karatu a makaranta to nayi ƙarya, abinda ya faru
tsakanina da baƙon gidanmu ya tsayamin a rai, babu abinda nake sai fargabar komawa gidan
ma, malamin mu na Geography har buguna yayi akan yana darasi ina duniyar tunani. Dai-dai
da yunwar cikina ban tuna da itaba har aka tashi, haka na nufo gida cike da tsoro dan bani da
inda nake dashi da ya wuce gidan, kuma dama can ban saba da yawo ba, da an tashi daga
makaranta gida nake nufa, shiyyasa yanzu ma naji can kawai nake buƙatar zuwa dukda kuwa
tsoron dake cike fal raina................âœí ¼í¿»








*_ALLAH ka gafartama iyayenmuí ½í¸­í ½í¹í ¼í¿»_**_Typing📲_*




*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_


*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na takwas_
*______________________________________*



............Shigowata soron gidanmu yaÉ—an sakamin nutsuwa kaÉ—an, dan yau babu mahaukacin
kiÉ—annan, sai da nai addu'a kafin na shiga da sanÉ—a tamkar wadda tazo yin sata.
Wata sassanyar ajiyar zuciya na kuma saukewa ganin ƙofarsa a rufe, sannan babu kowa a
cikin irin yaransa, sai wasu a tsirarun matan gidanmu dake Æ´an aiyuka a tsakar gidan.
Abinda ya bani mamaki yanda duk suka zubamin ido kamar wata baƙuwarsu, ni dai sannu

nai musu na wuce É—akin innar Firdausi kai tsaye.
Sannu Firdausi da inna dake zaune sukaimin, na amsa ina ƙirƙiro ƴar fara'a akan fuskata
tare da bin tarin kayanmu da aka jibge gefe da kallo.
Kafinma na tambaya firdausi ta fara min bayani,
“Bilkeesu kayanmu ne baba yace mu kwaso da ga baca mu maido nan, dan babu dacewa
zamanmu acanÉ—in saboda canjin da gidan ya samuâ€.
Murmushi nayi sosai wanda ya bayyana farin cikina yanzun kam, na zauna kusa da
Firdausi ina faÉ—in, “Amma inna idan mun dawo nan baba fa?â€.
“Karki damu kinji Bilkisu, babanku zai cigaba da kwana a bacar shi, kwananku acan babbar
barazanace a garemu da mutuncinku, waÉ—annan yaran sam zukatansu basusan yaren tsoron
ALLAH ba, abinda ransu keso kawai suke ji da gani a gaba É—aya duniyarsuâ€.
“Hakane inna, babu abinda zance daku nidai a wannan duniyar, ALLAH ya yalwata
rayuwarku da dukkan farin ciki har cikin aljanna, kun haska fitila a rayuwata lokacin da tsatona
suka kashe domin hana kansu ganin hanyar da zasu riskeni, kuÉ—in masu zinariyar zuciyace mai
haske fiye da ta dayimon (diamond), na.......†Katseni inna tayi saboda kukan daya sarƙe harshena, ta jawoni jikinta tana bubbuga bayana
alamar lallashi
“Ya isa haka bilkisu, kema ɗiyarmu ce tamkar Firdausi, ki daina kallonmu a waɗanda sukai
miki alfarma, muna yin abinda ya dace muyine kinjiâ€.
Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye.
Kusan tsawon mintuna uku tana lallashina, kafin na miƙe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login