Showing 24001 words to 26395 words out of 26395 words
Chapter 9 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf
“Mun baka kuwa Jay”
Sir Ahmad ya faɗa fuska ɗauke da murmushi.
Ƙamewa Jawaad yay tare da yin Salute nasu baki ɗaya.
Sun bashi izinin tafiya, duk da kuwa maganarsa ta ƙarshe tai musu tsaye a zuciya, sam
sun kasa fahimtar komai a kanta, domin dai hausace cikin hausa yayi.
Da tabbaci na dawowar abokansa uku garesa a safiyar gobe ya fita, koba komai ransa
yay masa daɗi idan ALLAH ya kaimu gobe iyanzu yana tare da aminansa, ƙashin bayan
jarumtarsa.
Duk bin ƙwankwantonka baka isa fuskantar yanayinsa ba, dan fuskarsa jarumar fuskace
ma'abociyar adana komai, Office ya koma, cikin hanzari ya haɗa komansa.
Yana fitowa Gimba ya ƙaraso gareshi, jikkan hannunsa ya amsa suka nufi mota.
Kowa yasan Jawaad mutumin kirkine a hukumarsu, sannan jajirtacce akan aiki, sai dai
sam baya ɗaukar wargi, yakanyi wasa da dariya da mutane idan yaso, amma kaɗan daga
aikinsa ya birkice ka kasa gane kansa cikin ƙanƙanin lokaci.
Gimba ya buɗe masa baya ya shiga, sannan ya koma ta ɗayan ɓarin ya ajiye masa
jikkarsa a gefensa, mazaunin driver ya koma yay bismillah tare da tada motar suka fice daga
station ɗin.
Luff Jawaad yay kwance jikin kujera, ƙwaƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ne kawai ke faman
aiki a lokaci ɗaya, hakan yasashi barin duniyar mutane ya koma zuwa wata duniyar ta daban.
Tun a shigowarsu farkon Layinsu ya buɗe idanunsa, da motar ɗaya da ga cikin
kawunansa ya fara cin karo, ya tsurama motar ido tamkar yaune ya fara ganinta.
Har aka wangale musu ƙaton gate ɗin family House ɗin suka shiga bai daina bin motar da
kalloba.
Sashin su Jawaad yana daga can ƙarshen gidan, hakan yasa saiya wuce dukkan sashin
kawunansa kafin yaje nasun, umarni ya bama Gimba akan ya tsaya inda Kawu Nasiru yay
fakin.
Kusan a tare suka fito da ga motocin, fuskar kawu Nasiru washe da murmushi yana kallon
ɗan ɗan uwan nasa.
“A'a Jawaad har an taso aikin yau da wuri haka?”.
Guntun murmushi Jawaad yay yana ɗan shafa kai, ya rissina a gabansa yana faɗin, “Eh
kawu mun dawo, ina yini”.
“Lafiya lau, Ja'iri kai dai kayi wuyar gani, muna a gida ɗaya amma sai mutum ya jera wasu
kwanaki bai ganka ba”.
“Ai min afuwa kawu, aikin namune sai addu'a, a koda yaushe mutum bashi da lokacin
kansa, ni kaina inason kasancewa a cikinku a koda yaushe, amma hakan bai samuwa”.
“ALLAH sarki karka damu, ai ka cancanci uziri ga kowa Jawaad, amma dai a rinƙa
daurewa ana shigowa kaji, musamman ma tsofaffinnan kullum zancensu na gareka, a daure
ana zagayasu akai-akai”.
“Insha ALLAHU kawu zan gyara, zuwa anjima duk zan shiga na gaishe da kowa”.
“To Alhmdllh, ka gaishe da baturiyar matar taka mai cika mana gida da kiɗa”.
Murmushin kan laɓɓa kawai Jawaad yay yana miƙewa, ya buɗe mota da kansa ya shiga,
Har gaban sashensu Gimba ya tsaya da motar, yazo da sauri ya buɗema Jawaad motar ya fito.
Sai da ya rakashi da jakarsa har gaban ƙofar falonsu sannan Jawaad ya amsa yana ɗaga
masa hannu ya shige.
Idanunsa ya rumtse da ƙarfi saboda su Shahudah dake baje a falo ita da ƴammatan
gidan, ga mahaukacin kiɗa na tashi a sifiku, wasu na rawa wasu na zaune wasu kuma a
kwance cikin kujera.
Sam babu wanda a cikinsu yaji sallamarsa balle motsin buɗe ƙofa.
Taku yake a hankali har gaban kayan kiɗan yasa hannu ya kashe, tsitt falon yayi.
Gaba ɗayansu a firgice suka maido kallonsu gareshi, kafin kace mi an fara ƴar reran gudu
ta ƙofar kichin, wasu kuma ta ƙofar falon.
Shahudah da ke kwance ta ɓata fuska tana masa kallon takaici.
Koda suka gama fita baice mata uffanba, kallo ɗaya yay mata yay hayewarsa sama inda
zai iske ɗakinsa.
Tundaga hawowarsa step ɗin farko ya fahimci Batool ko Nabeelah wani yazo yay gyara,
hakan saiya ɗan rage masa fusatar da yayi.
Ɗakin barcinsa ya zarce kai tsaye, yana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da murza key dan
karma Shahudah ta shigo.
Ɗakin yay ƙal saboda gyaran da ya samu, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi ga iskar hadari da ke
bada ƙamshin ƙasa.
Tamkar jira ake ya zauna ruwa ya fara sauka a hankali.
Yana zaune a bakin gado yana zame takalminsa yakejin bugun ƙofar da Shahudah ke
masa, baiko kalli ƙofarba balle tasamu darajar kulawa yay shigewarsa bayi bayan ya cire komai
na jikinsa, sai ƙaramin wando da ya bari.
Gaba ɗaya yarasa wane irin mataki ya dace ya ɗauka akan Shahudah ne ta dawo
hankalinta, shi yama fara tunanin ko bata da isashshen hankaline, dan sam baiga abubuwan
masu hankali tattare da ɗabi'unta ba, ko ada can yasan bata da kirrki sam, amma zaman
watanni bakwai da sukai a tare ya sake fahimtar dashi sanin da yay mata a baya ƙaramine
ashe.
Rai a ɓace yay wankan harya gama ya fito, baiji motsinta ba, hakan yasashi gane tayi
fushi, ya taɓe baki irin na rashin damuwa da hakan.
Zuwa yanzu ruwa ake zugawa sosai, hakan yasa yay sallarsa ta magriba a ɗaki, bayan ya
idar mai makon ya zauna tunani sai ya ɗauki Qur'an ya hau karatu cikin nutsatstsuyar muryarsa.
Bai matsa a gunba har sai da aka kira isha'i, har sannan kuma ruwan saman ake zugawa.
Wayarsa dake ring tun yana salla ya ɗauka, ganin Umma Bara'atu ce sai yay murmushi
(Umma Bara'atu ƙanwar mahaifiyar Jawaad ce, karku manta a labarinsa ya nuna mana tana da
ƙanne har uku duk mata).
Cikin girmamawa ya gaisheta, da ga can ta amsa masa cike da kulawa.
Bayan sun gama gaisuwarsu take tambayarsa koya ga abinci?.
Murmushi mai sauti yayi, wanda har tana jiyosa, ya kwanta rigingine a gadon ƙafafunsa na
ƙasa, “Yanzu nan Umma bazaki daina walar da kanki wajen aikomin abinciba kamar wani ɗan
primary ”.
Dariya tayi daga can, cike da son tsokanarsa tace, “Yo miye banbancinka dasu Jawaad, ni a
gurina ai tamkar tata kake, bama ni na aiko da abincinba, ƴar uwarka ce tayisa shine tabama
Nabeelah da taga zatazo tace ta kawo maka, sai kuma Nabeelar ta iske bama ka gidan ka fice”.
“Ayya, ALLAH sarki Sister, na gode mata kuwa, ALLAH ya bata miji na gari wanda zai
kulamin da ita, wlhy kiran gaggawa na samu da ga Office Umma shiyyasa na fice bata
iskeniba”.
“Aini wannan aikin naka dan banda yanda zanyine, amma da ga ni har Auta da Amina
bama sonsa sam, sai dai muna maka fatan alkairi a cikin, tunda kullum baba shi baya ganin
laifinka”.
Guntun dariya Jawaad yayi, da gani kasan hirar ta sakashi nishaɗi, dan a ransa ji yake
tamkar yana magana ne da mahaifiyarsa, “Karku damu Umma's ɗina, addu'arku ita nafi buƙata,
harma kinsa na tuna da Tsoho, insha ALLAH da safe asubanci zan masa naje shan saurar
furarsa”. “Ja'iri, zaka fara ko? To sai anjima”.
Sosai Jawaad ya ƙyalƙyace da dariya, ya shiga faɗin, “Haba Ummana karmuyi haka dake,
tsaya kiji......”
Ƙitt ta yanke wayar da ga can itama tana ƙyalƙyata dariya.
Sumbatar wayar Jawaad yay a hankali yana kuma faɗaɗa murmushin fuskarsa dajin ƙarin
ƙaunar ƙannen mahaifiyar tasa, masu ƙoƙarin share kukansa a koda yaushe.
_______________________
BILKEESU
________________________
Naji daɗin shigowa gida na iske su Jazuga basa nan, ɗakinsa a rufe.
Firdausi kawai na iske a ɗakinmu, Inna ta fita maƙwafta yin barkar haihuwa.
Tagumin da Firdausi tayine na janye, ta ɗago a firgice tana kallona, ganin nice sai ta sauke
sassanyar ajiyar zuciya.
Murmushi nayi ina faɗin, “Matsoraciya kin zata waye da?”.
“Ƴan ta'addan gidanmu mana, wlhy wannan rayuwar ta fara gundirata Bilkisu, nifa yanzu
ko shakkar banzan nan banayi balle tsoro, dan nakula ibilis ne kawai ya rikiɗa a mutum ya shigo
mana gida”.
Ido na zaro waje ina waige-waige, a tsorace nake magana ƙasa-ƙasa, “Firdausi bar irin
maganarnan dan ALLAH kar wani yaji”.
Baki ta taɓe tana miƙewa tsaye, “Ai kunji tsiyar, wannan tsoron naku shike ƙara masa
karsashi da jin ya isa, wlhy inhar a haka za'a cigaba da tafiya to lallai akwai babbar matsala,
dan kuwa sai kunkoma bayinsa tamkar a ƙarnin farko”.
Tsayawa nai kawai ina kallonta, dan na fahimci ranta a ɓace yake, hakan yasa nai shiru,
sam banason zancen yay tsawon da har wani zaiji, duk da Jazuga baya nan za'a iya samun
wani ɗan neman gindin zaman a gidan namu ya sanar masa.
Itama jin nayi shiru sai taja tsaki ta fice ta barmin ɗakin, murmushi kawai nayi ina girgiza
kaina, na cire kayana sannan na ɗauki abincinmu da nasan Firdausi bata ciba tana jirana na
fita, nasan bazata wuce tana soro ba zaune.
Ilai kuwa acan na isketa, dan haka na zauna kusa da ita ina ajiye kwanon tasar abincin a
gabanta.
Cikin sigar lallashi nake faɗin, “Haba dai tawan, wai fushi kikayi? To kiyi haƙuri kinji, taho
muci abinci, dan da gaske da yunwa na dawo mai katse ƴan hanjin ciki”.
Hararata tayi tana ƙokarin matse dariyar dake neman kufce mata, (haka muke sam bamu
iya dogon fushi da juna).
Munacin abinci muna ƴar hira jefi-jefi, sai ƙokarin kauda firar da Firdausi ke ɗakkowa ta
Jazuga nakeyi gudun kar'a samu matsala, a haka har muka gama na sake ɗaukar kwanon
abincin na maida cikin gida.
★★★★★★★
Kwanaki huɗu kenan cif Jazuga baya gidan, da alama dai yayi nisan kiwo, kallo ɗaya
zakaima gidanmu ka fahimci akuyoyin ɗaure sun samu sake, dan harmun fara sakin jikinmu
muna rayuwarmu tamkar ta baya.
Sai dai kash a ranar cikon ta biyar murna ta koma ciki, ɓeraye suka koma wasan ɓuya da
kuliya, dan kuwa da yammaci kwatsam saiga Jazuga da zugarsa sun dawo, tsit kakejin gidan
ya koma tamkar mala'ikan mutuwa ya shigo.
A ƙofar shigowa soro ya tsaya, sai da ya karema gidan kallon kamar yau ya fara shigowa,
sannan ya tako zuwa ciki, tafiya yake kamar zai tsinke saboda rashin ƙiba
Dan sam Jazuga bashi da jiki, gaba ɗaya wiwi ta gama kalace dukkan wata tsokar jikinsa
sai ƙashi data bar masa da fata
Amma a hakan akejin tsoronsa tamkar mutuwa, ga jiki duk yabi ya zane da tatu, daka
gansa kaga ainahin hatsabibi mai matuƙar haɗari da rashin imani, dan tsaf zai iya tsarwatsa
kwalwar kanka da bindiga ba tare da ya damu ba.................✍
*_ALLAH ka gafarta.a iyayenmu_*
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ ***************************