Showing 15001 words to 18000 words out of 26395 words
Chapter 6 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf
dan Shahuda ƙyaƙyƙyawace ta haƙiƙa, saboda mahaifinsu
bafilatanine ɗan asali mai asalin madarar ƙyawu, duk cikin yaran kuma Shahuda tafi biyosa, ga
jin daɗi da suke ciki, saboda inda suka taso, wannan ya haɗu ya maida Shahudah son kowa ƙin
wanda ya rasa.
Jawaad yana son Shahudah, sai dai halayenta na bashi tsoro, dan kuwa dai irin yarannane
da babu kwaɓa babu harara, idonsu ya buɗe da ƙazamar wayewa mai wahalar canja ra'ayi cikin
sauƙi. Dan haka sai bai wani cika sake mata fuska ba, dama can yaran Family ɗin shakkarsa
suke, dan bayan gaisuwa baya basu wata fuskar shiga huruminsa, sai dai fa yana ƙyautata
musu akan bukatunsu, idan abu suke buƙata kafin su tambayi sauran yayyensu sun nema da
ga wajensa, kuma inhar yana da halin yimusu yakan musu gwargwado.
Aikin da ya kai mahaifin su Shahudah ƙasar Holland ya ƙare, dan haka ya tattarosu suka
dawo ƙasarsu ta haihuwa, tunda suka dawo Shahuda ta dawo nan Tafida Family house ɗin su
Jawaad ta tare duk dan shi. Ba zamuce baya kulata ba, sake mata ne kawai bayayi, wannan
kuma badan hulaƙanci yake mata haka ba, rashin sakin jiki da jama'a halinsa ne kowa ya san
haka, ita kanta sanin hakanne ya sata bata damun kanta da lamarin nasa, burinta kawai ta
mallakesa matsayin miji, dan badan Jawaad ba bazata taɓa dawowa zaman ƙasarba sam, duk
abinda ya shafi afirika ɓata mata rai yakeyi, a haukarta bayan aurenta da Jawaad saita ja
ra'ayinsa sunbar yankin afirika gaba ɗayanta sun koma turai da zama. (Babbar magana
shahudah).
*★★★★★★★★*
Hankalin Hajiya Humairah ya tashi ganin tunda suka dawo ƙasar Jawaad yaƙi yay maganar
aurensa da Shahudah kusan shekara uku, hasalima yafi maida hankalinsa ga aikinsa fiye da
komai, ga Shahudah kullum cikin damunsu take akan batun Jawaad.
Shiryawa hajiya humaira tayi ta nufi *Tafida family house* domin tattaunawa da ƴan uwanta
akan batun auren, dama gashi lokacin meeting ɗinsu na family ya kusa. Koda takai kukanta
akan zancen sai kowa ya bada goyon baya, aka kuma tuntuɓi Jawaad akan maganar.
Haushi abun ya bama Jawaad matuƙa, dan sam bai shirin wannan auren nan kusa ba, so
yay sai ya maida Shahudah cikin hankalinta da aƙidar yankinta da addininta, amma sam an
wani zo an masa titsiye. Cikin ƙuluwar haushi akan zancen yace suyi duk yanda ya dace kawai.
Wasunsu sun fahimci bai soba, amma sai suka watsar da fushin nasa aka hau shirin biki
na ƴaƴan gata, dan dama babban burinsu suga yayi aure kamar sauran yaran gidan kodan su
gujema zaginsu da jama'a keyi akan sunƙi sakashi yay aure.
Sam ƙin bama bikin muhimmanci Jawaad yayi, hasalima hankalinsa na kan aikinsa,
komai sai iyayensa keyi, sai da Shahudah ta sakashi gaba da kuka sannan ne yaɗan maido
hankalinsa shima ba duka ba.
Haka dai dangi sukaita lallaɓata akan ta manta da lamarinsa tunda kowa yasan halinsa ayi
auren kawai, idan ta shiga zai bata kulawa insha ALLAH.
Son da take masane ya sata yarda da shawarwarinsu akai biki lafiya aka tashi, sai dai a
hidimar bikinma ta mugun shaƙar baƙin ciki, dan ƙin zuwa yay taro ko guda ɗaya har dinner ɗin
da suka shirya bayan ɗaurin aure ta garari ta nunawa a gidajen tv saboda tsabar haɗuwarta,
sam baijeba, a ranarma tsabar iskancin Jawaad a wajen aiki ya kwana, a washe gari kuma yaƙi
yarda ya hadu da kowa a gidan saboda tsiyar da ya tsula musu.
Shahuda kuma tace bazata tareba sai yazo ya bata haƙuri.
Nanma sharewa yay kamar baisan sunayiba, sai da Hajiya Ummah ƙanwar mama bilkisu
mahaifiyarsa ta kirasa tai masa faɗa sannan yaje, mai makon ya bata haƙurin sai ma ya sake
gaggasa mata magana, ya kuma ce inma bata tareba baida matsala da hakan.
Da yake su kaɗaine a ɗakin sai Shahudah ta ci kukanta ta share hawaye da burin sai ta
rama amma a gidansa, ga sauran ƴan uwa kuwa sai ta nuna musu ai ya lallasheta ne itako
tanata masa shagwaɓa ().
Kowa ya yarda da batubta, dan an tabbatar Jawaad nason Shahudah, halinsa na nuna ko
in kula da abu ne yake sakashi ɓoyewa, amma yanda ma yake ɗan kulata fiye da sauran yaran
gidan zai tabbatar maka da yana sonta.
Daga ƙarshe dai sai amarya ta tare a nan gidan sashin Alhaji Abdull mahaifin Jawaad,
dama tun bayan tashinsu babu wanda ya shiga sashen, yanzu kam sai Jawaad yay masa gyara
mai burgewa aka saka masa amaryarsa anan.
A farkon amarci abin nasu ɗoɗa-ɗoɗa,f amma son jiki da shegen ɗaukar dala babu gammo
na ɗabi'un Shahudah ne ya zamarma auren nasu matsalolin da baibayi da sukai ma zaman
nasu ƙullin goro. Tunda gashi har Jawaad na complain a kan auren watanni bakwai
kacal♀️..........✍
*_Mun dawo labari_*☺️
*_ALLAH ka gafarta na iyayenmu_**_Typing_*
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ ***************************
*_ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*
*_Bilyn Abdull ce_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull_
*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na shida_
*______________________________________*
..........A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take, yau ɗinkace kawai zata tabbatar maka
da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka. Rayuwa mataki biyu ce,
kowacce ka zaɓama kanka zaka isa zuwa makomarta, saɓanin shine kawai dace wajen
banbance nagartacciya ko gurɓatacciya. A yau dai ga ni a matsayin marainiya, wadda babu ɗumin duka mahaifa guda biyu, sannan
babu bangon jingina daga tsatson zuminci ko guda ɗaya. Rayuwata ta cigaba da tafiya a
hannun mutanen kirki ahalin fiddausi, sun zamemin uwa da uba bayan ƙasa ta rufe idanun
nawa, yanzu sune ci na sune shana da dukkan buƙatun rayuwa da aljihunsu sai iya ɗauka. Zuciyata na kewar iyayena, amma jarumtata na ɓoye hakan a koda yaushe, haƙuri kuma ya
zamemin sandar jagora yayin tafiya ba tare da na lalubi hanya ba saboda makantar zuci.
Tabbas rayuwar gidanmu ta canjamin ta kowanne ɓangare, dan a lokacin da iyayena na raye
akanji shakkar min wani abun, amma yanzu kam ƙiri-ƙiri wasu kan nuna ƙyamata ko hantara ta
ma kai tsaye, idanun maman firdausi ne kawai kan hana wasu cin zarafina koda da harara ne,
amma da zaran babu ita a tsakar gidan to kare ma ya fini daraja. Matsala ta farko dana fara cin karo da ita a gidan mai ƙona zuciya da barin tabon da ba'a
mantawa shine zuwan mai gidan Alhaji lado naira, koda iyayena suka rasu bana tunanin Alhaji
lado yazo gidan gaisuwa sam, amma rana tsaka sai gashi danƙyas-danƙyas yazo koramin
bayanin na kwashe kayana daga ɗakinmu zai zuba ƴan haya. Cikin ƙarfin hali da dogaro da kuɗin hayarmu na shekarar basuyi ko rabi ba na shiga kora
masa bayani akan ai da sauran lokacin tashinmu.
Alhaji Lado ya bankamin harara tare da watsamin yatsun hannunsa biyar cif alamar zagi
(daƙuwa) “Kinci uwarki, kujimin lalatacciyar yarinya, yo ko yau kuka biya tunda wanda yay biyan
ya tafi barzahu ai kuɗinku sunyi isfaya (expire) kuma, to dan shelen uwarki ma, gidan
tsohonki ko nawa da har zaki zauna jamin sharaɗi. Maza tashi kiyo waje da komai tafe nake da
mai fenti, ki zauna wannan bacar har kuɗin su kare, dan itama zaki fara biyan kuɗin hayane
tunda yanzu ƙofar ɗakin wasune”.
Kasare nai ina kallonsa tamkar wata wawuya ko sokuwa, wasu da ga jama'ar gidan ko
dariya suketa tuntsurawa, ƙalilanne basu ji daɗin lamarin ba, amma babu wanda yace ma Alhaji
lado baiyi dai-dai ba, dan sunajin tsoron ya shuka musu shika-shikan rashin arziƙinsa suma,
kaɗanma da ga aikinsa yace kaima ka tashi ka bashi ɗakinsa. Baka da yanda zakai dashi kuma
dolenka ka tashi, inba hakaba ya saka yaransa subi tsakkiyar rana ko duhun dare su naɗa
maka na jaki♀️.......
Tsawar da ya dakamin ce ta sakani zabura na miƙe tsaye, ya nunamin ƙofar ɗakinmu yana
haɗe fuska tamkar kashin ƙato na farar safiya.
Jikina na ɓari na nufin ɗakin, dan fuskar Alhaji lado tafi baƙin kashin shanu barazana idan ya
murkite ta, ina shiga itama firdausi na shigowa, itace ta taimaka min wajen haɗe kayan muka
ƙuƙƙulle ina sharar ƙwalla, sauƙina ɗaya ma kayan bawani uban yawane da suba, marasa
amfanin ciki kuma sunfi masu amfanin yawa. Bayan mun gama haɗesu ta taimaka min muka fiddosu zuwa cikin bacar da muke kwana,
wadda kayan suka mamaye kusan rabinta, dan dama bawani girman azo agani bane da ita.
Alhaji Lado bai kuma bi takaina ba sai ma yaransa da suka shiga suka fara fente ɗakin da
fenti mai ƙyau da ya bama kowa mamaki, dan duk ɗakunan gidan da farar ƙasa aka shafesu
maimakon fenti♀.
Da daddare munacin abinci a ɗakin su Firdausi innarsu ke bani haƙurin abinda ya faru
da rana, dan ɗazun bata da sukunin nuna tausayina suma ta shafesu, shiyyasa sukai gum da
ga ita har baba.
Murmushi nai mai ciwo ina faɗin, “Babu komai inna, ALLAHN da ya bashi muma bai manta
da muba ai”.
“Hakane Bilkisu” inna ta faɗa tana murmushi, ta dafa kafaɗa ta tana ƙara nuna min
muhimmancin haƙuri da amfaninsa.
Naji daɗin bayaninta, dan naƙara samun ƙwarin gwiwar ɗaura ɗammarar zama jaruma akan
kaina.
★★★★★★
Faruwar hakan da kwanaki biyu kacal waɗanda zasu zauna a ɗakin suka tare.
Abinda ya tada hankalin dukkan jama'ar gidan, shine wanda zai tare a ɗakin da muka
zauna.
Kusan sha biyun rana saiga ƙattai suna shigowa da kaya cikin gidan, waɗanda kallo ɗaya
zakai musu ka fahimci addu'a kawai rayuwarsu take buƙata. Sune suka saka komai a ɗakin
suka gyarashi tsaf, duk da bamu shigaba munsan dolene ya haɗu, dan kayan da akaita shiga
dasu babu ma mai kwatankwacinsu a cikin gidanmu. Mun daɗe bamu da wutar nefa a gidanmu, amma sai gashi anzo a ranar an gyara, washe
gari kuma sai ga masu gyaran fanfo tunda farar safiya.
Irinmu da bamusan wanene zai tare a ɗakinba dai mamaki ya matuƙar kamamu, burinmu
muga wanene zai zauna a ɗakin kawai.
Da yamma gan da magriba mun dawo islamiyya mukaci karo da baƙon lamarin da sam ada
babu kwatankwacinsa a gidanmu. Kana kusanto gidan kunnenka zai fara jiyo maka sautin kiɗa
da ke tashi da ƙarar Janareto (Genretor).
Kallon juna mukai ni da firdausi, dan munsan dai babu wani shagali da akeyi a gidan, koma
anayi ba'a taɓa kalar wannanba.
Badai muce komaiba muka shigo da sallama a bakunanmu. Fetal tsakar gidan yake tamkar
babu wani mahaluki mai numfashi, gidanmu da idan ka shigo da yamma zaka ɗauka biki muke
sai gashi tsitt, idanunmu suka sauka akan matasan samari da adadinsu zai kai goma sha uku
acan jikin ɗakinmu da muka tashi, wanda bacar da muke kwana ni da firdausi take kallonsa,
Mutum ɗaya ne zaune a kujera kawai yana zuƙar sigari, sauran kuma duk suna saman tabarna
babba da aka shinfiɗa, wasu karta sukeyi, wasu kuwa zaune suke suna kallon masu kartar, sai
ɗaya dake matsama na zaune saman kujerar ƙafa tamkar wani sarki.
Kallon juna muka sake yi ni da firdausi, yayinda suma matasan samarin suka zubo mana
idanu su duka.
Gyaran murya da na kan kujerar yayne ya saka dukkan samarin saurin nutsuwa kowa yana
sunkuyar da kai.
Baice uffanba shikam, sai zuba mana idanu da yay yana ƙare mana kallo da ga sama har
ƙasa duk da sanye muke cikin hijjabai har kusan ƙasa.
Firdausi ce tai ƙarfin halin kama hannuna muka cigaba da takawa dogon tsakar gidan muna
dosar inda samarin suke, dan ɗakin su firdausi shine jikin nami dama can, sannan bacarmu a
tsakanin ƙofar su firdausi da ɗakinmu na da inda samarn suke yanzu take, hakan yasa samarin
suke zaune har ƙofar bacarmu da gaban ɗakin iyayen firdausi. Duk da munga a yanayin da suke da bana mutanen kirkiba, ga kuma kiɗan dake tashi da
bamu da tabbacin zasujimu, hakan bai hanamu gaishesu ba. A mamakinmu sai mukaji suna
amsawa kuwa, wanda ke kan kujerarne kawai bai amsaba, kuma har yanzu idanunsa na
kanmu. Wanda ke zaune saman ƙofar su firdausi ne ya matsa mana fahimtar da yay kamar nan
zamu shiga, cikin sassarfa muka faɗa ɗakin kuwa da hanzarinmu ko sallama babu.
Maman firdausi dake zaune ta miƙe zumbur tana nufomu, hannunmu ta kama zuwa
tabarma jikinta har rawa yake.
Mamaki ya sake kamamu, mun buɗe baki zamuyi magana tai azamar mana nuni da muyi
shiru. Shirun kuwa mukayi muna cigaba da binta da kallo.
Haka mukai kwannan yau babu wani sikuni ga jama'ar gidan, kowa ya maƙure a ɗakinsa
yana tsoron fitowa, mu kanmu yau a ɗaki ɗaya muka kwana da iyayen firdausi, baba ya
hanamu zuwa bacarmu.
*MAFARIN MATSALA*
Baƙon dai da ya tare a ɗakin da na taso tun ƙuruciya na ganni a ciki matsayin namu, ɗan
Alhaji Lado Naira mai suna Jazuli (Jazuuuga) ne ya tare.
Jazuli ko nace Jazuuuga ɗane na huɗu ga Alhaji lado, shine namiji da aka fara haifa masa a
gidansa, yana matuƙar ƙaunar yaron tun yana ƙaraminsa, hakanne yasa ya tashi a sangarce,
sam Jazuuuga bayaji tun bai kai girma ba, tun yana secondary sukul ya haɗa dabarsa, yana da
yara masu take masa baya da haɗarinsu ya sa ake matuƙar tsoronsa, duk yanda kuke tunanin
takadaranci irinna Jazuli abin ya wuce gaban nan, bayan ya kammala sakandire dinne kuma
baban nasa ya ƙarama sheɗancin nasa armashi ta hanyar fiddashi karatu can kudancin ƙasar,
acewarsa zaifi samun ilimi acan.
Karku tunanin ilimin Jazuli ya nema koda yaje can ɗin, sam yama manta karatune ya kaishi,
ya shige cikin manyan marasa jin magana yay kane-kane yana ɗaukar nasa karatun acan,
tsawon shekara biyar iya abinda ya ƙaro ilimi a kansa kenan, idonsa ya matuƙar sake bushewa,
ya zama jan wuya na sosai. Abinda ya maido Jazuuuga gida kuwa kashe oga kwata-kwata na ƙungiyarsu da yay ne,
hakanne ya sakashi gudowa ya dawo gida dan yasan dai idan yazo nan ya tsira.
Duk da hankalin Alhaji Lado ya tashi akan halin da ɗansa ya sake ƙwarewa a kai hakan
baisa ya daina masa gata ba, saima ya ninka, a cewarsa ai hakanne zaisa ya shiryu.
Ɓarin kuɗin da Alhaji Lado kema Jazuli ne ya bashi damar jan ra'ayin yara takadarai irinsa,
wasuma abun nasu ƙaramine, amma saiya horar dasu matsayin sojojinsa, ya haɗa ƙungiya mai
matuƙar haɗari da barazana.
Akwai dalilin da yasa Jazuuga ya dawo gidan hayar na mahaifimsa, dukda gidansu kuwa
yaci yluban wannan sau fiye da goma, ga kayan alatu da morewar rayuwa a cikinsa, amma
saboda son samun cikar burinsa shine ya cema mahaifinsa nan yakeson zama, babu ɓata
lokaci kuma Alhaji Lado ya zo ya tada Bilkisu da ga ɗakinsa aka gyarama Jazuuuga...............✍
*_ALLAH ka gafartama iyayenmi_**_Typing_*
*_ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*