Showing 12001 words to 15000 words out of 26395 words

Chapter 5 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf

da mutanen gari ta kowanne fanni
amfanuwa suke da tagomashin arziƙinsa, ya zama bango abin jinginar kowa, sannan runfa mai
lulluɓe zafin rana ga kowa, dukda hakan kuma bai isa zama mai ƙyautata zukatan kowa ba, dan
ko UBANGIJI daya hakicci ɗan adam baya iya masa............✍

_Please mu haɗu page ɗin gobe idan ALLAH ya kaimu dan jin yanda zata kaya_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*I think you'd like this story: "ƘWAI cikin ƘAYA!!" by
BilynAbdull on Wattpad https://my.w.tt/tRmHPDmnJ5


*_Typing_*





*_ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*


*_Bilyn Abdull ce_*


*_SADAUKARWA:_*
_Aunty Fareeda Gachi_
_Aunty Rahma A-Majeed_


*_Wattpad_*:- _BilynAbdull_

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na biyar_
*______________________________________*


...........A yanda Abdul-Aziz ke bautama al'umma da hidimarsa, sai ka ɗauka bai ma san ciwon
dukiyarsa ba, kokuma a banza ya sameta ba da guminsa ya taraba. Abubuwa yake na bajinta
ko tunanin kuɗin zasu iya ƙarewa bayayi, kafin kace kwabo sunansa ya zauna ɗam abakin
mutane, ko yaro ƙarami ka ambatama sunan Alhaji Abdul-aziz tafida da gudu zai amsa maka
harma yay maka sharhi gwargwadon fahimtarsa.

Rayuwa ta ci gaba da shurawa, yayinda wasu da ga cikin jama'a suka fara kafa dandalin
kiranye ga Alhaji Abdul-aziz zuwa ga siyasa. Duk da yana jinsu, kuma yana ganinsu, sai ya
maida kansa makaho kuma kurma akan batun, dan shi sam siyasa bata cikin tsarin tafiyarsa ko
burinsa. A na cikin wannan yanayinne ya fara ginin wasu katafaren gidajen gona guda biyu, amma a
jihohi mabanbanta. Sai wani katafaren family house da zai haɗa dikkan ahalinsa waje guda,
kuma kowa da ɓangarensa babu ruwanka da shiga sabgar gidan ɗan uwanka, Wannan aikinne
ya kauda hankalinsa ga nacin jama'a na son ganinsa cikin siyasa. Lamarin kuɗi sai mai su, kafin kace wani abu gidajen gona sun kammala, hakama gidansu,
matasa da yawa harma da magidanta sun samu aikinyi a ciki, abubuwan alkairi harsun fara
fitowa ta gidan, sannan suma sun koma sabon gidansu shi da duk sauran ƴan uwansa da
iyalansu, mama maryam ce kawai taƙi tunda dai aure takeyi, sai Alhaji Abdul-aziz ya sayi gida
kusa da su suma suka koma.

Duk yanda Alhaji Abdul-aziz ya so zamewa siyasa lamarin ya faskara, dan kuwa sosai ake
masa bibiko da naci harta hannun aminan mahaifinsu da mama maryam kanta da mijinta.
Rana ɗaya suka ware wajen ritsashi, dan gangami akai masa na musamman tare da
manyan mutanen da zuciyarsa kejin kunyar bijiremawa. Ba da son ransa ba dole dole ya amsa
da addu'ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi.
Kowa ya amsa da murna da farinciki, tare da masa addu'oin na musamman wajen bashi
nasarar jagorancin al'umma cikin sauƙi.
Ƙyawawan halayensa ne yasa shi kasancewa mai kishin jama'ar sa, har suma sukeji a
ransu zasu iya sakar masa ragamar rayuwarsu ya mulka, babu ɓata lokaci rana tsaka ya afka
siyasa bisa jagorancin abokai da matsawar mutanen gari da suke ganin ya cancanci zama
jagoran nasu. Koda ya tuntuɓi ƴan uwansa sai suka bashi goyon baya, dan duk ya riga ya gama siye
zukatansu, zuwa yanzu ƙauna ta haƙiƙa suke masa da bashi kulawa wajen jansa jikinsu, (kowa
yasan ziciya da son mai ƙyautata mata), dama kuma suna cikin waɗanda aka kama ƙafa dasu
harya amince da batun. Mama maryam ma sai ta bashi goyon baya sosai, tare da binsa da addu'ar alkairi, sai dai
sam Bilkisu abin bai kwanta a ranta ba, amma babu yanda ta iya tabi ayarin ƴan binsa da
addu'a tunda taga kowa ya bashi goyen baya, bai kamata ita ta zama ƴar ta wareba a cikinsu.

Shekarar da Abdul'aziz ya shiga siyasa a shekarar Bilkisu ta sake samun ciki a bazata,
ai farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu bashi da kwatankwaci sam.
Bilkisu tanata rainon cikinta hankali kwance, ga kulawa tana samu ga kowa, watanta tara cif
da wasu kwanaki ta haife ɗanta namiji sargaɗeɗe, inda ranar suna yaci sunansa *Jawaad*.
Jawaad ya tashi cikin kulawar dangi da mahaifa, gashi yaro abin san kowa a zuciya, dan
danan ya fara wayo, gashi da jikin girma masha ALLAH, shekararsa ɗaya da rabi Bilkisu ta
yayesa, dan yana tafiyarsa ko ina, ga haƙora reras a baki, sai dai kumafa baya magana, dan
har Jawaad ya kai shekara biyu da wasu watanni baya magana, bayama yunkurin yinta, hakan
yasa kowa yake ɗauka ko bebe ne, dan sun tabbatar yanaji da kunnensa, tunda idan akai masa

magana yana fahimta, bakinsa ne dai baya furtawa. Tunma Bilkisu na damuwa harta daina ta
maida komai hannun ALLAH, dan koda Alhaji Abdul-aziz yace zai kaisa asibiti itace ta hana,
acewarta a jira aga zuwa wani lokaci dai.
Domin farin cikinta ne kawai ya so barin zancen sai dai kuma da ga baya saiya kasa hakan,
dan abin na damunsa, ga dai Jawaad da wayau harma na tsiya, amma yaro bai da maraba da
dutse a fannin faɗin albarkacin baki. Kuma zama yay ya lallaɓa bilkisu akan kai Jawaad ɗin
asibiti, da kyar ta yarda dai aka kaishi, sai gashi kuwa an gano yana da matsala ne a ƙasan
harshensa da maƙoshinsa, nan akai masa aiki yay tsawon sati uku yana jiyya kafin ya warke su
dawo gida. Ba'aja wani dogon lokaci ba Jawaad ya fara magana, zo kuga murna ga wannan
ahali, kowa na sake miƙa godiyarsa ga ubangijin al'arshi buwayi gagara misali.
Babu daɗewa da samun lafiyar Jawaad, a cikin matan Alhaji Yusif ɗaya ta rasu, Wannan
rasuwa ya mugun girgiza wannan ahali sosai, musamman ƴaƴanta.
Bayan wucewar komai na rasuwar jama'a suka takura ma Alhaji Abdull akan ya fito
takarar shugabancin jihar, sam ki yayi, danshifa dama bai shiga siyasa dan yazama shugaba
ba, ya shigane kawai dan ya zama jagora da zai tsaya kan masu mulkin su tallafi talakawa
kawai, amma badan yay mulkiba. Nanma dai caa aka sake masa, babu yanda ya iya sai ya amince kawai yabi ayarin ƴan
takara.
Abin zai baku mamaki idan nace muku komai yimasa akeyi, duk da talakawa sunsan yanada
kuɗin da zai iyama kansa komai haka suka tattalafa da kansu sukai komai, acewarsu ai sune
sukace yayi, dan haka sune zasuyi masa komai.
Wannan lamari ya sake girgiza duniyarsa, dan yarasa miyasa jama'a suke masa irin wannan
makahon soyayyar?

Ni ko nace Alhaji Abdul ai masu iya magana kance (Nagari na kowa, mugu sai maishi).

Bayan kammala duk wani hatsaniya da ruguntsumi na kamfen akai zaɓe, tunma ba'ai nisa
ba kowa ya fahimci Alhaji Abdul-aziza Yuseef ya bige abokin takararsa, tunkan sakamako ya
fito mutane har sun fara shagulgula, ana faɗa gari ya sake harmutsewa.
Shi Alhaji Abdul-aziz ma ana faɗan yaci kuka ya kamayi, dan haka kawai yaji zuciyarsa ta
karye ya shiga share ƙwalla.
Lokacin Jawaad na jikinsa yana wasansa, sai ya tsirama mahaifin nasa ido yana kallo duk
da baisan mike faruwa ba, murmushi Alhaji Abdull yayi ganin kallon kurilla da Jawaad ke masa,
ya ja kumatunsa kaɗan yana faɗin “Haba ɗan sanda kallon fa na minene? Yau nauyi ya haye
Abbanka mai girman gaske, kai min addu'a ALLAH ya bani ikon saukewa”. Duk da Jawaad baisan ma'anar maganarba sai ya ƙyalkyale da dariya shima yana jan
kumatun abbansa kamar yanda yay masa.
Murmushi Bilkisu da ke gefensu tayi kawai, dan batasan dalilin da yasa mijinta keson kiran
ɗan nasu ɗaya tilo police ba, tun baima kai hakaba yake kiransa da suna JAY -P!, tunma bata
fahimci ma'anar sunanba har dai ta tambayesa ya gaya mata.
Ko a lokacin batai masa jayayya ba sai fatan alkairi yazama ra'ayin Jawaad ɗin kenan idan ya
girma shima.
Tun a lokacin ya fara amsa wayoyin taya murna har ma kansa ya nema fara ciwo.

Bayan abubuwan da suka biyo baya dai a ƙarshe aka rantsar dasu, Alhaji Abdul ya koma
gidan gwamnati shi da iyalansa, sai dai su mama maryam basu bisuba, sunce zasu rayu anan
gidan da ya saya musu.
Harkar mulki ta fara gudana, inda Alhaji Abdul yazoma duniyar ƴan siyasa da sabon salo
mai ban mamaki, gaba ɗayan albashinsa ya sakashi a taskar gwamnati, an ware aiki na
musamman za'ayi ma talakawa aiki da kuɗin, sannan ya dage tsayin daka wajen gyara jiharsa
ta kowanne fanni, dandanan sunansa yay amsa kuwwa a ƙasar, komansa ya zama abin koyi da
alfahari ga al'ummar da yake jagoranta, ya zama zakaran gwajin dafi sannan tauraro mai
haskawa da zamaninsa.
Gashi sam bashi da girman kai, kowa nasane, babu ruwansa da wani banbancin jam'iyya ko
yare, tsakaninsa da ALLAH yake aikinsa cikin ƙwarewa da jagorancin UBANGIJI.

Adadin shekaru na hawan farko suka cika ga duk waɗanda suke kan mulki, mai makon
Alhaji Abdul-aziz ya koma sai jama'a suka nuna shugabancin ƙasar gaba ɗaya suke bukatar ya
karɓa. Wannan lamari yaso gigitashi sosai. A fili ya nuna sam bazata yuwuba, amma ina jama'a
sun tsaya kai da fata suna masa magiya da kai kukansu wajen ALLAH. To duk abinda ALLAH ya hukunta sai ya kasance koda bawan da abin ya shafa bayaso,
kana nakane ALLAH yana nashi, nashiko shine gaskiya.
ALLAH ya ƙaddara sai ya zama shugaban ƙasa, sai ga shi kuwa ya zama, dama wanda
yake kai ya gamane gaba ɗaya.

Zuwa yanzu Jawaad ya girma, dan shekarunsa bakwai a duniya, yaro mai wayo da
ƙyawawan ɗabi'u, kamar yanda ƴaƴan talakawa ke makarantar gwamnati sai ga Jawaad ma a
ciki, dan mahaifinsa yace ita shima yayi, a ma ƙauye, to ɗansa ma can zaiyi babu tantama. Aiko
hakance ta kasance, dan sai ga ɗan shugaban ƙasa a makarantar gwamnati, abin ya burge
jama'a, tare da jan hankali ga sauran masu mulkin suma duk sukaita maida ƴaƴansu can.
A gefe kuwa Alhaji Abdul nata sake cusama Jawaad son aikin ɗan sanda, cikin amincin
ALLAH kuwa sai gashi yayi tasiri a ran yaron, dan babu sunan da yake ƙauna a ransa kamar
*JAY-P!* da Abbansa ke kiransa dashi, ma'ana *_(Jawaad Abdul-aziz Yuseef police)_*.
Ko kayan wasan Jawaad duk zaka samu suna kamanceceniya ne da kayan jami'an tsaro,
abin ya riga ya shiga yaron jini da ɓargo.

Shekarar Alhaji Abdul-aziz ɗaya akan mulki ALLAH ya jarabcesa da ciwon da har ya
kwanta, ashe hawan jinine bawan ALLAH, kwanansa uku kacal da wannan ciwo zuciyarsa ta
buga yabar duniya.

Tashin hankali kenan wanda ba'a saka maka rana, wannan lamari harma bansan a yanda
zan musaltashi masu karatu su fahimta ba, dan kuwa ƙasarce baki ɗaya ta harmutse tare da
komai na cikinta, mutuwar Shugaban ƙasa Abdull-aziz ba batun iyalinsa kawai akeba, maganar
al'umma kawai akeyi, waɗanda sukeji basu taɓa gamo da rashi mai taɓa zukata da aiyuka irin
wannan ba.

Tunda wannan rasuwa ta gudana bilkisu ta rasa hankalinta, sam an kasa gane kanta,
hauka take tuburan wanda ya kai ga har an rufeta a ɗaki ma.
Mama maryam tsohuwa mai tawakkali da hakuri, baka ganin hawaye saman fuskarta sai dai
na zuci kawai.
Ƴan uwansa kam su kansu ka kalla abin tausayine, lamarin yay masifar ruɗasu, dan Abdul
mai biyayyane a garesu tare da ƙyautata musu, suka tuna irin gwagwarmayar da yasha a
rayuwarsa da bajintar da yay musu a rayuwa sai suji hankalinsu ya kuma ƙololuwa a tashi,
sunyi kuka harsun godema UBANGIJI. ALLAH sarki Jawaad, duk da bai kai hankalin da za'ace ya fahimci komaiba ya ɗanyi
kukansa ganin kowama yanayi, musamman ma halin da mahaifiyarsa take ciki na hauka, sai dai
zuwa wani lokaci kuma sai ya saki ransa, yakan dai zo ya tambayi mama maryam ina Abbansa?
Yaushe ne zai dawo?. Sam bata ɓoye masa, takan ce masa Abbansa ya tafi inda ba'a dawowa.
Wani lokacin yayi kuka, wani lokacin kuma yay zugum yana tunani kafin kuma ya saki ransa
ya koma wasa cikin yara sa'oin sa.

A haka aka share wasu watanni, riƙon Jawaad ya dawo hannunsu mama maryam, bilkisu
kuma ana cigaba da nema mata magani, dan bata ma ƙasar an kaita asibiti.
Haka rayuwar ta cigaba da shurawa, an maido Bilkisu gida, kamar taji sauƙi sai kuma abu ya
dawo sabo, lokacin har Jawaad ya fara wayo, yana shekara ta goma sha huɗu, ajin secondary
js2, ranar wata juma'a sai aka wayi gari Bilkisu ta bar gida, nema iya nema anshasa amma
babu ita babu dalilinta, lamarin ya girgiza mama maryam har itama ya zama sanadi a gareta. ALLAH yayma mama Maryam rasuwa sakamakon ɓatan bilkisun itama, wannan karon kam
Jawaad yaji zafi sosai na rasuwar kakarsa da ɓatan mamansa, yayi kuka har abin ba'a cewa
komai.
Ƙanwar bilkisu taso riƙon Jawaad ya dawo hannunta amma dangin mahaifinsa suma suka ƙi,
sai Abba Naseer babban yayansu Alhaji Abdull na farko a gaba ɗaya gidan ya amshe shi ya
koma hannunsa da zama.

*★★★★★★★*

Gata sosai Jawaad yake samu a wajen ahalinsa, dan a ganinsu lokacin da zasu nuna jin
daɗin ƙyautata musu da mahaifinsa yayi kenan, ɗan gatane ta kowanne fanni, riƙonsa ake
tamkar yana gaban iyayensa, ƙilama idan sune bazasu masa wani gatanba irin haka.
Kamar yanda marigayi Alhaji Abdul ya ajiye burinsa akan Jawaad na zama ɗan sanda sai
ALLAH ya amince masa yasamu cikar burinsa ta hanyar cusa son aikin ƴan sanda a zuciyar
Jawaad, sosai ya ke son aikin ɗan sanda, wannan shine burinsa, mafarkinsa, kuma fatansa.
Lokaci ƙanƙani ya samu cikar burinsa kodan tsatson da ya fito, da dattako irin na mahaifinsa da
baza'a taɓa mantawa ba.


*______________________________*

Shekaru sun shuɗa, komai ya sauya, Jawaad ya zama abinda yay fata, ya girma ya zama
babban mutum kamilallen saurayi mai aji da tarin cikar kamala da kwarjini na haƙiƙa, komansa
na nagartattun mutane ababen koyi da dubi, gaba ɗaya halayen mahaifinsa sun dawo jikinsa,
sam bashi da damuwa sai ta aikinsa tare da ƙyautatama jama'a. Mutum ne da bai damu da abinda bai shafesa ba ko ba'a sakashiba, abinda ke gabansa
kawai yakeyi, idan har bakai ne ka sakashi a lamuranka ba bazai taɓa shiga ba, bashi da son
hayaniya, bai da girman kai, bai da wulaƙanci, sanan sam ba miskili bane ba. Abu ɗayane yake
yawo a jinin Jawaad da ke saka jama'a dangantashi da waɗancan ɗabi'un na sama, shine
rashin sabo, sam baisan sabo ba, kana takashi zai shata maka dogon layi, tsautsayi ko rawar
kai ya saka ka ƙetara to lallai kun ƙulla kenan, kuma ka ɗaura kanka a danja mai haɗarin gaske.
Babu ruwansa da kai wanene? Ko kuma ina ka fito? Miye matsayinka a garesa duk ba'abin
kallonsa bane.
Jarumi ne ta fannin aiki da rayuwa, sannan gagararrene a duniyar tsagerun mutane, idan ya
ɓalle sam bai san bari ba, duk abinda ya saka a gabansa sai ya cimma manufarsa yake yankan
filin hutu.
Waɗannan ɗabi'un nasane suka jawo masa abokan tsama ta fannoni daban-daban, a cikin
hukumarsu da wajenta, harma da tsagerun gari.


★★★★

Shahuda ɗiya ce ga yayar marigayi Alhaji Abdull, wato Hajiya Humaira, tuni suna ƙasar
Holland ita da mijinta, yaransu biyar suma, mata uku maza biyu, asalin sunan Shahuda
*Sabeerah*, dan sunan mahaifiyar Abbansu aka saka mata, amma sai suke mata alkunya da
suna Shahuda, ita ce ƴa ta huɗu a gidansu, ƴan gatane na haƙiƙa, waɗanda suka tashi da
ɗabi'un turawa a cikin jininsu, sam basu san bari ba, dan bama a faɗa musu.
Hajiya Humaira tana son Jawaad, shiyyasa lokuta da dama take matsa masa zuwa ƙasar
Holland wajensu ya ɗan huta. To annan fa Shahuda ta ga Jawaad ta mutu a kansa, tun yana
basarwa dai har shima ya zurma,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login