Showing 9001 words to 12000 words out of 26395 words
Chapter 4 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf
Wannan shine dalilin
nutsuwarsu dan dole, kowacce ta shanye bala'in da kecin ƙahon zuciyarta zuwa maƙwallato
sukabi yarima akasha kiɗa dasu.
Bayan an ɗaura aure kai tsaye ɗaukar amarya maryam akai zuwa ƙauyensu Alhaji Yusif.
Duk da maryam a birni ta tashi taga iyayenta, annan aka haifeta har kawo girmanta, kusanma
dukkan danginsu anan suke, hakan baisa ta bijire akan bazata koma rayuwar aure a ƙauyeba,
sai tayi biyayya ga mahaifanta da kuma mijinta, ta zauna lafiya cikin ƙauyen tamkarma ta saba
da rayuwa a cikinsa da can, ta saki jikinta da kowa danginsa da jama'ar gari, sannan tanama
mijinta biyayya sau da ƙafa, ta tsaya tsayin daka wajen taimaka masa akan dukiyarsa da yake
kiwo a kanta.
Shekarar maryam ɗaya cif ta haife ɗanta namiji san kowa ƙin wanda ya rasa, bakin Alhaji
Yusif har kunne dan murna, sai kace yanzune akai masa haihuwar fari, ba komai ya girmama
murnar tasa ba sai biyayyar maryam a garesa da ƙyautata masan da takeyi, (kunsan zuciya
nason mai ƙyautata mata). Sosai maryam ke ganin gata fiye da ta farko a kan wannan haihuwa wajen dangin Alhaji
Yusif, dan kuwa hidima suketa mata da bajinta irinta mutanen karkara, tunda aka kawo maryam
garin matan Alhaji Yusif suka ɗauke ƙafa da ga zuwa garin, dama ƴaƴansu ba zuwa sukeba
sosai, amma wannan haihuwa yace musu tilasne su halarci taron suna daga su har yaransu.
Badan sunso ba suka shirya ana gobe suna suka nufi ƙauye, kai tsaye kowacce gidansu ta nufa
maimakon gidan mai jego, hakama yaran babu wanda ya nemi inda take, dan duk haushinta
sukeji, musamman ma ƙawayenta su Atika.
Itama dukda taji sunzo sai bata kulaba, dan danginta da suka cika gidan sun share mata
dukkan kukanta, ga kulawa ta dangin miji da jama'ar gari.
Washe gari yaro yaci suna Abdul-Aziz. Yanda hidimar suna ta gudana ma ɓata lokacine,
amma Alhmdllh komai ya tafi cikin tsari, matan Alhaji Yusif basu shigo gidan sunanba sai da
dare, koda sukazo sama-sama suka gaisa da dangin maryam suka ɗauki jariri suka ƙara gaba
bayan sun ajiye kayan da suka kawo. ALLAH sarki maryam ita kunyarsu ma taji sosai, domin dai kallon iyayenta take musu, gashi
yanzu ta aure musu miji harda rabon ɗa tsakani, ta baza ido taga ƙawayenta su Atika sun shigo
amma sai taji tsitt, bayan kuma ance dukansu sukazo, dama bata saka ran ganin su Yaya
Naseer da sauransu ba, tunda su mazane. Bayan suna kowa ya kama gabansa, Maryam ta cigaba da rainon ɗanta Abdul-Aziz da
kulawa da mijinta.
Rayuwa ta shuɗa, dan har maryam ta yaye Abdul-aziz, gashi yana tafiyarsa ko ina ga
surutu ko akku ta shafa masa lafiya, yaron akwai wayo na haƙiƙa, gashi kullum yana cikin yara
idonsa na sake buɗewa.
A hankali duk wasu wahalhalu da yaran ƙauyen keyi Maryam bata hana Abdul-Aziz shigaba,
kiwon dabbobin babansa ma shine ya koma bin yara daji yi, ko yabi zugar yara yo ciyawa, shine
zuwa gona shuka ko kwaso amfani da kaka, yana girma wahalhalu na sake hawa kansa, gashi
yanata zuwa makaranta anan cikin ƙauyen, dan da farko Alhaji Yusif yayi niyyar maida
Abdul-Aziz birni ya samu ilimi tamkar ƴan uwansa amma sai Maryam ta hana, cikin hikima ta
nuna masa ta fison Abdul ya tashi cikin wahalhalu irinna ƙauyen, hakan zai taimakawa
rayuwarsa ta gobe harma wani ya amfani jibinsa. Badan ya soba ya barsa, itako ta cigaba da
sakashi duk abinda ya dace, lokacin da Abdull yakai shekara goma sha biyar tsaf zai ja maka
kunyar gona sama da ashirin a nome, faskare wannan yinsa yake, ragamar kiwon dabbobin
gidan kam ya koma hannunsa baki ɗaya, duk safiya da an fito sallar asubahi yana makarantar
allo, zuwa takwas suke tashi sai yazo yay shirin makarantar boko ya tafi, yana tasowa abinci
kawai yakeci ya ɗebo ruwa ya zuzzuba a gidan ya ɓalle dabbobin gidan ya tafi jeji kiwo, bazai
dawoba sai gab da magriba, da yayi wanka zaije sallah shi da babansa idan yana gari, idan
yana birni wajen sauran matansa zaije shi kaɗai, baya dawowa sai tara da rabi, dan ana gama
sallar isha'i yake wucewa makarantar allo again.
Sai rayuwar Abdul-Aziz tazam sam babu hutu, har wasu na ganin maryam ta cika tsauri aka
sa, gashi shi kaɗai ALLAH ya azurtata da samu, tun bayan haihuwarsa bata sake koda ɓari ba,
baza'a ce bata damuba kam, amma ta danne ta cigaba da harkokinta hankali kwance, tasan dai
haihuwa ta ALLAH ce, kuma shine ke badawa ga wanda yaso a lokacin da yaso, guda
ɗayanma ta godama ALLAH, fatanta ALLAH ya rayasa ya zama amfananne ga al'ummar
musulmai da addinin musulinci.
Rayuwa haka ta cigaba da shillawa, Abdul-Aziz shine autan gidansu, dan suma matansa na
birni babu wadda ta sake haihuwa, abinda zai birgeka shine zuwa wannan lokacin kuma duk
sun saki jiki da maryam, komai ya wuce, yaransu kan ɗanje hutu wani lokacin wajenta, itama
Abdul kanje wajensu dukda dai baya jimawa sabida ya saba da ayyukansa anan ƙauye,
acewarsa canko sai dai aita yawon banza da barci da kallo bayan anci an ƙoshi, shiko sam
bazai iya rayuwar lalaci ba.
Sauran ƴan uwansa sukan masa kallon mahaukacin da baisan ciwon kansa ba, shiko ko a
kwalar rigarsa, har zuciyarsa yake faɗar abinda ke ransa ne.
Yayunsa mata kusan duk sunyi aure, mazanne dai babu wanda ya yunƙuro har yanzu, dukda
kuwa a cikinsu akwai waɗanda suka isa auren.
Lokacin da Abdul ya kammala secondary ne wasu a cikin yayunsa sukai aure, shiko Alhaji
Yusif yay masa zancen dawowa birni dole saboda cigaba da karatu, sam bayason dawowar,
idan ta shine abarsa yayta harkar nomansa da kiwo yafi birgesa, secondary ɗinma da yaya ya
gamata, gashi yanzu ne mahaifinsu yafi bukatarsa saboda kulawa da harkokinsa na kiwo da
noma, dan ƙarfinsa ya fara karewa girma ya fara kamashi, gashi sauran yayyen Abdul babu mai
son zuwa ƙauyenma bare su taimaka masa, su kawai boko suka saka gaba da burin samun
daula ta birgewa suci duniyarsu da allura, kasancewar mahaifinsu manomi makiyayi ma takaici
yake basu, a ganinsu ajinsu ya wuce ubansu ya ƙare a harkar noma da kiwo, bayan kuma da
itace duk suka samu tallafin karatun nasu.
Sosai Abdull ke lallaɓa babansa akan baison zuwa makaranta, amma sam yaƙi saurarensa,
yace dolene shima ya fita haƙƙinsa akan karatu tamkar sauran ƴan uwansa.
Babu yanda Abdul ya iya dole yay biyayya, amma koda yatashi karatun sai ya karanci fanin
kiwo da noma, dan aganinsa yafi fahimtarnan ɗin.
Ƴan uwansa dariya abun yayta basu, dan aganinsa abunfa na haukar Abdull ya fara wuce
makaɗi da rawa, yaro kamar tsatson ƴan rawar banjo. Sam baya kula zancensu, abinda yasa a
gaba yakeyi, ga ƙwarin gwiwa yana sake samu da ga mahaifiyarsa da babansa.
Kammala karatun Abdull babu jimawa ALLAH ya ɗauke Alhaji Yusif a duniya, wannan
mutuwa ta girgiza dukkan ahalinsa musamman maryam da Abdull, abin ya taɓasu masuƙa,
ansha ruguntsumi da tashin hankali har komai ya lafa zukata suka dawo hankalinsu bayan
haƙuri da dangana da ya riskesu bisa rahamar UBANGIJI. Ranar da akai addu'ar arba'in a ranar aka ɗakko zancen raba gado, babu wanda yay
jayayya wajen amincewa akai rabo, ita dai maryam bata da abin faɗa, dan ɗaya tilo ne gareta,
ita babban tashin hankakinta ma ta yadda zata bar ƙauyen, dan tasan tilas zamanta ya ƙare
kenan, gashi ta saba da kowa da komai na yankin. Ilai kuwa hakance ta faru, dan a yanda rabon gadon yazoma sai da gidan sukayi, dukda
Abdul yace abasa zai saya da ɗan kuɗinsa kakarsa ta wajen uwa mahaifiyar maryam sukace
zasu cika masa kuɗin, amma tsabar mugunta aka hanasu saya, maryam da ta lura zamansune
ba'a sonyi saita lallaɓa Abdull akan yayi hakuri yabar zancen, duk inda ALLAH ya sake ƙaddara
zamansu suyi haƙuri su karɓa kawai.
Da wannan nasihar taci ƙarfinsa yayi biyayya, angama raba gado tsaf, ɗan filin gonar da
Abdull ya samu ma bawata mai yawa bace, dan haka yay zuciya ya saida tasa, cikin yayyun
nasa da aka haɗasu ya saye suna masa dariya akan ya gama wahala amma ya tashi babu
tsuntsu babu tarko. Abdul ma yanada haƙuri, amma lallai akwai zuciyar masifa idan aka kai haƙurinsa tunga,
wannan kalmomi da aka jefesa da sune suka bashi ƙwarin gwiwar mikewa da ƙafafunsa ya
shiga fafutukar neman na kansa, yayinda maryam ta koma gidansu ta cigaba da rayuwarta,
dukda kuwa ana takura mata da batun tayi aure tunda bata wuce yinsa ba.
Abdul ya zage damtse wajen neman halalinsa, ya manta ma da wasu takardun kwalin
shaidar gama karatu, kai gaba ɗaya yama manta kansa matsayin ɗan boko, dukda kuwa ga
yayyensa sunaci da biro cikin sauƙi, 100% kuma shima ya goyi bayan mahaifiyarsa akan tayi
aure, dan shine mutuncinta. Maryam bata musaba tai aure anan ma cikin anguwar kusa da gidansu, ta auri wani
bawan ALLAH da matarsa ta rasu ta bar masa ƴaƴa har huɗu duk mata.
Mama maryam mace ce da ta san kanta, ta kuma yarda ɗa na kowane, dan haka ta
rungumi yaran a jikinta tamkar nata, ta kuma tsaya tsayin daka akan tarbiyyarsu musamman
babbar da ta zama budurwa. Wannan dalilinne ya jefa ƙaunarta mai tsanani a zukatan yaran da
mahaifinsu, harma da danginsa da na mahaifiyarsu. Shima sai ya sake jan Abdull a jikinsa
tamkar shine ya haifesa, ya kuma sake nuna masa hanyoyin neman na kai masu sauƙi, dan shi
ɗan kasuwane.
A cikin amincewar UBANGIJI sai ƙauna mai ƙarfi ta shiga tsakanin Bilkisu ɗiyar mijin mama
maryam da Abdul-Azez, duk da babu burin aure kusa a ransa sai gashi ta canja masa dukkan
tunani da tsarinsa, ya rikice ya fara kafa manufofinsa a gareta, koda mahaifinta ya fahimta sai
yayta murna, dan shikam dama halayyar Abdul na matuƙar birgesa, hakama mama maryam taji
daɗi sosai, ga yaran akwai tarbiyya dama, sannan gasu ainahin ƙyawawa abin son kowa.
Abdul sam bai ɗakko maganar auren bilkisu ba sai da yasamu ɗan abin dogara wajen
riƙeta, dan shima dai kudin farko da ALLAH ya albarkacesa dasu a kasuwa saiya koma
ƙauyensu ya sai gona ya tsunduma harkar noma tamkar mahaifinsa, ga kuma ɗan kasuwanci
yanayi na sai da dabbobi da abincinsu anan cikin binni, ganin yanada abinda zai riƙeta
gwargwadon iko sai kawai aka saka biki, haya ya kama na ɗakuna biyu a wani gida, su biyune
kawai suke haya a gidan, dan haka komai sai ya zam musu da sauƙi, dan matan nasu duk
masu hankaline, babu mai rawar kai aciki.
A Ɓangaren ƴan uwansa kuwa kowanne yana fantamawa rayuwa, dan mafi yawansu duk da
biro sukeci, matan kam ba laifi suna auren masu hali, arziƙin ƴan uwansa bai taɓa kwaɗarsa ba
balle ya zame masa abin rikewa wajen yimusu hassada, harkar gabansa yake da iya
gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa, bai dogara su bashiba, bai kuma zauna damuwa da
sunfishi ba. Suko kullum cikin kallonsa mafi ƙasƙanci a cikinsu sukeyi, suna ganin ya tashi a
ƙauye, sun fishi karatun boko, sun fishi komai na rayuwa, ko tarkacen kwancen kayansu ko
wani abu suka tashi saisu bashi, shiko ya amsa cikin murna da girmamawa, bai taɓaji a ransa
dan ƙaskanci sukai masa ba, yasa a ransa da yarda sun fisa ɗin da gaske.
ALLAH mai alkairi, harkar nomansa nata bunƙasa, hakama sana'ar saida dabbobi da
abincinsu, har lokacin bilkisu bata taɓa koda ɓatan wata ba, sai da suka shekara huɗu da aure
ALLAH ya bata ciki, zo kaga murna wajen Mama Maryam da shi kansa uban gayyar da ƴan
uwan bilkisu, ciki na kai wata baƙwai haihuwa tazo mata, aiko tasha wahala kafin ta haifi
bakwaini biyu tagwaye, ɗaya ma baizo da raiba.
Sun karɓa hannu biyu kuma sunyi murna da jin tausayin kansu na rasa ɗayan, sai dai kuma
hukuncin ALLAH shima ɗayan bai kai labariba ya koma.
Tun da ga nan Bilkisu bata ma sake samun cikiba tsawon lokaci.
*Komai na da sanadi*.
Wannan magana haka take, dan kuwa sanadin dam da akajema ƙauyen su Abdul ne ya
zamar masa wani gagarumin alkairi, gonarsa ta kasance ɗaya da ga cikin gonakin da dam ɗin
zai cinye, hakan yasa aka biyasu makudan kuɗaɗe gwamnati ta saya, shi kuma Abdul yana da
ilimi, sai yazama shine ya tsayama jama'ar ƙauyen da duk abinda ya shafa har sai da aka
biyasa haƙƙinsa, ya kuma basu shawarwarin su sake sayen wasu gonakin dan ga damar yin
noman rani ya sake samuwa, ɗari bisa ɗari suka amince da shawararsa da ga manyansu har
matasansu.
Turawan da sukazo wannan aiki sai al'amuran Abdul-aziz suka matukar birgesu, hakan yasa
suka jashi jikinsu ya zama abokin hirarsu duk da kuwa ba ko yausheba, dan shima yanada
harkokinsa da yakeyi.
Turawan ba cikin ƙauyen suke kwana ba, zuwa yamma suke tashi su koma cikin birni inda
suke da masauki, hakan yasa suka sake jan ra'ayin Abdull har yasan mazauninsu, suma kuma
sukasan nasa.
Kafin kace mi shaƙuwa ta shiga tsakaninsu sosai, halayensa na neman nakai da dattako na
sake birgesu, gashi dai ba wani babba ba can amma akwai halayyar manya, kafin su kammala
aikin ƙaton dam ɗinnan da ko Abdul baisan iyakarsa ba shakuwarsu ta wuce misali, dan har
bilkisu ya kaimasu suka gaisa, sannan wani lokacin yakan sakata tayi abinci ya kai misu,
acewarsu suna koyon cin abincin arewacin Najeriya.
Bayan kammala aikin nasune sukai haramar komawa, dukansu sun fuskanci halin kewa na
tsantsar sabo, sai kowanne ya tsinci kansa a damuwa, lokacin da zasu tafi suka damƙa gidansu
kacokan ga Abdull ƙyautar ALLAH, dama saya sukai dansu zauna harsu gama aikinsu, ganin
sun kammala kuma sai suka bashi da zasu tafi, rasama mizai faɗa musu yayi dan susan yaji
daɗi, dan gidane mai azabar ƙyau da tsari, kowa yasan dai yanda turawa suka amince da
gyaran muhalli, to shima wannan ya ɗauki tsari na musamman, gashi a anguwar manyan
mutane.
Duk sai da ya ɗauki ƴan uwansa ya kaisu suka sanya albarka da matan babansa, hakama
dangin mahaifinsa dake ƙauye, mota biyu suka ciko sukazo suka tayasa murna. Sannan ya
maida iyalansa can, harda mama maryam yaso amma mijinta da ita kanta suka ƙi, aganinsu
yaya zasuje suyima ƴaƴansu zaune dukda dai gidan babbane. Dole Abdul ya haƙura amma ya
ɗauke ƙannen Bilkisu biyu da suka rage ya maida gabansu, dan ɗaya a cikinsu itama tayi aure.
Shekara ɗaya kacal da faruwar hakan saiga turawannan sun dawo Najeriya, ashe zuwa
sukai tafiya da Abdull, dan su dai yamusu har ƙasan zuciya, bayan ɗan kace nace da aka samu
akan tafiyar tasa dai da ga karshe ALLAH ya amince su mama maryam suka barshi ya bi
turawannan, sai dai yabar matarsa a nan gida Nageriya. Wannan tafiya itace ta sake canja komai da ga rayuwar Abdul-Aziz Yusif Tafida, cikin
ƙankanin lokaci ya bunƙasa, dan kuwa acan ƙasar turawannan ashe sun jashine akan harkar
noma da kiwo irin nasu, suka sake wayar masa da kai, shima ya sake wayar musu da kai akan
nasa sanin da ALLAH yay masa, dama su kunsan komansu da tsari, tamkar kamfani nasu yake,
sai suka dirasa matsayin babba mai kula da komai, a duk bayan wata uku yake zuwa gida
Nageriya yay wata guda ya koma can ƙasar, sannan anan Najeriya ma ya kafa jijiyoyi
musamman a ƙauyensu, dan kuwa ya tallafa ma matasan ƙauyen da magidanta akan noman da
kiwo, harma ya kwashi wasu acikin matasan suma sunacan turai ɗin tare dashi.
Rayuwa ta matukar sauyawa, duniya ta bama Abdul-Aziz babban filin fantamawa a cikinta,
abin birgewa kuma yana amfani da damarsa sosai wajen gina kowansa, tamkar ƴan uwansa da
abaya suke ganin sun fisa yanzu ya zamar musu runfa, dan kuwa dukkan dukiyarsa da ke
Najeriya su ya ɗaura akanta, dukkan sirrinsa sun sanshi, duk abinda kaga bai sanar musuba to
lallai sai dai sirrin da ya shafi matarsa ko mahaifiyarsa, wannan kam da ga shi sai su sai
ALLAH, har zuwa yanzu kuma basu haihuba, kuma bai taɓa yunƙurin sake aure ba, hakama
babu wanda yace masa ya sake auren ko za'a dace. Yana son matarsa sosai, dan haka bai
taɓa nuna mata ya damu da rashin samun ƴayansu ba dukda yana kwaɗayin son ganin
tsatsonsa a duniya.
Ba a cikin ahalinsa kawai yake taimako ba, hatta