Showing 21001 words to 24000 words out of 26395 words
Chapter 8 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf
na cire Uniform ɗina naje naɗan
watsa ruwa, bayan na dawone na iske Firdausi ta ajiye mana abinci.
Munacin abinci inna na zaune gefe tana ƙullin kayan sana'arta, Firdausi ta haɗiye abincin
bakinta tana faɗin, “Bilki akwaifa matsala”.
“Tsayawa nai da ga ƙokarin kai abincin bakina ina kallota a tsorace”.
Inna ta harari Firdausi tana faɗin, “K Firdausi bana son ƙirƙire-ƙirkire fa, ya zaki ɓata mata
zuciya? Wannan ai shirmene”.
“Kiyi haƙuri inna” Firdausi ta faɗa a sanyaye.
Kallon Inna nayi nima a raunane, “Inna dan ALLAH karki hana ta sanarmin, da inji a wani
waje ai gara naji daga gareku, dama tunda na shigo naga matan gidannan namin wani kallon
ƙurullah daya tsoratani”.
Murmushin takaici Inna tayi tana girgiza kanta, “Suma son zuciyane ke ɗawainiya dasu, dan
abinda ya shafi kowane a gidane ai”.
“Dan ALLAH Inna miya faru?”.
“Karki tada hankalinki Bilkisu, baƙon gidanmu ne ya tara taro ɗazun bayan fitarki
makaranta, ya kafa sharuɗa ne a gidan, wai bayason hayaniya, sannan kafin ya tashi barci a
share tsakar gidannan a wanke tare da bayi, lokacin da zai fito kuma karyaga kowa sai.......”
Tai shiru cikin haɗiye wani takaici daya zame mata ƙululu a maƙoshi.
Cikin ƙaguwa da tsorata nace, “Inna sai me?”
Shiru tai ta kasa bani amsa, sai Firdausi dake sharar hawaye tace, “Wai sai mu ƴammatan
gidan kawai, kece zaki ringa masa gyaran ɗaki, ni kuma kai masa ruwan wanka, su Aina'u ma
kowa da aikinta, kinsan miya bani takaici Bilkisu?”.
Kaina na girgiza mata saboda hawayen da suka fara gudu a kumatuna. Ta goge nata itama
tana cigaba da faɗin, “Bayan wannan dokokin harda sharaɗi mai barazana ga duk wanda yace
zai bar gidannan ko zai sanarma hukuma, wai amma dukda wannan ruɗanin sai su Zee ke
murna, harma suna ƙokarin yin kwarkwasa a gabansa”.
Kasa cewa komai nayi, sai tsame hannuna danai daga abincin da mukeci na koma gefe,
hakama Inna da Firdausi kowa yay shiru yana cuɗawa da kwance abinda yakeji a ransa.
★★★★★★★
Kamar yanda Jazuga ya kafa dokoki a gidanmu haka kowa ke bi, ba komaine yasa
hakanba sai tsoro, dan ba gidanmune kawai ke tsoron Jazuga ba, gaba ɗaya layinmu a tsorace
suke dashi da yaransa, babu wani mai sukuni, dan yaran Jazuga sun addabi kowa a anguwar,
gashi sai ƙara jan yara matasa ya keyi masu rauni cikin tawagarsa. Abinda zai baka mamaki Police kansu tsoron shigowa anguwarmu sukeyi, ballema muyi
tunanin zasu iya kamashi ko ƙwatar mana ƴanci daga mulkin mallakarsa.
Tun ina damuwa da bautar gyaran ɗakinsa har abin ya zame min jiki, ƙa'ida kullum sai na
gyara sau uku, safe, rana, yamma.
Abinda kawai ke damun rayuwata dashi shine kallo, duk motsina a gidan idonsa na kaina
inhar yana gida, duk da kuwa a koyaushe cikin Hijjab muke ni da Firdausi inhar zamu fito tsakar
gida.
A cikin ƴammatan gidanmu kuwa wasu sai dai addu'a, dan kuwa sosai ake zargin Jazuga na
lalata dasu yana basu kuɗi, hakanne ke ƙara tada hankalin iyayenmu.
Muna cikin wannan halin ne kuma saiga ɗan uwansu Firdausi wanda yake matsayin zaɓin
iyayenta yazo daga can asalin garin su Firdausin, canjin daya tarar a gidanmu ne ya tayar masa
da hankali, dan haka ya roƙi baba akan kawai a saka musu ranar aure.
Na taya Firdausi murna, sannan na taya kaina kuka, dan kuwa koba komai itakam ALLAH
ya tsameta, niko da ko saurayi ban taɓa yibafa? Kunsan samarinma sunfi son ƴammatan masu
ƙyale-ƙyale, niko bani cikin jerin masu shi, wadda suturar sakawa bata wadaceta ba ina taga
kayan ƙyale-ƙyalen burge saurayi. Saurayin Firdausi bai bar garinba sai da aka tsaida maganar aurensa da Firdausi wata
biyu kacal..
Rayuwa a gidanmu ta cigaba da tafiya a ƙuntace, komai yabar mana daɗi saboda su
Jazuuga, abu mafi ɗagamin hankali shine saka idonsa a kaina fiye da kowa a gidan, wani salon
iskancima da ya ɓullo dashi shine danaje gyara masa ɗaki shima zai shigo ya zauna yana
kallona kamar wata tv, narasa miyake kallo tare dani, ni dai sam baza'a sakani a jerin ƙyawawa
ba, dan kuwa baƙace ni, bani da dogon hanci, bani da kayan ƙawa na ado da zasu fidda ƙyauna
ga kowa. Shiyyasa lamarinsa ke ban mamaki da al'ajabi.
Babban abinda na riƙe shine addu'a, dan itace babban makamina a gareshi.
Yauma kamar kullum na tashi da wuri saboda zanje makaranta, dukkan abinda ya dace muyi
ni da firdausi munyisa, hatta da aikinta da Jazuuga ya bata nakan tayata, saboda ni nawa saiya
tashi barcinsa na ƙaddara da ko sallar asubahi bana tunanin yanayi.
Shirin makaranta nayi, na dawo ƙofar ɗakinmu na zauna tamkar yanda sauran ƴanmata
gidan suka fito, wasu sunci kwalliyarsu saikace wasu matansa, sai binmu da kallon banza suke,
dan a ganinsu bamukai matsayin haɗa kafaɗa dasuba.
Sukan bani dariya da mamaki, dan inda son samunanema wlhy ni namu aikinma duk ya
haɗa ya basu.
Banfi mintuna goma da zamaba sai gashi ya fito, kamar yanda ya saba da ga shi sai
gajeren wando, kallo ɗaya nai masa na duƙar da kaina.
Shiko inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina tamkar kullum.
Hazbilannahu wa ni'imalwakil na shiga ambatowa a kan laɓana, kamar yanda na fahimta a
duk sanda nake karantata ko kallona yake saiya kauda idonsa sai naga yanzu ma yazo ta
gabana ya gitta.
Inajin yanda su Aina ke masa gaisuwa cike da kwarkwasa da salo, tausayinsu ya kamani,
dan kuwa ni nafi ɗaukarsu a jerin masu karancin tunani, da wannan takaicin na miƙe na nufi
ɗakinsa, kamar yanda na saba a gaggauce na shiga gyarawa, dukda nasan bazai shigoba sai
yay wanka, kafin lokacin kuma insha ALLAHU na gama nama fice abina zuwa majaranta.
Abinda na gani a ɗakin yauma ya tayarmin da hankali, dan haka na fice jiki na rawa ko
shara banyiba, saboda tsantsar tsoro da firgici dake sake tasirantuwa a gareni game da
tsagerancin Jazuga.
Ranarma dai ko'a makaranta daka ganni kasan babu nutsuwa a tare dani, haka dai aka tashi
na nufo gida, ashe nabar baya da ƙura akan rashin shara da banma Jazuga ba.......
*____________________________________*
*_JAWAAD_*
*____________________________________*
Izinin shigowa aka bashi, ya turo ƙofar ya shigo, cikin risinawa irin ta girmamawa yake
faɗin, “Sir! Ƴan jaridar nanne suka sake dawowa”.
Shiru Sir Ahmad barewa yay yana kallonsa na tsawon sakwanni, kafin ya sauke numfashi
da masa alamar yaje.
Bayan fitarsa ya maida kallonsa ga Jawaad dake kallonsu ba tare da ya fahimci komai ba.
“Jay! Rayuwa na bani mamaki, bansan miyasa a duk lokacin da case irin wannan yazo ba
hankalin duniya yafi tashi akansa, shiyyasa talakawa har abadan bazasu daina ƙalubalantar
manyan ƙasa ba komai gaskiyarsu”.
Murmushi Jawaad yayi irin na takaici, yaɗan lumshe ido yana faɗin, “Kuskuren daga mu
yake Sir”.
“Jay miyasa kace haka?”.
Murmushi ya sakeyi mai ciwo, “Abun a bayyane yake muma mun sani sir, mubar wannan
maganar kawai bata da muhimmanci a yanzu”.
Kai Sir Ahmad ya jinjina kawai yana cije baki, sai dai acan ƙasan ransa maganar Jawaad tai
mugun sukarsa, ba komai ya sa hakanba sai sanin tsantsar gaskiyar Jawaad, amma wasu
dalilai bazasu bar muryoyinsu ɗaguwa ba har suyi kururuwar da duniya zataji, ta gaskatasu
cikin jerin jami'an tsaro masu gaskiya da son shinfiɗata.. Ya sauke numfashi mai zafi yana maida hankalinsa ga Jawaad, “Jay waɗanan ƴan jaridane,
tun safe suke jera mana kira domin sonjin mi'ake ciki, inaga yakamata kaje garesu”.
“Okey Sir”
Jawaad ya faɗa yana miƙewa, gaba ɗaya fuskarsa ta canja launi, sam babu ɗigon fara'a ko
sauƙi a cikinta, sai tsumamman fushi mai gauraye da takaici irin mai zafafa zuciya.
Harya fice Sir Ahmad na binsa da kallo, yana ƙaunar yaron saboda nagartarsa, duk da
mahaifinsa yay suna irin na zama wani shi sam baya alfahari da hakan, ko yaushe tunaninsa
akan talaka yake, da ace yanda Jawaad keda zinariyar zuciya haka sauran jami'an tsaro suke
da tuni ƙasar ta canja daga yanda take yanzu.
Koda Jawaad ya fito sai ya samu Qaseem tare da ƴan Jarida, kallon ido cikin ido
sukaima juna. Jawaad ya janye nasa yana sakin wani lallausan murmushin daya soki zuciyar
Qaseem.
Office yay wucewarsa, ransa na susa akan shirmen Qaseem, baisan miyasa sam
jininsu bai haɗuba.
Cikin kujera ya shige yana mai lumshe idanu da faɗawa duniyar dogon tunani.
Damuwa tai masa ɗaurin gori, saboda sabgogin aiki, ga matsalar gida na halayyar matarsa
da taƙi ta zama irin kowacce mace, waje zafi, gidansa ƙunci, babu uwa ko uba da zasu fuskanci
matsalarsa kai tsaye balle su taimakesa koda da shawarane.
Ina zaiga mahaifiyarsa? Shin tana raye ne kokuwa shiɗin marayane gaba ɗayansa? Wasu
hawaye masu ɗumi suka gangaro a kumatunsa, bai damu daya sharesuba, haka ya barsu suna
kwarara. (Haka yake dama, aduk lokacin daya tuno iyayensa yakanyi kukansa ya ƙoshi).
Ya rabbi ka gafartama iyayenmu baki ɗaya.
Sai da yasha kukansa ya more sannan ya share hawayensa.
Nutsuwa yay ta musamman domin yin nazari akan wannan case da aka damƙa a
hannunsa, dolene idan yanason aikinsa ya tafi dai-dai sai ya nemo abokansa, aminansa sun
dawo kusa dashi, kuma insha ALLAH zaiyi komai da kula yanda bazai ƙara bada wata ƙofa da
za'a farraƙasu ba koda na a awoyine. Bai ɓata lokaci ba a take ya rubuta takardar neman izini tare da shawarar da yay alƙawarin
badawa kamar yanda sukai da Sir Ahmad...............✍
https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q
*MANHA HAUSA NOVEL'S* takuce, maza garzaya domin bada gudunmawarka, danna
Subscribing domin nuna ƙaunarka garemu, kuyi shiri na musamman domin samun daɗaɗan
shirye-shiryenmu tare da nagartattun labaran novel's masu daɗi da ma'ana nan da lokaci
ƙanƙani, MANHA HAUSA NOVEL'S ta shirya tsaf domin baku farin ciki insha ALLAHU, ku
garzaya kada ƙuda ya rigaku, Bilynku ma har taje tayi subscribing tun farar safiya, goyon
bayanku shine ƙwarin gwiwarmu.
MANHA HAUSA NOVEL'S
(Ƙyautar ALLAH).
Ku isa da hanzari domin samun ƙyautar kuma, dan ALLAH a danna subscribing.
Ga link ɗin can a sama
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_**_Typing_*
*_ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*
*_Bilyn Abdull ce_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull_
*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na tara_
*______________________________________*
............Tun ƙarfe huɗu na maraice garin ya fara haɗa gagarumin hadari, wanda alamominsa
suke nuna zai zubda ruwa mai yawa.
Duk da yana a office hakan bai hanashi fahimtar canjin da garin ke cikiba, miƙewa yay
zuwa jikin window ɗin Office ɗin ya leƙa, tabbas hadarine mai ɗauke da alamomin iska kuma, ya
kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana huro iska a bakinsa, yana da sauran ayyuka,
gashi bayason ruwannan ya samesa a waje.
Barin Window ɗin yayi ya koma gaban desk ɗinsa, wasu takardu ya haɗa waje ɗaya kafin ya
fito da ga office da hanzarinsa irinna masu cikakkiyar lafiya.
Kai tsaye Office ɗin Sir Ahmad ya nufa, dan tun kusan mintuna goma baya ya aiko
kiransa, bai fita bane saboda wani ɗan aiki da ya sakashi yakeson ƙarasawa ya kai masa gaba
ɗaya.
Sallama yay a ƙofar Office ɗin kafin ya shiga, su uku ya iske a office ɗin, gaba ɗayansu
kuma suna cikin manya-manyan ƴan sanda, gaisuwa yay irinta girmamawa a garesu, ya
miƙama Sir Ahmad takardun yana faɗin, “Sir gasu na kammala, kayi haƙuri da lattin da nayi, na
ƙarasa aikinne”. “Babu damuwa Jay, dama tunanina ya bani hakan shiyyasa ban damuba, duk da kuwa
jiranka muke”.
“Sorry Sir's” Jawaad ya faɗa yana maida kallonsa ga sauran mutane biyun dake zaune .
Ɗaya a cikinsu ne yay magana fuskarsa sam babu walwala, cikin tsare Jawaad da idanu
yace, “Jawaad Abdul-aziz ko?”.
Cikin girmamawa Jawaad yace, “Yes Sir!”
Zama wancan ya gyara sosai yana fuskantar Jawaad, ya fara magana cikin dakiya da
kuma tsuke fuska.
“Jawaad kai ɗan sandane, ɗan sandanma (SAS) ƙwazonka da ƙwarewar aiki ke ƙara
maka ɗaukaka ga kowa dake a cikin hukumarnan, kamar yanda muka baka yarda a baya
yanzunma munason ƙara baka a kan wannan aikin, dan tabbas inaji a jikina zaka iya, saboda
kanada NAGARTA irin ta jami'an tsaro na ƙwarai, bamason wannan case ɗin ya wuce sati biyu,
ya kake ganin zaka iya kuwa?”.
Jawaad dake tsaye a tsume fuska sam babu fara'a yay ajiyar zuciya yana sake tsuke
fuskarsa, “Sir insha ALLAHU ina fatan hakan, sai dai bazan zama mai alƙawari akan abinda
bani da ilimin sanin gaibu a kansa ba, ina dai muku albishir da koda ƙasa da kwanakin da aka
banine zan iya yin hakan, alfarma ɗaya zuwa biyu nake nema a gareku, dan hakanne zai bani
ƙwarin gwiwa akan nasarar da kuke fata daga gareni...”
“Wace alfarma ce wannan?”.
Ɗayan a cikin baƙin yay tambaya yana kallon Jawaad.
Gyara tsaiwa Jawaad yayi yana satar kallon Sir Ahmad, Sir Ahmad da shima ke kallonsa
ya jinjina masa kai alamar ya faɗa.
Kai Jawaad yaɗan ɗaga masa, kafin ya maida hankalinsa sosai garesu yana cigaba da
faɗin, “Alfarma ta farko itace inason a dawomin da abokan aikina tare dani, ina magana ne
akan, Hafeez Umar, Aliyu S marwa and Jabeer Abdul-razaƙ. sai alfarma ta biyu kuma kununa
ma abokan aikina cewar kun cireni da ga wannan case ɗin, a ɗora Qaseem Ali matsayin jagora,
nikuma zanyi nawa aikin ne ta ƙarkashin ƙasa tare da abokan aikina ba tare da kowa yasan
muna tareba”.
Shirun da yayne ya basu damar fahimtar ya kammala magana, hakan yasa su duka suka
sake zuba masa ido tamkar wani baƙonsu, kusan minti ɗaya da rabi kafin ɗaya a cikinsu ya
miƙe, kafaɗar Jay ya dafa yana murmushi da fadin, “Jawaad tunaninka mai ƙyaune, kuma
hakan yamin ɗari bisa ɗari, abu ɗaya nake tsoro da shakku akan dukkan bayananka”. Cikin izza da jin yakai jarumin na gaske ya ɗago kai yana kallon boss ɗin nasa, sai kuma
ya sake wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa duka biyu loɓawa, “Sir! Miyasa kakejin
shakku?”.
“Gudun rashin samun nasara, ina gudun yazam ba'ai nasaraba akan tsarinka Jawaad, dan
rashin nasara a aikinnan tamkar zubewar mutuncinmu ne, samun nasara kuwa kimace a
garemu, sannan kowannenmu kuwa ribace a gareshi, kuɗi zasu jiƙamu, sannan zamu ƙara
nagarta a idon duniya harma da shugaban ƙasa”. “Hummm” Jawaad ya faɗa a can ƙasan maƙoshi, kafin ya kallesu gaba ɗaya cikin takaici,
“Insha ALLAHU zamuyi nasara, domin inaji a raina da NASARA AKE FARAUTO NASARORI a
rayuwa, insha ALLAHU a karon farko da nake hangen samun damar farko zan sadaukar, badan
komaiba sai dan farauto nasara ta gaske, abinda kawai nake buƙata a gareku goyon baya”.