Showing 3001 words to 6000 words out of 26395 words
Chapter 2 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf
niyyar tashi ma.
Kusan mintuna arba'in da shigarsa bayin sai gashi ya fito ɗaure da tawul ruwan sararin
samaniya, yayinda ya rataya ƙarami fari a wuyansa, ya kama can ƙarshen tawul ɗin yana goge
gefen kumatunsa.
Shahuda da har yanzu take kwanci ta a hankali ta buɗe ƙyawawan idanunta ta sauke
akansa, hakan yayi dai-dai da kai nasa duban gareta shima. Kuma tamke fuska yay yana kauda
idonsa a kanta tare da nufar mirror kansa tsaye. Kamar yanda baiyi magana ba itama sai bata
ce uffanba sai binsa da kallo da takeyi. Duk da Jawaad naji a jikinsa kallonsa takeyi bai juyoba, amma yana kallonta ta cikin mirror,
murya can ƙasan maƙoshi yace, “Kinyi salla?”.
Ɓata fuska tayi tana kuma narketa alamar son yin shagwaɓa, “Haba bb, kamun laifi
maimakon ka lallasheni da ban haƙuri saika wani faramin tambaya”.
Duk da ya jita sarai sai ya share tamkar bai jiba, ya cigaba da shafa mansa yana lullumshe
ido saboda ciwon da har yanzu ya keyi, sauƙinsa ma ruwannan da ya sakarma kan ya ji
daɗinsa sosai gaskiya.
Ba ƙaramin ƙunar zuciya ta kama Shahudah ba jin Jawaad ya shareta, ta turo baki gaba
tana yaye bargon da take ciki.
Masha ALLAH na sake ambata ganin haɗaɗɗun kayan barcin da take sanye a ciki, sun
mugun mannewa da farar fatarta, tare da zama ɗam jikin surarta tamkar dan ita aka halicci
figigiyar rigar barcin da kaɗan ta gota mazaunanta, siririyace sai dai jikinta a murje yake alamar
hutu, ba kowa ne zai ga Shahuda ya yarda ta haɗa jini da HAUSA FULANI ba, dan komai nata
yafi kama da na masu jajayen kunnuwa.....
Saurin janyeta yay da ga jikinsa jin ta rungumesa ta baya yana kuma ɓata fuska, a matuƙar
harzuƙe ya juyo yana sanya jajayen idanunsa cikin fararen nata masu cikar gashi da gira baƙa
wulik a sama. Sam bazata iya jurar kallon cikin idonsa ba, dan haka ta wani yi farr da nata cikin
salo irin na manyan yara da ke taƙama da wayewa.
Hanya kawai ya nuna mata ba tare da yace uffanba.
Yanzu kam ranta yakai maƙura da haushin wulaƙancin Jawaad, dan haka ta yamutse fuska
cikin tsiwa ta taka gaban gadon ta saka silifas ɗinta masu taushi ta nufi hanyar fita.
Sai da ta kama hannun ƙofar ne ta tsinkayo Jarumar muryarsa na faɗin, “Saura idan kinje
canma ki sake kwanciya kar kiyi sallar”.
Harara ta watsa ma bayansa da ya juya mata ta fice tana ƙunƙunin da ita tasan mi take
faɗa.
Bai sake bi ta kanta ba ya kammala abinda zaiyi a gaban madubin ya nufi Wadrobe ɗinsa
ya saka boxer kawai ya fito falo. Kayan tea da ke ajiye saman D/table ya nufa, ya ɗauki kofi ya
haɗa komai kafin yaje ga disfensa ya matso ruwan zafi dai-dai buƙatarsa. A haka ya koma
bedroom ɗinsa yana juya cokali cikin kofin shayin da keta tururi. Zama yay bakin gadon yana shan shayin a hankali, ko zafinsa baya ma damuwa da shi. A
da can sam baya shan shayi sosai, ya kan sha amma ba ko yaushe ba saboda baya cikin
abinda ya damesa, amma tun bayan auren sa da Shahudah suka ƙulla abota da tea, a yanzu
baya da abincin da ya bama muhimmanci a rayuwarsa irin shayi, tun yana sha akan dole harya
fara zame masa jiki, inma bai sha ba sam baya jinsa dai-dai, a baki sunan kawai yana da
matane, amma a aikace ita da hotiho babu banbanci, dan babu wani abu na matan kirki masu
daraja da Shahudah ta iya, banda tsagwaron son jiki da son hutu babu abinda ta tara, a
ɓangaren gyaran jiki dai kam gwana ce, dan ƴar gayuce ta gani kasheni, sai dai sam babu
tarbiyya mai birgewa da akasan ƴaƴan musulmai da ita, komai nata kwaikwayone daga jinin
yahudu da nasara, salla wannan sai yayi mata jan ido take yinta, daga lokacin da yay nisan
kiwo kuwa a aikinsa baisan wace wainar take toyawa ba a ɓangaren bautar ALLAH....
A hankali ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana ajiye kofin hannunsa saman durowan
gefen gadon, magani ya ciro a ciki ya sha kafin ya haye gadon da ke manne da ƙamshin
turarensu ya kwanta yana jan bargon ya lulluɓe har kansa.
Koda Shahuda ta koma ɗakinta sam bataji gargaɗin Jawaad ba akan tayi salla, sai ma
gado da ta faɗa tana ƙunƙuni wai baza tayin ba, a haukanta da gajeren tunani tunda Jawaad ya
ɓata mata rai to itama saita ƙuntata zuciyarsa da ƙinyin sallar da yace tayi, dan haka tai
kwanciyarta barci ya sake kwasheta saboda sanyin garin na ruwa da aka maka a daren jiya.
ALLAH ya ƙyauta to, saikace kabari ɗaya za'a saki da Jawaad ɗin Shahuda? kokuma shike
bada sakamako idan anyi sallar♀️?, ALLAH ka rabamu da wayewa mara amfani⛹♀️.
★★★★★★★
Ring ɗin wayarsa ne ya farkar da shi da ga nannauyan barcin da yay nisa a ciki, ya janye
bargon da ga kansa da ƙyar tare da miƙa hannu saman dirowan gefen gadon ya ɗauki ƙaramar
wayarsa da ke vibration. Ba tare da ya duba wanene ba ya ɗaga kawai ya saka a kunne yana
sake maida idanunsa ya lumshe. Tsawon seconds arba'in yana sauraren mai maganar da ga
can, kafin ya furta “Ok sir” cikin nutsatstsiyar muryarsa da ke gauraye da barci. Ƙarƙashin filon
ya tura wayar yana sake juya kwanciyarsa hankali kwance, sai faman ɓata fuska yake na jin
takaicin katse masa barci da akayi. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya ture bargon yana
jan dogon tsaki, ƙaramin agogon dake gefen dirowan gadon ya kalla, ⏰11:29am, numfashi ya
sauke a hankali dan sam baiyi tunanin barcin nasa yayi dogon zango haka ba, tashi yay ya
sauka daga gadon gaba ɗaya.
Sosai ƙyanƙyamin bayin nan yakeyi, dan yakai kusan kwana huɗu kenan babu wanki, tun
randa Batool tazo bai sake ganin gyara ba saboda tsabagen lalacin matar gidan.
A ɗarare yay abinda zaiyi ya fito ba tare da ya sake wanka ba, baƙar jallabiyarsa mai dogon
hannu ya ɗauka ya zura kawai da silifas ya fice zuwa ƙasa.
Sai sha ɗaya saura Shahudah ta tashi a sabon barcin da ta sake komawa, sai faman ɓata
fuska take tamkar ance ta tashi dole ne, rigar barcinta ta zame tare da sakinta a tsakkiyar
ɗakin tai tsaye tsirara da ga ita sai pant wanda shi da babu duk ɗaya, hankalinta kwance ko
tunanin bayan jinsinta akwai na aljanu da ido baya ganinsu a ɗakin batai ba, a haka ta nufi
bathroom.
Tsawon lokaci ta ɗauka a ciki kafin ta fito ɗaure da wani mitsitsin tawul kalar ruwan hoda,
shima tana zuwa gaban mirror ta sakeshi ƙasa, a haka ta shafa mai kafin ta buɗe Wadrobe ta
ɗauki doguwar riga ɓaƙa ta saka, tare da naɗa ɗankwalin rigar ta ɗau abin salla ta shinfiɗa.
tsantsar mamaki da al'ajab sun rufeni ganin sai yanzune Shahudah zatai sallar asuba, sha
ɗaya da kusan ƙwata♀️.
Ina nan zaune ganin ikon ALLAH harta idar da sallar tata a cikin ƙanƙanin lokacin da bazai
gaza mintuna uku ba. Rigar ta sake cirewa ta ajiye, ta ɗauki tawul ɗinta ta sake ɗaurawa tare da
jan stool ta zauna aka fara tsara ƙwalliya ta garari.
Kai tsaye ɗakin Shahudah Jawaad ya shiga, juyowa tai ta ɗan kallesa ta ɗauke ido ita a
dole fushi takeyi da shi.
Shima sai da ya fara ƙarema ɗakin kallo kafin ya kai dubansa gareta, kallon kusan
seconds goma yay mata sannan ya cigaba da takowa cikin ɗakin, jikin bangon da mirror yake
ya jingina tare da harɗe ƙafafunsa waje guda ya tura duka hannunsa a aljihun jallabiyar.
Tsayuwar tasa sai ya zam tamkar sun fuskanci junane shi da Shahudah, hakan yasa ta
sake ƙwaɓe face ɗinta tana cigaba da zana kwalliyarta.
Tsawon mintuna biyu suna a haka, babu wanda ya cema ɗan uwansa ci kanka, sai zuwa can
Shahudah ta ɗago manyan idanunta da gashin ya sake jin maskara ya miƙe gazar-gazar fiye da
da ta kallesa, “Nikam karka cinyeni dan ALLAH bb”.
Idanunsa ya janye a kanta yana sakin guntun murmushi da ya saka kumatunsa loɓawa,
itama Shahudah sai tayi murmushin.
“Breakfast fa?” yay maganar yana sake maido kallonsa gareta.
Sosai ta sake zuba masa idanunta tana narke fuska, sai dai batace komaiba.
Hannayensa ya zare daga aljihu ya maida a ƙirjinsa ya harɗe, “Yanzu nan Hudah kina
ganin wannan rayuwar itace ta dace da matar aure ta hausa fulani? Wata bakwai kawai da
aurenmu amma matsaloli sunzo sun mana ɗaurin goro a cikin gida, wanda duk kece sanadinsu,
shin ke wai bazaki taɓa canjawa bane?!.....” ‘Ya ƙare maganar a tsawace’.
Razana tayi matuƙa, dan haka ta zabura tana jan jikinta baya tare da waro manyan
idanunta waje, “Wai ni bb ya kake so in maka ne? Kaifa nace a ɗakko kuku da wanda zaike
mana gyara amma kace baka yarda ba, ta yaya kake tunanin zan iya aikin gyaran wannan
ƙaton gidanne saboda ALLAH, kum....” Haɗiye sauran maganar tata tayi tana ƙunƙuni saboda wani ɗan iskan kallo da yake mata,
wanda ta tabbata yafara harzuƙa, idan ko ta bari ya kai ƙarshe zai iya ɓarota a kujerar ya haɗa
kanta da mirror.
“Shahudah baki kai matsayin sakani yin abinda ban niyyaba, dan bazan taɓa kawo wani
ƙaton banza gidana ba da sunan ma'aikaci, ki kama kanki kafin na raba shi da wuyanki a
gidannan wlhy, stupid girl kawai”. Ya ƙare maganar da juyawa zai fita.
Cikin ƙunƙuni Shahudah ke faɗin, “Karka kawo ɗin, kata zama a gida tamkar tirken akuyiyin
ƙauye kuwa, dan nikam ba ƴar wahala bace, kake wani cewa kamar ba matar hausa fulani ba,
ALLAH ya rabani zama irinsu waɗannan kidahuman da basusan ko yanda zama su gyara
jikinsu ba balle su san miye rayuwa, da ana canja yare ma da tuni na canja nawa anbar
dangantani da wasu hausa fulani can mtsowww.
tab, babbar magana, Shahudah anya kinada man kai kuwa? Matan hausawan ne bamusan
abinda mukeba♀️? Rigiji gabji☹️.
Sarai Jawaad yaji abinda Shahudah ta faɗa, amma sai ya fice ko waiwayota baiyiba,
bedroom ɗinsa ya koma ransa duk a jagule, ya ɗau babbar wayarsa da ke a kashe ya kunna,
wata Number ya lalubo tare da danna mata kira, bugu biyu aka ɗauka.
Sama-sama sukai gaisuwa da wadda ya ambaci sunanta da Hibba, kafin yace, “Cikin
yarannan wace a gida?”.
Bansan mi aka ce masa da ga canba, ya dai sake faɗin “turomin ita” kawai ya yanke wayar
ya ajiye.
Tsaki yaja yana jingina da fuskar gadon tare da lumshe idanunsa ya afka duniyar
tunani............✍
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_**_Typing_*
*_ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*
*_Bilyn Abdull ce_*
*_SADAUKARWA:_*
_Aunty Fareeda Gachi_
_Aunty Rahma A-Majeed_
*_Wattpad_*:- _BilynAbdull_
*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na uku_
*______________________________________*
..........Zaman duniya da kayan cikinta buƙatar kowacce, amma waɗanda duniya ke buƙata da
amfanuwa da kayan cikinta mutanene ƙalilan. A lokacin da wasu mutane ke bushasha da wani
yanki na jin daɗin cikinta wasunsu kuka suke da kwankwaɗar ɗacin cikinta.
Yayinda idanun wasu ya bushe da ga kwaranyar ruwa mai amsa sunan hawaye, a
lokacinne ijiyar wasu ke ambaliyar zubarwa da buƙatar abin gogewa koda ace ruwan hawayen
bazai dakata daga malala ba.
Zuciyoyi duk iri ɗayane a suna, amma a aiyuka kowa da irin tasa. In dai zuciya zata kasance
mabanbanta a ƙirazan mutane, to lallai dolene launin halayya da ɗabi'unsu ma ya banbanta. Sai
dai wanda ya halicci duniyar da kayan cikinta, ya fika sanin miyasa ya banbanta ma'abota
mu'amulantar ta da shawagi a cikinta harma da gudun zukatansu. Kamar yanda duk ilimin ɗan adam bai isa ƙayyade numfashin da ke fita daga huhunsa
zuwa maƙogwaro ya fita ta hanci ba, to lallai babu mai ilimin ƙa'idance ko banbance yawan
jinsin ƙabilu da mutanen dake danƙare da duniyar nan sai wanda ya halicceta. A lokacin da
fankama da tinƙahonka ke kwarzanta abincin tukunyar gidanka, da zaka leƙa ta gidan wani sai
kaga ta fita abin kallo da kayan alfarma masu armashi.
Sai dai duk wannan ba shi bane tushen zancen, ba kuma shi bane abin dubi da hange ko
burin riska, tsarin shine waiwaya can bayan bayanka ka hango waɗanda ko tukunyar ɗorawar
basu da ita balle tunanin hura wutar da zata dafa musu.
Wani tun haihuwarsa ALLAH ya azurta tushensa ko zuri'arsa da rahamar fitowa cikin
gingimemen hasken da ko baka mallaki komai ba a duniya sai shi to lallai ya gama maka komai,
domin ya baka abinda ya fi komai tsadar tsada a cikin alfarmarsa. Sai dai abin mamaki da
al'ajabi sai ka samu mafi yawan masu wannan damar sunyi wasarere da ita tare da mata riƙon
sakainar kashi suna hange da gudun kamo wasu al'adu da ke da alaƙa da kishiyar nasu.
Zancen nawa a bayyane yake, sai dai fa fahimtarsa ba kowace kwanyace hasashenta zai kai
canba, ba kuma toshewar basira ce zata kawo rashin fahimtar ba, sam ko kusa ba hakan bane,
ɗunbin abin tarawa ne kawai kema ƙwaƙwalen jama'a yawa su gaza warware wani ƙullun igiyar
a jikin gugar da takai kimanin dogon zamani ana cuɗanya da ita a rijiyar mai bakandamiyar
alfarmar ruwa buƙatar kowa. Shi wancan dama ya samu, amma rashin fahimtar hanyar da yake jefa ƙafa ta sakashi gaza
fahimtar akwai waninsa da ke da buƙatar koda kwatankwacin tasa damarce shima ya shigo a
dama dashi.
Gashi dai a cikin duniyar irinta wadda ke da damar a tafin hannu, ga kuma gangar jiki da
fitar numfashi duk ALLAH ya haliccesa da ita shima, sai dai sam ba ƙofa ɗaya ya ke shiga da
fita tsakaninsa da mai damar a cikin duniyar ba. Hakan yasa yake kallon tasa duniyar da ban a
cikin duniya, ba dan baya ci ko sha ba kamar kai, hatta barci da kake domin hutu da dariyar
farin ciki duk ALLAH shima ya azurtashi dasu, abin lurar shine kai duniyar rungumeta kayi tsam,
itama ta tallafeka tare da sake cusaka jikinta kuna kwasar ɗumin juna saboda tsantsar
buƙatarka da takeyi, Shiko waninka rakaɓe yake a jikinta tamkar hawainiyar da ke ɗauke da ciki
ta ke jiran ranar haihuwa.
Bara dai mu ajiye duk wani dogon zance mu tsunduma cikin labarin ko mai karatu zaifi
fahimtar gonar audigar da nake masa nuni da ita mai ɗauke da buɗaɗɗiyar kaɗa da
gwaiduwarta ta fashe sumfut a filin gona.
Ni dai sunana *Bilkeesu* ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko
tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.
A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun
rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan
kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki.
A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa
muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za'aci. Abin da zai matuƙar birgeka a
rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya
gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai
da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita.
Sana'ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran
kayan nau'in ɗinki